Showing 246001 words to 249000 words out of 281103 words
Chapter 83 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
rasu?”
Ya shafa kansa yana murmushin rashin gaskiya.
“Kin san ko da ta rasu ina Abuja, amman dai na kirata a waya”
“Abdallah baka da kirki sam, kai kullum aiki ƴan uwanka ma baka da lokacin ziyartarsu? Sai yaushe zaka huta ne?”
“Ai yanzu zani iya zuwa na mata gaisuwar daga nan na duba jikin nata”
“Allah ya sauwaƙe maka wannan rayuwa, wai ya maganar yarinyar nan ne?”
“Muna nan muna ta sutsa kai, yanzu haka maganar da Mai Martaba yake min kenan, yace min yayi magana da Abbah”
“Ban gane ba, ita bata son ka ne?”
“To gani dai wani ne yake min zagon ƙasa, ita kuma tana min jan aji, yanzu haka anjima kaɗan gurinta zanje, domin hankali yaƙi kwanciya tun lokacin da yaron nan na zo gidansu, last week ma da naje gidan kamar...”
Sai kuma ya fasa maganar ya miƙe tsaye.
“Muje na dubata Ummi, sai na wuce airport flight zan hau”
“Ka fara bani labari baka ƙarasa ba, zan ƙarasa”
“Zan ƙarasa miki idan na dawo”
“Ƙanenka dai ga su nan sai himmar fitar da maza suke kai kana nan”
“Nima ina kan hanya”
Dariya ta yi ta miƙe tsaye suka fita tare. Kai tsaye asibiti suka nufa, ko da suka shoga ɗakin tana kwance wata ƴar'uwarta tana jinyarta, ta rane sosai bakinta duk ya bushe, Abdool ya ji tausayinta sosai da sosai, duba da yadda take damawa kuma gata mai jiki amman yanzu ta dawo haka. Tana ganin Ummi ta fara hawaye.
“Nikan tawa ta ƙare, Nabila ta tafi ta bar ni”
“Kiyi haƙuri Hajiya Sadiya duk mai rai mamaci ne, duk haka ƴaƴanki suke mutuwa kuma ki haƙura, na san Nabila ita kaɗai ta rage miki amman Allah baya barin wani dan wani, dan Allah ki sawa zuciyarki sassauci”
Shiru bata ce komai ba, sai hawaye take ita kaɗai ta san dalilin mutuwar Nably kuma ita kaɗai ta san dalilin wannan ciwon nata.
“Sai Yaushe zasu sallame ki ne?”
Ummi ta sake tambaya. Wacce ke jinyarta ta kada baki tace
“Ba yanzu ba, wai sai sun mata aiki”
“Aiki kuma?”
.
“Eh wai wasu abubuwa ne a cikinta masu kamar ƙanƙara sun ce dole ne sai anyi aiki za a cire”
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. To Allah ya sauwaƙe, amman da waje aka je naga sun fi ƙwarewa a irin aikin nan”
“Nima haka na ce mata, amman ta ƙi”
“Allah ya bata lafiya ai da nan da can duk ɗaya a gurin Allah”
Wannan karon Abdool ne ya faɗa yana kallon agogon hannunshi. Dubu talatin da ƴar siyayya Ummi ta aje mata sannan suka taso muna mata Allah ya sauwaƙe ya bata lafiya.
A mota Ummi take ta labartawa Abdool irin rayuwar da suka yi ta ƙurciya, yadda aka riƙa ta a gidansu da kuma irin nasarorin da tada samu a rayuwarta.
“Kai Mai rai ba komai ba ne”
Abdool ya faɗa yayinda yayi parking a harabar gidansu. Cikin yanayin damuwa da jimami Ummi ta fita daga motarsa, shima ya fito yana faɗa mata yanzu zai kama hanya.
“Allah ya tsare ya kiyaye ya kuma kai ka lafiya”
“Amin Ummi”
Sai da ya shiga part ɗinsa ya fito, sannan ya shiga wata motar direbansa yayi driving ɗinsa zuwa airport.
***
An sake fitar da shi waje kamar yadda Abbah yayi alƙawari, sai dai tun daga lokacin Abbah be sake leƙa asibitin da sunan yazo ganinshi ba, wani kuma daga gidan be sake zuwa ba, duk da ƴan'uwa sunta ƙoƙarin shiga tsakani na ganin an sasantashi da Abbah, amman Abbah be saurara ba dan ya riga ya bashi baya a yanzu, kuma duk wanda ya ji dalilinsa dole yayi masa uzuri, dan kaf a ƴaƴan ƴan'uwa Abbah ya fi son Uzair da kowa. Babu wanda be yi mamakin jin abunda Uzair ya aikata ba na neman maza ƴan'uwansa, a lokacin ne wasu ke cewa ashe Namra tana da gaskiya, wasu kuma su labarta tsegumi da zargin da suka ji ana masa, daman abun duniya baya ɓoyuwa. Har kuma tsawon lokacin Yasmin bata taɓa zuwa ta duba shi ba ko da sau ɗaya. Shi kam duk ya biya rame ya lalace, sauƙi ɗaya ya samu yanzu yana iya tashi zaune,ko ya kwantar da kansa, kuma ya kam miƙa hannunsa ya ɗauki abu ko ya karɓo, sai dai bayan haka babu wani abu da yake iyayi ma kanshi.
Bayan ya gama cin abinci likita ya shigo ya duba shi, ya bashi magani sai kuma yayi masa allura, sannan ya rubuta wasu ya bawa Umma yace a siyo masa su. Sai da ya fita Umma ta rafka uban tagumi tana kallon ɗanta, tabbas be kyautawa kansa ba da ya saka kansa a wannan rayuwar, gashi yanzu kowa ƙyamarsa yake ana masa kallon kamar ba mutum ba, shi kansa a yanzu ya gane ba kowa ba ne, duk abokaninsa sun guje shi cikin ƴan watan ni sun manta da shafin rayuwarsa ga matarsa ta nuna masa tsantsar ƙiyayya, yanzu da Mahaifiyarsa bata raye haka rayuwarsa zata ƙare kenan a wulaƙance?
Turo ƙofar da akayi ne yasa duk suka ɗago suka kalli ƙofar daga shi har Umma, Yasmin ce sanye cikin suit da alamu daga gurin aikinta ta biyo asibitin. Ba Umma kaɗai ba shi kansa da yake mijinta sai da yaji tsoron zuwan nata.
“Miya kawo ki mi kika zo ki yi? Ai na ɗauka kina da zuciyar da ba zaki iya taka ƙafarki ba ma a asibitin sai idan ya mutu a akai miki gawa, wai ke nan har kin isa ki wulaƙanta mijinki akan wannan abun daya aiakata, kowa fa be wuce ƙaddaraba, mutane nawa ne suke zama da mijinsu bayan kuma sun san mijin yana aikata irin wannan abun, amman su rufa masa asiri su zauna da shi”
“Matan da suke rufawa mazansu asiri akan wannan aikin suna yi ne akan kwaɗayin kuɗin mijin, ni ko na dan dukiya na auri Uzair ba, wasu kuma suna yi saboda ƴaƴansu, ni ko ya keta haddin ɗa na, ko be faɗa miki yayi raped ɗa na ba? Idan be faɗa miki ba to yau ki sani, kuma dalilin zuwa na a nan saboda ina son na karɓi takardata ne, idan kuma be shirya sakina ba ni na shirƴa kai shi kotu”
Yasmin na maganar hawaye na zuba a idonta, hannu Umma tasa ta rufe baki tana kallon Uzair, furucin da Yasmin ta yi a yanzu yayi nauyi, sai dai ta fahimci gaskiya Yasmin ta faɗa tun da ya kasa ƙaryatata har ma ya sadda kansa ƙasa yana hawaye.
Yasmin ta kalleshi tana share hawayenta
“Ka daina yaudarar kanka da sunan wani yayi maka asiri, mugun abunda kake aikatawa ne ya kama ka, kuma Allah ya yanke maka wahala komai ya zo maka da sauƙi, da ace kana da lafiyarka wallahi da ko wace jarida sai ta buga hoto na da naka, dan sai na bawa duniya mamaki da kai mijina kuma uban ƴaƴana kotu, kuma ko yanzu ka taki sa'ah ne mahaifiyata ta hana ni, amman idan har shiga kotu kake so ka yi ƙoƙarin yin jayayya da ni akan aurena...!”
Juyawa ta yi ta fice tana kuka. Ajiyar Zuciya Umma ta sauke cikin muryar kuka ta ce
“Abun naka har ya ɓace Uzairu, wannan ba halina ba ne kuma ba halin Baban ka ba ne, ban san inda ka ɗauko wannan rayuwarba, yanzu a ce har ɗan cikin ka zaka aikatawa wannan abu? Ko a masu yi ƙoƙarin kare iyalinsu suke kada su faɗa wannan halaka balle kuma har su saka su da kansu, abun da naki ji a redio yau a gidana zai faru? Na yi tunanin ko zafi ciwo ne yasa ka faɗar haka a baya ashe dai da gaske ne, Uzairu baka kyautawa kan ka ba”
Ta rufe fuska tana kuka. Shi kan hawaye yake sai a yanzu yake ayyana zancen Allah na cewar cikin matan ku maƙiyanku, a cikin ƴaƴanku akwai maƙiyanku, ji yake kamar ma shi aka saukarwa ayar dan tsanar da Yasmin ke nuna masa ta yi yawa.
Wasa-wasa abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa magani yake amman babu sauƙi, haka ya kwashe wata shida a asibitin sannan aka sallamoshi ya dawo gida gurin Umma. Daman tun a asibiti aka siya masa keken guragu yana tura kansa a ciki duk lokacin da wani abun uzuri ya same shi ko kuma yayi sha'awar fita waje.
Ranar da Yasmin ta samu labarin ya dawo gida, ta samu Mahaifiyarta a falo akan maganar shigar da shi kotu tun da har yanzi ya kasa aiko mata da takardarta.
“Wai ke Yasmin wace irin zuciya ce da ke haka? Ke bakya ganin tausayinsa ne? Ki duba halin da yaron nan yake ciki wannan kawai be isa ya saka ki barshi da Allah ba, ai da Allah ya tashi kama shi sai ya kama shi ta wannan hanyar da babu wanda ya isa yai masa magani sai shi, ko ba komai fa Uzair ɗan'uwanki ne Yasmin ya kamata ki riƙa tausayinsa, sannan uban ƴaƴanki ne, ko ƙin ki ko kin so kin riga kin haihu da shi, nan gaba kina tunanin yaransa zasu ji daɗi idan suka samu labarin abunda kika yi ma Ubansu?”
Fashewa ta yi da kuka
“Idan na fita wani lokacin har nuna ni ake, na rikice gaba ɗaya yanzu ko gurin aiki ba komai nake ganewa ba, so nake ya sake ni ko na samu sukuni na natsu”
“Damuwace kika sawa ranki, bayan kuma be kamata ya dame ki, tun da ba ke kika ƙaddarawa kanki wannan rayuwar ba, focus on your journey ki cire komai a rankiz ina nan ina miki addu'a da sannu komai zai wuce”
Tashi tayi ta shige ɗaki tana kuka.
NAMRA POV.
Satin Hajiya Barau biyu ta Abbah ya dawo da ita saboda haƙuri da ake bata da kuma ganin idon ƴaƴanta, ita kanta yanzu ta saduda dan satan bata kyauta ba, duk abunda take tana yi ne dan kishin Anty Amarya tana ganin kamar Abbah yafi sonta da ita.
Ga kuma ƴaƴanta da suka sata gaba suka nuna mata rashin jindaɗinsu, ko ba komai dai ya ga ishara a zmfitowar da ƴarta tayi wato Zinatu, yanzu ba Namra ba ce kawai take zawarci a gidan har da ƴarta da uwar miji ta hanawa zama.
***
Anty Amarya na kallonta ta yi murmushi.
“Wannan shaddar duk tsadarta Lamido zaki bawa?”
Ta gyaɗa kai tana murmushi.
“Lallai ana jin Lamido nan, kar fa ya karɓe min faɗar ɗa”
Dariya ta yi wannan yaron tana shafa shaddar.
“Anty kina jin ɗan nan na ki”
“Ai bana da kamar sa ne Namra, kema kuma idan ba kin yi butulci ba baki da kamarsa, abubuwan da kike masa basa min daɗi, yaron nan yana son ki wallahi, kin san yafi ƙarfin wulaƙanci idan ba ke ba babu wacce ta isa ta wulaƙanta namiji kamar Abdallah”
“Ba wulaƙanci ba ne Anty, ni rayuwarsa ce bana so, ya cika zafin kishi, kuma bana jindaɗin abunda yake ma Lamido”
“Ai naji mahaifinki yana zancen sama masa aiki dan yace ya kusa barin driving ɗin ki”
“Saboda me?”
“Nima be faɗa min ba”
Ta faɗa fuskarta da Murmushi. Namra ta baro gurin da take zaune ta zauna kusa da Anty.
“Dan Allah Anty ki faɗa min”
“To aure zai miki”
“Anty Aure yanzu? Ni gaskiya ban shirya ba, halin mazan zamanin nan duk yaushe na fita daga wannan rayuwar kuma za a ce na sake wani”
“Toh sai ki tashi ki faɗawa Mahaifinki ai yana part ɗinsa”
Ta yi saurin rufe baki tana dariya, sai ta tashi ta ɗauki shaddar ta fice. Murmushi Anty Amarya ta yi tana unƙurin tashi ta nufi part ɗin Abbah.
Yau weekend ce daman babu aiki kuma babu wani taro ko wani abun da zai fitar da Abbah, dan haka yana part ɗinsa yana hutawa. Da sallama ta shiga, ya amsa mata yana kallon labaran bbc. Plate ɗin dake kusa da shi da ɗauke ta aje ƙasa ta zauna bakinta ƙumshe da murmushi.
“Yanzu na ke shirin kiranki”
“To Allah yasa samu ne”
“Samu ne kan, ɗana nake nemawa auren ƴarki idan kun aminci”
“Ai Abdool ɗana ne ba ɗan ka ba, ni ya kamata na nema masa aure”
Dariya Abbah yayi yace
“Amman miya hana ya biyo ta gefen ki? Ko dai ƴarki bata son sa ne? Bana son na sake mata wani zaɓin ne wanda ba shi ranta yake so ba, kar a sake samun matsala”
“Ba wata matsala, yanzu haka maganar da na gama da ita kenan”
“Toh Allah ya shige mana gaba, amman zan so jin ta bakin Namra”
“Ai gaka gata, waya isa ya shiga tsakanin uba da ƴa?”
Anty Amarya ta faɗa tana dariya.
*** *** ***
Kai ya girgiza mata alamar ba zai karɓa ba.
“Ba dan ki bani abu na zo gidanku ba”
“Ni ma na sani shiyasa na siya maka wannan shaddar, da wata manufa na yi ba”
“Na sani na gode?”
“Ba zaka karɓa ba kenan?”
“Gaskiya bana so”
Miƙewa ta yi tsaye ciki da jin haushin ƙin karɓar da yayi ta baro garden ɗin. Ko da ta shigo falo wayarta dake kan kujera tana ringing cikin sauri ta kai hannu ta ɗauka, Abdool ne rubuce a screen ɗin wayar. Tsayawa tayi kallon wayar sannan ta danna picking ta kara a kunne.
“Abnam gani kan hanya?”
“Ba zaka daina yi min zuwan ba zata ba ko?”
“Zan daina daga ranar da kika zama mallakina”
“Allah ya kawo ka lafiya”
“Amin Sweet Abnam thank you”
Shi kanshi baya son zuwan ba zata da yake mata, sai dai yana yin hakan ne dan ya riski Lamido gani yake kamar ya tare masa komai ƙara dai ya riƙa masa ba zata yadda zai riƙa fahimtar alaƙar dake tsakaninsu.
Kitchen ta shiga ta sarrafa masa abu mai sauƙi sannan ta haɗa masa fruit salad dan ta fahimci yana son sa sosai. Sai kuma ta shiga ta yi wanka ta saka abaya da jan mayafi. Tana jin lokacin da mota ta shigo harabar gidan kuma zuciyarta ta ayyana mata shi ne, amman saboda ƙarfin hali ta ƙi ta fita ta tarbe shi, har sai da ya buga ƙofar falon.
Turare ta ɗauka ta feshe jikinta sannan ta fito falo taje ta buɗe masa ƙofar, jinginawa yayi yana kallonta fuskarsa sa annuri, sai dai hakan be ma murmushinsa damar fitowa ba.
Yadda ƴake kallonta ta yi zaton zai ce mata tayi kyaune kamar yadda ya saba sai kawai taji ya ce.
“Ina Anty?”
“Tana ciki, ka shigo mana”
“No ba sai na shigo ba, ai baki bukatar ganina”
“Nace maka? Abdool miyasa kake irin wannan maganar ne? Sai kace wata maƙiyiyarka kace bana son ganinka”
Ya wara ido.
“Wasa nake miki fa, ai nasan ni kika yi wa wannan kwaliyar”
Sai kuma ta ji kunya.
“Zaka shigo ko part ɗin Abbah zaka je”
“Cikin wata tara kin zama wata babbar mace”
Ya salam. Ta juya ya bar masa jikin ƙofar, sai kawai yayi murmushi ya shigo. Daman gidan ba baƙonsa bane sai dai duk lokacin da zai zo Abbah ne kawai yake sanin shigowarsa garin. Kasa sakewa Namra ta yi haka take duk lokacin da ya shigo part ɗin shi kuma sai ya bi ya tsare ta da ido duk wani motsi nata yana idonsa.
Fruit salad ta fara kawo masa da ruwa sai kuma pineapple juice da ta haɗa masa. Gabanta sai faɗuwa yake kar Anty ta tararda su, tana jin kunyar Anty ta ganta da Abdool sosai.
“Gaskiya na yi sa'a, Matata ga iya abinci ga iya kwalliya ga haƙuri da kawaici”
Ƙasa ta yi da kanta tana murmushi, this is not the first time da yake yaba girkinta a duk lokacin da ta girka masa wani abu.
Kamar munafuka haka take satar kallonsa, yana mata kyau yau fiye da ko yaushe, ga wani ƙyalli da fuskarsa take.
Ƙarar da wayarta ta yi ne ya dukan su suka kalli wayar, ita sam ta ma manta da wayarta tana saman kujera dan tun da tayi waya da shi ta aje ta a gurin. Hannu ya kai ya ɗauka.
“Waye Dr Faruk?”
“Likita na ne”
Ido ya sakar mata kamar be yarda da maganarta ba, kuma yaƙi ta bata wayar sai ringing take.
“Me zai sa ya kira ki yanzu? Baki da lafiya ne?”
Kasa amsa mashi ta yi. A take yanyinsa ya canja sai kawai ya miƙe tsaye ya aje mata wayar ya fice, zuciyarsa na masa mugun zafi.
AMIRA POV.
Kullum cikin ɗaki ta wuni duk tabi ta takura kanta, akan abunda ta san har a bada ba zai taɓa zama nata ba, babu yadda Ammy bata yi akan ta riƙa fita tana shan iska amman ina, har ta gaji yanzu ta saka mata ido sai kuma addu'ah da take mata.
Cikin rashin ƙwarin jiki ta fito ta daga ɗakinta ta haɗawa kanta tea, bayan ta haɗa tea ta zauna a falo, saboda ta samu falon babu kowa a ciki sai tv dake ta aikinsa.
Ƙofar falon aka turo aka shigo, mai gadinsu ne, hannunshi riƙe da wasiƙa, sai da kai ƙasa sannan ya miƙa mata takardar.
“Gashi inji wasu mutane suka ce a baki”
“Su waye?”
“Wlh nima ban sani ba, cikin mota suke kuma sun tafi”
Hannu ta kai ta karɓa, shi kuma ya tashi ya fice, sai da ya fita sannan ta warware takardar ta fara karantawa...
ASIM POV.
Yanzu tsawon wata tara kenan ana abu ɗaya, a duk lokacin da ya gina gida da sunan Mardiya sai gidan ya ƙone, idan ya kama haya ma abu ɗaya ne, tun lokacin da aka ɗaura auren ta gagara tarewa sai dai su kwana a hotel ko kuma gidan abokai, dan ko lokacin da aka ɗaura auren hotel ya kama mata, baya jin zafi cire kuɗi ya gina mata gida ko ya zuba mata dukiya amman ta kasa mararta saboda yawan gobara da take. Ita kanta yanzu abun yana damunta sosai, musamman da ta samu labarin Asim yana neman auren ƴar masu kuɗi, tasan babu namijin da zai juri zama da ita tana gora dole ko wanene ya nemin ƙarin aure, ga mafarkin wutar da take har yanzu bata daina ba, lallai haƙoƙan mutane da yasa yana kanta, domim ba Namra ce kawai ta taɓa cuta ba, mutane da tayi ma cuta suna da yawa ga satar da tayi ta yi, ga kuma yawan banza data ɗaukarwa kanta. Shi kansa Asim sai yanzi ƴake gane yayi zaɓen tumun dare, dan duk ƙyalƙyalin da yake hangowa sai ya tarar na ɗan maciji ne, be same ta a budurwa ba, kuma daman be aureta dan Allah ba, auren sha'awa yayi mata daga lokacin da ya kai ga jikinta sai duk