Showing 207001 words to 210000 words out of 281103 words
Chapter 70 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
ciki sai wasiƙa, to me wasiƙar ta ƙumsa ne haka?
Zaunawa ta yi a kusa da kwalin ta warware wasiƙar, gabanta sai faɗuwa yake ta soma karantawa.
_Zuwa ga Azzalumin mutun, macuci mayaudari, nasan kana nan raye kamar ƴadda nima na ke raye, ko kuma na ce ka so ka halaka ni Allah be baka dama ba, ka yaudare ni Uzair kace Namra zamu ma Asiri ashe ka haɗa kai da ita ne ni kuka yi ma wannan asirin na bar gida, ban taɓa gane haka ba, sai a yanzu da nake da buƙatar da dawo na kasa, Wallahi Wallahi kaje ka karya wannan asirin ko kuma na sa a kashe ka, dan kasan na san ka, kuma na san inda kake, ni ko baka san inda na ke ba a yanzu, kuma ina tabbacin baka san ko wacece ni ba_
Sai number wayarta daga ƙarshe. Abunda ya tsayawa Yasmin a rai, wacece wannan yarinyar? Sannan mi suka ƙulla da Namra? Mi mijinta ya aikata ne?
Ta miƙe tsaye cike da rashin kuzari, abubuwa biyu sun tsaya mata a lokaci ɗaya kuma akan mutun ɗaya. Wani tunanin ne ya zo mata, da sauri ta ɗauke kwalin ta fita da shi ta saka cikin shara, sai ta dawo ɗakin ta ɗauki wasiƙar ta mayar da ita a yadda take, sai ta je cikin littatafanta na aiki ta samu wata silver paper, ta yi wrapping ta naɗe wasiƙar ciki da kyau ta saka salatif, ta kai masa ɗakinsa ta aje masa.
Tana shigowa ɗakinta jiri ya kwasheta, ta faɗi dafe da kai.
ANTY AMARYA POV.
Cikin ƙarfin hali ta unƙura ta nufi part ɗin Abbah, dan yau bata jin daɗin jikinta sosai, wata ƙila fever ɗin ne zai sake dawo mata. Yadda ta tararda Hajiya Barau da Abbah a falon ya ɗan tashi hankalinta, dan a zatonta ya aika kiranta ne dan su tattauna maganar auren da ake na su Hindatu da Maryam. Zaunawa tayi tana kallon yanayin Hajiya Barau da ta riƙe baki tana kallon Abbah, sam bata lura da takardar dake hannun Abbah ba sai da ya mika mata takardar.
“Wai wasiƙa ce daga Faɗar Mai Martaba sarkin Katsina, wai ana bukatar gani na gobe”
“Subhanallahi miya faru?”
Anty Amarya ta tambaya zuciyarta na rawa fat fat fat.
“Wallahi ban sani ba, ni abun ya ban mamaki mi na aikata da Sarki Katsina zai aiko kirana? Ina ma na san shi?”
Hajiya Barau ta mere baki, har da wani ƙis take.
“Allah yasa ba Namra ta yi maka janye janye ba”
Kallo ɗaya Anty Amarya ta yi mata ta ɗauke kai, maganar na sukarka, ta miƙe tsaye ta bar musu falo.
“Zan sa ana ma min jirgin da zai je Katsina gobe da wuri zan sauka dan jin ko minene”
“To Allah yasa mu ji alheri, Amman da ka kira Abdulraman (Baban ɗansa) kun je tare, kar ka je kai kaɗai”
Ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman ɗaya, Yana sosa gemunsa da hannunsa.
“A'a da Larai zan je (Anty Amarya)”
Uffan Hajiya Barau bata ce ba, dan maganar bata mata daɗi ba, sai kawai ta miƙe tsaye ta fice daga falon.
___________________________________________
There are no words to explain how sorry I am. Nasan duk abunda zan faɗa muku ba zaku yarda ba, wallahi i'm kind of busy those days, ku yi Hakuri dan Allah ku gafarta min Love you all Fisabilliah 🌹
I dedicate this chapter to Hajiya Ramatu, Mrs tijjani, My Asmee, Ahmad Ismael. I really did not know how will to write in words! But your gesture is such 😘 Thank you very much Allah ya ƙara arziki, ya bar zumunci.♥️
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *76*
“Me kike a nan?”
Ya tambaya yana haɗe fuska. Bayanta ta nuna ba tare data juya ba, sai dai bata san abunda zata faɗa masa ba. Ya nunata da phone ɗinsa.
“ I know kin karanta wasiƙar nan Yasmin”
Still wata kalma bata fito daga bakinta, wani kallo take masa kamar mai nazari. Raɓawa yayi gefenta zai wuce sai kuma tsaya yana kallonta ido cikin ido.
“Ba sai mun yi playing wannan game ɗin, nasan ke lauyer ce”
Da kallon mamaki ta bishi, ta kasa gasgata abunda kunnuwanta da idanunta suka ji mata. Me yake nufi da Namra bata zame masa matsala ba ita ba zata zame masa ba? Wacece ita? Da waya yake waya?
Da sauri ta rufa masa, sai ta same shi sitting room ya haɗa kansa da guiwa ya dafe. Tsaye tayi masa aka.
“Me waɗannan abubuwan suke nufi Uzair? Wacece wannan ? Mi kuka aikata kai da Namra? Da wa kake waya?”
Ɗagowa yayi ya kalleta, idonsa sun kaɗe alamar damuwa da ɓacin rai na tare da shi lokaci ɗaya.
“Miyasa kike son saka kanki ga abunda idan kika ji zai iya zame miki matsala? Miya kike son saka kanki ga abunda be kamata ya dame ki ba?”
Ya tambaya muryar ƙasa ƙasa kar ba komai. Zama tayi kusa da shi tana masa kallon mamaki.
“Ni matarka ce Uzair, damuwarka damuwata ce, Namra kuma ƴar'uwata ce, be kamata ka ɓoye min komai ba, please tell me maybe i can help”
ya shafa fuskarsa yana cikama bakinsa iska.
“Is about some business da zamu yi da yayanta, shine take min sheri, shine nace Namra bata zame min matsala ba ita zata zame min yarinyar da ta yi min ƙazafin Luwaɗi”
Wani ɗan murmushi tayi mai cike da rainin hankali, shi kansa ya fuskanci hakan.
“To be frank i read the message, Uzair you can't hide the truth jus...”
Yayi saurin riƙa hannayenta jikinsa a mace.
“Yasmin trust me please, kin san ina son ki”
“Ba maganar so ko ƙi muke a nan ba”
“Just promise me ba zaki bar ni ba”
Hawaye sun zubo mata.
“Idan har zargina ya tabbata a kan ka dole ne zan rabu da kai, ba zan iya zama da mutuemn daya zaɓi saɓon Allah sama da tsoronsa ba, mutumen daya zaɓi zubar da mutuncin iyalansa, zan iya yafe son da nake maka Uzair”
Ya girgiza mata yana ƙara damƙe hannunta cikin nasa.
“No Wallahi sherin sheɗan ne Yasmin, ba da son raina na aikata ba, kuma duk zugar su Najeeb ce, kuma nayi ne dan na kare kai na daga cin mutuncin da Namra ta yi min”
Maganarsa ta sha banban da tunaninta, ita gun data dosa daban shi kuma maganar da yake mata daban.
“Me ka aikata Uzair?”
Ya saki hannayenta.
“Ina ruwanki da abunda na aikata ne Yasmin?”
Ya faɗa a tsawace, sai kuma ya dafe kansa ya miƙe tsaye ya nufi windo.
“Ki tsaya a matsayin ki na matata Yasmin, zai fi miki”
Ta miƙe.tsaye itama cikin ɓacin rai.
“Yes zai fi min idan na rabu da Azzalumin mutun irinka, tirr da halin ka Uzair, ina kotu ina cases ashe akwai babban Case a gidana, nayi nadamar Auren ka a yau nayi nadamar daka kasance a cikin zuri'ar mu, nayi nadamar da ka zama uban ƴaƴana, ashe gaskiya Namra take faɗa, amman ka murje ido ka ƙaryatata...”
Ya juyo a fusace yana nuna saman kamta da ɗan tsayansa.
“Ke je ki faɗawa duniya nine na sace Namra, ni na haɗa kai da amiyarta aka mata asiri ya koma kan ƙawarta, amman karki manta ɗan'uwanki kika tonawa Asiri, kuma mahaifinta zai karɓe komai nasa daga hannuna, but i'm still your husband Yasmin the love of your life kuma uban ƴaƴanki biyu, asirina asirinki ne, kuma tona min asiri kamar tonawa kanki ne da ƴaƴanki”
“Ka buɗe shafin da ban san da shi ba Uzair, ashe kai ka sace ta? Sannan ka haɗa kai da amiyarta ka mata asiri? Wane irin zuciyane da kai Uzair? Wata ƙila ma ita ka aikata mata irin abunda ka aikatawa ɗan ka, you raped your very own son Uzair Allah yayi tirr da halinka”
Dariya ya soma yi ya doso inda take.
“Allah ya faɗa acikin matan ku akwai maƙiyanku, sai yanzu na gane kan ayar nan, amman ke babbar maƙiyiya tace Yasmin, ki rasa abunda zaki zarge ni da shi sai wannan? Kina da wata hujja ne? Ke daina ganin ke lawyer ce zan iya maka ki kotu, akan wannan mummunar kalma da kika jefe ni da ita, ai ko da gaske na aikata masa be kamata ki fito ki jefe ni da wannan maganar ba, idan ma na masa ina ruwanki ɗan ki ne?”
“Shiyasa bana burge ka ko? Baka da time ɗina, saboda ba mata bane a gabanka maza ne, mu kwana gado ɗaya mu tashi amman baka yarda ka bani haƙƙi na ba, da na maka magana, ka ce baka da lafiya, ko na cika desire, ashe kasan abunda kake aikatawa, kasan irin hukuncin da Allah ya tanadarwa masu irin wannan aikin kuwa? Cewa aka ƴi idan an kama su a jefosu daga saman bene su faɗo ƙasa, ko kuma a samu dutse a buga musu a kai, miye bana da shi ne Uzair? Wace hasara ce ta cin maka na neman maza ƴan'uwanka? Uzair me kake ji idan ka neme su?”
Hannayenta ya kama, ya faɗi ƙasan gwuiwoyinsa.
“Ki rufa min asiri Yasmin, ki taimaki rayuwata, kar kowa taji maganar nan, na miki alƙawarin ba zan ƙara ba, kuma zam je nasa a kare asirin dake kan Amira i promise, Yasmin ki dubi girman Allah ki yafe min, sherin zuciya ne, da zama da miyagun abokai”
Kuka da take ne ya ƙaru.
“Ka cutar da yarinyar nan Uzair, kasa mahaifinta da duniya suka zargi ta gudu taje gurin saurayinta ne, sanadinka kowa a familyn mu ya tsane ta, duk halin da ta shiga kai ne Uzair”
“Ki yi ta tunanin wasu har ki manta da ni, ki rufa asirin wasu ni ki tona nawa, idonki yayi ta rufewa akaina har maƙota suji abunda na aikata”
“Ba maƙota kaɗai zasu ji ba, duniya ce zata ji, sai duniya tasan wanene kai, sai kowa yasan abunda ka aikata”
Ya miƙe tsaye
“Wallahi duk kika bari wannan maganar ta fita, sai kin yi nadamar zuwanki duniya, sai kin gwammace kiɗa da karatu, kuma komai na zama ni mijin Yasmin ne, ai komai yana da buƙatar uzuri da bincike, kije duk abunda zaki aikata ki aikata ɗan shege ka fasa, indai kotu kike taƙama da ita sai na nuna miki baki san komai ba akan aikin ki”
“Haka ka ce?”
“Wanda duk yaƙi ji aiba zai ƙi gani ba”
“Baka bani mamaki ba, daman masu aikata irin aikinka ai basa da kunya, kuma basa tsoron Ubangijinsu balle jama'a tirr da halinka, wallahi sai na ƙwatowa Namra haƙƙinta, sai ka raina kan ka Uzair”
“Ni mijinki kike faɗawa haka?”
“Kai mijina ne zaka taka min bayan ɗa?”
“Sai ki fito fili ki faɗa mana, kice ɗana zaki min ƙazafi, ba wai ki raɓa da Namra ba, aikin banza kaiwai... Mtssssswww”
Yaja wani dogon tsaki ya wuce daga falon kamar walƙiya. Ita kamar jiran take ya fita, ta shiga ɗakinta ta zari mayafi ta, ta goyawa Mai mata reno little Namra, ta kama hannun Adnan suka fice.
NAMRA POV.
Da hawayw ta shiga cikin gidan, sai dai kasancewar dare ne, kuma babu wutar nefa a gidan shi ya hana su gane akwai hawaye a fuskar Namra, da wannan tayi nasarar shigewa ɗaki ta kife saman kafitar tana kukanta a hankalin ta yadda ita kaɗai zata iya jin sautin kukanta.
Da sallama Anty Amarya ta shiga cikin gidan, sai duk suka haɗa baki gurin amsa mata, gaisuwa ce ta biyo baya, sannan ta ɗora da tambayar Namra, duk kallon rashin sani suka mata, ko wanne abunda zuciyarsa ta bashi, wata ce ta tare da Yarima, wata ƙila taƙi ta saurareshi ne shiyasa ya turo wata.
“Eh tana nan ciki lafiya?”
Lamido ya tambaya. Cikon murya mai kamar ta kuka Anty Amarya ta ce
“Dan Allah ku yin magana da ita...”
Kamar an jefo Namra haka ta fito daga cikin ɗakin, tana ganin Anty Amarya ta rumtse idonta ta damƙe hannayenta gam, tana maimaita.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Saboda ta kasa yarda da abunda kunnuwanta da idonta suke nuna mata, ji take kamar mafarki take kuma ba mafarkin ba ne. Ta buɗe ido ta ƙarasa gaɓan Anty Amarya ta kama hannayenta, ta taɓa ta murja ta sake kallon fuskarta, sai kawai ta rumgume ta fashe da kuka.
Anty Amarya ma kuka take, ita da Namra aka rasa mai rarrashin wani, su kam su Neina sai kallon ikon Allah suke. Kuka sosai Anty Amarya da Namra ke yi kamar an muutuwa, sannan Namra ta zube ƙasan kafafunta ya kama kafafun Anty Amarya.
“Ki yafe min Anty, na tuba dan Allah ki yafe min, ki roƙi Abbah ya yafe min, haƙƙinku ma ta bina Anty, dan Allah ki roƙa min Abbah ya yafe min”
Ta ƙamƙame ƙafafun Anty amarya, tana wani irin kuka mai yaɓa zuciya. Yanzu kam Neina da Lamido sun fahimcin wacece Anty amarya. Anty ƙasa magana ta yi saboda majina data cika mata hanci. Can Namra ta ɗago kai ta kama hannayen Anty Kaamar wace ta ruɗe.
“Anty da gaske kece?”
Ta kalli Lamido da Uwani.
“Kuna ganin abinda nake gani, ko dai mafarki nake?”
Lamido ya ɗaga mai cike da ɗaurewar kai, Uwani kuma tace
“Muna gani Namra”
Anty Amarya tasa hannu biyu ta riƙo Namra ta tashe ta tsaye.
“Nice Namra, ba mafarki kike ba, Mahaifinki ma yana nan waje, tare muka zo da shi lokacin komawarki gida yayi”
“Anty waya faɗa muku nan? Na kasa yarda ba mafarki nake ba, kaina nake jin yana juyawa”
Ta miƙe tsaye ta nufi ƙofae waje. A gurin ta samu Abbah tsaye ya maida hannayensa baya kansa ƙasa kamar mai nazari.
“Abbah....”
Ta furta tana kallonsa da kyau da kyau. Ɗan murmurshi yayi kaɗan irin murmushin da be kai zuci ba. Sai kawai Namra ta faɗa jikinsa ta rumgumeshi numfashinta na rawa, kuka yazo mata a lokaci ɗaya.
Sai da tayi kukanta mai isarta taji ta samu natsuwa sannan ta sauko gurin ƙafafunsa ta riƙe.
“Dan Allah Abbah ka yafe min, ban kyauta maka ba, kwata-kwata abunda na aikata be dace ba, Abbah Asim ya sake ni, tsoron abunda zaka min ya hanani komawa gida, dan Allah ka yafe min Abbah”
Kanta ya shafa fuskarsa ba yabo ɓa fallasa.
“Idan ban yafe miki ba, ba zan zo nan ba Namra, nasan yanzu kin riga da kin gane kuskurenki, tashi tsaye kar ki tara mana mutane”
Fitar Namra yaba Anty Amarya gaisawa da ƴan gidan, wato su Neina har take faɗa musu ai tare da Abbah ta suke yana waje.
“Haba kije kice ya shigo mana ya zai tsaya daga waje”
Sannan Anty Amarya ta nufi ƙofa da jimmar faɗa masa sunce ya shigo. Sam sam sam Lamido be jidaɗin ganin iyayen Namra ba, duk wani farinciki da son da yake ta shirya da iyayenta sai yaji baya sonsa, musmaman yadda zuciyarsa take raya masa Yarima ne silar hakan,ko ba komai yasan Namra zata fi son Abdool sama da shi, shi ko yana da ƙudurora da yawa akanta, dan ya ɗaukarwa kansa alƙawarin sai ya nuna mata banbancin dake tsakaninsa da Asim na kyauwon hali, duk da suna ɗaya zasu amsa a fagen talauci,so yake Namra tasan ba duka talaka ne mai irin zuciyar Asim ba.
Wani abu yaji yazo ya tsaya masa a zuciya, tun ba aje ko ina ba, yana jin ya fara missig Namra, zata nisanta da shi yanzu, kuma ba lallai bane ya sake ganinta.
Sallama Abbah ce ta katse masa hanzari, ya dawo daga duniyar tunanin da yake ya miƙa idonsa i zuwa inda ƙofar gidan take yana kallon Namra dake riƙe da hannun Anty Amarya. Saman shimfiɗar da Neina tayi musu suka zauna, ita kuma ta zauna a saman ɗaƴar tana gaisawa da Abbah.
“Amman na jidaɗin da kuka zo gurin ƴarku, Namra bata da tunani sai naku, kullum cikin kuka take, nasan babu iyaye na gari da zasu ƙyale ƴarsu, matuƙar ƴar nan ta sunna aka haife ta, su iyaye dole sai kana kai xuciya nesa, sau da yawa ɗa zai aikata abu kai ka daurewa zuciyarka ka ƙyale gudun kar ɗan nan ya faɗawa halaka, kuma idan mutum ya gane kuskurensa babu a abunda ya cancanta da shi sai yafiya da kuma nuna masa illar abun nan da ya aikata, ƴaƴa da mata kamar kiwo ne, ko wanne za a tambaya ubngidansa akan irin kiwon da ya bawa iyalansa, yadda mu muke da haƙƙi akan ƴaƴanmu haka muma ƴaranmu suke da haƙƙi a kan mu. Wallahi kun faranta min zuciya dana ganku da ƙafafunku kun tako cikin gidan nan ku tafi da ƴarku, a halin da Namra take da ace bata haɗu da mu ba da zata iya faɗawa ko wane irin hali, saboda bata san kowa a Kaduna ba, kun ga ko a nan rayuwarta tana cikin haɗari”
“Gangar jikina ne kawai a gida, amman kullum zuciyata tunanin Namra take, ban san aurenta ya mutu ba, da wallahi ba zata zauna ko ina ba sai a gida, kowa kuwa mahaifinta zai zaɓi rabuwa da ni ne, kullum a tunani tana can yana azabbatar da ita, nasan Halin Namra idan abun duniya zai cita ya cinye ba zata faɗawa kowa ba, itace babba amman ita marar wayo da tunani a cikinsu, da wannan tunanin naƙe bachi naƙe tashi wannan tunanin ya kan hanani sukuni wani lokacin, shiyasa ƴan'uwanta suke ganin kamar itace silar ciwon nan nawa, kullum cewa suke, Namra ce ta kwantar da ni, duk da nasan gaskiya suke faɗa amman a haka zan musa musu, kudun kar suce nafi sonta sama da su, ni ko kullum tunanin kar na mutu na barta a cikin wannan halin”
Namra ta kama hannayen Anty Amarya ta riƙe.
“Ba zan sake aikata abu makamancin wannan ba Anty, ni ba zan sake aure ba balle har na tsallake wani sharaɗi na ku, hawayenki ba zai sake zuba a kan Namra ba”
Uffan Abbah be ce ba, idonsa na kan pure water da Maryam ta aje musu mai tsanyi, wadda ta siyo shago.
Maganar duk da suke tana cikin kunnensa, sai dai be jin zai iya furta wata kalma data ɗanganci labarin da suke. Ba laifi sun ɗan yi fira sosai da Neina, kamar waɗanda daman can san juna, sai duk firar da ake Namra na cikin jikin Anty hawaye sun ƙi su tsaya mata. Abbah ya kalli agogonsa tare da miƙewa tsaye yana faɗin.
“Ya kamata mu tafi yanzu, da safe Namra zata zo ta muku sallama kamin mu kama hanya”
Yana faɗar hakan ya saka takalminsa ya nufi ƙofar fita, Lamido da kallo ya bishi yana aunasa a matsayin lallai zai iya aikatawa