Showing 3001 words to 6000 words out of 281103 words

Chapter 2 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt

28 Dec 2024

61292

yi ya hanata aikin tun da mahaifinta ya tsaya kai da fata akan lallai sai ƴarsa ta yi aikin banki.
Yana kwance a gurin har ta yi wanka ta shirya yana kallonta, sai daf da zata fita sannan ta zo daidai kunnensa ta yi masa kiss


“Take care of yourself okay, idan Rafiq ya tashi ka shirya shi idan zaka je aiki ka aje shi kurin Hajiya, zan ɗauko shi idan na dawo, idan kuma su Ulfah sun dawo abincin su na nan a flask, love you my hubby my Doctor”


Daga haka ta fice tana murmushi, da kallon ya bita har ta fice, sannan ya ɗauke kansa yaja bargo ya lulluɓe ya soma sana'arsa.




_______________________________


Hello my beautiful people, ina fatar kuna lafiya kuma ina fatar wannan tafiyar zata muku daɗi zaku kuma bani haɗin kai kamar ko yaushe.
Wannan tafiyar ba irin wacan bace ce, ba zan baku kunya ba In'shallahu, iyana gayyartar ku a sabon shafina wanda zan riƙa zuɓa duka littafaina a can, zan riga yin update a can sama da ko'ina zaku iya samun shafuka na akan kari Just click the for your updated.

www.khadeejacandy.com.ng


Zan cigaba idan na ji ra'ayoyinku 08036126660 na gode ☺


Best regards 💖
Khadeeja Candy🌺
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa03.html




🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*


Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


*PAGE - 2*


NAMRA POV.


Yadda Namra ta ga rana haka ta ga dare, dan kwana ta yi kuka da tunanin Asim, da safe ma bata fito ba sai da ta yi shirin fita, sannan ta leƙa ɗakin Anty Amarya dan gaishe ta, daga bakin ƙofa ta tsaya tana miƙa mata gaisuwar tana ɗan kare fuskarta.


“Anty Ina kwana?”


Yanayin muryarta kaɗai ya isa ya karantar Anty Amarya halin da ƴarta take ciki, daman ta san za'a rina, ko babu dalili Namra ta kan yi kuka balle yanzu da kuka ya zame mata jiki.


“Ba zan hana ki kuka ba Namra, dan kina da dalilin yinsa, amman nasan kin sauke Alƙur'ane kuma kin haddace hizo arba'in daga cikin Alƙur'ane, ashe ko ya kamata a'ce idan kin shiga damuwa ki riƙa faɗawa Allah buƙatarki kina kai kukan ki a gareshi”


Daga inda take tsaye ta amsa da


“Na gode sosai Anty In'shallahu zan yi, zan je gidan su Anty Yasmin”


“Allah ya kiyaye hanya, amman ki tabbatar kin ci abinci ka min ki je”


“Toh”


Bayan ta amsa da to ne ta juya ta fice, dinning ta nufa ta haɗa tea kaɗan ta sha, dan bata jin cin komai, ta daɗe a gurin zaune sannan ta ɗauki handbag ɗinta ta rataya ta fice daga palour, direct ta nufi gurin da Motar ta take.


Bayan ta yi addu'o'in data saba, sannan ta yi ma Motar key ta yi horn Mai gadi ya buɗe mata ta fice.
Tuƙi take kamar marar lakka, gashi zuciya ba ƙwari, sai tunane-tunane take.
Hannu ta ga ana mata gefen hanya alamar ta tsaya, tana ganin Asim ta yi saurin taka burƙi ta yi ribas ta dawo dai-dai inda ya ke ta faka, buɗe Motar tayi ta fito jiki na rawa ta ga masoyinta.


Matsowa ya yi kusa da ita yana murmushi


“Namra”


“Asim”


Haɗa baki suka yi gurin kiran sunan, sai ko wannensu ya yi shiru yana kallon ɗan'uwansa.
Da sauri Namra ta kawarda fuskarta saboda hawayen da suka cika mata ido. Hankali Asim ya tashi sosai ganin hawaye a idon Sahibarsa.


“Jiya na kira ki ya fi a ƙirga amman baki ɗaga ba, yanzu kuma ga hawaye a idonki, hakan ya tabbatar min da akwai abunda yake damunki”


Ta share hawayen da suka zubo mata.


“Babu komai, ba abunda ya ke damuna”


“Kina ɓoye min wani abu Namra, kina son tunani ya yi min yawa ko, ina tunanin halin da muke ciki, ga halin talaucin da nake ciki ga rashin aikin yi da ke damuna, Namra da wanne zan ji?”


“Faɗa maka bashi da amfani Asim, zai ƙara maka damuwa ne kawai”


“Saboda ba zan iya miki maganinsa ba ko Namra?”


“Ba haka bane, Asim zan baka wasu kuɗaɗe da zaka ja jari da su...”


Hannu ya ɗaga mata


“Tun yaushe nake faɗa miki ba dukiyar ki nake so ba Namra, ke nake so ba abunda yake cikin gidan ku, ko abunda kika mallaka, kawai ina son ki yi min alƙawari duk rintsi duk wuya ba zaki rabu da ni ba, ki min alƙawarin zaki aure ni Namra shi kawai nake so”


Kai ta girgiza masa tana wasu irin zafafan hawayen


“Ba zan iya ba Asim, ka gafarce ni ba zan iya ba...”


Dammm! Ya ji kamar an jefa masa dutse a zuciya, a take idonsa suka rine suka cika da ƙwallah, sai ya yi saurin sadda kansa ƙasa yana zauke ajiyar zuciya.


“Ashe gaskiya Umma take faɗa min, ashe yaudara ta kike ba zaki aure ni ba, amman kin ban mamaki Namra, ban tsammaci haka daga gareki ba”


Ta yi saurin kama hannunsa tana kuka


“Ba laifi na bane Asim, iyaye ne...”


Ya katsa mata tsawa


“Iyaye? Ni bana da iyayen ne Namra? Mahaifiyata bata son tarayyata da ke amman na tsaya kai da fata akan sai na aure ki, sai ke? kin fi ni sanin darajar iyayen ne ko me?”


Kasa cewa komai tayi, daman ta san ba zai fahimce ta ba, ba zai mata uzuri ba, zai zargera da da cin amana, ita kam ta san bata kyauta masa ba, sai dai babu yadda zata yi.
Hannunta ya ture, ya share hawayen da suka zubo masa ya juya a fuce ya kama hanya.


“Asim!Asim!! Asim!!!”


Haka ta bishi da kira tana kuka, amman ko waigowa bai yi ba balle ya amsa mata. Zubewa ta yi a gurin tana kuka, kukan tausayawa kanta da zuciyarta, dan ita ma kanta ta san tana son Asim, zata yaudari zuciyarta ne kawai idan har ta ce zata iya rayuwa da wani namijin da ba Asim ba.
Ta kusan minti goma shabiyar a gurin tana kuka, sannan ta buɗe Motarta ta shiga. Hanyar da zata sadata da gidansu ƙawarta Amira ta ɗauka tana wani irin gudu na fitar hankali.


Cikin ƴan mintuna ta isa gidansu Amira, daga wajen gidan ta faka motar ta dan ba zata iya jira mai gadi ya buɗe mata ba, sai ta fito ta taka da ƙafa ta shiga cikin gidan still tana kuka.
Mahaifiyar Amira ta yi mamakin ganin ta haka, sai tambayarta take lafiya, ita dai bata yarda ta faɗa mata komai ba, ta wuce ɗakin Amira kasancewar gidan ba baƙonta bane.


“Ke lafiya miya same ki?”


Amira ta tambaya cike da tashin hankali tana girgiza Namra. Bata ɓoye mata komai ba, tun daga yadda suka yi da Abbah, har abunda ya faru tsakaninta da Asim a yau.
Wani dogon tsaki Amira taja ta ɗauke hannunta daga jikinta


“Ke dan Allah duk kin tayar min da hankali, ni na ɗauka ma wani abun ne”


Kallon rashin fahimta Namra ta yi mata da idanunta da suka rine saboda kuka.


“Ban gane ba, Amira ko baki fahimci abunda na faɗa miki bane?”


“Na fahimta sarai, ai da hausa kike magana, naga dai babu wani abun tada hankali a ciki, tunda kina da mafita”


Namra ta ƙara kallonta


“Wace irin mafita? Ai nima mafitar nake nema”


“Kawai ki bishi ku gudu kuje can wani guri a ɗaura muku aure, daga baya iyayenki zasu yafe min idan suka fahimci irin son da ke tsakanin ku”


“Wannan ba mafita bace Amira, ni ba zan iya wannan ba, duk son da nakewa Asim bai kai wanda nake yi ma iyayena ba, ko wanne muhallinsa daban”


Amira ta taɓe baki


“Ashe ko ba son ƙwarai kike masa ba, tun da har ba zaki iya sadaukar da kan ki a gare shi ba”


Shiru Namra ta yi kamar mai tunani, sai kawai ta share hawayenta ta ɗauki jakarta ta rataya tana faɗin


“Bari na wuce akwai inda zanje, sai mun yi waya”


“Toh, Allah ya kiyaye hanya”


Lokuta da dama haka Amira take nata yaɓen maganar duk data zo bakinta, ta kan bata shawara tsaɓanin tunaninta, sai dai babu wanda zata faɗawa damuwarta kamar ita da Anty Yasmin.
Da wani mugun kallo Amira ta bita tana harararta, can kuma ta taɓe baki.


“Wahalalliya, ashe ƙaryar so kike tun da ba zaki iya barin iyayenki ba”


Wayarta ta jawo ta soma danne-danne, kamin ta tashi ta nufi ɗakin mahaifiyarta dan labarta mata abunda ya faru.




Har Namra ta fito daga gidan nazarin kalaman Amira take, sam bata ganin dacewa akanta guje iyayenta, saboda saurayin da zai iya barinta ya ɗauki wata, taya zata iya gudu mutanen da suka shekara ashirin da biyu suna bata gudummawa, akan saurayin da haɗuwarsu bata wuce shekara uku ba, idan har ta yi hakan ta yi babban butulci wanda ta cancanci ko wane irin sakamako. Sai dai wani ɓangare na zuciyarta, yana karantar da ita akan abunda Amira ta faɗa mata shine mafita, dan idan ba haka ba mahaifinta ba zai taɓa bari ta auri Asim ba.


Har ta isa gidan Barrister Yasmin wannan tunanin take, tana hangowa kanta illa da kuma alfanun da ke tare da ita idan har ta zaɓi guduwa ta bar iyayenta.
Ta daɗe a cikin motar tana kiran wayar Asim, amman yaƙi picking at the end ma sai ya kashe wayar gaba ɗaya, cikin rashin kuzari ta buɗe motar ta fito tana kallon balcony ɗin ƙofar Yasmin, sai a lokacin ta lura da Motoci uku da aka faka a gurin.


‘Waɗannan ba Motocin Ya Uzair bane, kar dai ace baƙin har sun iso, ko da yake abuja ba nesa bace idan sun shigo jirgi’


Shine abunda take rayawa a zuciyarta tana ƙoƙarin duba agogon hannunta, 11:23am ya bata hakan yasa ta saki jiki ta nufi ƙofar, tana isa ta kai hannu ta murɗa ƙofar. Abunda ta yi arba da shi yasa ta mutuwar tsaye, zaro ido ta yi ta rufe bakinta da sauri taja baya.


Cikin sauri Uzair ya ture Mutumen da ke samansa ya tashi ya nufi inda take, har ya iso kusa da ita jikinta rawa yake, gashi be da riga daga shi sai gudun wando. Shima hankalinsa ya tashi sosai bai tsammaci a buɗe ya bar ƙofar ba, mamakin kansa yake ma yadda bai ji buɗe gate ɗin gidan ba da fakawar Motar ta.


Da hannu ta nuna shi, sai kuma ta kasa magana. Cikin zafin hannu ya kai hannu ya cafko hannunta ya jefa ta cikin parlor.
Baya-baya tayi tana neman mafita sai kawai ta shige kitchen da samawa kanta makami, tana shiga ta nufi inda wuƙa take ta kai hannu ta ɗauka. Shi kuma ya kunno kai cikin Kitchen ɗin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.


“Ba zan miki komai ba Namra, matukar kika rufa min asiri, wallahi kuskure ne ba a son raina bane cilas ta ni suka yi”


Nuna shi ta yi da wuƙar da ke hannunta tana girgiza kai


“Ba zan rufa maka asiri ba Ya Uzair, tun da ba rufin asirin kake so ba, tun ba yau ba na taɓa ganin wani video a wayarka, Namiji na kissing ɗin Namiji ɗan'uwansa sai kace min sabon Memori ne ka siye baka san da video ba, yanzu kuma na kama ka da ido na.


Kai wane irin Namiji ne dan Allah? Matarka ta yarda da kai ta baka amana amman kana cutar, cutar ma bata tsaya akan ka har sai ka neme ni! Kuma miye abun son ga Namiji ɗan'uwanka? Tirrr da kai Ya Uzair, na yi baƙinciki da ka kasance mijin Anty Yasmi, sam bata cancanci zama matarka ba”


Murmushi ya yi ya jawo ƙofar Kitchen ɗin ya rufe.


“Na nemeki ne saboda naga abunda nake so a jikinki, lokacin da nace na aureki ai cewa kikayi kina da wanda kike so, daman nima ban shirya zama da mata biyu ba, shiyasa na nemi yin sex da ke.


Amman yanzu bari kiji na faɗa miki, duk kika kuskura kika bari maganar nan ta fita, kika faɗawa duniya cewar ni ɗan homo ne sai na tarwatsa rayuwarki, ki rubuta ki aje”


Ya faɗa mata haka fuska a ɗauri babu alamar wasa a lamarinsa, sannan ya buɗe ƙofar kitchen ɗin


“Zo ki fice, amman ki rubuta ki aje duk kika kuskura fitar da wannan maganar sai na salwanta rayuwarki”


Daga haka ya fita ya bar mata kitchen ɗin.
Ita kam bata yarda ta fito ta nan ba, sai ta buɗe ƙofar baya ta kitchen ɗin ta fita gabanta na mugun faɗuwa, har ta shiga Motarta jikinta rawa yake, zuciyarta na raya mata karta ɓoyewa ƴar'uwarta kuma aminiyarta abunda mijinta keyi, gani take idan har tayi haka bata yi mata adalci ba.
Tana fita daga gidan ta faka gefen ti-ti ta dannawa Yasmin kira, three miss call tayi mata amman bata ɗaga ba, ta san ba zai wuce tana cikin kotu ba, sai kawai ta yanke shawarar tura mata saƙo.


Ko da ta isa gida Anty Amarya bata nan, part ɗin kuma babu kowa, ƙannenta duk suna makaranta, hakan ya bata damar shiga ɗakinta ta baja kolin hajar tunaninta.


UZAIR POV.


Lokacin da Uzair ya ga Namra ta fita sai ya gargada ƴan iskan friends ɗinsa, ya gyara gidan tas kamar komai bai faru ba. Ba ayi minti Arba'in ba, sai ga Yasmin ta dawo gidan, cikin sauri ta shigo parlor tana dube-dube.
Uzair na zaune saman kujera yana kallonta, hankalinsa kwance kamar ba komai, sam be yarda ya nuna akwai wani abun a fuskarsa ba, tashi yayi ya tare ta, tare da rumgumeta yana kissing


“Lafiya wife?”


Ta sakar masa jikinta sosai


“Wallahi miss call ɗin Namra na gani da text ɗin ta, wai na yi sauri na zo gidana, shine duk hankalina ya tashi”


Dariya yayi sosai a zuciyarsa yana jinjina ƙarfin hali irin na Namra.


“Haba dai sai kace baki san Namra ba? Zata iya disgaki fa ai ba yau ta saba ba, karki tashi hankalinki”


Juyowa tayi sukayi kissing ɗin junansu sannan ta ce


“Ta katse min aiki na, ina fatar dai tayi maka kosan kazar?”


Hancinta ya laƙata


“Namra bata ma zo nan gidan ba, friends ɗina kuma har son kama hanyar Abuja daman ɗaurin aure suka zo”


Da haka ya shammace ta ya cigaba da kissing ɗinta.


NAMRA POV.


Duk yadda ta so ta labartawa Anty Amarya abunda ke cikin ranta na game da Uzair sai ta kasa, haka ta wuni tana tunanin abunda ya faru tsakaninsu da Asim, da kuma shawarar da Amira ta bata, a ɗayan ɓangaren kuma ƙwaƙwalwarta na ɗauke da hoton abunda taga Ya Uzair yayi.
Har bayan Sallah Isha'i tana kiran wayar Asim amman ya ƙi ya ɗaga, ta tura masa massage no reply, abun duniya duk ya bi ya dame ta.


Shigowar Anty Amarya ne yasa ta tsaita natsuwarta, har tana ƙoƙarin gyara zamanta.


“Abbanki yace na faɗa miki baƙonki ba zai samu zuwa ba”


Anty Amarya ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zaunawa saman gadon kusa da ita. Namra ta ɗan kalleta kaɗan


“Miyasa?”


“Nima ban sani ba, amman na naji a waya yana cewa wai kin masa ƙarama, kuma yana jin nauyinki”


Namra ta ɗan yi murmushi ƙaɗan ta kwanta jikin Anty Amarya.


“Shima dai yasan ni ba sa'arsa bace”


Anty Amarya ta shafa kan ƴarta.


“Allah dai yayi miki zaɓin da yafi alheri, ya yaye miki damuwarki”


“Amin Mamana”




KALSOOM POV.


Around eight thirty Kalsoom ta fito ɗakinta, a lokacin Saleena har ta wuce makaranta. Ita ta haɗa musu breakfast bayan ta gama, ta zuba ma Dad da Momy nasu ta ɗauka ta nufi part ɗinsu.
Bayan ta gaishe su, ta aje musu abincin tana ƙoƙarin rasowa Momy tayi mata tuni da zuwa gidan ƙanwarta Zainab.


“Ban manta ba Momy, yanzu idan na shirya can zan fara zuwa na aje kayana sannan na wuce aiki”


“Hakan yayi Allah ya kawo miki naki mijin”


Sai da ta amsa sannan ta tashi ta fice. Kala biyar ta ɗauka a maimakon uku, dan tasan sai ta fi kwana uku a can, cikin ƙaramin akwati ta saka su, sannan ta shirya kanta ta fice.
Kamar yadda ta tsara sai da ta fara biyawa gidan ta aje kayanta sannan ta wuce gurin aiki. Biyu da rabi ta tashi daga aikin direct gidansu ƙawarta Salma ta wuce.


Ta taki sa'ah, tana shiga mijinta na fita. Sai da tayi Sallah Salma ta ɗebo mata abinci ta ƙoshi sannan ta ɗauko mata zance.


“Kalsoom wani gari ne nake son muje tare da Ruƙayyah ita zata kai mu, ance malamin yana aiki sosai dan mutane da dama suna dacewa”


Kalsoom ta sauke ajiyar zuciya


“Ni wallahi har na gaji da irin wannan shige-shigen, kullum ana abu kamar ba'ayi, wani gurin ace aljanu ne wani su kuma su ce sihiri ne, na rasa gane kan matsalar nan, Wani lokacin har ji nake kamar na kashe kai na”


Salma ta dafata


“Subhanallahi, haba Kalsoom ki daina wannan maganar mana, Allah ya baki aikin da zaki iya taimakon kanki, Allah ya rufa miki asiri aure ne kawai Allah bai kawo miki ba, shine kuma kike ƙoƙarin butulce masa, kina wannan maganar sai kace ba musulma ba?”


Kalsoom ta lumshe ido ta buɗe ta kalli Salma cike da damuwa ta ce


“Salma duk abunda Allah ya ban da wanda zai ban bai kai kamar aure ba, aure shine cikar mutuncin ko wace ƴa mace, ni fa ba dotse bace Salma ina da sha'awa ina tsoron abunda zai kai ni ga halaka”


Salma ta riƙata tana ƙoƙarin kwantar mata da hankali.


“Roƙon Allah baya faɗuwa ƙasa Kalsoom, komai zai zo ya wuce kamar ba'ayi ba, kuma ba asan inda rabo take ba wata ƙila mu dace”


“Ni dai ba zan sake zuwa ko ina ba, na haƙura ballantana kinsan Ruƙayya ba a sirri da ita, kuma ko munje ba wani dacewa za muyi ba, tun da babu wanda zai iya matso maka da nesa kusa, babu wanda zai iya goge abunda Allah ya rubuta maka, sai dai kawai su ci kuɗinka, na fawwalawa Allah komai daman da shi na dogara”


Duk yadda Salma ta so ta lallaɓa Kalsoom su je, sai taƙi dan ita yanzu ta riga ta sadaƙar. Sai da Yamma Kalsoom ta bar gidan Salma.






__________________________________


How about dis journey?


#threefamily
# Vote
#Comment
#TeamNamra
#TeamKalsoom
#TeamHilal
#Candy
#Blog


Always check my website for more.


BEST REGARDS💖
Khadeeja Candy 🌺


www.khadeejacandy.com.ng
🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login