Showing 162001 words to 165000 words out of 281103 words
Chapter 55 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
tana nan babbar asibibiti, layin masu ciwon ulcer”
Kallonta yake da kyau, irin kallon da idonsa zata siffanta masa sigar jikinta, yarinya sai dai ba sosai ba, fara ce kyakkyawa mai ruwan fulani, ko kuma na ce buzayen jajaye. Hawunta ya haɗe a bakinsa kana ya ce
“Nawa ne ake buƙata?”
“Dubu ɗari biyu da sittin”
“Tam yanzu kin ga mahaifina baya nan, ya za'ayi”
“Ina zan same shi?”
“Baya nan ta tafi Lagos ganin shugaban ƙasa” (A lokacin Lagos ce fct ba Abuja ba)
“Yaushe zai dawo?”
“Wallahi ban sani ba, amman idan kina so ni zan iya taimaka miki”
“Ina so dan Allah”
“Amman fa sai idan nima za ki taimaka min”
Kallon rashin fahimta tayi masa dan a iya ganinta da tunaninta baya buƙatar wani taimako daga gareta.
“Me zan taimaka maka?”
“Idan har kina son na baki kuɗi to ki iskoni a ɗayan gidan baban mu da yake nan kwalkwaɗa, zan ninka miki fiye da abunda kike so ba”
Sak tasan abunda yake nufi, kuma ta fahimci inda kalamansa suka dosa, ita kuma bata koyi wannan tarbiyar ba, kuma bata ji zata iya sadaukarda mutuncinta ba. Sai kawai ta kaɗe jikinta ta tashi tsaye.
“Ni ba ƴar iska ba ce, dan kawai na zo neman abu gurin mahaifiya ba shi yake nuna ni ƴar iska bace, rashi mahaifi ne, kuma duka dangi babu mai shi, idan har zaka taimaka min dan Allah ka taimaka min”
“Daman ƙarya kike ciwon mahaufiyarki be da me ki, da kin aikata komai akan ta. Wuce ki ba mu guri”
Da kuka yarinyar ta bar gidan. Shi kuma ya juya ya shiga ƴar marsandin mahaifinsa ya fita daga gidan. Kai tsaye ɗayan gidan mahaifinsa ya nufa, dake can bayan babban gidansu, daman ya saba a duk lokacin da mahaifinsa baya nan a can yake tarewa yana sharholiyarsa da abokansa wani lokacin har da mata, abu ɗaya ne baya yi shine shaye-shaye.
Bayan kamar sa'a ɗaya da isarsa gidan sai ga yarinyar ɗa zu ta dawo, a nan ma sai da ta nemi iso suka zo suka faɗa masa sannan suka bata dama sannan ta shiga.
Har cikin faɗar da yake zaune ta isa ta zube masa a ƙasa tana kuka.
“Na roƙe ka, na haɗa ka da girman Allah ka taimaka min mahaifiyata zata iya rasa rayuwarta daga yanzu har zuwa wani lokaci inji likita, saboda ulcer ta taɓa hanjinta har ya lalace”
“Idan kina son ran mahaifiyarki ai sai ki bada na ki rai, ni bana da wani taimako da zan miki wanda ya wuce wannan, idan kin san riƙona ne kawai ya kawo ki to ƙara ma ki tashi ki koma kar dare yayi miki”
Ɗaga kai tayi tana kallon idonsa, rashin imanin dake zuciyarsa take hangowa. Ta karanci tantiranci da ke cikin idonsa lallai idan har bata shirya siyar da mutuncinta to ko mahaifiyarta zata iya rasa ranta bayan kuma ita kaɗai ce ta rage mata a duniya. Hkan yasa ta yarda ta amince tana ji tana gani ya keta mata haddi, abunda bata taɓa kawo ma zuciyarta ba, cewar zata bada budurcinta ga wani wanda ba halalinta ba.
Wani tsabar zalumcin kuma sai da ya gama amfani da ita sannan ya ƙirga rabin kuɗin ya bata wai shi kawai suka rage masa, da tayi maganar har da zaginta yana faɗin daman ai buzaye kowa yasan ƴan iska ne. Da kuka ta bar gida tana mai jin zafin keta mata haɗi da yayi. Shi kuma ya kwanta a ɗakin zuciyarsa cike da nishaɗi, yana jindaɗin abunda ya aikata wanda a gareshu ba sabon abu ba ne.
bachinsa ya kwasa a gurin har sai da ya hantse, sannan ya tashi, yayi salla, sai ya aika mai musu aiki ya siyo musu abincin. yana cikin cin abincin sai ga yarinyar ta dawo idanuwanta a kumbure, wannan karon bata sha wahala a gurin shiga gidan ba ganin ɗazu yace a bar ta ta shiga. A falon ta same shi yana cin abincin hankali kwance. Kuɗinsa ta aje masa tana kuka.
“Ba ayi mata aikin ba saboda rai yayi halinsa, ga kuɗinka bana buƙatar ganin su ko amfani da su, dan amfaninsu a gare ni ya ƙare. Ka kita min haddi akan abinda be wuce ka bani sadaka ba, saboda kawai na zo nema gun ka, to ka rubuta ka aje ko ba daɗe ko ba jima, sai an yima ƴarka abunda ka yi min, sai ka ɗanɗana idan da daɗi, sai Allah ya ninka maka baƙincikin raina sau biyu, wata rana sai ka wayi gari kana nadamar abinda ka aikata min, na roƙi Allah ya isar min ya nuna maka a kan ƴar cikin ka...”
Bata gama kalamin ba ya ɗauki abinci ya jefeta da shi, ya hau ta ta shuri yana zaginta. Shi kansa ya ji babu daɗi a kalaman da tayi masa, duk da ya ba, amman duk waɗanda yake da su, sune suke kawo kansu ko ya neme su kusan dai za'ace karuwai ne, wannan ce kawai ya keta ma haddi da gangan...```
Ajiyar zuciya Dady ya sauke, hawaye suka silalo daga idonsa, sai jan majiya yake. Yanzu kan ya tabbatar da alƙawarin Allah gaskiya ne, kuma kowa yayi da ƴar wani sai an yi da tashi, sai dai nashi sakamakon mai zafi ne, tun da na ƴarsa har da cutar kanjamau, kuma ta keta mutuncin aurenta, wannan babban abun baƙinciki ma ita ta ba da kanta ba wai keta mata haddi aka yi ba, dan baya tunanin hakan da keta haddin ne da tuni ta faɗa.
Miƙewa yayi tsaye zuciyarsa na masa wani irin mugun zafi ya shiga ɗakinsa hawaye na cigaba da masa zuba. Nadama ce tsantsarta a zuciyarsa sai yanzu yake baƙincikin abunda ya aikatawa ƴar mutane, lallai zina bashi ce! Dole wata rana ka biya ko a biya maka....
RASHIDA POV.
Ɗakinta ta koma ta zauna tana rare kukan baƙinciki daya cika mata zuciya. Ji take kamar ta rataye kanta ta huta, ta san duk wanda yaji tana ɗauke da wannan cutar ba zai zauna da ita ba, ga kuma Hilal da yanzu take da tabbacin ta rasa shi kenan har a bada. Iyayenta ma a yanzu ta san ta rasa su dan ta san zamanta da nasu dole zai banbanta, dole a yanzu duniya ta san abunda ta aikata, rayuwar da take gudun shiga ta san a yanzu dole ita zata yi.
Duk kukan da take Momy na tsaye jikin ƙofar ɗakin tana kallonta tare da rera nata kukan. Haƙiƙa tana tausayin ƴarta sai dai babu yadda ta iya tun da ita ta jawa kanta.
“Za muje mu ƙara gwaji, so that mu tabbatar idan har da gaske kina ɗauke da cutar”
Ɗagowa kawai ta yi ta kalli Momy da idanuwanta da suke ta zubar da ƙwalla har ɓata gani sosai da su. Sai kuma ta maida dubanta gurin hannayenta tana duba jikinta kanta take kaɗawa tana jinjina lamarin ubangijinta dan shi kaɗai ya isa yayi mata haka, sauyin rayuwa a take....
HILAL POV.
A firgice ya isa asibitin dan tun bayan abunda Nurse ɗin ta faɗa masa sai hankalinsa ya tashi sosai.
Ko parking ɗin kirki be yi ba ya buɗe motar ya fito hankali tashe har yana gudu. Likitan yara uku ya tararar akan Rafiq suna ƙoƙarin ceto numfashinsa, amman ina rai yayi halinsa. Ƙasarawa yayi a rikice yana girgiza Rafiq, tare da kiran sunansa. Da sauri ɗayan likitan ya riƙe shi yayi baya da shi yana masa magana.
“Haba Doc ya kake abu kamaɗ ba likita ba, mutuwa wace iri ce ba mu gani ba? Ka yi imani da kaddara mana, komai ka yi ba zai sai Allah ya fasa abunda yayi niya ba, dan kasan ba'ayi Rafiq dan kai ba, kamar yadda ba'ayi Rafiq dan ka ba”
Lumshe ido Doc yayi ya dantse bakinsa, yana ta ganin Rafiq yana masa yawo a ƙwaƙwalwa, ƴana buɗe idon sai hawaye. A hankali ya furta Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Sannan ya juya ya fita daga ɗakin. Rufa masa baya likitoci suka yi suna tausasa masa zuciyarsa.
Ba laifi ya samu gwarin gwuiwa daga ƴan'uwnsa likito wanda hakan ya hana shi bayyana damuwar mutuwar ɗansa a fili, duk da yasan abunda da zai daɗe a zuciyarsa yana masa yawo kasancewar ƙananan yara suna da shiga rai.
Da kansa ya kira Hajiyarsa ya faɗa mata, kamin ya kira wasu daga cikin ƴan'uwansa da kuma ɓangaren Rashida.
Sannan abokansa suka saka shi a motarsu , shi kuma ya shiga a ɗayar motar abokinsa suka nufo gida dashi. Tun da Kalsoom taji ƙarar buɗe gate ɗin gabanta yayi mummunan faɗuwa, tana jin tsayawar mota ba ɗaya bugun zuciyarta ya ƙaru. Balle kuma da taga Hilal ya shigo idonsa a rine.
“Ya rasu ko?”
Kai kawai ya ɗaga mata ya zauna saman kujera. Ita kuma ta ɗora hannu saman kai ta fashe da kuka ta durƙushe a gurin. Yana unƙurawa zai tashi Hajiya ta turo ƙofar falon ta shigo tana kuka, tare da wasu sisters na shi.
Da sauri Hilal ya tare ta yana faɗin ta daina kuka.
“Hajiya be kamata ki masa kuka ba, haka Allah ya kaddara babu yadda muka iya”
Hajiya bata daina kukan ba ta nuna Kalsoom ta ce
“Idan baka saki wannan yarinyar ba ban yafe maka ba Hilal, kuma sai dai ka nemi wata uwar ba ni ba...!”
A gigice ya kalli Kalsoom sai kuma ya kallon bakin Hajiya da yayi wannan furucin. Kalsoom ma kallon Hajiya take hawaye na bin fuskarta. Rashida ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana kuka.
“Ina ɗa na? Ka hana ni ganinsa lokacin da yake da rai yanzu na zo na ga gawarsa ina ɗa na yake?”
Rumtse ido Hilal yayi ya zauna saman kujera ya dafe kansa ya dantse bakinsa gam.
NAMRA POV.
Ana kiran salla magariba suka sauka babbar tashar kaduna, da sauri passengers suke fita wasu saboda suna nesa ganin dare ya soma yi wasu kuma dan su samu bin jam'in salla magariba. Ita ce kawai ta fito daga motar kamar marar kuzari tana tafiya tana kallon tashar da bata taɓa mafarkin zuwa ba. Tana fita daga gurin da motoci suke sai masu Nepep irin wadanɗa suke tsayawa a gefen tashar suna neman masu shiga gari.
“Malama ina za kije?”
Ɗaya daga cikin matasan dake tsaye a gurin masu Napep ya tambaya yana shafe ruwan dake alwala dake fuskarsa. Matashin saurayi ne mai jini a jika fari kyakkyawa da shi, a zahiri akwai natsuwa da sanin ya kamata a shimfiɗe a fuskarsa. Ga sajensa gwanin sha'awa.
“Cikin gari...”
Ta faɗa da muryarta mai kamar zata yi kuka.
“Okay, shiga muje amman zan tsaya a hanya na samu jam'i”
“Ba matsala”
Ya jefar ledar pure water dake hannunsa ya shiga napep ɗin tasa mai kamar sabuwa ya kunna, ita kuma sai ta shiga gidan baya ta zauna tana ta tunanin inda zata ce ya kai ta. Har ya kunna Napep ɗin ya fara tuƙi be tambaye a ina za'a kai ta cikin garin ba, dan shi dai danuwarasa a yanzu ya samu jam'i.
Ba suyi tafiya mai nisa ba ya faka a gafen titi, ya fita yana faɗin
“Bari na yi salla a masalacin”
Kai ta ɗaga masa tana kallon mutane dake ta haɗa haɗa a kan babban titin. Tunanin unguwar da zata ce masa ya kai ta take, amman har yayi salla ya dawo bata samu unguwa ɗaya da zata ce ya kai ta, dan bata san garin kaduna balle yace ga inda zai kaita.
Sai da yayi mata sallama sannan ya shiga Napep ɗin ya tasheta ya hau titi. Can ya ciro wani ƙyale ya kare ƙasar salla dake goshinsa ya juyo kaɗan ya kalli Namra.
“Wace Unguwa za muje?”
“Uh...m ca..an can..gur.in gra”
Ta faɗin hakan ne dan bata san inda zata ce masa ba, amman ta san ko wane gari akwai gra.
“Okay GRA ta gurin ina?”
“Ta gurin manyan gidajen nan”
Daga nan wata kalma bata sake shiga tsakaninsu ba, shi dai ya mai da hankalinsa gurin tuƙinsa, ita kuma hankalinta gaba ɗaya ya tattara ya koma gida da tunanin inda zata kwana yau a garin kaduna. Ganin sun shiga GRA har suna ƙoƙarin wucewa bata ce ga inda za a sauke ta ba yasa yayi mata magana.
“Malama mun shiga GRA ɗin fa”
Sai kawai tayi shiru ba dan kuma bata ji shi ba, sai dai bata san abunda zata ce masa ba. Hakan yasa ya ƙara maimatawa yana mai rage gudun da yake.
“Gaskiya ni ban san inda zanje ba”
Juyowa yayi ya kalleta.
“Baki san sunan mai gidan ba ne? Kuma baki da number waya?”
“Ban sani ba, kuma bana da number, sau ɗaya na taɓa zuwa”
“Amman irin wannan tafiya ai it risk, ace baka da number wanda zaka sauka gunsa kuma ba kan guri ba?”
Tayi shiru bata ce komai ba. Sai a yazu take nadamar zuwan da tayi a kaduna ita kanta ta san tayi wauta.
Jin bata ce komai ba yasa ya ce
“Ina zan sauke ki dan ni akan aiki na ke”
“Wallahi idan ka sauke ni ban san inda zanje ba, dan bana da kowa a kadunar nan sai Allah, tun da ban san gurin wanda zan sauka ba”
Cikin muryar kuka tayi maganar, juyowar da zai ya kalleta sai kawai yaji shesshekar kukanta. Baya iya ganin hawayen idonta dan Napep ɗinsa bata da wutar ciki wance wasu suke sakawa, hasken dake gefen titin be iya ya haska fuskarta har yaga hawayenta ba,amman a yadda ya karanta kamar tana cikin wani hali ne.
“Bawai Allah ke mutum ce?”
“Ni mutum ce wallahi kuma ba cutar da kai zan yi ba”
A nan ta saka ƙafarta ta sauka daga cikin Napep ɗin ta saka hannunta a jaka ta ciro ɗari biyu ta miƙa masa.
“Ba ni canji”
Ta faɗa tana ta ƙoƙarin tare kukanta dake son fitowa. Kasa karɓar kuɗin yayi kuma ya kasa tafiya, kallon fuskarta yake dan yanxu hasken gurin ya haska fuskarta, bata yi masa kama da mugayen mutane ba, jikinsa be bashi zata cutar da shi ba, hakan yasa shi idan har ya barta a nan gurin be kyauta masa ta, kuma besan abunda zai same ta ba tun da tace masa bata da kowa sai Allah.
“Shiga mu je”
“Na gode”
Ta faɗa tana share hawayenta, sai ta shiga Napep ɗin da sauri. Tun da ya soma tuƙin be tsaya ko ina ba sai malali, a mararraba ya tsaya ya miƙa ɗari da hansi aka bashi canji sannan ya ƙarasa ƙofar gidan na su mai cike da rufin asibiti, dan a kira su da talakawa ba kasancewar suna da rufin asiri da wadatar zuci. Sai dai a zahiri kan talakawa ne sosai masu ginin bulu wanda ba ayi ma filistaba.
“Fito muje”
Ya faɗa bayan ya kashe Napep ɗin. Cikin sanyin jiki ta fito tana dansar bakumi saboda mugun murɗa da mararta take mata. Yana gaba tana biye har suka shiga cikin gidan mai ɗauke da ɗakuna uku, duk da dare ne hakan be hanata ganin yalwantaccen tsakar gidansu ba mai ɗauke da bishiyar mangoro guda biyu ɗaya a jikin ɗaki ɗaya kuma a tsakiyar gidan.
“Neine (Inna da yaren fulatancin) ga baƙuwa”
Wacce saurayin ya kira da neiner ta miƙe daga saman tabarmar da take ta nufo Namra tana murmushi.
“Maraba maraba laƙe marhabun baƙonƙa annabin ka, siter ƴata sita (Zauna zauna)”
Ya faɗa lokacin da take ƙoƙarin zaunar da Namra saman tabarmar da take zaune. Namra ta zauna tana kallon yaran gidan da suka kewaye waya suna kallon india hausa a wata ƙaramar wayar hannu. Gaba ɗaya hankalinsu ya tattara ya tafi can sam basu ma san da zuwanta ba.
Neine da kanta ta shiga ɗaki ta ɗauki ma Namra tuwon masara ta aje mata gabanta, sai ta nufi wani ɗan madaidaicin tulu ya bulbulo mata ruwa a kofi ta kawo mata tana mai sakar mata fuska kamar ta santa.
Shi dai yana daga can gefe yana bawa cat ɗinsa kifi, amman hankalinsa yana gurin Namra yana kallon yanayinta.
-----------------------------------------------------------------
I PITY RASHIDA 😢
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *64*
Suna ta gaba-gaba suna tare Abdool kamar wanda wani abu zai same shi, sai kirari suke masa wasu na ture mutane dake gefen gurin dan Abdool ya samu hanya. Mutane sai kallo a ke wasu ma har sun wuce sai suka dawo ganin duka numbobin motar an saka YARIMA ABDOOL, duk wanda kuma yaga jajaye kaya yasan sarki ne ko kuma ɗan sarki.
Abdool be nuna tausayi a fuskarsa ba, na ganin irin raunin da aka yi ma Lamido, sai dai a can zuciyarsa ne yake tausayinsa ganin yadda jini yake masa zuba a kai kuma ya riƙe ƙafarsa sai cizar baki yake alamar yana jin zafi sosai, kowa yaga yadda Napep ɗin tasa ta yi sai ya tausaya masa duk ta lalace kai baka ce ma wanda yake ciki zai yi rai ba, saboda buguwa da tayi da transformer garin ya kauce musu har ya transformer ta faɗo kan Napep ɗin tasa, shi da be yi hanzarin fita ba da Allah kaɗai yasan irin ciwon da zai ji.
Lamido ya kalli Sadauki ya soma magana da shi kaɗan-kaɗan, yana gama maganar ya juya da sauri suka soma take masa baya, suka buɗe masa motar ya koma. Sannan Sadauki ya kalli sauran dogara ya ce
“Yarima ya yi umarnin a kai shi asibiti”
Da sauri Dogaran suka nufi gurin Lamido suka riƙa shi suka saka shi motar su. Sai suka sauya hanya daga masaukin Abdool zuwa Asibiti mafi kusa da su.
Anyi masa kyakkyawar karɓa, a asibitin, duk da kasancewar basu san Yarima Abdool ba amman suna ganin motoci ya dogarai sun san babban mutum ne.
Duk abinda aka yi aka maga Abdool na ciki mota zaunensa har aka gama dubasa aka saka masa baldeji a kai suka rubuta masa magani, a cikin asibitin dogaren yaje ya siya masa magani sannan suka dawo da shi gurin motar. Da gudu Sadauki ya nufi Motar Yarima Abdool ya ƙwanƙwasa gilashin motar sai ɗayan dogaren dake ciki ya sauke gilashin motar.
“Ran Yarima ya daɗe, an kammala masa komai, sun ce yaji ciwo kai sai kafarsa da ɗan targaɗe kaɗan”
Da Abdool yake magana amman yayi kamar be jisa ba, idonsa na kan Lamido dake tsaye jikin wacan motar yana kallon titi. Kallonsa sosai Abdool yake a zahiri yana da kyaun natsuwa da kuma kyaun fuska, gashi dogo ga fari ga dogon hanci gashin kansa kawai idan ka kalla zaka gane