Showing 123001 words to 126000 words out of 281103 words
Chapter 42 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
abinci kawai ko kuɗin cefane ina su ke? Ba sai da abu ake yinsa ba? Ko babu zan ba ki?”
“Amman naga kana fita aiki Asim ba za ace kullum baka samowa ba ki kaɗan ne dole wata rana sai ka samo”
“To ɗan abinda na ke samowa ai ba zai wuce na hau achaɓa ba, ba fa wani samu muke sosai ba, ni kaina na fiki son na ciyar da ke dan Aallah ya fi bawa mai yi iyalansa, sannan babu Namijin da zai so mace ta ciyar da shi ko dan gudun irin wannan gorin”
“Ba gori na ke maka ba, gaskiya nake faɗa, idan mu ka zauna muka ce wannan kuɗin na sana'ah kullum shi za'a ci, sai mu cinye sana'ar mu zauna a haka babu komai”
“To ya zan yi Namra? Sata zan yi na baki ko kuma kai na zan siyar na ciyar da ke? Kina gani ba wata sana'ah ce da ni ba daga yanzu ki lissafa duk abinda san kin kashe na ciyar da kan ki da ni idan na yi kuɗi zan biya ki, ni bana son gori akai na farau rashin arxiki? Ko kuma ni na kawo tauasaci duniya? Idan ma kin gaji da zama da ni ne sai ki faɗa min kawai ba wai ki riƙa min magana any how ba”
“Babu mace da zata zauna da kai a yadda na zauna da kai Asim, na watsar da jindaɗin gidan mu dan kawai na yi maka biyayah na zo na zauna a nan gidan ina rayuwar da ban taɓa mafrkin shiga, ka dubi jikina, duk wanda yasan ni ya gan ni a yanzu ba zai ce ni ba ce, amman kullum baka gani sai anbanta ni kake”
“Mtssswww kaji ba, sai jawabi da ƙaryar arziki, duk arzikin gidan ku me suka ƙulla miki? Babu wanda zai gan ki yace ke ƴar gidan ce, tun da kika yi aure har yau babu wanda ya taɓa tako ƙafarsa ya zo gidanki, haka ake rayuwa, ai ko bunsuru kike aure idan basu yi dan ni ba sayi dan ke, ko riƙon ki ake ya kamata ace wani naki yazo garin nan ganin amman ko ciwon da nayi har na warke babu wanda ya leƙo kamar na kashe musu wani”
“Me zai kawo ƴan uwana a gidan ka, bayan sun san dalilin aure na da ka yi? Me za su zo su yi? Ciwon da ka yi wane irin jawabi ne ba ka min akan jinyar da kayi sai ka ce sune suke da alhakin ɗaukar naunyin ɗawainiya da kai, Mama da take mahaifiyarka me tayi maka? Kuɗin data karɓo ai dashen da kuke ne, duk ni nayi ɗawainiya da kai”
Tasss ya watsa wanke mata fuska da mari, ya hau shurinta sai kaurar fuskarta yake yana faɗin.
“Duk iskancin ki ya tsaya a kan ki, karki kuskura saka uwata a cikin sheɗancin ki, dan ba warin ki ba ce”
Kuka take yi sosai tana rufe idonta da ta ke jin kamar ƙasa ta watsar mata a cikin. Be kula irin aika-aikar da yayi ba yasa ƙafa ya fice.
Haka ya wuni a ɗakin tana aikin kuka kamar ta cire idonta, sai da aka kira salla azahar sannan ta samu kukan ya tsaraita mata har ta unƙura ta tashi.
Wanka tayi tare da alwala sannan ta saka wasu tufafin tayi salla. Sai ta ɗauko qur'ane tana karatu.
Guraren uku da kwata wayarta tayi ringing ita har ta manta da sha'anin wayar sai yanzu. Bata kula wayar ba sai data ta kai ƙarshen suratul Yasin, sannan ta rufe qur'anen ta yi addu'ah daga bisani ta maida alƙur'anen mazauninsa, sannan ta nufi wayar ta duba.
Number Anty Yasmin ce. Ta yi mamakin ganin kiran Yasmin har four miss calls, ta manta when ma Yasmin ta kirata tun suna shiri. Bata da kuɗin da zasu isheta magana amman tasan ba zata rasa na flashing ba.
Kamin ta kira sai ga Yasmin ta ƙara kira. Namra tayi saurin picking ta kara a kunne.
“Assalamu alaikum Anty”
“Na'am My Sis ykk”
“Lafiya ƙalau, ya Gwaggo”
“Tana can gida, ni na zo katsina seminar ne, tun shekaran jiya yau zan koma, kuma bana son na wuce ban gan ki ba”
Gaban Namra ya faɗi bata ƙaunar wani yace zai kawo mata ziyara a yanzu, sai dai bata jin zata iya hana Yasmin zuwa gidanta tun da har ta nuna son zuwa.
“Ayyah Anty Yasmin yanzu za ki zo?”
“Eh anjima kaɗan zamu koma”
“Okay ki ce a kawo ki Nasarawa, idan an kawo ki sai ki shiga ta cikin unguwar zaki ga gidan daya ƙone sai ki shigo nan”
“Okay gani nan zuwa yanzu”
Ta kashe wayar. Namra ta juya tana kallon ɗakinta, to be frank bata son kowa ya san halin da take ciki, sai dai babu yadda ta iya.
Kimtsa ɗakin ta shiga yi dan yau duk batayi shara ba tun da wuni tayi kukan dukan da Asim yayi mata.
Wajen gidan ma ta gyara bakin inda zata iya dan baɗin gidan ba mutum ɗaya ne zai iya share shi duka ba, yaro ta aika da kuɗi aka siyo ma Yasmin gala da ruwan sanye ta aje mata. Sannan ya canja tufafin jikinta ta saka masu ɗan kyau ta zauna zaman jiran isowar Yasmin.
Tana jin an turo ƙofar gate ɗin gidan gabanta ya yi mugun faɗuwa. Cikin ƙarfin hali ta taso ta doso gate ɗin gun da Yasmin take tana doka sallama da kallon gidan tana mamaki.
Rumgume ta Namra ta yi tana nuna murnar ganinta. Ita ma baki har kunne, ta ke ɗokin ganinta.
“Namra ke ce? Duk kin canja”
“Ni ce Anty”
“Duk kin canja kin, kin yi baƙi Namra kin lalace”
“Bana jindaɗi ne kwana biyu, mu shiga ciki”
Cike da ƙyaƙyami Yasmin ta zauna dan ita duk gidan be mata ba, mamaki ma take yadda Namra take zaune gidan.
Namra ta dire mata gala da ta siyo mata ta aje mata tare da ruwan sanyi
“Ban yi girki ba yau shine na siyo miki gala”
“My Sis meya samu fuskarki?”
Ta tambaya ganin fuskar duk ya kumbura. Namra tayi shiru bata ce mata komai ba.
“Haka kike wannan rayuwa Namra? Dube ki dubi gidan da kika zaune, yaushe kuka yi gobara?”
“Tun Asim na asibiti an kwana biyu, abubuwan ne suka sauya amman yanzu ai ya samu aiki komai zai walwale”
“To Allah yasa”
Sama sama suka yi fira, bata wani daɗe ba tayi ma Namra sallama ta ciro 20k ta bata. Har bakin gate Namra ta rakata, sai da ta shiga motar da ta kawo suka kama hanya sannan Namra ta koma cikin gida.
ASIM POV.
Cike da ɓacin rai ya fito gida, ya doshi gurin sana'arsa. Ko da ya isa ya tararda abokan aikinsa har sun buɗe shagon suna fitar da kayan aikin.
Haka ya samu guri gefe ya zauna sai fuci yake kamar sune suka masa wani abu. Har suka gama fitar da kayan aikin suka rura wuta suka zauna suka fara zuga. Yana can gefe yana tunanin rayuwarsa yadda zai yi ya rama abinda Namra da iyayenta suka masa.
Wayarsa ya ciro ya dannan number Hajiyar nan dan yayi saving ɗinta tun jiya. Ringing tayi sai da tana daf da katsewa sannan ta yi picking.
“Hajiya Ina wuni”
“Lafiya ƙalau who's this?”
“Asim ne Hajiya, wanda kika ba number ki jiya, kika ce za a miki gyaran gate”
“Oh that Handsome Guy ko? ”
Yayi dariya cike da jindaɗin lafazinya
“Hajiya, ɗan talakan nan dai”
“Ai ajinka ya wuce talaka, kawai dai ka riƙe sana'ar da bata dace da kai ba ne”
“Hajiya abin ne sai a hankali kin san nigeria tayi zafi”
“Ta yi zafi ga wanda be san kanta ba, amman wannan sana'ar ai bata dace da kai ba sam. Anyway yaushe zaka zo ka duba min gate ɗin ne?”
“Wai da yanzu zan ɗauko abokanin aikina sai mu zo mu gani”
“Eh amman kai ya kamata ka fara zuwa ka ga yadda aikin yake, sai ka ce su zo daga ba ya, ko kuma ka koma ka ɗauko su”
“To aikin yana da yawa ne”
“Ba wani yawa gefe ne kawai ya ɗan ɓalle”
“Okay to bari na zo yanzu na duba yadda aikin yake”
“Sai ka iso, number ka ne wannan?”
“Eh Number na ne Hajiya”
“Okay”
Ta kashe wayar. Shi kuma sai faman murmushi yake
“She's so friendly, bata wulaƙanta mutane duk da tana da arziki, ta hutawa kan ta”
Ya faɗa a fili sannan ya tashi yana kaɗe rigar ya nufi gurin aikin nasa, sai da ya sanar musu da aikin ya faɗa zai je ya duba ne sai ya dawo sannan ya tari ɗan a chaɓa ya hau.
Kai tsaye gidan Hajiya Sadiya ya nufa, be sha wahalar ganewa ba, saboda ta karanta address ɗin na ta tun farko.
House number 7 ya shiga, kai tsaye ya shiga gidan kamar wani wanda ta saba zuwa, sai wara ido yake yana ƙara kallon gida da kyau da kyau. Mai gadin ne ya tare shi yana tambayar inda zaije.
Kamin yayi ma mai gadin magana ya ciro wayarsa ya kira number ta.
“Hajiya ga ni na iso, mai gadin ki na ƙoƙarin hana ni shiga”
Sai kawai ya miƙa masa wayar. Mai gadin na karɓar wayar ya kara a kunne sai kawai ya ce
“To Hajiya”
Ya miƙawa Asim wayarsa, yana nuna masa inda zai shiga. Ka ɗa kai kawai yayi ya doshi gurin daya nuna masa yana tsaki, dan ya tsani mai gadi ya wulaƙantasa, shiyasa baya son zuwa gidan da za a tambayeshi inda zai je.
Manyan motoci ya gani a harabar gurin jere, ciki har da wacce taje da ita gurinsa jiya. Tsayawa yayi ya ƙwanƙwasa ƙofar har sai da aka masa ixinin shiga sannan ya tura ya shiga yana sallama kamar ba shi ba.
Da murmushi a fuskarta ta tarbeshi tana nuna masa kujera.
“Maraba da samari”
“Hajiya ina wuni”
“Wuni ko kwana? Ko ɗazu fa wuni kace min ko matar ka ta caja maka kai ne? Kasan matan yanxu sai a hankali, ko da yake baka yi kama da mai aure ba”
“Bana da mata gaskiya, sai dai zafin ƙasar nan”
Tayi dariya tare da nufar gurin freezer ta ɗauko masa lemu da kofi ta zuba masa.
“Ga lemu ka sha, na san dai ka karya ko a kawo masa breakfast?”
“A'a na gode”
Ya ɗauki lemun ya sha, yana kallon ƙaton tv ta na bango dake can ƙarshen ɗakin.
Kallonsa take sosai tana murmushi, tare da gyara doguwar rigar atmafa dake jikinta.
“Na ce ka duba gate ɗin in ya zo gobe sai ku zo ayi aikin, dan yau zan yi baƙuwa gaskiya”
“Okay to ba matsala, gate ɗin na bakin ƙofa ne?”
“Wh ka tambayi mai gadi zai nuna maka”
Ya aje lemun bayan ya shaye shi kaf sannan ya tashi.
“Yo bari naje na duba gobe kamar gaushe zan zo?”
“Da la'asar idan rana ya yi san yi”
Wani irin rausayarda ido take lokacin da take magana da shi tana wani langaɓarda jiki. Shi kuma yayi murmushi yana sa hannayensa aljihu.
“Tau ina zuwa”
Ta juya ta soma tafiya cikin wani irin karairaiya, ta nufi ɗakin. Bata wani daɗe ba ta fito riƙe da sabbin yan ɗari biyu biyu ta mika masa.
“Ga 10k ka hau a chaɓa, sai na gan ka goben”
Ya faɗa tana murmushi tare da shafo hannunsa a lokacin da zai karɓa ɗin.
“Haba Hajiya ayi haka?”
“Ba komai ai irin ku abun tausayawa ne masara aikin yi”
“Na gode Allah ya saka da alheri ya ƙara aixiki”
Ya fito daga falon baki har kunne. Sai da ya tambaya mai gadin ya gwada masa gurin da gyaran yake sannan ya wuce.
KALSOOM POV.
Yau da wuri ta sallami yara da Hilal kasancewar yau Monday ce ranar aiki. Sannan ta shiga gyara gidan, baya ta share ko ina tayi mopping sannan ymta shiga kitchen ta haɗa kayan wanke-wanke ta somawa wankewa tana sauraren ƙira'ar dake wayarta.
Tsin-tsin'tsin ta riƙa jin kamar ana tsokararta, sai tsikar jikinta ya fara tashi.
“A'uzubillahi minal shaɗanin rajin”
Ta furta tana girgiza kanta da take jin yayi mata nauyi. Tunawa tayi da bata da ɗankwali a kanta, sai ta yi saurin komawa falo ta ɗauki ɗankwalin ta ɗaura, ta koma kitchen ɗin ta cigaba da wanke-wanken. Tana cikin wanke wanke ta ji kamar an kiran sunan, cikin muryar Hilal tsayawa tayi tana saurere ba tare data amsa ba, daman can bata da ɗabi'ar amsa kira idan har sau ɗaya ne, sai kuma ta ƙara jin kiran a karo an biyu, a maimakon ta amsa sai kawai ta aje wanke-wanke da take ta nufo falo dan taga idan har Hilal ɗin ne. Har waje ta fito tana dubawa amman vata ga motar Hilal ba balle alamunsa. Tana juyawa ta koma ta sake jin an kirata in Hilal voice.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Allaahumma munzilal-kitaabi, saree'al-hisaabi, ihzimil-'ahzaaba, Allaahumma ihzimhum wa zalzilhum. اللَّهُمَّ مُنْزِلَ الْكِتَابِ، سَرِيعَ الْحِسَابِ، اهْزِمِ الأَحْزَابَ، اللَّهُمَّ اهْزِ مْهُمْ وَزَلْزِلْهُمْ ”
Gabanta ya faɗi da farko, kuma ta tsorata sai dai addu'aj ɗa tayi yasa taji tsoron ya guje mata a take. Daman addu'ah ce ta neman tsari daga makiya.
Sai kawai ta koma ciki ta cigaba da wanke-wankenta. Wani irin ƙwallowa tayi Rafiq dake bachi ya buga. Ba shiri tayi bar wanke wanke ta nufin ɗakin yaran. Ƙasa ta tararda shi yana fisge-fisge kamar wanda za a cirewa rai.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Ta ƙarasa da sauri inda yake ta ɗaukesa tana girgixawa. Amman ina ido da jiki duka a ƙafe sai wani ƙogi yake yana kallon silin, aje shi tayi ta nufi ɗakinta da gudu ta ɗauki wayarta ta kira Hilal.
AMIRA POV.
Tana shiga ɗakin ta tararda komai na ɗakin pink color ne, sai manyan hotunan Amal dake jikin ginin ɗaki har da waɗanda ta yi ƙasar waje, wani gurin tana tare da Abdool wani gurin kuma da Ummi wani da Meesha wani da Fauza sai kuma wanda suka yi da Haleema, ma bin su shine wanda tayi da duka familynsu Hilal yai ma Ummi side hug yai mata kiss irin na nuna tsatsar ƙaunar nan na ɗa da uwa.
Wanda Amal tayi da Hilal ta fi tsurawa ido tana kallon yadda Hilal yake feeding ɗin Amal ranar birthday ta. Hannu ta kai ta shafa hoton tana murmushi.
“Kai na daɗe ina mafarki Abdool, kai ne irin mijin da nake so, sai yanzu na gane dalilin daya sa na bar gida na, ashe rabo ne kirana, saboda kai akayi ni Abdool nima kuma saboda ni aka yi ka, haƙiƙa ban yi sadaukarwar banza ba”
Ta juya ta jingina da ginin gurin ta lumshe ido tana sauke wani sayyayen numfashi.
Babu wanda take gani sai Abdool, rayuwarta da tasa take hangowa irin jindaɗi da kuma rayuwar da za su yi idan ya aureta.
Bayan tayi wanka ta maida tufafin dake jikinta ta zauna ta ci abinci tana ƙara ƙarewa ɗakin kallo. Ta jinjina kai
“Lalai ba ƙaramin dukiya Abdool ya tara ba shi da mahaifiyarsa, amman ina mahaifinsa yake? Ina jin baya nan gidan dan gidan be nuna alamun gidan sarauta ba”
Ta sauke ajiyar zuciya tana auna kanta a matsayin matar Abdool. Irin kallon da yayi mata take tunowa yadda idonsa yake da fari har wani ruwa ya kwanta a ciki kamar balarabe. Tashi tayi ta ƙasara gurin madubi tana kallon kanta, bata da munin da namiji zai ganta yace baya son ta. Idan har baka yabe ta ba to ba zaka kusheta ba.
Shukura ce ta dawo da dare ta kawo mata abinci sai ta kunna mata tv ta ɗauki wasu ɗaga cikin kayan da Amal za tayi amfani da su, da dukan alama Amal ɗin ce tasa a ɗauko mata har da ƴar ƙaramar iphone ɗinta.
________________
Ni kam nace Kar Hajiya ta lalata mana Asim 😏😏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *52*
KALSOOM POV.
Ta yi masa kira biyar be ɗaga ba, ga dukan alamu suna tiyata ko meeting dan shi kaɗai ne yake hana sa ɗaukar wayarta.
“Wayyo Allah na na shiga uku Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”
Ta furta cikin muryar kuka hawayen na bin fuskarta, zubewa ta yi a gurin hannunta ɗaya saman kai, ɗayan kuma riƙe da waya tana ƙoƙarin kiran Hilal. Still be ɗaga ba, a nan ta jefar da wayar ta koma ɗakin da Rafiq yake tana kuka. Wannan karon abinda ta gani ya bata tsoro dan har kumfa yake fitarwa a bakinsa.
Da sauri ta ɗauke shi ta fito da gudu ta nufi harabar gidan tana ihu. Mai gadin ne yayi kanta yana tambayar ba'asi. Ganin halin da yaron yake ciki ya sashi sallalami tare da karɓarsa ya girgiza.
“Hajiya ki kira Alhaji ki faɗa masa”
“Na kirasa be ɗaga ba”
“Ki sake kiransa kar yaron nan ya mutu”
Jin an ambaci mutuwa yasa ta ƙara rikicewa ta falla da gudu ciki, ta koma ɗakin ta ɗauki wayarta a inda ta jefar da ita.
A rikice ta kira numbersa wannan karon tayi sa'ah kira ɗaya ya ɗaga cikin muryar daya saba mata a duk lokacin data kirasa
“Maman yara...”
Kukanta da yaji yasa gabansa tsinkewa ya faɗi.
“Kalsoom what happend?”
“Rafiq ne Hilal ka zo gida yanzu kar ya mutu...”
Tana jin haka ya katse wayar ya mike daga zaman tattaunar da suka gama yanzu-yanzu ya nufi gidan hankali a tashi. @360 ya hau titi duk hankalinsa sai ya tattara ya koma gida, zuciyarsa sai yayo masa take, wani abun Rafiq ya hau ya faɗo ko kuma wuta ta jashi, kwata-kwata be kawo ma ransa abinda ya tarar yaron na yi ba. A firgice ya fito motar ya nufo gurin da Kalsoom take riƙe da Rafiq tana kuka.
Ya sa hannu biyu ya karɓe sa ta juyo da sauri ya nufi mota, dan babu lokacin tsayawa tambayar abunda y same shi.
Komawa tayi ciki ta ɗauko Hijabinta ta saka, ta ɗauki jakarta ta fito da sauri kamar tana son haɗaw da gudu, sai kuka take irin mai nuna tsantsar tashin hankali. Ba tare data kulle gidan ta fito titi, tari adai-dai sahu ta hau, tana faɗa nasa inda zai kai ta. Be sauketa ko ina ba sai American hospital inda Hilal yake aiki, sai da ta sallami mai Napep ɗin sannan ta nufi emergency duk da bata da tabbacin can ɗin ne ya kai shi ko a'a. Wasu nurser ta tambaya, suka tabbatar mata da xuwansa da kuma ɗakin daya nufa da yaron. Da gudu ta ƙarasa gurin tana share hawayen da suka ƙi su tsaya mata.
Kai da kawo ta