Showing 270001 words to 273000 words out of 281103 words
Chapter 91 - ZAGON KASA Book Complete Document by Khadeeja Candy .txt
lafiya ya kama shi, da ace ma shine yayi rantsuwa kamar yadda Namra ta yi da take zai faɗi ya mutu saboda bashi da gaskiya, da kama-kama suka fitar da shi.
Falon yayi tsit kamar ba kowa sai lamarin Allah suke jinjunawa, bayan kamar mintuna goma Mai Martaba ya ɗaga kai ya kalli kowa da ke cikin falon ya ce.
“Allah kenan ba a masa wasa, wani lokacin ɗan'adam muna da rauni da gazawa, da kuma isgili da gajin haƙuri, bayan ba mu wuce Allah yace mana ku mutu mu faɗi mu mutu ba, ko da beyi wannan isgilin ba dole ne yaga ba dai-dai ba saboda ƙoƙarinsa na raba auren sunna da kuma ƙoƙarinsa na saka auren cikin rikici.
Nasan hakan zai faru, dole ne a cikinsu akwai mai gaskiya, walau ita ko kuma shi yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa na hana Abdallah yi masa komai saboda za ayi duban kamar shi Abdallah baya da gaskiya ne ko kuma an zalumce amman yanzu shi kansa ya san tsakaninsa da Allah ne ba da mu ba, ƙara Allah yayi masa sakamako da ace nan aka cutar da shi, nasan zuciyarka ta kawo Abdallah zaka iya masa komai ido a rufe, sai dai ko da yaushe ina yawan faɗa muku da ku cuci mutum ƙara ka bari shi ya cuce ka, kar ka yarda ka ɗauki haƙƙin wani ko kuma ace haƙƙin wani yana kan ka, Ubangiji yana yafiya, amman baya yafe laifin wani akan wani, kuma duk lokacin da kaci amana ko haƙƙin wani ya hau kanka zaiyi ta cinka ne a dukiyarka ko lafiyarka sannan kuma idan kunje lafiya Allah ya karɓa masa haƙƙinsa.
Ko wace rayuwa tana zuwa da jarabawa, wani lokacin aka gwada mutun dan a auna imaninsa, kuma aga iya tawakkalinsa da haƙurinsa, abunda duk haƙuri be baka ba to rashinsa ba zai baka shi ba, da ace ba ayi haƙuri ba da yanzu ba kawo nan ba, kuma daga ƙarshe ba za a ga abunda ake so ba. Ina addu'ah wannan aure Allah yasa masa albarka kuma ya kawarda duk wata fitina da zata zo nan gaba, Allah ya muku albarka, kuma yau Namra zaki kwana ɗakinki da yardar Allah”
Nasihar Mai Martaba ta ratsa zuciya da jikin duk wanda ke cikin falon, tabbas mai martaba yayi musu nasiha mai haɗe da wa'azi a lokaci ɗaya.
Hajiya Sadiya ce ta riga tashi ta fice daga falon, sannna Ummi ta tashi tare da Namra suka yi ma Mai Martaba sallama, sannan suka fito, jingine da mota suka samu Hajiya Sadiya tana hawaye, har sun buɗe motar sun shiga sai Ummi tace a ɗan jira kamar tasan Mai Martaba zai aiko kiran Namra, sai ga Waziri da kansa ya zo ya faɗa ma Ummi cewar Mai Martaba yana kiran Namra, sai Ummi tace ta buɗe mata motar ta fito ta bi bayan waziri. Falon da suka fito suka koma sai dai wannan karon babu kowa sai Anty Amarya da Abbah, da alama Mai Martaba ya basu dama su tattauna ne, waziri ma yana kawowa bakin ƙofa ya kama gabansa.
Ƙarasa Namra tayi cikin kuka ta faɗa jikin Anty Amarya da ke murmushi ta rumgume ta.
“Mamana kenan kin ga rayuwa, wannan duka sharar fage ne alamu ne na rayuwar jindaɗi da farinciki tana nan tafe, Allah ya miki albarka”
Bayan abunda Abbah ya faɗa sai Anty ta ɗora da nata nasihar akan rayuwa da kuma zaman aure kamar yadda tayi mata a can gida. Abbah ma sai da ya kara mata da wani abu, sannan suka mata sallama saboda yau zasu koma, aiko nan Namra tasa musu kuka kamar zasu yi rabuwar har abada har Anty sai da tayi kuka, sai da Ummi ta shigo.ta fita da ita sannan ta tsagaita kuka da take. Sai dai Hajiya Sadiya kan har aka koma gida kuka take, a motar Hajiya Mairo ke ce mata ta barsa da Allah ai ga amana nan ta fara kamashi, a tunaninta Hajiya Sadiya tana kuka ne saboda ƙazafin da Asim yayi mata.
Ko da suka isa gidan ana shirye-shiye fara walimar da Ummi ta shirya zata yi, wasu tufafin Ummi ta ɗauko ma Namra sanna aka kora Mai Makeup cikin ƙanƙanen lokaci da canja mata kamanin zuwa na amare, sannan ta ɗaura mata ɗankwali.
Fauza da Haleema ne suka riƙa hannun Namra suka fita da ita gurin walimar suka zaunar da ita a muhallin da aka tanada na zaman Amarya. Kowa ya fita zuwa gurin Walimar banda Hajiya Sadiya da ke ƙunshe cikin ɗakin tana aikin kuka, sai kuma Ummi dake cikin gida tana gyara wasu abubuwan, sai da Hajiya Sadiya ta tabbatar hankalin kowa yana can gurin walimar sannan ta suɗaɗa ta fita ta bar gidan gaba ɗaya.
Anyi walima lafiya, kuma an tashi kowa na sam barka da yabawa. Bayan mutane sun watse ne Ummi tasa Namra a mota ita da su Maryam da Raihanatu da kuma Gwaggo Ramatu aka maida su masaukinsu tare da sauran mutane da suka zo walima, bayan sun koma gida ne Namra take labarta musu abunda ya faru.
ASIM POV.
Babu mai mota a cikinsu kasancewar Mai Martaba shi ya aika aka ɗaukosu hara Asim ɗin, a dole tasa sai da suka fita masarautar gaba ɗaya sannan suka samu Napep suka hau, sauran kuma suka hau wata Napep ɗin ana shawarar inda za a kai shi, wasu su ce asibiti wasu kuma su ce gida ya kamata a barshi albashi sai a fidda masa konon rantsuwar da yayi. Daker aka shiga Napep ɗin da shi saboda ƙafafunsa da basa tafiya, ko da suka isa fida a wahale yake saboda shi kaɗai yasan abunda yake ji a jikinsa.
A falon Amarya aka aje shi a take ta bada kuɗi aka je aka siyo gero aka cire masa kono sai dai abunda basu gane ba ai ba shi yayi rantsuwarba, shi isgili yayi na cewar kada Allah ya tashe shi lafiya idan har ƙarya yayi. Babu irin kuka da Mardiya ba tayi ba sai nanata zancen take wai daman tasan haka zai faru tun da yace be sake ta bayan kuma ya san ya sake ta.
Ganin har rana ta faɗi babu wani sauyi, yasa suka ɗauke shi zuwa asibiti, ana kiran magariba aka bashi gado, likitoci suka shiga bashi taimakon gaggawa, sannan suka tura shi ɗakin hoto. Allura suka masa a nan ya samu bachi.
***
Ƙarfe tara dai-dai aka jera motoci ƙofar gidan da su Namra suke wato masaukinsu. Hajiya Shafa da wasu family na mai Martaba suka shiga ciki suka yi bikon amarya da kuɗi da kuma siyayya.
Ana guda aka fito da Namra tana cikin lifaya fuskarta a lulluɓe, sai ƙamshin turare take.
Barorinta suka buɗe mata mota ta shiga sai aka maida ƙofar motar aka rufe, sai sauran suka shiga sauran motocin, aka akama hanyar gidan Mai Martaba da ita, lokacin da aka shiga da ita faɗar Mai Martaba na shaƙe da mutane da kuma talakawa, sai ta yi gaisuwar ban girma Mai Martaba yayi musu addu'a sannan aka shiga ɗakin ɗayar matarsa tayi musu addu'ah sannan aka yi canji mutane da wato mutanen da suka je bikonta ba su zasu raka ta ɗakinta ba.
Ko da aka isa da ita ɗakinta shaɗaya har ta gota, babu wanda beyi mamakin ganin irin gidan da aka kaita ba duk kuwa da kasancewar dare ne, baka iya banbance shi da rana saboda hasken da gidan ke da shi, yanayin gidan zuwa fenti da kwaliyar gidan duka irin na masarautarsu ne yayi, wani abun burgewa kuma yadda aka ƙawata gidan da komai fari kamar fentin gidan, wato furnitures da aka zubawa Namra komai fari ne har labulayenta, da center carpet, kai har agogon bangonta fari ne, duk inda suka yi masu camera na biye suna ɗauka, tun farkon fitowarta har zuwa gaisuwa da kuma kawo ta gidan.
A ɗakin da yafi ko wannne haɗuwa aka kaita, kasancewar ɗakuna biyar ne a gidan kuma ko wanne sai da aka saka masa kaya, sai ta hau tsakiyar gadon ta zauna, kanta lulluɓe da mayafi.
Wasu daga dangin ango suka mata Allah sa albarka suka fice, sannan wasu daga ƴan'uwanta suka kama hanya, sai aka bar Maryam kawai sai Raihanatu da kuma wata ƴar'uwarsu Husaina.
Bayan kamar minti talatin sai suka soma jin busa da algaita da kirari irinta ta ƴaƴan sarakuna, shi ma mai nasa video yana biye da shi yana ɗauka. Har aka shigo da shi cikin ɗakin, sai ya zauna bakin gado yana ƙamshin turare, fuskarsa ta sha rawani kamar Mahaifinsa. Abokaninsa sai zolayarasa suke shi ko bakinsa har kunne.
Nasiha suka musu akan zamantakewar aure da kuma haƙuri, masu auren cikinsu sai zolayar samarin suke, wasu kuma na zolayar Abdool wai ango sai sha mai. Sai da suka ga shabiyu ta gota sannan suka musu addu'ah da fatan alheri, sannan suka saka Maryam da waɗanda suke tare gaba, har wasu na cewa suna son Maryam a zatonsu budurwa ce.
[8/5, 7:03 PM] Khadeeja Candy♥: *96*
Bayan abokansa sun wuce Abdool ya tashi ya rufe ƙofor falo ya dawo ɗakin fuskarsa da murmushi, rawanin kansa ya fara cirewa ya aje sannan cire babbar rigarsa.
“Amaryata wacce ta wacce amarya tsada”
Ya kai hannu zai yaye gyalenta, sai ta matsa baya ta ƙara jan gyalen ya sauko. Matsawa yayi kusa da ita ya sake miƙa hannun sai ta kauce hannunta mai zanen lalle ta ziro masa. Murmushi yayi yasa hannunsa aljihu ya ɗauko wani ɗan ƙaramin box ya ɗora mata saman hannu, sai ya miƙa hannun ya yaye mata mayafin. Idonta a rufe fuskarta ɗauke da murmushi
“Har da idon sai na siya...?”
“Ai kace wannan amaryar ta fi ko wace Amarya tsada”
Murmushi ya sake yi sai ya cire tsadadden agogon hannunsa ya ɗora mata saman hannu, sai a lokacin ta buɗe ido ta saka su cikin nashi haƙoranta a washe.
“Kin manta ban siye murmushin ba”
“Maganar ma ai baka siya ba an yi maka nasiha ne kawai”
Hannu ya kai ya riƙa gefen fuskarta yana shafa shi da babban yatsansa.
“Godiya ga Ubangijin da ya mallaka min wannan halittar, lallai na fi ko wane Namiji sa'a a duniyar nan”
“Kana koɗa Namra da yawa, har kana sa tana jin kamar ta fi ko wace mace zama sarauniya”
“Na haɗu da mata da yawa ciki da wajen ƙasar nan amman babu wacce ta sace min zuciya sai Namra, she ko ma ƙaramar sarauniyace ba”
Lumshe ido tayi tana murmushi. Box ɗin ya amsa ya buɗe ya fiddo zobe mai kyau ya kama hannunta ya saka mata.
“I Love you so Much Abnam”
“Na gode sosai”
Matsawa yayi kusa da ita.
“Godiya kawai? Ai hausawa na cewa yaba kyauta tukuici”
Ta rufe fuskarta domin ta gano ma'anar zancensa. Shi ma dariyar ya yi, ya jata ƙirjinsa ya rumgume, a hankali ya sauke numfashi ya ɗora kansa kaman nata.
“Gani komai nake kamar a mafarki, ina tuna lokacin da na fara ganinki irin halin rayuwar da na shiga saboda ke kuma gashu yanzu komai ya zama tarihi, inshallah ni ne mijinki ke kuma matana har Aljanna”
Lafewa ta yi a ƙirjinsa kamar babu wanzuwarta a doron ƙasa, gudun zuciyarsa take sauraren tana auna yada nata zuciyar yake hawa da sauka tare da ta shi.
Sun daɗe a haka sannan ya ɗagota ya mata kiss saman ido.
“Karki min bachi saman jiki kisa na ƙarye”
Tayi dariya tana bugar masa chest.
“Ouuuuch”
Ya faɗa yana kanne mata ido ɗaya. Shi ya fara sauka saman gadon sannan ya miƙa mata hannun, ta riƙa hannunsa ta sauƙo suka shiga bathroom ɗin tare, shi ya fara alwalar sannan ya taimaka mata ita ma tayi suka fito. Sallaya biyu ya shinfiɗa ɗaya a gaba ɗayar kuma tana baya da shi kaɗan.
Mayafinta ya ɗauka ta rufe jikinta kasancewar fafaɗa ne kuma mai kauri. Yana gaba tana biye har suka yi raka'ah biyu, sannan suka sallame. Hannunsa ya ɗaga masa ya riƙa kwaroro musu addu'ah tana amsawa da amin sanna suka shafa, sai ya juyo ya kalleta.
“Hajiya Akwai wata sunnar bayan wannan?”
Ta zare masa ido. Sai ta gurgiza masa kai alamar a'a. Dariya yayi ya tashi ya ɗauko ledojin da gefen gadon ya kawo gabanta ya aje, sannan ya fita daga ɗaga ɗakin gaba ɗaya. Be ɗauki dogon lokaci ba sai gashi ya dawo da plate da cup ta aje a gabanta sannan ya zauna yaja ledar ya buɗe ya fido ƙatuwar kaza ta ɗora saman plate ɗin sai ya mayardar ragowar gajin a gefe ɗaya, ya buɗe madara ya zuba musu a cup ɗaya sannan yasa hannu ɓare kazar ya soma kai mata a baki. Kawar da fuska ta yi tana murmushi.
“Ki taimaki bawan Allah nan ki bar shi ya ciyarda dake a wannan daren da yafi ko wane dare muhimmanci da daraja a gareshi”
“Na hutar da kai, zan iya wannan aikin”
“Ai bana son hutun ne, idan dare ya lula ke da kanki zaki min kukan gajiya ki neman na hutar da ni, amman ba yanzu ba yanzu ai ai ba aiki na ke ba”
Ta ɗan fiddo ido tana kallonsa, sai ya kanne mata ido ɗaya, ba shiri ta buɗe baki tana mamakin yadda yake ƙoƙarin faɗar maganganu kai tsaye. Hakan ya bashi damar saka mata naman a bakin.
Cikin so da ƙauna yayi feeding ɗinta, sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya cilasta mata ita ma ta yi feeding ɗinsa a dole ba dan ranta ya so ba, bayan sun ƙare ya kwashe plate ɗin ya buɗe wardrobe ya fiddo kayan bachi kala ɗaya amman na maza da mata, na matan ya miƙa mata shi kuma ya shiga ƙoƙarin zame kayan jikinsa ya canja zuwa na bachin sai ta zaro ido.
“Wai nan zaka canja su?”
“To miye? Naga an zama ɗaya”
“A'a da saura, bari na baka guri ka canja”
Wani shu'umin murmushi yayi har da cije baki.
“No ba sai kin fita ba, bari na baki guri ki canja nima kuma sai na canja a wani ɗakin ko, ƙina da gaskiya ai ba mu zama ɗaya ba amman mun kusa raba gari”
Ya fice yana dariya kamar ba shi ba. Yana fita ya ɗauki kayan bachi da zimmar canjawa sai ta ga ɗan ƙaramin wando sai wata fikicar riga iya cibiya sai kuma babbar mai kamar rariya wacce zata rufe jikin gaba ɗaya. Mayardar kayan ta yi ta aje taja gyalenta ta ƙara rufe jiki.
Shima irin kayan bachinta ne jikinsa bancanci shi baya da wannan ficikar rigar ƙirjinsa a sake yake. Tana kallonsa gabanta yayi mugun faɗuwa, ta razana sosai kamar bata taɓa ganin ƙirjin namiji a waje ba, yana doso inda take ƙanshin turaren da ya saka ya riƙa dukan hancinta, ko da ya ƙaraso kusa da ita ta rufe idonta gan numfashinta har rawa yake.
“Baki canja kayan ba?”
“Da wannan zan kwanta”
Ta faɗa ba tare da ta buɗe idon ba.
“To tashi ki hau gadon ki kwanta”
“Na fi jindaɗi a ƙasan”
“Ƙasa zamu kwanta kenan”
“A'a kai ka kwanta saman gadon, ni na kwanta a ƙasa”
Duk maganar da sukw bata yarda ta buɗe idonta ba. Shi kuma ya lura da hakan.
“Look Abnam karki tauye kan ki, ni ba baƙon tsanani ba ne, ma zan zo na takurawa masu gida ba, idan kina son kwantawa saman gadon kawai ki kwanta”
Ta yi saurin kwantawa a gurin.
“Ni ko gida ƙasa na ke bachi”
Ya ɗaga gira ɗaya like serious. Ya sauko da bedsheet ɗin ƙasa.
“Tashi a shimfiɗa”
“Dan Allah Abdallah ka bar ni nan”
Ta faɗa kamar mai shirin yin kuka. Sai kawai yayi murmushi ya mayardar bedsheet ɗin ɗale saman gadon ya jefo mata matashin kai.
“Gashi nan kar na matso kuma ki ce wani abun zan miki, amman kin san shure-shire baya hana mutuwa ko?”
Sai a lokacin ta buɗe ido ta ɗauki filon ta tare kanta ta yi rufa da gyalenta. Hannu ya kai gurin kan bed ɗin ya kashe wutar ɗakin. Wani tsoro ne ya ƙara baibayeta, kwatakwata ta manta da irin rayuwar da ta yi a gidan Asim, ta fi jin sakewa da shi fiye da Abdool wata ƙila saboda yanayin hallitarsu ba ɗaya ba.
“Ka kunna wutar man...”
Bata ƙarasa rufe baki ba taji mutun a bayanta yasa duka hannayensa yajata jikinsa ya rumgume ta. Sai ya kawo bakinsa dai-dai kunnenta.
“Shiiiiiiii ba wani abun zan miki ba, kawai dai ba zai yayu nakwana da mace ɗaki ɗaya ba kuma ace mu kwana a rabe ba, kawai ina son jinki ne a jikina that's all”
A dole ya gunɗe bakinta ta rumtse ido, tana jin yana ɗan taɓa ta amman ta haƙura har bachi yayi gaba da ita. Washe gari ta rigashi tashi saboda bachin rabi da rabi tayi ko da aka kira assalati idonta huɗu ba ma biyu ba. Tana unƙurin tashi sai shi ma ya tashi saboda tana a ƙirjinsa ne duk wani numfashinta yana ji balle kuma motsinta.
Sai da ya fara shiga bathroom ɗin yayi wanka da alwala sannan ita ma ta shiga ta yi alwalah, tare suka yi sallah sannan ta koma bachi, shi kuma ya buɗe ƙur'ane dake cikin wayarsa ya soma karatu, ba shi ya tashi daga gurin da yake ba sai da aka buga masa waya aka sanar masa an aiko musu da abinci. Wannan karon Ummi bata aiko masa ba saboda ta san za'a aiko masa daga gidan Mai Martaba.
Sai da ya zuba abinci sannan ya shiga ɗakinta. Zaune ya sameta a gurin da ta yi bachin tana kallon ƙofa.
“Acici daga jin motsin ƙuloli har kin tashi”
Dariya ta yi
“Ai ba kai aka kawo ma abincin ba ni aka aiko ma”
“Ai ba kai aka kawo ma abincin ba ni aka aiko ma, yanzu ai kin kina da baki ko?”
Ya kai kayeta yana wani girgiza kai da kashe murya. Ya miƙa mata hannunsa
“Zo nan muje ki wanke bakin ki”
Kamar wata ƙaramar yarinya haka ta miƙa masa hannun ya tasota, da kanshi ya wanke mata bakin bayaɓ sun gama ya ɗauke ta ya kaita dinning.
“Kai a she nauyi ne da ke, na ji kamar jijiyoyina zasu katse”
Ya faɗa yana dariya. Shi yayi feeding ɗinta sannan yayi feeding kansa. Ko da aha biyu ta yi daga ita har shi duk sun shirya cikin fari yadi mai kamar shadda sky blue. Tana gaban madubi tana kwaliya ya ƙaraso kusa