Showing 24001 words to 27000 words out of 145392 words

Chapter 9 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8145

bayi ko wasu da na fi a duniya, ama su din masu aikina ne, ita kuma jikata ce, yarinyar nan na mutuntani tamkar ni na haifi mahaifinta, a nan tare da mu zata zauna "


Naman goshinta ke dan tatarewa tana kallonsa, ta jima kadan a haka tana nazartarsa, sai kuma ta tabe bakinta tana kawar da kanta gefe ta ce" Ba damuwa, ama sai dai ta zauna a dakin kasa ba nan sama ba!"


Murmushi ya yi a bayane ya mike ya kama hanyar fita , sai kuma ya dakata ya juyo yana kallonta ya ce" Idan kina da fita yau ki ajiyeta gefe ki kula da ita, zan so ki rarasheta dan kin san me ake nufi da abinda aka so yi mata"


A tausashe ya yi maganar, sai dai wani irin gundumemiyar guduma da ta daki kirjinta ta hanna mata kyakyawan motsi ta raka kofar da ya ja mata da kallo


A hargitse ta so mikewa dan bin bayansa, kwata kwatama ta manta shekarun yanzu da na da ba daya ba , sai daa ta ji kafafuwanta sun wani irin rike mata ta saka hannunta tana rike abin gadon hadi da rintse idannuwanta a bayane ta shiga karanta dukkan adu'ar da ta zo bakinta sannan ta koma ta zauna a bakin gadon


Ido rufe ta shiga tunani a cen kasan zuciyarta da tarin takaici, ta zauna? Kar ta fita? Sabon salo kiran sallah da usur, yaushe rabonta da irin haka da shi? Me zata yiwa yarinyar da shekara ashirin da biyar kadai ta bata a duniya? Menene yarinyar bata sani ba? Yanzu shi dan ance an dira mata har wani daga masa hankali zai yi? A tunaninsa zata zauna har wannan shekarun bata san hanyar kashe kishirwarta bane? Itace MAI SHANU zai ringa jerawa wulakanci kala kala dan kawai an santa fa hakuri (🧐), walahi ba zai yiwu ba, bafa zai yiwu ba, bara kafarta ta saki ta sauka ta tarda shi a yi wace za'a yi! Ina dalili wai zai ringa caza mata kwakwaluwa ? Kiri kiri ya ki tankwasa fitinanen jikansa da ya yi gadon halinsa! To daga shi har shi din ba zai yiwu ba, gashinan yarinyar da yake nema ko jiya sai da ta mata maganar daga ce masa kwana biyu bai leka gidansu ba ya daina dan kiran da yake yi mata , gashi ya hannata kiransa kowani time yace baya so yana cikin aiki ko cikin jama'a ko ibada ta shagaltar da shi, wai a haka yana son yarinyar be kowama ya sani? Ita kam ta gaji da fitinarsu walahi!


Baba bai sauko daga dama da wuri ba, sunna nan zaune dai Babar ma'aikaciyar gidan ta zo ta wuce baban dakin kasa da yan mata biyu a bayanta bayan sun gaisa duka shiga gyaran dakin, domin babu mutane ciki ba zai rasa kura ba,
Sai kuma dakin kusa da shi nanma aka gyara tsaf har bayi aka wanke tasss
Sunna gamawa suka bata kys din dakunnan biyu suka ce in ji baba , baban nata ne dayan kuwa na ƴaƴanta


Ita dai amsa ta yi tana shafa kan Hasan da har yanzu fushinsa bai sauka ba sai cije lebe yake yi baya kula kowa
A haka aka kuma kawo masu abinci shake da plate baba da cokula, ga jus da ruwan sanyi aka ajiye masu cike da kula da mutuntawa


Da kyar ta samu Hasan ya yarda ya sauka dan cin abincin, shima dai sai da yace sai dai idan tare zasu ci, a dole ta ringa fan tsakura tana kaiwa bakinta , su kuma sunna ci sunna korawa da Jus


A haka Baba ya sauko, cikin shigar manyan kaya na daraja a jikinsa, sai kanshi yake yi ga hula ya kafa a kansa


Sosai ya ji dadin gannin sunna cin abinci, da kula sosai ya ce" Idan kun gama ku shige ciki ku huta kin ji Uman biyu?"


Amina ta amsa kanta a kasa , biyu kuwa suka ringa yi masa adu'ar a dawo lafiya har ya fice a falon yana amsawa


Gurin Man Liman suka je suka dauke shi da motar suka wuce gidan Iyayenta, watau yayan mahaifinta, wanda yake da dan teburinsa a kofar gidansa, sun tabata ko yayane zasu same shi a gida warhaka, sai dai idan rasuwa ko wajen daurin aure ya tafi, koma ina ne in sha Allah ya yi niyar sai ya hadu da shi a yau


Sun taki Sa'a, sun samu Malan dan iya a gida , a kofar gida yan kukula kayan sana'arsa saman tabarmarsa


A mutunce suka gaisa da junna, domin ya san waye MAI SHANU farin sanni, bai taba zuwa gaishe shi bai masa alheri mai girma ba


A saman tabarmar suka zauna, Mai Shanu na tsokanarsa cewa yaya haka ya tsufa? Shima yana yar dariya da fadin to yaua za'a yi neman na gero kadai ya isa ya tsufar da talaka
Mai shanu ya ce Allah ya dafa mana, suka amsa da amen


A nutse Mai Shanu ya shiga bayanin abinda ke tafe da su, a tausashe da kalar fahimtarwa ya ringa fahimtar da shi abinda yake dauke da maganar , har ya dire aya da fadin" Wannan lamari na damuna Malan, yarinyar nan tana da bukatar taimako sosai, da ace zata samu da hankalinta zai fi kwonciya, ga rainon ya'ya bayan ita dinma yarinya ce"


Malan dan iya da kansa ke sade yana sauraronsu har Mai Shanu ya gama maganar yana ta dannar harshensa da irin magangannun da yake tufka masa mararsa dadi a zuciyarsa, yana kwabar kansa cewa ya bi a hankali dan ya ci ribar zaman ya fuslanci mai Dambu a yannayin da yake tunanin maganarsa mai ma'ana ce ya ce" Haka ne, Allah gafarta malan da Elhaji gaba daya na ji maganar nan, kuma idan na fahimta da kyau so kuke ta dawo gidan nan ta zauna?"










*Page 1️⃣0️⃣*




Baba Mai Shanu ya ce" Kwarai kuwa, zan fi so Amina ta dawo gidan nan ta zauna kusa da mutane, cikin mata da jama'a yan uwanta, zata fi sakewa ta ci gaba da karatunta har Allah ya kawo miji a yi aure"


Irin abin nan na wasu tsofin idan abu ya basu mamaki ko takaici ya yi yana dafe haba ya ce" Aure? Yanzu tsakaninku da huwa rahamanu baku gane yarinyar nan ta gama wulakantar da kanta bane ya sa ta kasa samun miji? To ai mai sunnan iya ko dan gidan na kawota na kawowa kaina fitina da balaki ne, domin a cenma da bata giga ba dan kawai yayansu ya daki kanwarta furduduwa take ko wa? Ta dauki ice tace ko shi ko ita, a haka wani sakarai ne zai dauka ya kai gidan watarana gardama ta hada su ta masa tsinanen duka? Ta zo ta kalli tsabar idona da nace a siyar a raba masu gado a saukewa bayin Allah nauyi a kansu tace aa su ba za'a raba masu gado ba, yarinyar nan a nan na hanneta maganar karatu da tace an ce iyayensu su zo nace me ake da boko? Boko ai lalacewa kennan! Tace da ni ba lalacewa a maganar boko , ilimi ne halal ne a neme shi!, Na kuma yi tataki na mata magana a kan rikon yara har biyu maza, da me zata ciyar da su? Waye zai aureta da yaren nan maza ? Zamanin nan waye zai iya rikon ɗan wani? Ama idona idon mai sunnan iya tace Baba zan iya ka bar min su kawai zan iya! Yarinyar nan gardama a kanta ta sauka kamar a kwakwaluwarta aka rawaito, ni kuwa yaya zan yi na iya rikonta? Ai kawai gidan nata zata koma ta je ta rayu da ya'yan ta ci gaba da gantalinta har ta tsufa, shi kam Uban mai sunnan iya ya yi asarar haihuwa walahi!"


"Subahanalah, subahanalah malan, subahanalah, fal yakul khairan au li yasmut malan, yaya da girmanka da hankalinka malan da kanka zaka yi furuci irin haka? Yau kofa yar zumunka *LALATACIYA* ce ai zaka siranta,, harshenka ya bita da addu'a bale mu zahirinta da muka sani yarinyar tana da kamun kai, ba zamu yi shedar badininta ba, ama abinda idannuwanmu ke gani tana dauke da sheda ta alkhairi sosai, to ni a ganina ai rikon ƴaƴan y'ar uwarta da take yi dan tana da zuciya mai kyau ce, ga jajircewa a wajen baiwar Allahn nan, mai zuciyar alkhairi kan yi mata dan talafi a gareta, ka tausasa kalamanka malan a kan yarka" Liman ya fada cike da jin ba dadi a furucin Uba a wajen Amina


Sai dai su suka san dadin abinda suke hange, basu san shi ya riga ya yi nisa baya jin kira ba sai da ya kara gyara zamansa yana dan kada kafarsa ya ce" Tototo, Aya, Allahu akhbar, kennan Man liman fadin gaskiyarma matsala ne? To Allah shi kyauta, ama ni kam Mai sunnan Iya ta fi karfina walahi, ba zan iya zama da ita ba"


Baba Mai Shanu ya fi kowa jin takaicin bawan Allahn nan, wani irin mamaki ke lulube zuciyarsa da mamakin zumuncin zamani, y'ar zumunka? A gobe kiyama ita zaka gani fa! Itace kake wulakantawa haka? Maganar Liman ce yau ko bariki aka tare a kan yarinyar nan ai zai siranta ya bita da adu'a balle babu wanda zai ce ya taba gani ko ya ga wanda ya gani, shin menene a cikin rikon baki uku kawai? Yarinyarma bata da zubuwa, ko kyauta ka yi mata sai ka zare ido zata amsa, shine har zai kireta da sunnan idan ta gama dadiron? Ta tsufa? A cikin haka? Wannan dan uwa ne ko makiyi ne?


Datijantaka da ilimi da salatin annabi da ya yiwa harshensa kawaya ya saka shi tausasa lafuzansa sosai hadi da iya kiyaye harshensa ya ce" Dama mun zo ne dan mun san a yanzu a duniya babu wanda ya kaika kusanci da ita, kuma babu wanda ya isa ya yanke hukunci ba tare da ya tuntubeka ba, Alhamdulilah tunda har ba zaka iya rikewa ba ni zan riketa, har Allah ya fitar mata da mijin ta yi aure, ko bayan raina na san iyalina zata rike min!"


Malan Liman ya gyada kansa ya ce" Kwarai kuwa, ai ko ni nan zan rike Baiwar Allah mai baban sunna, ka duba ka ga yau a masalaci irin taimakon da suka tara dan ance an tafi asibiti da ita, yanzu haka ana amsar kudin mai dari mai dubu kowa na bado talafi da kuma alkawarin za'a hadu a saka ido sosai dan a kama azalumin dake son karya mana haki a ido, ai in sha Allah yarinyar ba zata tabe ba, sai ta zauna a gidanka Elhaj idan Allah ya fitar mata da miji sai a daura mata aurenta ta yi tafiyarta gidanta"


Da aka ce ko yaya ka yi da jaki sai ya ci kasa haka ne, kamar wanda wannan bawan Allahn yake gudun abin alkhairi da rahamar ubangijinsa, shin bai san falalar shafa kan maraya kadai bane a rayuwarsa bale kyautata masa da cireshi a kunci uwa uba ciyar da shi? Shi dai koda ya sani to fa shedan ya yi galaba a kansa a wannan lokacin da lada ke binsa yana zundumawa a guje tamkar mai gudun fanfalaki, a takarkare ya warware wani nadin na arzikin yana nuna hali ma rashin arziki ya ce" Ban taushi numfashinku ba, ba zaku gane abinda ni na gane dangane da yarinyar nan ba, kamar yadda ta fita daga gidan nan dan ta raina rikona da ikona ta gwamace zama a gidan ubanta haka zata koma yanzuma ta ci gana da zaman a cen! Walahi ba zan barta ta je gidan kowa ta zauna ba! Ba da yawuna ba, idan kuwa wata iyakar tawa zata nuna min bismillah sai na ga idan ta samu mijin wanda zai daura mata shi! Ai ta gani da kanwarta ta min rashin da'a yadda muka kwashe da ita!, Itama bata fi karfin hakan ba, babu abinda ya shafeni da barikinta ko kudinta, idan ta bijire min in na kama tsine mata sai ta bi duniya wa bilahilazi!, Alkawarina ne wanann!, Gwarama ta gyara halayarta ta koma ta kama mutuncinta ta zauna ko ta samu mashinshini, idan har ta bar gidan nan da nufin zama wani wajen sai dai idan da auren wani a kanta ne!"


Daga Liman har Baba Mai shanu ido waje suke kallonsa
Baba bai san lokacin da ya ce da Malan dan iya" Aman Malan me yarinyar nan ta yi maka da kiyaya hala? Ko dai kiyayar ta mahaifinta ce ke shirin shafarta?"


Malan Dan iya har huci yake yi ya cire kansa gefe, irin wannan karron iko a hannunsa yake din nan , zai gwadawa Amina bata isa ba, ita din ba kowa bace , idan tana tunanin ta kai wani mataki ne dan tana da gida banzar bazara ce ita! Ya ce" Ba maganar gaba ranka shi dade, ai na yi rantsuwa ne sai dai idan da auren wani zata je gidansa ta zauna!"


" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, innalilahi wa inna ilaihi rajune, yanzu fisabililahi Malan wannan din ina anfaninsa? Idan fa bata fa maneman a yanzu? Shin baka gane cewa ana so a yaga mutuncin yarinyar nan bane ko me? Wani irin uba ne kai? Anya zaka so a yiwa ƴaƴan cikinka?" Liman ya fada da jimami yana kallon Dan iya


Dan iya ya tabe baki ya ce" Liman ba zaka gane ba, mu mutanen karkara munada namu ka'idojin da ba'a takewa, a shekarun fa ta tara kadai laifi ne a kauye, tana yawo waje waje , bata zauna ba, baka san yaron mai garin garinmu sai da ya fito aurenta ba? Mahaifinsa ne da kanda yace aa wannan din ai ta tsufa sai dai ya nemi wata, wannan abu ya min ciwo a rayuwata, kwata kwata bata da sa'ar rayuwa ne!, Da yanzu ta malaki shanu uku ko hudu nata na kanta!, Sai karyar bokon tsiya, wannan din itace maganata, yarinyar nan ba zata je ko'ina ba ta koma ta zauna, wani mutuncin kuma? Kai ni fa dai na rantse bata da shi , kai baka ga rawar kanta ya yi yawa ba?"


Baba mai Shanu tunda ya rufe baki da hannunsa yana kallon larkararen rashin ilimi da shirme ya kasa furta koda A ne, yana kallon yadda Malan ke iya kokarinsa dan ya dawo da Dan iya hanya, ama abin ya gagara, du inda ya bila sai ya bile, irin girman zumunci yake nuna masa da irin alkawarin Allah a kan wanda ya yanke zumunci, ama sai ya zile ya nuna masa ai yarinya ta lalace ba za'a iya talafa mata ba, Liman har zufa yake yi, gardama da mai lafiya ce da ita, domin ba za'a kirayeshi da jahili ba yana da nasa sannin daidai gwargwado!,


A sanyaye Baba Mai shanu ya ce" Ka yi shiru abinka Liman, ba fa zai saurareka ba"


Sai kuma ya fuskanci Dan iya ya ce" Shin yaushe ka yanke aurar da ita? Ina nufin zaka iya bata koda kwana uku ne ta dan saku daga wannan tashin hankalin a gidana? Idan ya so ni zan dawo maka nan da kaina da maganar aurenta, domin nima alkawari na daukarwa kaina ta gama zama a gidan nan ita kadai!"


Dan iya kallon Baba mai Shanu yake yi, so yake ya kara kafewa ya kara zilewa, sai dai gaba daya mutumen yanzu da ya zo masa a tausashe sai ya kasa yi masa musu


Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Ai ka isa da ni Elhaji, ba damuwa tana iya daukar har sati daya ta huta din, duda na san karya ne bata da wata damuwa, ama bayan nan idan bata samu mijin ba ta tatara ta koma rayuwar ta da, ba zata hanna kowa zaman lafiya da gidansa ba"


Malan Liman gyada kai yake yi yana karra kallon mutumen, Baba Mai Shanu kuwa harda godiya da nunin ya gode da akai masa wannan alfarmar


Ai kam kamar ya sani, alkhairin aka yi masa mai tsoka, yan dubu dubu sababi dal kafin su tafi, sunna daukan hanya shima ya dauki tasa hanyar ya nufi kasuwa dan ya yi sare sare, ba zai yarda ba matarsa ta ga kudin nan ta rabashi da su da jarabar lalurar yara!




Mai Shanu ya jima a wajen su Malan Liman sunna tatauna maganar nan, karshe suka rabu bisa shawara daya tak, wace ta yiwa Malan liman dadi har cikin zuciyarsa, ya kuma dauki alkawarin daukan kwana uku yana fadawa Allaj da sake neman zabin Allah a kan lamarin


Koda ya koma gida wajen hutunsa ya je ya dauki alkur'aninsa ya shiga tilawa, dan sosai zuciyarsa ta tabu da wannan lamari, hankalinsa ya tashi sosai da wannan abu, tausayin kansa ke lulube shi, da tunanin abinda dan Adam ya zama
Baima koma saman hajia baba ba, bai sani ba dan rikewar kafar nan harda su docter ya zo ya dubata tana ta zubawa jikan shagwaba a waya ya mata alkawarin zuwa ya dubata shima, danma tafia ce ta fado masa wace dole shi da kansa zai je, a kan maganar taki ce da yake son buda kampaninsa na kansa dan ya fara fitar da takinsa yana siyarwa sannan yana anfana shima waa kansa


Sarai Baba ya lura maganar da ya mata kan ta ja yarinyar a jiki bata yi, hasalima tunda ta yi wunin dayaa bata fita ba a na biyin shi da kansa da ya sauko bai sameta a gidan ba,
Bai nuna damuwarsa ba ya kama hannun biyu suka wuce da kansa ya masu rakiya makaranta sannan ya bada damar idan baba Lauratu ta zo a barta ta shigo wajen Amina dan ta fada cewar a jiyama ta zo bata samu shiga ba, da wannan Amina ta wuni tare da baba dake karra tausarta da nuna mata hakan ya fi mata alkhairi, kuma da ta ji baba ya mata shiru a kan tafiyarta gidan yayan mahaifinta itama ta yi shirun kawai, ta tabata zai waiwayeta ko me ya yanke, sosai ta yi mata nasiha cewa ta yiwa matar gidan biyaya, ko menene ta tabata idan har bata taka dokarta ba ba zata wulakantata ba, kuma fa ba laifi tana da dan mutunci fa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login