Showing 120001 words to 123000 words out of 145392 words

Chapter 41 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8144

yana gyara zamansa ya ce" Anya wani ya isa ya fada min bayan ni kadai na diga abina?, Sai dai na fadi ranar da lokacin da tsayin lokacin da ya dauka, Allah dai ya fido shi lafiya"


Kukan da yake ta so ya ganin ne aka fashe da shi, ta nuna kanta, sannan ta nuna shi ta ce" ABDUL, ni kake wulakantawa ko? Ba damuwa Ai damarka ce, ka wulakantani son ranka, ni ga banza ko? Ai na laifi samu ka yi ABDUL, kuma babu inda zani!"


ABDUL yana kallon fuskarta da kukan da ba hawaye ya yi dan murmushi kasa kasa ya ce" Ai ba damuwa idan baki je ba ni sai na aunaki a gida,sai an jima Amina"






Tsuru ta masa kukan na daukewa cik, itace Abdul ke wulakantawa haka? Jama'a ga mari ga tsinka jaka? A guje ta juya tana sake fashewa da wani kukan Bilhaki, wanda ya saka shi dan mikewa kadan yana kallonta har ta bacewa ganninsa ta shige bangarenta


Labulen ya saki ya dawo a ransa yana Adu'a kamar haka ' Ya Allah, ka kare min ita da abinda ke cikinta, sam bata bi a hankali , gudu fa take yi da cikina a jikinta"






Amina naa shiga falonta ta karasa wajen Fido ta fada jikinta tana kukanta hadi da neman yin burgima


A rikic Firdausi ke tareta dan kar ta jima kanta ciwo tana fadin" Aunty, subahanalah aunty lafiya?"


Amina na kuka ta ce" wai ni ce zai ringa kora?, Nice zai ce na je awo ko ya ringa aunani a gida?, Nice zai ringa wukakantawa dan ya rungumin wanncen abar kamar karauki tana tafe frikyau firkyau kamar diban raba? Duwawu a shafe kamar bayan plat sai wasu shangalalun hannaye kamar kanlemun fara cici kashi?"


Firdausi ta kwalalo idannuwanta cike da alj'ajhabin wannan ba'a layayiya ta ce" Awo na me aunty? Aunty, wayo Allahna aunty ko dai ciki ne da ke?"


Cak ta tsayar da kukan tana zarro idannuwanta tana kallon Fido ta ce" Ciki kuma?"


Firdausi ta kureta da kallon itama ta ce" Eh mana aunty, na ji kina cewa an ce ku je awo, kowani abu ne za'a auna? A sanina ciki ne ake zuwa awonsa asibiti ko?"


Amina ta sake hade fuska ta ce" ciki kike min fata ne ke?"


Firdausi ta sake zubawa karfin Hali irin Na Amina ido,kafin ta ce" Aa, Aunty ana zancenma? Ai baban farin cikina da na twins a duniyar nan ki bamu baby, baki ji yadda muke fatan gannin haka ba"


Amina ta shiga tureta daga jikinta tana silalewa kasa ta ce" Ta yiwuma bakinku ne ya kamani, ta yiwuma kunne kuka min fatan nan abin nan ya sameni, shikenan na shiga uku kin sani Fido, ciki ne na kanina a jikina Fido"


Firdausi ta shiga tafa hannu ta kwashi kururuwar da ta saka Amina yin wuki wuki tana kallonta


Salati take tana salamewa da sanarwa ubangijinta, a rikicen da gangan ta ce" Wannan da ace su Uma da rai har sai sun sakaki a ukun da gaske, mijin naki kike wani cewa kannenki? Yo ko kin bashi shekarun haihuwarsa tunda ya zama mijin ki ai komai ya kare, Kunya? Abin kunya? Halal din? Allah ya rabamu da abin kunya, kuma walahi kinga awo ko? Tsaf zamu je awo gobe, ni nan zan rakaki abinda yace shi za'a yi gaskiya, kuma a dai ringa tunawa da mutuwa, idan ta zo a hali irin haka ai an shiga uku , me za'a amsa a gaban Allah? Mace marar yiwa miji biyaya ake sak, kuma dai ai an yi islamiya an san makoma, ko shi yasa kwana biyu ba ruwanki da kowa kike ta masifa? Mu kam abin dadi ya same mu sai sallah da sanarwa ubangiji walahi aunty , haba dai ai godiyar Allah ya dace ba wai a nuna rashin gldiya ba"




Har baki Amina ta kama da mahaukacin Mamakin Fido ta ce " Ke, kin ci kaniyarki,na ce kin cikaniyarki kin ji? To sai ki kaini asibitin na gani!"


Ta mike ta wuce ciki tana fafa tamkar zata ari baki


Firdausi kuwa ta yi tsit sai da ta shige ta mako kofar sannan ta mike tana dariya hadi da zagayawa tana sake godewa Allah


Karshema dakinta ta wuce ta shiga duba abinda zata saka na fitar da zata fara yi a gobe, har Allah Allah take yi goben ta yi, a jiyama har yar dariya Yaya ABDUL ya bata da ya yi maganar ida, wace idar kuma ita da ta yi jinnin haihuwa? Ai an wuce wajen kawai kowa ya yi ta kansa, ita dai yanzun zata maida hankali ne ta gina kanta da taimakon ahalinta, namiji kuwa sun yi hannun riga da shi, ai an gwada tunda ba riba an hakura


Wainar Baba ce ta raba dan Amina fushi take yi, Baba kuwa ta tsaya a kanta da jan ido ta ja rantsuwar gobe da sasafe maza a shirya a je maganar miji , idan ba haka ba ai ta san ana mutuwa kuma ba'a yafewa kowa ba!


Kukanta ta sha, kuka da biyu, dayan abinda ke mata ciwo wai ita ABDUL ya kora, dayan kuwa na zuwa awo ne


Da kyar ta yi barci, haka kuma safiya na yi Firdausi ta tasheta, lahadi ne ama da yake clinik ce, kuma ya san da zuwansu haka ta shirya rai bace suka tafi asibitin ta su Mansur


A asibitin sunna karasawa Muhammat ya fita ya shiga ciki


Jim kadan ya fito tare da Mansur din da waya a kunnensa yana magana yana tsaye gefe guda


Muhammat ya daka hannunsa ya bude gefen da Fido ke zaune yana fadin" Bismillah kanwata ku fito "


Firdausi dake karra tausar Amina tana yi mata maganar ta daina to hade ran ta fito da dan gudu sakamakon daga hannun da Amina ta yi tana cik alwashin sauke mata biyar a kumatunta


Birki ta ja tana kallon barin da MANSUR ke tsaye ta ce" Ina kwana?, Zata fito yanzu in sha Allah"


A hankali Mansur ya dauke dubansa daga kanta yana maidawa kasa, dan haka kawai ya ji haka ya dace ya yi , sai kuma ya dago da murmushi yana jin furucin ABDUL dake Fadin" Mansur, ka ga idan docter ba zata dawo yanzu ta duba min mata ba kawai ka sakata a office dinka kai ka fita ka tafi wani office din ni na zo na aunata, kar ka bari wani kato ya mata tambayoyin da bai bata ajiya ba, ka ga rantama a bace yake, inaga ba zasu wanye lafiya ba fa?, Docter ita ta san yadda ta vi da ita wancen karronma , kawai ka nemota zai fi"


Docter Mansur na murmushi ya ce" Ka ga wasa fa nake maka tun jiya na sanar mata, yau bama ta aiki ama tuni ta zo tana office dina , su ladai take jira ta tarda mujinta da ƴaƴanta park"


Ajiyar zuciya ya sauke mai dan dumi ya datse kiran yana dan sosa kansa a hankali da jin haushin nemansa da fitinar da Mansur ke yi, shi kuwa sai ya wani manta komai ya biye masa su yi ta yi kamar wasu yara ƙanana
Koda yake gaskiya ba zai iya lamuncewa a yiwa iyalinsa dala dala ba! To ai bama kyau hakan a adinance




Sun ga likitar, sosai suka zanta cikin hikima da iya aiki,
Abinda docter ta fuskanta ya sakata fara dauko strategi na sakawa Amina cikin nan a ranta, ko tace na bayana mata tsantsar kaunar da take yiwa cikin ama takw dannewa dan wani dalili nata, domin uwa ba zata taba kin cikin dake jikinta ba ko a wani irin hali, sai dai wasu lokutan wani tashin hankalin kan dane soyayar , idan ya yi mugun karfi harma yakan rinjayi soyyayar, sai wani gyara na Allah


Hotunnan da ta ringa hasko mata na yayan larabawa da turawa cikin kyan kama da kyan shiga, da yayan hausawa cikin kyan shiga da yannayi na farin ciki, da tarin kaunar dake idannuwan iyayen ta ringa kallo har suka gama bayan ta tabatar batada wata matsala na laulayi da ya wuce cin abinci da barci, ta karra mata nasiha sosai a kan yadda zata kula da kanta sannan ta fada mata ainahin lokacin da zata fara awo mai sunna awo, ama kafin nan ko me ta ji marar dadi to fa ta dawo ko ta yi kiranta ta sanar mata bama sai Sir ya sani ba, sunna iya yin magana a tsakaninsu


Sosai ta sakata ta saki jikinta da ita suka cenza number sannan suka fito ta rakata Ofice din Docter Mansur domin Fido na cen zaune tana jiranta


Sunna zuwa suka tarar da Fido din zaunenta ga su jus a gabanta ama bata dauki ko daya ba, hasalima kamar a takure take a zaunen da take har suka zo ta mike suka yi masa salama suka wuce dan zuwa wajen da zata fara nata karatun da sauransu


Kwonci tashi, a hankali Amina ta ci gaba da rainon cikinta,
A fannin ci, da sha, da sutura sai dai tace abin har ya wuce tunaninta, daga gidan Baba mai shanuma ya zamto bini bini za'a turo mata da kayan kwalam da makulashe, irin abubuwan kwadayin da wasu har mamakin inda aka samo su ke kamata, haka kuma du ranar Juma'a Baban ne da kansa da Hania zasu zo gidan, duda ba maganar dake hadasu da Hajiar sai tsatsareta da ido da zatana yi da yawan fada mata ta ringa kiyayewa , ta ringa cin abu kaza ta daina cin kaza, daga hala ba wata hirar kuma a tsakaninsu, karshema takan tafi lamuran gabanta ne sai Baba ne zai baje abinsa ya wuni a gidan a sha hira tare, kuma harda Risala yake sakawa a kirawo yana tsakiya abinsa idan ya dauko wannan hirar ya tsoma su baki daya, wanin su amsa gaba dayansu, wannin kuwa wata ta yi shiru, kowace dai da kalar nata isar da kalar nata nuna kulawar da sauransu, har sai yama ta yi a mayar da shi gida abinsa, wani lokacin Biyu su bi shi, wani lokacin kuwa su kiya su nuna gobe asabar abansu na gida zasu buga game da shi


Abinda ke damunta kuwa ta gwamaci barawa kanta a zuciyarta, domin bata san me zata fasara haka ba


Kiri kiri ABDUL ya dauki kwananta ya hadewa Risala
Babu abinda ya dame shi da ita
Ba gaba yake yi mata ba, ama kuma babu irin wancen kulawar
Rabonsa da ya shiga dakinta tub ranar da aka samu matsalar nan a gidan Baba
Tun daga ranar tana tunanin ko dakin biyu ya daina shiga ya masu addu'a
Gaba daya ya yi watsi da ita
Abinda yake mata a rayuwa shine ci, sha sutura, bayan wannan idan ka ga ya mata magana ido da ido dan ya tambayeta ne yana fatan cikinsa lafiya kalau? Yana fatan tana tune da ranar awonta, awon da ya fita irgen lokacinsa, har mamaki take yi a kan haka


Risala sai tunkaho da daga kai take yi mata a cikin gida, domin ba dai an fada mata ba, da idannuwanta ta isa ta gane miji ya mayar da ita banza a cikin gida, gaba daya ta zuba masa ido ne, jira take yi ta haihu sai ta bashi gidansa ya yi yadda yake so da wadda yake so!


Yau kwanakin watan musulunci ashirin da daya, haka watanin cikinta wata bakwai ne
cikinta ya riga ya fito da kansa, ba maganar buya, domin ko tafia take yi shine a gaba, shi yasa sam bata fita in ba abu ya zama dole ba balema irin girman da ya yi ne abin a dubeta a yi mata sannu, dan ya kai girman cikin da ya isa haihuwa, shi yasa take komai a hankali da kuma lalaba lafiyarta, idan Baba ya zo nema yake sakata dole yawatawa a cikin gidan wai su je su yiwa ma'aikata ziyara, ba dan ta so ba, a dole take binsa dan bata da yadda zata yi masa


Ya zamana a yanzu ABDUL kan ajiye fitar juma'a koda bayan sallar juma'ar ne ya yi tsaye daga dakinsa yana hangensu
Yakan yi murmushi mai taushi yana kallonta n cikinta
A irgensa, nan da wata biyu da yan kwanaki abinda ke cikinta zai fito duniya , shima zai rungumi baby a hannunsa daga Aminansa
Harta da ranar da aka bata a asibiti na haihuwa ya ware sati kafin ranar, da kuma sati biyu bayan ranar, koda takan haihu kafin lokacin, ko kuma bayan lokacin in sha Allah, ba zai fita ko nan da nan ba bi'izinillah, zai zauna kusa da ita har ta sauka ........ In dai yana raye




_________________________________


Kamar yadda aka saba, sabon sati na sabon watan watani takwas din Amina da ciki


A juma'ar yau falon nata ya dauki Harda ABDUL ne, sakamakon zazabin da ta tashi da shi, wanda Firsausi kafin ta fita ta sanar masa, domin jikinta da zafi sosai, gashi ba'a so mai ciki da irin haka, dan yana gagawar ratsa babyn da ita kanta, yana haifar da matsala


Daga kicin ta fito rike da plate din da ta je ta yanyankowa su Baba fruits ba tare da sun san abinda ta shiha yi kennan ba, da Hajiar da kanta ce zata hannata, domin Hajia bata hada cikin nan da komai a duniya


A hankali ya mike ya nufeta dan amsar plat din, domin baba ne ta ciko, kuma tafiyarta kanta wata iri ce baiwar Allah, gajiya na tatare da ita a bayane ba a boye ba


A hankali ya rike Plat din hadi da hannunta, hakan ya sa ta dago manyan idannuwanta ta saka cikin nasa, dama abinda yake bukata kennan


A saman lebensa ya ce" Yaya jikin ki?"


Amina ta lumshe idannuwanta itama a saman lebenta ta ce" Ya dameka ne?"


ABDUL ya tsatsareta da ido ya ce" Ya fi damuna fiye da kowa a duniya "


Amina ta tabe bakinta, kasa kasa ta ce" Ka fafi gaskiya , ko kana tunanin Risala ke gabanka?"


Idannuwanta ya tsatsare da ido, so yake yi ya ga abinda Mansur ke fada masa dangane da ita da shi, ama shi a kulun ganu yake yi bata ra'ayinsa bata ra'ayin kasancewa kusa da shi


A hankali ya budi Baki zai yi magana Kukan Fido ya karade wajen, ta shigo da gudu hannunta saman kanta tana kuka, ta rasa ina zata nufa domin Hajia dai ta san ba wace ke ra'ayin janta a jikinta bace


Da sauri ya Rike Amina gannin zata je da sauri Wajen Fidon da ta nufi Baba da ya mike yana kiranta da salalami yana tambayarta lafiya?


Zaunar da Amina ya yi saman kujera sannan ya dubi Fido dake kukanta hankalinta tashe tana wani irin haki


ABDUL ya ce" Firdausi menene kike kuka haka, zo nan taho nan na ji?"


Firdausi ta karasa inda yake ta duka kanta a kasa, Hajia dake dadana wayarta ta dan dago ta sake duban Fido, ta sake maida kanta kan wayar tana ci gaba da dadanawa


Firdausi na shashekar kuka ta ce" Dady, wai , wai Mudi ne ya tarda ni cen wajen koyon girkina, yau muna koyawa baki ne , muna tsakiya da aikinmu ya cewa security wai shi mijina ne, aka barshi ya shigo, a cikin mutane ya ringa zazagina yana ce min wai karuwa ce ni na kashe aurena ina yawon cakuduwa da maza, na kashe masa ya'yansa har biyu ina zaune ina yawon ta zubar, Dady ana rikeshi yana fadin a barshi sai ya yi ajalina, da kyar Bintu ta fitar da ni a motarta ta kawo ni gida "




Da mamaki ABDUL da ya mantama waye wai Mudi, dan shi ba wani rike sunnan yaron ya yi ba ya ce" Mudi? Tsohon Mijinki Kennan?"


Fido ta gyada kanta tana sake tare hawayenta


Amina haka jikinta ke rawa, wata irin dunkulaliyar Ashar ke makale a wuyanta, wace a zaunen da take gwara ta saka ihu da ta yita, domin irin zaburariyar ashar din nan ce mai sakawa a maka kallon lalatace komai girmanka da darajarka, ji take tamkar ta hira ta je inda yake yau ta kwakulo idon marar kunya!


ABDUL da bacin rai ya dubi Baba dake tambayarsa wai yaron nan bashida kunya ne ko me yake nema da mutane ne kuma?


ABDUL ya dan dantse lebensa na kasa, sannan ya saki ya ce" Bashida kunya, kuma bai gane an kyale shi ne dan takardar rashin kunyarsa bata kai inda za'a yi fito na fito da shi ba, ama yanzu na amshi tayin, ina zuwa!"


Mikewar da ya yi daga zaune ya saka Hajia mayar da wayar gefe tana kallonsa a tausashe ta ce" Honorable ina zaka je?"


ABDUL ya dakata dan ya dan shine ai Honorable din dai da Hajia ke kira kulun, Aminama da ta fara murmushi tana jin inama a je da ita ta ga yadda ABDUL zai ci uban dan iskan cen dakatawar ta yi tana kallonsa ta ji ya ce" Zan je na dawo ne"


Hajia ta yi murmushi tana fadin" Koma ka zauna, kai da matarka bata da lafiya?, Wannan ai ba aikinka bane, ka ga ya kule kansa fa yaron da kansa, tunda yace zai halakata a cikin jama'a, kuma ya je har wajen da yake na gidansu ya zageta, tunda wajenka ne kai kuma Uba kake a wajenta, sannan ya yi karyace karyace da yawa.......ka barshi kawai ya kule kansa ai"


Alkali ya zuba mata ido, yadda take maganarta a nutse hankali kwonce ya san abin kansa zai karkato


Ai kuwa ta dube shi tana daukan wayarsa da sam bai cika anfani da ita ba ta mika masa ta ce" Alkali kana ji jikarka za'a kashe, ka dan yi wani abu mana"




Amina dake zaune sai da ta ji kamar numfashinta zai katse dan wani abu dake ratsa mata zuciya da jiki


Alkali kuwa murmushi ya yi yana dan rage girman idannuwansa dan ya lalubo sunna, ama ya kasa a dole ya mikawa Amina da ta fi kusa da shi ya ce" Uman biyu, lalubo min DPO Mustapha na sojojin ba polisse ba"


ABDUL ya saki murmushi yana gannin yadda Amina ke danne dariyarta, wada karars ya fahimci dariyar farin ciki take son saki ama tana hanna kanta har ta lalubo ta dannawa Baba kira sannan ta kara matsawa tana sauraron maganar da Baba da DPO


Tsaf Baban ya gama bayaninsa, amsar da DPO ya bayar da tambayar su Hajia da Honorable ya saka ABDUL sake yin murmushi, watau gaba daya makaraban Hajia Honorable suke kiransa, bayan kasa ya gama nikawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login