Showing 114001 words to 117000 words out of 145392 words
Chapter 39 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
kai koshi, domin yanada yawa a nanage yake, ga ruwa gefe na goran da ABDUL ya bata ajiye ta dauka ta kora tana jin yanzu kam batada wata matsala a duniyar da ta wuce maganar ciki,
Murmushi Baba ya yi zuciyarsa cike da farin ciki ya sake mayar da dubansa kanta bayan ta gama shan ruwan tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa domin cikinta ya cika ba laifi ya ce" Su Uman biyu sai kike dubi tsabar idannuwan kakar gwamna kika nuna bakya son jikanta da dan tayin shalelen da na tabata idan har kakar geamna ta yi tsayin rai sai kun ga kauna gannin idannuwanku tsakaninta da dan jikanta, shine nake shan dariya, oh dan fari kam sai shi"
A hankali ta fara shashekar kuka tana jan hijabinta ta kai wajen fuskarta tana sharewa
Tsakani da Allah wata irin kunyar baban ce ta kamata wace a dazu bata jita ba
Maganarsa ta doketa fiye da tunaninsa
A hankali tana shashekar kukan ta ce" Baba, ni fa ba wai cewa na yi na tsani kowa ba fa baba, kai ai ka sani Baba"
Baba ya gyada kansa yana fadin" Na sani sosai Aminar Gwagwo, nima ai na san zakiji kunya , to ama kuma abinda na gaza ganewa ta menece kunyar?"
"BABA Abdul kanina ne fa......" Ta fada tana rushewa da kuka
Baba ya kama bakinsa a hankali ya ce" Toh fa, haba ni kam nace kukan nan da kika samu Uman biyu ba kalau ba, ashe dai na gane, To Allah ya baki hakuri share hawayen mu yi magana kin ji?"
Kai ta gyada tana share hawayen tana sauke ajiyar zuciya
Baba ya sauke ajiyar zuciyar shima, yanzu kuma sai kalar damuwa ta bayana a fuskarsa
A tausashe ya ce" Shin dama bakya son hadin nan kika yarda na yi? Ko wani abu yake maki na cin zali ne ban sani ba?"
Amina ta rasa amsar da ta dace ta bashi, kanta a sade ta samu kanta da gyada kai da kuma girgizawa lokaci daya, irin amsar da mutun zai rasa me kake nufi, watau ita kanta a cikin rudun amsar dake zuciyarta take
Baba ya karra tausasawa ya ce" Amina, ba zaki iya zama da Aban Biyu bane? So kike ya sawake maki ne?"
Haba, kofa itace yar fari a wajen iyayenta ta dan halaci
A duniyar kaf bayan rasuwar iyayenta Baba shine wanda ya fara talafata, sai Baba Lauratu, sai daidaikun datijan anguwarsu
Mutumen da bai kyamaceta ba, bai nuna mata bambamci dan tana talaka ba, karshe yake cin abin hannunta da take jan ruwan rijiya ta girka masa, ya zo ya hada aure da ita da gudan jinninsa kwalin kwal wadda itace zata fadi girma da soyayar yaron a zukatan kakaninsa, idan ta bude baki a karro ba biyu ta yi wata wautar da kanta zata ba kanta amsar abinda ya dace da ita
A yanzu haka abinda yake faruwa tsakaninta da bawon Allahn cen ma gidan cen zata ce a maza da ta sani babu wanda ya kaishi kima a idannuwanta
Kawai ita dai bambancin shekarun nan ne baban damuwarta , bayansu batada wata damuwa da shi
Baba ya sake tausasawa gannin ta lume a tunani ya ce" Idan har wannan din shine burinki, ki sani, ni Uba nake a wajenki, da farko zan fara baki shawarar ki je ki yi nazari, ki yi dogon nazari na rayuwa, ki sani koda kin rabu da Abdallah ba zaki koma gidan cen ba wannan alkawarina ne, ni zan zame maki gata a gidan duniya har na bar duniya, kar ki yi tunani a kan kaka naka yi ta rayuwa , ina nufin ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, muhali, da dukkan hutun da ya dace........tunanin da zaki yi shine na mutuncinki, abinda yake cikinki, yayanki dake kiransa Aba, uwa uba shi din da kansa Amina......., Ki yi tunani a kansa da kansa kin ji? Ki auna ki gani, shin wannan mutun ya cencenci zama da ke? Na san ke ba jahila bace, ba zaki yi riko da karfi dan kar ace ba, ki saki maganar kar ace, ki gyara Amina............. Kar ki manta komai girman abinda ke tare da na farin cikin da kike sama masa wata na iya bashi, haka kuma wannan baban abin dake tare da ke mai daraja mai mahimmanci kina iya rage kimarsa a zuciyar mahaifinsa............., Idan har kika yi tunanin nan kika yanke hukuncin ba zaki iya zama da shi ba, in sha Allah zan sama maki nutsuwar zuciya kin ji?"
Amina da kanta ke kasa bata iya yin kwakwaran motsi ba tana sauraron Baba
Baba ya sake maimaita cewa " Uman biyu kina jina kuwa ?"
A hankali ta gyada kanta tana sake sauke ajiyar zuciya
Baba ya ce" Zaki je ki yi nazari a hankali ko?"
Kai ta gyada tana sake sada kanta
Baba ya yi murmushi ya ce" Masha Allah, ki cire damuwar komai a ranki kin ji? Zamanin nan da shegema am daina boyewa bale dan Abdul? Ai ni nan in fada maki shagali kawai da kakar Gwamna, na tabata yau idan ta fara sadaka harda ni"
A hankali Amina ta samu kanta da yin murmushi, domin irin yadda Baban ya yi dole ya saka ka darawa
Dan shiru ne ya biyo baya, a lokacin Hajia ta sauko daga sama da waya a kunnenta tana amsawa ta nufo falon ta karasa kusa da Baba ta zauna wayar a kunnenta dai tana amsa abinta
Baba kasa kasa ya ce" Ai in fada maki inaga harda party zamu sha"
Amina ta sake sada kanta gabanta na faduwa, tsoro ya cikata, tana ji kamar zata tashi sama dan tsoro ta tsere
Hajia na gama wayar ta sake Bin Amina da kallo sannan ta kalli Baba ta ce" Ita kuma me yasa bata bi mijinta ba?"
Baba ya yi murmushi ya ce" Zantawa muke yi, kin san yar dakina ce , zancen sirri muke yi ai"
Hajia ta tabe bakinta tana sake kallon kafafuwan Amina dake nanade ta ce" Ki mike kafafuwanki , ki daina dogon zama a haka, kuma kin ga miyar bikin nan da magi da komai kika tashi kika ci, ki daina haka yana da ila wa mai ciki kin ji?"
Cike da kunya da tsoro Amina taa gyada kanta tana sake sinne kan nata
Hajia ta dubi Baba ta ce" Kun gama sirrin ne Alkali?"
Baba ya dubi Amina ya ce" Uman biyu, mun gamaa sirrin ?"
Da sauri ta gyada kanta
Baba ya ce" To bakua marmarim waina, ko dambu, ko kauco, ko tafasa, ko agwaluma, ko rake dai da sauransu? Ko madasho bakya son ci?, Idan kina son daya ki fada sai Kakar Gwamna ta maki ko a siyo maki kin ji?"
Da mamakin Baba da neman rigima ta kafe shi da ido, tana jira ta ji saukar masifar matarsa kan yace wai ta mata abu ta ci? Sai ta ji shiru, asalima itama kallonta take kamar mai jiran amsarta
A sanyaye ta ce" Bana son komai Baba "
HAJIA ta dauki wayarta ta yi kiran Baba direba
Minti kalilan ya shigo, ta dauki kudi ta bashi tace" Ka kaita gidanta, wannan idan ta ga wani abin a hanya ka siya mata yadda zai isheta, Ke tashi ku tafi gida mana yama na karra yi"
Cicibawa ta yi ta mike tana kallon dabinonta da ya rage ta kasa dauka har sai da Baba ya ce da Baba direba ya daukar mata yana murmushi suka fice
A cikin motarma kanta a hade da jikin madubin motar ta lumshe idannuwanta tana jin maganar direba sai tambayarta yake yi me za'a siya? Ama ta kasa bashi amsa har ya gaji da yawatawa da ita ya kaita gidan
Tana fitowa daga mota Twins dake buga balll suka nufota da gudu sunna murnar dawowarta
Hasan ya ce" Mama, kin ga wai ball dim da dady ya siya mana? Mama dady dinmu yana sonmu, muma muna sonshi Mama"
A zabure ta kalle shi, Husaini ya katse mata kallon yana fadin" Bakiga fadan da ya yiwa prncipal din makarantarmu ranar da kb yace wai mu kamar shegu bamuda uba ne? Yace mata laifinsu ne da basa tsawatarwa yara har yaro ya iya fadawa dan uwansa haka sunna kallo, daga nan ai ya ciremu a makarantar yace shine ubanmu!"
Numfashinta ta ringa ji yana mata sama da kasa
A hankali ta ce" A makaranta ya cire ku?"
Husaini dake rike da hannunta jin yannayin muryarta ya dago dubansa yana kallonta ya ce" Mama bakida lafiya ne?"
Amina ta girgiza kanta ta ce" Mura nake Fadeel, nace a makaranta ya cire ku?"
Hasan ya ce" Eh mana mama an jima ai, an sakamu a wata baba mun je da uncle ya biya komai kuma Dady ya je ya gani yace ta masa, sai ake yi mana lesson akace sai mun yi lesson na wata guda kafin mu shige aji da sauran yaren Ko Husaini?"
A hankali ta dakata tana fadin" My boys, ku tafi ku buga ball din mana"
Kai Husaini ya gayada ya tafi da gudu, Hasan kuwa ya sake zuba mata ido kadan, sai kuma ya saki hannun nata ya juya a sanyaye damuwar yannayinta na kama shi
Sai da ta ga sun fara buga ball din ta idasa karasawa bangarenta ta kama abin budewar ta bude ta shiga falonta
Nzl 48
Sai da ta ga sun shiga buga ball din sannan ta karasa bangaren nata ta kama abin budewar ta bude ta shiga tana jin tunaninta na sake harhade mata
Daga kicin take jin dan motsi, bata nufa ba dan ta tabata ba zai wuce Fido ke girki ba , ya zama hajiar girke girke na gargajiya tana ta dura mata bata san abinda ke tare da ita ba, du sunna tunanin cenjin yannayi ne , basu san abinda ta kumsa ba
Dakinta ta shige ta rufe ta karasa bakin madubi a hankali tana cire hijabinta
Rigar dake jikinta ta lesh ta ja zif dinta kasa a hankali tana kallon kanta a madubin
Jikinta ta zubawa ido, kan cikinta
Shafewarsa ke son karyata maganar da ba likita bane ya tabatar mata
A hankali ta dora hannunta tana kallo , tunani na yi mata yawa a ranta
A hankali ta idasa tubewa ta kwashe ta kai wajen shanya ta shanya su sannan ta wuce bayi dan yin wanka
Bayan ta fito harda alwalarta ta dauro ta dawo ta zauna ta sake daukan carbi tana ja hadi da zama ta hade jikinta waje daya
A ciki ta yi sallar magariba, bayan ta gama a dole ta fito dan Firdausi sai bugawa take yi , suka ci abinci tare da yaren da Firdausin dake ta faman tambayarta maman biyu shin menene? Bakida lafiya ne? Hakama twins sai tambayarta suke yi shin lafiyarta? Batada lafiya ne? Ama amsar daya ce barci take ji
Sai da suka gama ta mike tana duban Fido ta ce" Fido, dan Allah ki tabatar yarana sun yi wanka ku masu addu'a kafin su yi barci kin ji? Ni yau barci ke damuna"
Firdausi da ta fahimci bayan barcinma akoy wata damuwar a tatare da yayarta, sai dai ba zata matsa mata da son ji a yanzu ba dan bata san me hakan zai haifar ba a hankali tana murmushi ta ce" Aunty, keda kin san ko sun yi barci Abansu sai ya kuma dubawa idan an masu komai yadda ya dace? Ke dai jeki ki yi sallah ki kwonta, Allah ya tashemu lafiya"
Amina ta dan kura mata ido, sai take tunanin du kamar da gangan suke yawan sako maganar mutumen da take so ta kawar da maganarsa a ranta dan ta manta da shi kwata kwata
Baki ta tabe ta juya ta nufi dakinta bata ce komai ba
Firdausi ta bita da kallo tana sauke ajiyar zuciya, a koda yaushe ta dora kanta saman abin sallah adu'arta itace, Allah ya sa yayarta ta sauko dubanta gabanta ta gane me ke tare da ura na alkhairi, ta sani sarai yayarta ba dai son girma ba, tunda abu ya kasance haka kuwa sai a hankali, ama baban dana sannin da ba zata so ya tabata a garesu ba baki daya shine yayarta ta ki mijinta
Mijinta shine mijin da kowace mace zata yi burin samu a rayuwa
Wanda ya cancaleka, ya cancali ahalinka? Wanda ya mayar da naka nasa da zuciya daya? Bata taba tunanin akoy namiji irin wannan a duniya ba, ta zata masu kirkin basa tsayin kwana suke tafia su bar matan, lalatatun sunne cika gari, gashi dai jibi zata zubar da wankan haihuwar da ta yi da kuma rabonta da gidan ukuba, ita kam ta san ba ita ba aure, ba zata kuma ba, ba zata yarda ta kuma ba koda wasa, mijinta da ya zo babu wanda ya kaishi adini da nuna talaucinsu baya damunsa, ya kasance yakan talafesu da nasiha da yin uzuri, ama tana shiga gidansa ta zama tamkar makiyiyarsa, basa shan innuwa guda, a kulun kuma abin sake lalacewa yake yi.....bata yarda da bashida imani da tausayi ba sai a nakudarta, ba kowa ya kashe mata ƴaƴanta ba sai ubansu, wannan kalma tana fatan maimaitata a gaban mahalincinta da Mudi!
__________________________________
Tunda ta shiga dakin nata ta yi shirin kwonciya barci ta kwonta da carbinta a hannunta bayan ta gama yin sallah tana saurare
Kunnayenta ke sauraron falo har karfe goma na dare ya yi ta ji shiru ba ihun yara ba hayaniya ba komai
A hankali ta tashi zaune tana duban agogon dakin da wani tunani na daban a cikin zuciyarta
Sai da ta ga batada mai bata amsa ta koma a sanyaye ta kwonta ta sake yin addu'a ta lumshe idannuwanta
Da kyar barci ya dauketa , barcinta mai nauyi
A cikin barcinta kiraye kirayen sallar asuba ya farkar da ita , ta mike jikinta da nauyi na abin barci ta nufi bayi ta dauro alwallah bayan ta watsa ruwa dan ta saku, sannan ta fito ta gabatar da sallah still kunnayenta a waje,sai dai yanzunma babu hayaniyar komai, shiruya fi yawa
Barci ta koma dan shi ya fi cin karfinta, har sai da kusan takwas na safe ta tashi a gigice sakamakon yinwar dake kwakular hanjinta
A gagauce ta kimtsa kanta ta shafa turare sosai sannan ta fito falon
Murmushi ta yi gannin Baba da Firsausi zaune sunna cin abinci
Karasawa ta yi ta zauna kusa da su ta shiga hannu Baka , hannu kwarya tana gaishe da Babar lokaci guda
Baba ta yi murmushi ta ce" Amina ki ci a hankali mana"
Amina ta gyada kanta tana tausawa har ta hadiye sannan ta ce" Baba, wannan cenjin yannayi da saka cin abinci yake , bakiji cikina ba, jikina har rawa yake yi fa"
Baba ta ce" Aya, hakane kin san sai a hankali dama , yanzu daga yannayinki ya saba shikenan, sai ki ga kin daina"
Kai ta gyada a ranta tana ayana' Ba zan fada maku komai ba in sha Allah bale ku min wani kallon '
Sai da cikinta ya dauka sannan ta iya samun nutsuwa tana share zufa ta gyara zamanta tana kallon Baba dake yi mata bayani a kan maganar kwana arba'in din da Fido zata yi da haihuwa, waina da ake toyawa a yi sadaka koda abun ba rai, bale za'a hade da ta arba'in din yaren dai da sauransu
Amina ta gyada kanta ta ce" To Baba , in wannan ne nima sai na bada kudin hatsin ai da kudi a wajena fa, ba sai na fada masa ba inaga"
Baba ta dubeta da kyau ta ce" Aa Amina, ai dole ki fada masa, kin ga yanada hakin sannin hakan, bayan wannanma ai Uba ne baban wa uba ne Amina"
Amina ta tsare Bakin Baba dake taunar goro yana kira mata ABDUL uba ne a wajenta
Baki ta tabe ta kawar da kanta ciki ciki ta ce" Zan sanar masa"
Baba ta kureta da kallo, Hakama Firsausi
Baba ta gyada kanta ta ce" Allah shi kyauta, ni yau banma ganshi ba ai da ban tsaya shiriritar baki sako ba, na san ya fita tunda safe ko? Abdallah kennan sarkin nema"
Firsausi ta ce" Nima jiya har na yi barci dai bai shigo ba, ama na san ba zai ki shigowa gannin ƴaƴan ba komai dare in dai ba tafia ya yi ba?, Uman biyu ko ya yi tafia ne?"
Amina ta ciciba ta mike ciki ciki ta ce" Je ki gani mana dilla sai tambaya"
A ranta kuwa ayanawa take ' Yaya za'a yi ya zo? Bai zo ba ai, dama ni ba wani son zuwan naka nake ba, kar ka zo din ma mana!'
Baba ta cire kanta daga rakiyar Amina da ido ta maido dubanta kan Firdausi ta ce" wannan ya dai Allah ya tarota yarinyar nan"
Fido ta talabe haba ta ce" Amen Baba, haka jiya bata tsaya ta kula kowa ba, tun nan na gane ba lafiya, shi yasa na ki kwonci sai da ya shigo gidan nan, wai ace Aunty ta bude baki a gabansa da gaban hajia ta ce baya sonsa?"
A zabure Baba ta dafe kirji ta ce" Na ga annabi idan na yi hali na gari, ita Aminar? Kice ta lalatamu ta sa an saketa?"
Firdausi ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Ya ki fada min komai, wannanma da kyar ya fito daga fatar bakinsa, shi dai damuwarsa ta yi hakuri ta kula da cikin nan, daga nan ya shiga dakin nata ya dan jima ya fito ya shiga na biyu ya fito yace min kar na nuna ya zo kwata kwata "
Baba ta sake talabe kumatunta, tunaninta faya ne har ga Allah kar aje Amina na fama da aljannu masu taurin kai basu sani ba? Aa ita kam zata fara nemo taimako na rubutu da dan turare na aljanu ta fara yi mata ko a dace
Nan suka wuni tare, kowa na walwala banda Amina dake cicin magani, abubuwan dake ranta gani take ya fi na kowa muni, shi yasa da ta ga su basuda wata damuwa ta saka hijabinta ta fice ta ringa kale kalen tsuntsaye da yannayin ginnin gidan ABDUL, tamkar ba za'a mutu ba, an yi gini kamar ba a duniya ba jama'a kuma mamalakin abin ya sheka a shekashi kabari daga shi sai likafani ko matashin kai babu
A haka ta karasa wajen ginnin da akai mata
Tun daga yannayin wajen take ta kallon tsaruwar ginnin da irin zannen da aka yi na gyare gyare kala kala, zane ne aka yi a jikin ginnin ba hoto bane aka lika
Tunda ta karaso mai ba fulawowin da aka shushuka ruwa ya gaisheta sannan ya tambayeta shin ya amso ky ne?
Samun kanta ta yi da zubawa wajen