Showing 141001 words to 144000 words out of 145392 words

Chapter 48 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8167

sakawarta a saman turaren wutar da matar nan ta hada mata mai mahaukacin dadi ta bude kayan gyaran fuskarta , alamu sun nuna harda fuska zata fence da son ranta........?
Murmushi ta sake yi tana hayewa da kyau saman gadon tana bin fatar jikinta da kallo, sun murje, sun wanku, harta maganarsu ta zama irin ta yayan gatan nan ....bama kamar Hasan da Husaini jama'a, sun zama basa doguwar maganama da hausa sai turanci, sun zama wasu irin rikakun yayan gatan nan, a yanzu da suka yarda da HAJIA itama ta yarda da su ta karra rikitasu da ruwan gayu, har wani koya masu shan madara mai dumi da sasafe ta yi, ita da turancima sak take masu hira, Baba da Umansu nema ke masu hausa wadinnan kuwa irin tunaninsu dawa, gargajiya sak wai




Sai da yama sosai suka karaso, su dukansu sunna cikin sasaukar shiga mai kashe zuciyoyin yan mata, ashe su Hasan ana dauko su daga makaranta wajensa aka wuce da su, yara sai ihun kayan wasa suke sun zo da wasu sun ce wasu na gida, harta kayan jikinsu sababi ne suka ce Abansu ya sa Aunty ta gida ta shirya su,
Sosai a nan aka baje a falo kowa da kowa ana ta labari kamar wanda ya shekara baya nan, amna da Amman sun sha shirinsu sai kanshi suke abinsu, shi kuwa sai shinshina yake yana sake hangen mamansu dake cen barin Hajia cikin hijabinta har kasa domin ta sanshi, ta san waye shi, idan ta bude kwaliyarta haka a gaban Mansur sunna iya hautawa sama, bata san me yasa yakeda kishi har haka a kanta ba, ko a yanzu idan sun hada ido sai ya dan lumshe mata idannuwa , ita kuma sai dai ta yi dan murmushi kawai ta sada kanta


Hajia ta Umarci Fido ta kaiwa Mansur abincinsa cen bangaren baki, ba dan komai ba dan su dan karra zantawa ko yayane, bangaren dai ba waje bane mai mugun shiru, waje ne mai jama'a, yanzu kuma zata mike da kanta ta fadawa datijuwar ma'aikaciyarta ta ringa dan kai kawo a wajen, ba dan wani abu ba, sai dan gudun lamari na shedan, Firdausi dai ba yarinya bace, hakama Mansur, rashin zamansu yaren nema matsala, domin hakan na iya haifar da wani abin daban.....Allah ya sawaka basa fatan hakan sam shi yasa ta mike ta fita bayan Fido din ta dauka ta tafi jiki a sanyaye


Ya kasance saura Baba, da ABDUL, da Uman biyu




Ya kasance sauran Baba, Abdul, da Umman biyu a falon,


Abdul ya kalli Amina, da wata tattausar murya yace MEENAL,"


Baba ya dago da sauri daga kama yatsun amma da yake yi ya kalle shi, ya kalli Amina ido ya kanka ce yace waye meenalu kuma? Kamar bawan rake? Sunanta Amina ko kace gwaggon malan"




Abdul ya kalle shi, shi da aminar, Amina ta sadda kanta tana yar dariya shi kuma ya gyada kai a tausashe ya kuma cewa meenah nima a zuba min abincin yunwa nake ji




Baba ya kalle shi kallo irin na basira, baki ya tabe yace gwamna ina ga daga gidanka ka fito? Mene na san a baka abinci kuma a nan? Matar ka ta chan fa?


Amina ta dan saka birki daga mikewar da tayi ta koma tana sadda kai tana kumshe dariyarta


Abdul ya kalli baba, kallo irin na su fahimci juna a tausashe yace baba ya maganar wannan dokin daka ce kana so, na gidan gona fari kal din nan?


Bana yace fari na saraki wanda ka cimin amana ka siya daya tal ba kace Ni hawa zan yi ko kuwa na dame ka?


Abdul ya jinjina kai yace shi fa' yanzu ka zabi daya ka dan je wajen su Hassan kadan gobe sai kaje ka dauki dokin ka idan ma nan kake so ka aje shi sai zai dashi" ko ka zauna anan kana abinda ba shikenan ba kuma kayi asarar dokin ka


Baba yayi tsai na dan lkc sai kuma ya dafa gefe yace kawo yar nan na tarbi kakar gwamna dashi kar ta ce zata shigo nan bayan mutun da matar shi haka kawai azo a dame shi,


Kawo ta nan kasan ta shanu da ya'yan nan kamar ta maku kwace bayan ba bata zaku yi ba,Bara muje chan Bata mu zauna ai yau yanayin garin da dadin zaman waje yake , Allah dai yasa mu cika da kyau da imani gwamna.


Abdul ya mika mishi yar hankali kwance ba kunya ba wani Dar, inda Amina taji kamar jinin jikinta zai kafe da tsananin kunya, kanta a kasa sai mirza yan tatsuniya take kamar ta fashe da kuka dan kunya


Ba za a zo ba ko? Ko na zo? Abdul ya fada yana murmushi dan ya lura qarara ta aka cikin duniyar kunya ne


Fuskar ta ta dangi ta shagwabe fuska tace ynz ka kyauta kenan


Abdul ya dage mata hira irin mai anyi? Amina tace haba annan amna ai sai kasa malam ya min wata fassara ta da ba dadi ko, Abdul ya mike tsaye dan ya kula yan mulkin ke san dawowa a daidai wannan gabar su cire shi, a nutse ya karaso inda take ya rage tsayin sa sosai ya kamo hannayenta ya mikar da ita sannan ya sa hannu ya janye hijabinta baki daya ya tsaya yana kallan kwalliyarta ta malam bahaushe atamfa riga da skirt an kafa masa sauri ya zauna das a gaban goshi


Ajiyar zuciya ya sauke ya rungumeta a jikin sa tsam a hankali yace "har ynz wai jinin nan bai tafi ba dan Allah?


Amina ta hadiye yaqin wuya da tsoro ta gyada kanta a hankali tana kakkaucewa domin lalubawa yake tsakanin shi da Allah, janye wa ta samu ta danyi da sauri tana nufar wajen table tana cewa Bismillah kazo kaci abincin Abban amna, sai da ta kule wa ganinsa yana kallon kayan kallon data hasko masa ta baya, sannan yaja mika yana murmushi a hankali yace gwaggon malan Allah dai ya qara lfy da nisan kwana dani a gefe na ringa mulmula da mulmulawa dan samun ingantacciyar lafiya. Da wannan suka janye table suka fara cin abinci da zuba soyayya tsaftatacciya da tsari.....


A bangaren fido kuwa a darare take tunda ta shigo falon, sosai taki yarda su hada ido dan ita wlh kunyarsa ma take ji, Ma sur kuwa ya bata dama ya mata uzuri sosai domin shi fa ya idasa fitar da jaririyarta daga cikin cikintq, yana cikin wa'inda sukai mata aiki kodan wannan lamarin mata sai taki amincewa auren sa bayan shi kam ba wannan bane ya sa shi kwadayin ajiye ta a matsayin iyali, ta masa ne yana so ya aje ta su rayu a matsayin iyali


Bayan ya gama taba abinda ya aje masa ne ya bata damar kashewa sai da yazo dauka ta duka zata kwashe a nutse yace fido? Firdausi taji gabanta ya fadi a hankali ta dago ta kalle shi mamaye ya sakar mata murmushi a hankali yace Allah saka da alkhairi nagode sosai, sai firdausi ta rasa godiyar mai cece tama rasa amsar da zata bashi, a sanyaye ta dauke ta nufi hanyar fita jikinta ba kwari




Mamaye ya sake ambaton sunanta yana kallon ta hijabinta sakakke ne har kasa ba a ganin jikinta ko kadan ko lafewa baya yi a jikinta, a sanyaye yace fido ' Ina son ki irin sosai din na fa kuma daddyn ku ya bani ke.....


Ido ta zaro hannayenta suka nemi zubar da babban farantin dake dauke da kayan kwalam da kwamulashe, da sauri ta sadda kanta karshema nan ta dungura abin ta balle da gudu domin ji tayi idan tace zata gudu da kayan zubarwa zata yi kuma gudanar ita ce abinda yafi sauki a gareta a irin wannan lkcn, kirjinta na dokawa kamar zai ballo ya fito daga bakin ta, ta samu waje ta labe tana Dora hannu a saman kirjin nata....




Da wannan Abdul da doctor suka rikita yan amtan hajia da kalar nasu salon, suma suka rikita su da kalar nasu innocence din da sassa yar soyayya har ma ya fadi cewa zai turo wacce zata musu lesson na koyan tukin mota, idan an gamsu da kwarewar su sai a basu takardun tukinsu




Bai tafi ba saida ya nunawa hakka motar daya dauko musu Amina da risala da gudu, sai dai tasu Amina iri daya ce kala ce kawai ta banbanta ta dodo kuwa jakarta daban, motocin dai baki dayan su irin hawan mata ne sannan ya tafi cike da kewaye iyalinsa da tunanin ta a zuciyar shi da kuma ya'yensa dake dariya duk da basu san abinda duniyar take ciki ba amma da zarar an dan tattauna kumatunsu sai su d,inga dariya wannan ya kara sanyaya masa zuciya




Bayan kwana biyu haj suka shirya suka fita tare da matar da zata yi aikin koya musu mota, saida suka fara zuwa gidan ya'yan mahaifin yaran tare da yaran, domin tunda aka yi haihuwar bata je wajen rasuwar ba, Abdul da baba ne kaɗai suka je sai yau da suka fito suka nufi can yana cikin shiga irin ta larabawa watau bakar abaya bakar nika Safar kafa data hannu, sun tarar da ya'yan mahaifin nasu cikin shiga mai kyau ba laifi saidai yar rama da yayi da tunanin rayuwa dake damunsa, gidansa kansa ba laifi domin a gyare yake ga kuma mutun biyu dake kula da tsaftar gidan da kuma ta abincin sa mata da miji ne a gidan


Karshe dai da jikansa da komai ya dinga labarta musu irin abinda ya faru, ya fada musu ai yana cikin halin rashin sanin inda kanshi yake mijinta ya mayar dashi babban asibiti da kakanshi aka dinga bashi kulawa har ya dan daidaita, ba laifi ya'yan mahaifinsu yayi nadama amma kanin mahaifin su abin ba sauki gidan shi ya zama tamkar gidan karuwai yana ji yana gani sai ya taso kato dakin shi bai isa yace komai ba haka suke rayuwar su




Sun yafe masa dayan ma sun nema nashi sauki a wajen Ubangiji domin babu abinda ya gagari Allah shima ana iya wayar gari aga ya samu canjin rayuwa, da suka fito sun gaisa da dayar matar tashi wadda kanta ke sadda kasa a dole sbd hajia tsaye cikin shigar nan Tata ta Alfarma ga kanshi tana ta badawa ga kyauta ko baka mata biyayya dan komai ba kayi mata dan kyautata, hajia hauwa kenan matar Alkali. Hart's cousins din su saida suka gani suka sake jajanta wa juna sannan suka wuce wajen koyan motar, hajia ta zauna cikin rumfar da jarirai ta da wayarta tana shan iska tana kuma cin wariyar rikici irin ta yan siyasa, a ynz ma bata daina siyasa ba




Abinda ta daina makauniyar siyasa mai tura bawa cikin rami irin siyasar dake sa mutun har addini shi ya manta,daga nesa take yin siyasar ta wadda ba tana yin ta bane ynz dan ayi mata wani abu ba a gwamnati, tana yin tane dan ra'ayi, tana son siyasa a jinta take amma kuma kaunar jariran nan tazo ta make komai bazata iya fita nesa dasu ba, bazata iya wuni basu a gefanta ba wani irin son su take kamar ranta murmushi tayi ta kai idon ta chan gefe inda biyu ke buga gama a iPad dinsu suna gardama da kyautata dariya, idannuwanta ta lumshe tana yiwa Allah godiya da kadaice kadai ya ishe ta babu wadannan a kusa da ita idanuwanta sun rufe bata gane komai..... A ynz kuwa gata ga su ga farin cikin rayuwa a tare da ita ko a ynz ta koma ga mahaliccin ta Alhamdulillah






58


A hankali aka dinga koya musu mota wani ikon Allah tun a fitar su ta uku suka ba mai koya musu mamaki tukin a hannun Amina ras abin ba a magana, a kadan sai da aka musu lesson takwas sannan suka shiga gari tare watau ta dauko su suka tukata cikin gari hanyoyi mafi hatsari wajajen da motoci, mashina da manyan motoci ke yawo san ran su sun tsira da farko domin harda ihu Amina ta saka da suka iske wani dogon go slow amma tana kwantar mata da hankali sai gashi sun fita amma sun sha nawa domin koda wasa bata yi tukin ganganci ba ko nuna iyawa a hankali ta tuka har suka fita, a kwana na goma sha biyu ta kawo musu takardunsu shedar sun gama iyawa bata da darr akan su ai kuwa an sha murna domin da Abdul a cikin gidan ya shiga Umman biyu ta yawa ta dashi a Hakim ce irin madame tukin nan, ya zamto kwanan su talatin da uku ne a kirgen shi sauran kwana bakwai umman biyu tayi kwana arba'in din da ake yi ta tattara ta koma inda tafi wayau


A ranar da wuri ya koma sbd kansa na dan damunsa da ciwo a washegari kuma yayi safiya ya leka ya amshi magani ya sha sannan ya wuce office ya kwanta domin kansa ke masa ciwo ya sha magani ya kwanta don samun barci wayarsa kan ta ya manta ta a gida dan samun barci....






Tunda ta farka daga barci take ta gwada kiran layin shi amma amsar daya ce a kashe, tun bata damu ba har dai ta kasa hakura ta fito cikin shigar abaya baka da dogon wando a ciki da mayafin abayar haka yafe saman kanta taje dakin hajia tana tambayarka ko sun yi waya da Abdul? Anan hajiyar tace mata itama ta neme shi Bata same shi ba sai muhammet ta kira yake ce mata bashi da lfy ne amma ya amshi magani Yana office, hankalinta ne ya tashi har ta kasa boyewa a saman fuskanta ta samu ta jingina e da bayanta a jikin kujera a dakin hajia bayan bata taɓa zama haka a dakin ba duk tsakanin su tayi shiru kanta a sadde, har hajia ta fito daga wanke Ammar domin ya bata pampas din sa ta gan ta a yanayin nan, murmushi tayi tace Amina da sauki fa jikin nashi kar ki saka damuwa a ranki mana ai shiru sauƙin kenan inda ba sauki da an nemo mu ko? Amina ta gyada kanta jikinta a mace dai ta mike a sanyaye zata tafi kasa Hajiya ta kira yi sunan da juyo tana kallon hajia idanuwanta sun cika da kwalla hajia tayi murmushi tana nuna mata saman sif tace kinga laluba chan kin ga key din mota ta chan dauki kije wajen aikin ki ganshi sai hankalinki ya kwanta tunda na aiki direba ke kuma naga kamar zaki suma dan rashin kunya.


Amina taja numfashi da dan sauri ta dauki key din ta juya har tana hade ta sauka da dan saurinta ta fice bata tsaya daukar hijabi ba balle ta tuna da wando ne a jikinta ta qara wajen mahaukaciyar motar hajia baka sidik ta bude ta shiga tayi mata key tayi addu'a a hankali tayi ribass ta nufi hanyar fita daga gidan mai gadi ya bude mata yana kwararo mata addu'a yana mai washe baki cike da mamakin Amina da hajia, ya yarda cewa Allah shi ke gyara komai,. Nutse ta dinga tukin tana gane hanyar rass har ta iso tafkeken kampanin, a hankali ta karasa wajen da aka bata damar shiga sannan ya aika motar ta wajen ajiye motoci tana hangen daidai kun mutane dake shawagi su ciki harda muhammet daya Qura wa motar ido yana tunanin hajia ce ta zo domin matar hajia ce mota mai masifar tsada da bakin glass, mota ta manyan alhazzai duniya guda.




A nurse ta bude ta fito takalmin dake kafata flat ne ba wani mai tudu ba simple ne bashi da wani kwarafniya Asalinsa na fido ne ta zira ta bar na cikin dakin ta anan falon hajia tayi gaba, du idan tana tafiya kuwa ana ganin wando dake ciki mai roba roba, abayar mai botira ce kuma mai dan shara shara ce, mayafin kuwa bashi da girman a zo a gani dama mayafin bayar ne ta dan yafa a saman kanta, ido Muhammad ya zaro yace uban wa, baiwar Allah jaraba kike san ja mana baki dayan mu.


Nufo ta yayi yana cewa hajia ce da kanta? Amina ta dan dakata sai kuma tayi murmushi tace muhammat kana nan kai ma ashe? Dan Allah yimin iso ko sa bar Ni na je wajensa, ya jikin nashi ne? Muhammat ya rasa ta yaya zai fada mata dama hijabi ta saka, bafa dan shigar tayi muni bane, no a wajen mijinta ne zata yi muni dan wani irin birkitaccen namiji ne balle a kanta bashi da hankali, a kanta baya kara, kowa ya fahimci kishinsa a kan ta bayyananne ne shiyasa ake guje masa bacin Rai akan hakan ana kiyayewa.


Saidai bazai iya maganar nan da ita ba a dole yayi mata ja gaba suka shiga ta lifta ya haura dasu ya kai su har babban wajen ma'aikatan nan da aka sha rigima da ita a wajen, magana daya ya fadawa wanda ke tsaye a wajen cewa matar oga ce suka saki hanya gaba dayansu suka wuce har kofar office din sa


Camerar dake haska ko waye muhammat ya daga kai ya kalla ya saki murmushi irin na cikin hancin nan sannan ya nuna umman biyu, yan saka Ni kadan kofar ta bude muhammat ya koma gefe yana mata nuni data shiga sannan ya juya abinsa ya rufo yayi gaba.




A hankali ta shiga tana tuni yanda taga office din sa a wancan lkcn ynz an kara chanja masa waje hakan yasa ta dinga dube dube har ta waigo inda yake tsaye da dan abin goge ruwan da wanko fuskar ynz daya tashi daga bacci kuma alhmdl kansa ya daina ciwo ya samu barci maganin ya masa aiki. Tun daga sama har kasa ya dinga kallon ta ta karaso kusa dashi tana murmushi tace abban amna ashe ka mike? Yaya jikinka? Ni na damu sai dana taho


Daga bakin mai maganar har kalaman nata sai da ya cije ya ba kansa hakuri sannan ya fahinci me take nufi" a nutse yace zo nan




Amina ta kalli fuskarsa dan kamar a kausashe yayi maganar, sake kallo da take shima yana kallonta, a hankali yace cewa nayi kizo nan umman biyu, yawun bakinta ta hadiye sannan ta daga kafa ta karasa inda yake a tsayen kara kafewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login