Showing 42001 words to 45000 words out of 145392 words

Chapter 15 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8151

sanyaye ya ce"








*NZL PAGE1️⃣6️⃣*






A sanyaye ya ce" wa ya kawo ki ne?"


Itama a sanyayen ta ce" Ni na yi driving "


Kansa ya gyada yana dan tabe bakinsa, sai kuma ya yi shiru yana kallonta tanai masa byby har ta fice a falon


"Why ba zaka ce da ita auren hadaka ne aka yi da yarinyar dan hankalinta ya karra kwonci?" Mansur ya fada da mamakin irin yadda ABDUL ya ki fadin gaskiya dan ya kare kansa a wajen budurwar tasa dan su zauna lafiya ba sai an yi ta jan zancen ba


ABDUL RA'UF ya yi dan murmushi yana kallonsa ya ce" A kan me zan zauna na bata labarin abinda yake sirrin gidanmu bayan bata zama sirrina ba?......koda sirrina ce idan abun zai iya haifar da fitina gobe ai zan rufe mata shi, bale auren da ba zai zarce gobe ba in sha Allah?"


Da mamaki Mansur ya wara idannuwansa yana kallonsa ya ce" Kamar yaya?"


ABDUL ya tsareshi da duban mamakin shima, tabas yayi mamakin da Har MANSUR ke tambayarsa kamar yaya idan auren nan ya zarce gobe, lolz auren na gigitar Baba? Tabas kakansa ya rikice ne a jiya zuwa yau da ya dauko nazawara uwar ya'ya biyu matar da wani katon ya aura ya saki ko yaya ne oho ya maka masa shi ga shashasha!, Y'ar fa ta daga hannu zata sharara masa mari? Shi fa bai taba gannin mai hayaniya irinta ba, bai taba haduwa da ita bata hadasa masa ciwon kai ba, wannan aure na *SA'O'I?*, Uhum.......
Bai ce masa komai ba ya ciciba ya mike yana duban hanyar hawa sama ya ce" Barci, Mansur barci nake ji sosai, Ni kam bara na je na ga ko zai samu"


MANSUR ya mike shima yana dubansa a lokacin da ya fara hawa ya dan daga muryarsa kadan ya ce" Sai ka sauko zan kalli balll, Hei Man?"


ABDUL ya dakata yana juyowa
MANSUR ya ce" Ka yi dogon tunani a kan lamarin nan"


Murmushi ya sakar masa ya idasa hawa ya nufi dakinsa dan ya huta


A ranar kwata kwata bai amsa kiran kowa ba, haka kuma bai nemi kowa ba, Mansur ne da dare da ya fito daga asibiti kafin ya isa gidansa ya biya ya duba Mai Shanu da Hajia, a nan ne ya hadu da biyu , Husain ya fada masa cewa mamansa na daki bata yiwa kowa magana Baba lauratu na shafa mata kwai a fuska karni jirr
Hasan kuwa bai ce masa komai ba , ama kuma yau ya dan sake da shi dan yakan dan yi masa murmushi kadan , ama baya yi masa hira
Da wannan ya wuce gida zuciyarsa cike da dariyar yar kakanin nasu, Shi Baba Mai shanu yana bangarensa hankali kwonce yana ibadarsa, matarsa kuwa ta kile ta kulle bata kula kowa ta labewarta itama a nata dakin, dan tunda ta shige bata sauko ba, bata nemi kowa ba, danma mai aikin nasu an jima da ita ta san kan gidan fiye da tunanin mai karatu, ita ke kula da abubuwa da dama, dana Hajiar kan bata umarnin a dafa kaza, ko a kiyaye da tsaftar gidanta , da irin cimar Elhajin wadda yawancin lokuta abinda zata ce a girka masan baya son cinsa a ranar sai an yi ya sa a tuka masa tuwonsa da man shanu ya rangada


Washe garinma tun karfe tara ya wucewarsa bakin aikinsa, ya sauka a ma'aikatarsa ya shiga aikinsa tukuru, neman kudi a jinninsa yake, baya gajiyawa da mayar da biyar goma, ya fi sakewa a harkar neman kudinsa, a nan nema ya ringa samun kira jefi jefi daga manyan abokanan aikinsa ana masa barkar auren da aka daura a lulube
Shi dai yakan amsa kawai idan ya kashe sai ya yi murmushi ya girgiza kansa
A haka ya gama ya koma gidansa yauma bai nemi kowa ba, ciki harda kakansa


A kadan sai da ya dauki kwana uku, hankalinsa ya kwonta, tunaninsa ya fiafaita waje daya, zuciyarsa ta dan samu nutsuwa, ya ji eh lalle yanzun yana iya zama da kowa su zanta a kan lamarin sannan ya turawa Risala sakon cewa zai zo gidansu a yau, dama su Hajia yana samun sakwaninsu ne daga wajen Mansur, domin summa daina kiransu ya yi


Tunda ya fada mata ta tayar da tashin hankalin shirye shiryen tarbansa
Du ta hargitsa ma'aikatan gidansu da basu umarnin a dafa wannan, a sauke wancen, har abin ya kular da mahaifiyarta dake binta da kallo


Rai bace ta ce" RISALAH, ba zaki yiwa kanki da kyau a lamarin Yaron nan ba ko?, Ba zaki daina rawar kafar nan ba ko? Ke anya kinada zuciya a kirjinki? To walahi bari ki ji ni a kan y'ayana ba ruwana da maganar dukiya ko mulki!, Ko mahaifinku na ga zai sakaku a matsalar da ba itakenan ba zan nema maku mafita mai kyau, sakarcin banza sakarcin wofi"


Har RISALAH zata tafi kicin dan ta karra masu maganar idan ya zo yana zama mutun biyu su kawo masa abin tabawa su gaishe shi kafin su tafi su basu waje ta ja ta tsaya


A hankali ta dawo ta zauna a gaban mahaifiyarta ta sha kwaliya har ta gaji


Hannayen mahaifiyarta ta kamo tana kallonta a hankali ta zauna gabanta ta ce" Mama, dan Allah ki yi hakuri, Mama na san kudinsa, kyansa ko sunnansa ke baya gabanki, na fi maki komai, Abane ke son tarayarmu ko dan sunnansa, Mama ni kuma.......ni kuma ina son shi, yanada halin girma, Mama a samarina kafin na tsayar da shi na jima ina bincike, kin ga yanzu da na tsayar da shi ina mai tabatar maki ya isa da hakan..... Please Mama idan ya zo kar kice zaki yi masa wulakanci a kan maganar aureb naj nasa, ki barni mu yi magana da shi, dan Allah kar ki shiga, idan baki manta ba mun taba yin fada da shi kika yi kiransa kika yi masa fada, Mama tsakanina da shi ne, ama kika shiga kika fatatakeshi, kin ga sanadiyar wannan da kyar ya dawo ya saurareni, har cewa ya yi dan shi bashida iyayen ne zai fuskanci haka? Shi bai maki rashin kunya ba ama sai ya shafa min lafiya.... Please Mama ki bani dama ni na san lagonsa, idan har na sada kaina zai turo a yi maganar aurenmu, ni kuwa na maki alkawarin ba dai ya zauna da wata mace ba ina raye! Mama ba zan je gidan da niyar zaman lafiya da kowace shegiyar dake tsakanina da ABDUL ba!, ABDUL nawa ne, idan ta min shigar sauri sunnanta kishiya uwar gida mai shishigi!, Ni na fi kowa sannin ABDUL dina, ni zan yaki abina.... plz Mama zaki yi min haka?"


Sosai uwar ke tausayawa yarinyarta, ba komai ya sa take jin tausayinta ba sai idan ta duba ta ga zazafar soyayar da y'ar ke yiwa yaron nan, a bayane yake ta fi sonsa fiye da son da yake yi mata, a bayane take nuna masa zazafar soyayar da har take ikirarin tana iya mutuwa a kansa, wannan abu shi ya fi komai bata mata rai, idan ta kalli santaleliyar y'arta takan ji damuwa ta lulube zuciyarta, shin wace riba yarinyar zata ci da take kokarin wulakantar da kanta a kan Da namiji? Itafa inda ta rako mata kennan, itafa ba zata dauki irin abubuwan nan ba, shi yasa ko ubansu idan ya zo maraba, in ya tafi ya gaishe su walahi,


Mikewa ta yi ta haye sama domin ba zata iya daukan takaici ba, dakinta ta fada ta dauki wayarta ta zauna a bakin gado ta shiga lalubar number HAJIA Hauwau wace rabonta da ita kusan kwana hudu kennan, ta yi kiranta sau kusan bakwai bata daga ba dan kwarai ta ji haushin abin nan,


Tana ji lokacin da motoci ke shigowa, dan haka ta mike ta daga window tana hangowa daga sama


Cikin rantsatsiyar shada yake sai walwali take ruwan baka sidik da dan zubi na bakin zare da dan rastsin ash color mai haske kadan ba da yawa ba
Kafarsa sanye da takalmi kafa ciki ba mai tsini ba, mai daidaituwa da kafar mutun ruwan ash color, sai hularsa mai duhu da dan ash kadan


Kayan sun matukar amsarsa, kuma duda shada ce haka ake gannin irin yadda wajen hannayen suka rike hannun taf suka kuma kama wajen kirjinsa kadan


Irin tsayuwar da ya yi a jikik mota ya dan harde hannunda daya yana duban agogo ya sakata ayyana magana kamar haka' A kulun idan ya kawo mata ziyara yana gagawa ne '


Kwarai itama ta san sirikin nata ba dai a yi maganar haduwa ba, classs, gayu, uwa uba yan cenji, matsalarsa daya ce da bata tunanin in zai cenza mumunar akida da isa


Tana hangen irin yadda Kyakyawar y'arta mai ji fa kyau da isa ke yi masa magiyar shiga ciki, da wani zumbulelen hijabin da ta zumbula a kan mahaukacin lesh din da ta sha, du dan kar ransa ya baci ya mata fadan ya zo da maza ta fito ba hijab, hum, ita gani take yi yarinyar tata ta cika azarbabi a kan lamarin yaron nan, tun bai zama mijinta ba yana dora mata dokoki haka ina da ya aureta?


Lebe ta ciza kadan tana amda salamar Hajia Hauwau fa ta yi mata a nutse, a hankali kamar yadda ta saba magana idan zata yi in ba bali za'a yiwa dan tsoho mijin arziki ba


Bakin gadon ta koma ta zauna itama cike da nata ajin ta ce" Kwana biyu Hajia?"


Hajia Hauwau ta dan yatsina fuskarta daga ringeshen da take tana mamakin isa da raini irin na matar nan, in ba dan abinda take hangowa na harkar siyasar jikanta ba har ta isa ta ringa kiranta har sau bakwai bata amsata ba?, Shi yasa itama yanzu ta ki amsata sai da ta mata kira na biyar tukunnan


A takaice ta ce" Fine " ta ja bakints ta rufe


Wayar ta sake kallo, ta tabata hajiar ce sai dai irin yadda take bata amsa ya tabatar mata ko yayane hajiarma ta shaka


Dan haka wannan karron sai ta dan sasauta ita mahaifiyar Risalar din a hankali ta ce" Hajia kennan, sai labari ya zo min na auren HONORABLE ko?"


Hajia ta dan mike zaune daga ringeshen da take tana duban agogo, har karfe shida na yama ya shige dare na son sanyo kai ta ce" Uhum " ta kuma jan bakinta ta kyale
To in ba rashin mutunci irin na uwar RISALA ba ita har ta isa ta wulakantata? Me take takama da shi ne wanda ita bata malaka ba? Kai idan bincike ko bibiyar asusu za'a yi ta dameta ta shanye a ya'yan banki da kuma hawa manyan motocin, dan ana wani lalabata saboda y'arta sai ta ni rainawa mutane wayo? Maganar siyasarma ba wai ana tare da su bane dan su din zasu bada wani abin, an hada karfi da karfe ne dan a cimma matsaya guda, mijinta shine dan siyasarsu shi ya kawo maganar ABDUL RA'UF din da nufin da zai amince da shi suka tsayar a takara, ABDUL din da har yanzu bai zauna sun zanta a kan maganar ba ya dai saurara ya yi shiru ne, shine zata wani dauki kanta ta kai inda Allah bai kaita ba? Ita yau mace ko ita ke ciyar da ita ai na zata dauki salon wulakanci ba, ta kama kanta dilla tun kafin ya gudu ya barta!


Hajia ta sake gyara zamanta ta ce" Hajia sai nake gannin kamar ranki ya bace bayan ni aka wulakanta ni ya dace raina ya bace na yi dogon fushi a kan lamarin?, Kina gani fa irin wahalar soyayar da RISALA ke yiwa ABDUL, ama fisabililahi sai dai mu ji a duniya wai ya yi aure? Wannan wani irin tashin hankali ne, a kan maganar summar Risala biyu Hajia, yanzu haka bata cikin hayacinta, baban damuwarta maganar aurensu da kuma sakin yarinyar dan ba zata iya zama da ita ba a matsayin kishiya ba Hajia"


Hajia ta mike tana bude kofarta ta dan shiga takawa kafarta sanye da takalmin bakin bed wanda take dan yawatawa da shi a cikin samanta bangarenta zuwa na mijinta ta ce " Ai a ranar da nake kiranki mun yi maganar da mijinki ne, yanzu haka mun gama maganar da shi kawai, kunna iya zantawa idan hakan ya yi fine, idan bai yi ba sai a hakura kawai dan bana ciki da abinda zai taba mutuncina da girmana !"


Tana dasa aya ta katse kiran tana jan tsaki hadi da fadin" dan ubanki nada kudi sai me? Mijin naki da kike takama da shi yaron jikana ne, kuma ke din a kadan na baki shekara goma a duniya! Shine sai ki ba kanki damar raina ni? Ko mijinki karya yake ya san wacece ni kuma yana min *LADABIHHHH* dan ya samu abinda yake so a duniyar siyasarmu, da ake mutuntaki dan ana tunanin yar mutuncin kike, bayan wannan ABDUL yana iya daukan yar gidan ubanda yake so ba za'a hanna shi ba, kin yi kadan mu yi maganar cikin gidana da ke, duma abinda aka je aka fada maki hakan ne! Nonsence kawai!"


Tana yi ne tana saka hannunta da nufin tarda Mai Shanu a yau, dan ta tabata ko meye ya kwontar masa yanzun


A bangaren Hajiar kuwa sakalau ta yi da waya a hannunta cike da mamaki


Da sauri ta shiga lalubar number mijinta
Tana fara ringin ya daga dan shi din baya wasa da lamarin matar tasa,
Hankalinta a dan tashe ta shiga labarta masa komai, har kiran da hajiar ta yi mata kwanaki bata daga ba, da zuwan ABDUL, da kuma yadda suka kwashe da hajiar


Da mamaki ya shiga balbaleta da masifa, abinda yakan jima bai yi mata ba, domin sai ta yi laifi dari bai kula ba sai idan abin ya girmami tunaninsa yakam fadanta a kai
Yana fadan ne yana salalami ya ce" Na rasa yaushe wannan girman kai naki na dan Aba yana da kudi zai barki, ki sani gaba da gabanta ne a rayuwa, kuma ko dan bawa ya ci ribar zama da mutun zai sasautawa kansa wasu abubuwan, ke na tambayeki meye ribarki a cikin nan? Kin sani ne idan kika matsa kika raba RISALA da Honorable kece sha wuya, domin a yadda kike da son Yar nan sai kin fi kowa shiga uku, dan kin san RISALA tana iya rasa ranta a kan HONORABLE, mts ku kam mata kunna bani mamaki, meye a ciki dan ya yi aure? Ke ace aurwn soyaya nema ya yi sai me? Ba hudu yake da damar dauka ba? Ni ina nan ina yakin a karshen watan nan a kawo nata itama ta je ta baza mulkinta son ranta domin itace matar so, ke kina kokarin wargaza min? "


"Elhaj!" Ta fada da dan karfi kadan


Shima da karfin ya ce" Na maki shiru na rufe maki baki kar na maki ihu ko?, To sai na maki ki gyara ko ki kwaba tuwonki ne, abinda zan tabatar maki shine kece da asara a wannan gem din, shi yana iya daukan wasu ukun bayan bazawarar da aka maka masa, kawai baku yin bincike a kan magana sai ku hau ku zauna? Ki yi kokarin matse lamba ta bangarenki kema ta yadda yaron zai turo a wuce wajen kin ji abinda na fada maki!" Kitt ya kashe kiran


Wani gauron numfashi ta sauke mai zafi ta zubawa wahe daya ido
Sai kuma ta mike ta dauki mayafinta dan yololo ta yafa a kanta zuwa kafadarta ta karra fesa turare ta juya ta shiga saukowa cike fa takama irin tata da isarta da nata ajin


Tunda ta sauko sau daya da ya kalleta dan ya gane ko wacece bai sake yi mata wani kuraren kallo ba, ko dan rashin yalwatacen rufa ne? a mutunce ya gaisheta sannan ya dakatar da katse latsen wayar da yake yi dan bata girmanta


Sosai ta fuskanci zaman nasu, da kuma karantar fara'ar dake kan fuskar yarta


Ajiyar zuciya ta sauke, da kalar nata makircin itama dan ta kai ga ci a karro na farko bayan a kulun takan nuna ya bar yarinya ta hau kan nata ra'ayin da nata tsarin, ama a yau sai kunnayensa syka tsinci maganarta tana dan basarwa da dan murmushi ta ce" Ur excellency, ina fata ta sanar maka cewa na hannata maganar saloon ko?, Ai ni ban san wai hannawa ka yi ba, in ba shirme irin na RISALAH ba a kan me zata yi bayan ka hanna?, Ke da ake maganar turo da magabata a yi maganar aurenku kin tsaya shirme ne? Haba baby ai na yi mata fada tace zata baka hakuri ba zata kuma fita shagon ba, to mema ake yi da wani shago bayan ke din kece zaki kasance uwar masu gida? Uwar gida kuma amarya ke daya kwalin kwal?"


A yanzun kam a dan fuzge ya dan kalli mahaifiyar Risalar, sai kuma ya dan kalli RISALAH
Bai ce komai ba ya sake maida dubansa kan TV din dake kunne ama ba amo ko daya dan yana zama ya dauke amon baki daya, ya dan yi murmushi yana ayanna abubuwa a kan irin expression din dake saman fuskarsu baki dayansu


Mahaifiyar Risala ta sake yin dan murmushi ta ce" Uhum, Elhaji mace ba, yaushene za'a turo a yi maganar? Abanta yace idan ka zo a yi maka tambayar"


Sosai kunya ke son kama shi, mahaifiyarta? Lalle, ita kuma mamaki da farin ciki ke neman lulubeta, ta sake sinne kai ita ala dole kunya take ji bayan baban burinta shine ta mike ta kwaso shokiiiiiiiii gannin yau mahaifiyarta ce da kanta ta sauko a kan lamarin Abdul? Lalle ita kam alhamdulilah


Sai da ya gama yanke abin fada sannan ya dubeta a tausashe ya ce" In sha Allah karshen watan nan"


Daga ita har ita murna da farin cikinsu kasa boyuwa ya yi, kafin uwar ta mike sai da ta jadada koda an kawo bata so ya wuce sati biyu domin su sun jima da suka shirya


Shi kam bai sake cewa komai ba har mahaifiyar Risala ta idasa hawa ta tsaya ta harde hannayenta tana murmushi mai daci a bayane kasa kasa ta ce" Ba takamarki jikanki ya isa ba shi wani ne ko Hajia HAUWAU? , Lalle sai ganninsa ya gagareki, takamar da kike yi da kudi kuma ya zamto maki tarihi!,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login