Showing 78001 words to 81000 words out of 145392 words
Chapter 27 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ta dauki maganar da mahinmanci
A nutse ya ce" Zuwa na yi na ganki, na yi maki oyoyo sannan na maki sai da safe"
'Sai da safe?' ta ayanna a kasan zuciyarta, tana kallonsa ta ga ya mike yana dube dubensa ya sake juyowa ya ce" Hop komai lfy baki da bukatar wani abu?"
Da mamaki ta ce" Sai da safe?"
Juyowa ya yi ya fuskanceta ya ce" Eh "
Da mamaki ta sake dubansa ta ce" U said sai da safe, safe? Hakan na nufin zaka je part dinka ka yi sleep ? Ko kana nufin na taso mu tafi sai da safe na dawo nan?"
Ita da kanta da ta yi furucin sai da ta ji wani iri, ama kuma abinda take hange ya fi mata wannan jin nauyin a zuciyarta
ABDUL ya dan lumshe idannuwansa yana jin wani iri a furucinta, duda ya san gaskiya ta fada kuma ƙarin haske take so a furucinta, ama sai ya ga zuwan kai tsaye ai na namiji ne, a duniyar hausa
Dan sake matsota ya yi kadan ya zauna yana fuskantarta ya ce" Oh sorry, kin san a hukunce dole sai na yiwa UWAR GIDANKI sati kafin na yi maki ko?"
"Uwar gidana?" Risala ta fada idannuwanta na kankancewa
Abudl ya sake fuskantarta ya gyada kansa ya ce" Eh, yar uwarki, yayarki, ko kin manta ne?"
Gaban Risala na dukan tara tara, ranta na neman jagulewa ta sake dubansa ta ce" ABDUL, wannan wace irin magana ce? Kana magana kamar wanda ya tare da matar cen?, I said uwar gidana, yar uwata....kamar wata wace take da isa da takama a wajenka wace kuka yi auren soyaya da ita irina?"
ABDUL ya dafe habarsa dan magangannun sai ya ga kamar ba wani ilimi a cikinsu gaskiya
A hankalinsa ya ce" Risala, tanada daraja mana, ba magana ce ta na yi auren soyaya da ita ko akasin hakan, tunda har igiyar aurena ya rataya a wuyanta ai tanada daraja, nd maganar tarewa kuwa ai inaga sirri ce ko?"
Risala yanzun kirjinta ya fara dokawa da karfin da har gaban goshinta ke dokawa, a yamutse ta ce" Please, please ka yi shiru..... Please ka rufa min asiri ka yi shiru da maganar nana haka ......kar ka saka na tsorata da furucinka mana?......................, Na san an aura maka ita ama darajarta bata kai tawa ba, domin ni kake so ita kuma hadaku aka yi....., Nd maganar tarewa wannan ai inaga ba wani maganar da zan iya fahimta a cikinta tunda an jima da daura maku aure, kuma bayan wannan idanma maganar wace ta fara zuwa ne ka tambaya mun rigayesu zuwa gidan nan, wai bama wannan ba kamar wata budurwar yarinya zaka ce idan ka yi mata sati? Wani irin sati matar gotai gotai da yaranta da komai?"
"Risala, are u okey?" ABDUL ya fada a hankali yana kallon Risala da mamakinta
Risala ta kamo hannayensa tana mai tabatar masa lalle a cikin hayacinta take
Hakan ya saka shi fuskantarta ya ce" Am, RISALA, kina ji? Ina so ki kiyaye dukkan abinda zai shafi irin magangannun nan idan har bai shafe ki ba, sam bana tunanin zan lamunci haka ta fara fitowa daga kowace daga cikinku, maganar daura aure hakane ama bata tare ba sai a jiya"
Risalas da jikinta ke neman daukan zafi da wani irin yamutsa da ske yi mata a cen cikin kanta kamar zata haukace ta ce" No, no, ba jiya bane yau ne , kuma yau dinma na rigayeta"
ABDUL ya sauke numfashe ya ce" Jiya ta tare, ban san me kuke kira da tarewa ba, wanda na sani nake maki bayani a kai, kuma ta dauki karfin fara yin kwanakinta ne dan ba a rana daya aka daura aurenku ba, kin ga idan har hukunci zamu bi bisa adalci kwanakinta ne muka fara.....so ki yi hakuri koma menene abinda yan kwanaki ne zasu shige na dawo?"
Walahi, ita ba mashayiyar abin maye bace, ama a yanzu sai ta ringa jin ana yi mata mugun kida a cen cikin kanta kamar wace ta saba busawa bata busa ba
Kasa maganar da ta yi ya saka shi mikewa bayan ya mana mata pk a goshi ya fice yana janyo mata kofar, domin kansa shima har ya kwashi ciwon , dama ya wuni da abinsa ya nufi bangarensa dan yin wanka yana tunanin ba zai juri yawon dakunnansu ba, idan komai ya lafa na maganar bakunta zai dora dokar du wace keda shi ita zata zo turaka ( wo wo wo malan, wai kai yaya haka? Mufa sakinmu muke jira me kake jira da mu ne)
ABDUL na fita RISALA ta silale kasa daga saman bed din tanaa kunce daurin kanta ta warware shi sosai tana cusa hannayenta a cikin kitson tana yamutsawa da kardi ta kama jela guda ta ringa ja har sai da kan ya kama sara mata da wani irin karfi sai kuma ta dakata tana kallon waje daya ta ce" ABDUL, ABDUL, kana nufin dakin wancen matar zaka je ka kwana? ABDUL kana nufin dakin wancen matar zaka tafi? Me ma'anar ta tare? Me husarka ke nufi? .....Abdul!" Ta fada da karaji tana sake damkar gaban rigarta da kanta da hannunta ta sake fadin" ABDUL, don't tell me abinda ta fada cewa ta yiwu cikinka ne a jikinta dazu da irin tafiyar da take yi da komai cewa ka sadu da wannan matar?"
Da karfi ta daki abin gadon da hannunta ta ce" ABDUL!, ABDUL!, Kar ka ce min burina da rike kaina da na yi dan darenmu ya zamto unik,na kasance ta farkonka kai har ka ba wata wannan darajar ba ni ba?"
Da wani ihun kuka ta sake fadin
*NZL PAGE3️⃣1️⃣*
Da wani ihun kukan ta sake fadin" ABDUL, ka kirayeta uwar gidana, yar uwata, yayata.....kana son nuna min cewa ne kana sonta itama bayan an fada min grandfather dinka ne ya aura maka ita, an kuma fada min ita din ko wacece?, An fada min har ta haihu? Zaka kai mata kwanakina ne dan cin zali har sati daya dan ta asirceka ko me? Tunda dai kowa ya san ga yarenta nan a kan me zaka wulakanta ni? Waye bai sheda cewa na rigayeta zuwa gidan nan ama sai a bata kwanakin da suke nawa?!, Abdul uwar gidan banza uwar gidan wofi bayan nice amarya koda auren so ka yi da ita ka fi dokina ?, Abdullllllllllllllllllllllllllllllllll kisa kake so na yi? Wayo Allahna, wayo Allah................." Ta karashe da kukanta, sai kuma ta zabura ta rarumo wayarta ta shiga dokawa nahaifiyarta waya
A irin wannan lokacin maman nata kanta tana dakin mahaifinta sunna hirar dare kira ya shigo wayarta na Risala
Tana dagawa Risala ta shiga labarta mata duka yadda suka yi tana sheka kuka
Mahaifiyarta ta shaka iya shaka, rai bace ta ce" Tun ba'a je ko'ina ba kin ga ilar zurfafawa da namiji soyaya ko? Ba laifi yana iya yin abinda ya ga dama tinda an asisrceshi an nashi ya ci a waina, ama ba zan taba lamuntar wannan wulakancin ba, in sha Allah zamu zo a zauna gobe da safe a kan maganar nan, ina hadin bazawara da budurwa? Kuma mu ina ruwanmu da maganar wai itace uwar gida bayan kin rigayeta shiga gidan?, Ai walahi ba zan lamunta ba tsaf ya dawo dakinki idan ya maki sati ke mai darajar a tare da ke sai ya koma mata ya yi mata kwana uku irin na zawarawa irinta, in bandama cin zali ina hadinki da naa wata bagidajiya.....? No ba zan dauki haka ba, ki kwontar da hankalinki in sha Allah goben zamu zo gidan , saima na faraa biyawa na dauko kakarsa mu wuce dan ba zai yiwu ba walahi, a kan haka sai na amshi takardar sakinki!"
Sosi ta hau take zage zage har ta kwontarwa da y'ar hankalinta sannan ta juya ta fuskanci Mahaifin Risalar da yake fadin" Meye kuma daga zuwa yau yau har ta fara kawo kararsa, kin ga ki yiwa yarnan tsawa fa, na kula so take yi ta saka ni a cikin jin kunya , yaushema har zata fara an yi mata an yi mata, aa ni fa bana son irin haka nan gaskiya, ki kwabi yarki ko zata zauna a gidan miji kar ta kaso auren ko sari bai yi ba!"
Mahaifiyar Risala ta mike tana fadin" ai kuwa elhaji sai fai ka shiryawa jin kunya, domin ba zan taba yarda a cutar min ya ba a banza a wofi, shi yasa bana yarda da siyayar dangi dan idab danka ya yiwa yarana na tsaya tsayin daka na hukuntaka daidai da laifinka, danginama ban dagawa kafa ba a kan y'ayana bale jikan yar talakawa? Ai Walahi ba zai yiwu ba".....
Yana kallonta ta shige ciki sai mita take yi da rantse rantsen ba zata sabu ba bindig a ruwa, ta yaya za'a ba ƙatuwar mace kwanan y'arta, ko amarci basu fara da miji ba
Kai ya kada ya yi kwonciyarsa bai bita ba, abu daya ne ya sani idan takamarta ita karyar kudi hajia Hauwau ta dameta ta shanye, kuma a kan jikanta sai ka ga rashin wayonta, bata hada jikanta da kowa fa a rayuwa , ita nan har so ne take nunawa ya? Ta bi a hankali dan yana guje mata garajenta ya hadasa mata husumar da ta fi karfinta, domin lalle ita din yar mai kudi ce, ama ta kasa ganewa gaba da gabanta, su kam
sun yi biyaya
___________________________________
Dakin yaren ya fara zarcewa bayan ya rufe falon da ky yana mamakin Uman biyu da shiririta ta kwonta ne bata rurufe ko'ina ba?
A hankali ya bude dakin ya shiga da salama kasa kasa dan ya tabata warhaka ai sun yi barci
Turus ya yi yana zuba masu ido su uku a saman gadon Uman biyu ta bararaje abinta a daman gadon yaran nan du ta takurasu ta matse masu waje har kamar zata tunkudo Husaini kasa tunda tsakiyarsu ta shige abinta
Habarsa ya kama da hannu biyu, irin idan abu ya bashi mamaki ko haushi da yakan yi dan nuna girman mamakinsa ko jin haushinsa a abun yana kallonta a hankali ya ce" Bata jin magana fa yarinyar nan ko kadan"
Kai ya girgiza ya shige bayi ya duba an kashe dukan abinda zai iya zamowa damuwa wa barcinsu, ya dawo falon, a nan ya ga kaskon turaren wuta da hayaki kadan kadan na dan tashi irin ya cinye din nan saura dan kadan ne a ciki
Ido ya zubawa kaskon yana tunanin anya wannan aikin aikin daya daga cikin ma'aikatan familly dinsu ne? A formation da ake basu na kula da gida idan suka saka turaren wuta sukan tsaya ne har ya gama waje sannan su dauke su tafi da shi
Sake juyowa ya yi ya dake kallon wajen AMINA
Dan kankance idannuwansa ya yi a kanta , sai kuma ya karra tabe bakinsa ya dauke ya fitar ya kashe ya yarda mata kasko a cen ya dawowarsa
Adu'a ya shiga yiwa yaren a hankali yana dafa kansu daya bayan daya har ya gama sannan ya sake kallonta da mamakin nauyi barci ne haka ko dai summa ta yi?
Hannayensa ya saka bayan ya tatare hannun jalabiyar tasa a hankali ya saka a hamatar Amina ya yi mata dagowa irin ta yara sannan ya talabi bayanta ya cicibota gaba dayanta ya mike tsaye da ita a hannunsa
Ido ya sake zarrowa gannin bata farka ba,
Kai ya gyada ya juya a hankali ya fito da niyar mayar da ita dakinta sannan ya dawo ya rufewa yaren dakinsu
A hankali yake tafe da ita yana sake wara dubansa a kan fuskarta domin har wani dan lilo lilo take tana murmushi ga dukkan alamu mafarki take yi ko kuwa idannuwanta biyu neman fitina take yi da shi
A daidai zai shige da ita dakinta ya gwara mata kai da garun wajen, hakan ya saka Amina bude idannuwabta da sauri jin an kwala mata dutsi tana barcin
Ido hudun da suka shi da shi ya sakata sakin ihu ta kubto ta dirmiyo kasa , sai kuma ta saka wani ihun tana kokarin mikewa da dan wara kafa domin ai dinkine a kasanta jama'a
Tsayuwa Abdul ya yi yana binta da kallo tana dan kai kawo tana yarfe hannu yana tanbayar kansa hala dinkin da yawa ne akai mata? Ko kuma an bar mata abin zare na sukarta a wajen?
"Yanzu ni zaka dauka? Ni Amina? Wai kamar wata kanwarka? Mema ya dawo da kai dan girman Allah? Me yasa kake shiga harkata ne ni? Me na yi maka kuma yanzzzzzzzzzzzz"
Gannin yana matsowa kusanta maganarta ta dauke tana zaro ido tana kallonsa
Hannunta ya kama ya nufi bakin gadon da ita ya zaunar da ita yana kallonta cen ciki ya ce" Ina zuwa"
Juyawa ya yi ya fice, hakan ya sa Amina kokarin tashi dan ta rufe dakinta da ky ta zo ta yi tunanin yadda ya dace ta yi da wannan yaron, domin bafa zata yarda ya ringa raina mata wayau ba da girmanta!
Dawowarsa da rufewar kofarta da ky da ya yi ya sakata komawa ta zauna a saman gadon tana zarro ido tana kallonsa
Fitilar dakin ya kashe sannan ya kunna ta kusanta mai hasken ja mai ragagen haske
Yana yi yana fadin" Ki kiyaye barin abin turaren wuta kuma ki yi barci kin ji? Ita wuta batada kadan, kuma aikinta mai girma Ne Amina"
Amina dake binsa da kanta kamar zai karye dan son gannin me yake nufi da ya kama sunnanta gatsau sai da ta ji wani iri, ace kanninka na kama sunnanka fisabililali?
Da gunguni ta shiga fadin" Ko wa'inda suka girmeka Aunty suke ce min, dan ka dauki karfe ka wani ja dare kamar daren mutuwa shikenan sai ka nemi raina wanda ya girmeka?"
A lokacin ABDUL ya gama dube dubensa ya karaso inda take zaunen ya duka kasa hannayensa a saman katifar, hakan ya sa ta ja baya tana son hantsilawa hadi da fadin" Kai wai meye haka?"
Da sauri ya rike kafafuwan nata daria na son kwace masa, shi walahi har yanzu ya kasa yarda bata wuce wata sha bakwai haka ba, wannan shiririta haka?
A hankali ya ce" Me kika ce?"
Amina dake hadiyar yawu da sauri da sauri ta ce" Me zaka min dan Allah?"
ABDUL ya yi dan murmushi ya ce" Ba komai fa, cewa na yi me kika ce?"
Amina ta ringa dauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Cewa na yi wai da, ka ga tunda na girme maka da yawa na ce min aunty , wa'inda na girma haka ka fahimta?"
Kai ya gyada , a hankali ya ce" Nima na ringa ce maki Aunty ne?"
Amina aka wani mane baki aka gyada kai, ita ga Aunty
Murmushi ya yi ya ce" To Auntyna"
Amina ta dan tsatsareshi da ido dan sai ta ji kamar da gatse ya kireta auntyn
A hankali ya shiga dage doguwar rigar barcin nata, a gigice ta daka hannunta tana rike nasa taba kallonsa bakinta har yana hadewa ta ce " ABDUL , menene haka kake shirin yi? Me zaka min? ABDUL ka tashi daga kusana kuma ka daina tabani , ka ga lokaci nake jira ka bani takardata ko? Dan Allah ka barni haka ya isa"
Kansa ya dago a cikin ragagen hasken yana kallon yadda du ta rikice, tsoro na dawainiya da ita karara
A hankali ya ce" Ba komai ba fa zan yi maki"
Amina ta ringa girgiza kanta tana fadin " Ka sake ni, dan Allah ka bani takardata na koma gidana da y'ayana mu yi zamanmu, dan Allah kar ka sake min abinda ka yi min kar ka wulakantani"
Idannuwansa ya dan lumshe a hankali sai kuma ya shiga ambaton Allah a cen kasan zuciyarsa, haka kuma fargaba na cika masa ciki
Shi bai taba haduwa da rigimar dake nufo shi baya son kulawa ba irin wannan, shi a rayuwarsama fadan mutun biyu kawai yake gujewa, bayansu idan rigima ta yi salama yakan nema mata amincin ne shima ya rikota a yi ta yi
Ama wannan yarinyar sam sai ya ringa jin baya so su yi tashin hankali, kuma baya so ya fada mata maganar da zata ji mata ciwo
A hankali ya cire hannayen nata ba da kwaramniya ba ya ce" Dubawa ne zan yi, kar aje da ta maki dinkin ta bara maki yan tsirarun zare, kin san yanada dan kaifu da kuma tsini yana iya damunki ya hannaki sukuni , ko zama kika zo yi a karkace dan kar ya ringa sukar maki wajen, bari in gani?"
Amina, ta kasa fahimta idan ta yi magana baya gane yarenta ne ko kuma bata isa ya ba maganarta mahinmancu bane ya sa baya bi ta kan abinda ta fada, sake maido hannunta ta yi zata kuma rike shi, sai dai yanzun da dan karfi ya tare mata hannunta ya dago da idannwansa da suka fara dan cenza kala, dan Walahi ta cika caza masa kwakwaluwa ya ce" I said , ki barni na gani "
Daidai da amon muryarsa yanzun a wani irin kusashe ya yita, kuma yana yi kamar sai ta bari zai gannin ne bayan tuni ya kaita kwonce ya saka kafafuwansa ya yiwa cinyoyinta yannayin da idan tace zata yi wani motsi mai karfi tana iya jiwa kanta ciwo mai masifar zafi, a dole ta rintse ido jikinta na rawa kadan kadan tana suararonsa hankalinta tamkar zai bar kwakwaluwarta a lokacin da ta ji ya dora hannunsa a hankali yana shafa saman jikinta sannan ya kunna fitilar kusa da gadon ya haske da kyau yana kallon dinkin, harma ya kai yar yatsarsa wajeb zaren ya dan danna a hankali
Kwarai ta zabura, ama ba irin zaburar da idan da sauran zaren zata yi ba, hakan ya sa a hankali ya cire hannunsa yana kallon wajen, dan makoloton wuyansa na ta kai kawo , tunaninsa na neman cenzawa a irin wannan lokacin, inda harshensa keta neman zirowa ya kai ziyara a wajen, sai dai irin yadda jikinta ke rawa a hankali ya ja mata rigarta yana dan jimke hannunsa da ya fara dan bari kadan sannan ya haura saman gadon a hankali ya ja bargo ya luluba mata bayan ya jata saman gaba dayanta
Idannuwanta a rintse suke, ita dai ta kasa kwakwaran motsi domin tsoron da take ji ya fi komai yin tasiri a kanta a yanzu
A hankali ABDUL RA'UF ya shige cikin bargon da ta kudunduna