Showing 129001 words to 132000 words out of 145392 words
Chapter 44 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
daga ciki ta dan dago daga gyara ruwan wankan, da ruwan gyaran da tun yau ta dauri aniyar fara shi na jego ba ja da baya ba gudu ba sasautawa ta ce" Kwarai kuwa maza tube malama "
Baki ta turo tana karasawa kasa kasa ta ce" Ai inaga ke baki damu ba ki ringa sala min wanka abinki, haka kika min ai na nonon rakumi"
Baba ta yi daria ta ce" Bakin nan ba zai mutu ba, Fido taimaka min ta cire komai"
Ido ta zarro ta ce" Ah wannan fa daya, fido fita dilla, kin wani tsaya a gaban manya zaki tubeni, jeki jeki kawai"
Su duka daria suka saka dan a yadda ta yin tana hararar Fidon dole a dara
Tubewa ta yi da kyar ta zauna saman kujera, Baba kuwa ta shiga kwatanta mata komai dan kar ya zo mata a ba zata sannan ta shiga kwatanta mata zafin ruwan
Ai kuwa an sha daru, domin da kyar ta zauna aka yayaba mata ruwan wankan jegon, sannan aka mayar da shi gefe aka matso kayan gyara
Kayan take kallo, a zuciyarta tana jin eh lalle tana na'am da su, haka kawai wannan karron take jin har sai ta karra gyaran jiki na zama cikin dumamar madara da kurkum, ji take yi a cen kasan zuciyarta tun kafin ta gama jinnin haila zata fara dafa kaza da bankanr dukkan abinda ya dace na gyara, haka kawai take ji idan bata yi haka ba, ba zata iya fuskantar du wani mai ruwa da tsaki a hargitsata ba.........
Sosai ta nutsu Baba ta darjeta, sannan Fido ta sake kawo wani ruwan aka sake sirka shi sosai aka sake binta da shi
Tana fitowa Fido da ta gama hada mata danyar madara sabuwar tatsa da maganin gyaran noni ta mika mata ita kuwa ta zauna ba gardama ta kafa kanta ta shanye tasss
Baba ta ciro mata abin daure ciki, Fido kuwa ta sauko kayanta da ta turara mata sasaukan kaya mararsa nauyi, riga da sket na yadi mai laushi da rigar mama harda wani tsuma mai kyau wanda ta tanadar mata shi ne dan idan nononta na zuba ta ninka shi ta saka shi a wajen dan kar ya bata mata jiki da karni
Tana zaune da tawul din sai da Fido ta busar mata da gashinta sannan ta daure da dan ribom karami tana jin wankan nan sosai take jin jikinta ya yi dama dama , gajiya ce dai ta haihuwa wannan sai a hankali, ama ba ita zta hannata kimtsa kanta yadda ya dace ba
Sai da ta turara jikinta da sansanyan turaran wuta, ta dauko kwalin da ta jima bata saka ba ta sakawa idannuwanta , sannan ta dauki jan bakin da ta yi dan tsai tana kallonsa, sai kuma ta yi murmushi ta dan gogawa lebenta ƙadan ba da yawa ba sannan ta daure cikin nata ta saka bra din da rigar , kuma ta saka sket din tana dan buda kafarta ta ce" Fido kin tabata zan iya barcin kirki da sket din nan?"
Fido ta ce" Sosai aunty, ko kim fi son zani ne?"
Baba ta dago daga tatare kaya tana mayarwa ta ce" Ke rabani da wani zani, wannan din ya isa ai gayanan yana jayuwa sosai kuma ya zauna mata bai matseta ba, barta ta fara abin kirki kar ki sa ta fasa
Abaya fara mai haske sosai , watau shara shara ta dora sai mayafin abayar ta ce" Baba wannan abayar fa sabuwa ce kamar wace zan je anguwa?"
Firdausi ta ce" Aunty kin san yanzu baki zaku yi ta yi, da abokansa da yarensa da matansu da mazansu, ga mai wancen dakin itama ko?"
Amina ta yi murmushi a ranta ta ayana' Ga shima da kansa mai gidan, wanda sai na bambance masa kalar nawa rike wuyan namijin da na wace ke lasarsa!, ABDUL........... Mutu ka raba da ni da kai, na yi aniyar zama da kai, babu mai rabani da kai...... Ciki ko kai ne!, Sai dai JARABAWA!'. ( ABDUL mata bisa kanka fa)
A hankali take takawa yanzun , Fido na gefenta , Baba Kuwa tana idasa kimtsa dakin da saka turaren wuta
Dan dakatawa ta yi tana hutawa, Fido kasa kasa ta ce" Aunty mijinki sai kallonki yake"
Amina da ta sani sarai, domin tunda ta fito ta tsinci idannuwansa a jikinta ama ta basar ta dan harareta tana fadin" Zan fa mare ki"
Firdausi ta yi dariya da sauri tana tare yaren da suka saka ihu sunna nufo mamansu ta ce" Kai meye haka dilla ku nutsu kar ku kayar da ita!"
Amina ta dubeta ta ce" Firdausi kin ga bana son haka kin ji, matsa min na ji dumin y'ayana mana haba dan Allah"
Firdausi ta dan matsa tana karasawa ta ce" Ai sai ku yi tunda sabonku ne!"
A hankali ta ringa rungume su tana ta aukin tambayarsu sun ci abinci? Sun yi kaza? Sun yi kaza?, Tamkar wace ta shekara bata tare da su
A hankali ya karaso hannayensa rungume saman kirjinsa yana kallonta , girman cikin nan ya ragu sosai ga daure shi da aka yi, sasaukar shigarta ta tafi da imaninsa, nutsuwar kan fuskarta, da dogon karan hancinta, zuwa lebunnanta na gigita duniyarsa
A hankali ya ce" Amyn Farid, Fadeel......Amna nd Ammar?"
Wani irin tsammmmm. Ya sake ratsa dukkan jikinta, a hankali ta dago idannuwanta tana dan son riko Hasan da ya rage domin Husaini tuni ya koma wajen Hajia dan ta bude yaren a karro na biyu tana jajen a zo a basu nono su sha
Hannunsa ya janye cike da farin ciki shima ya nufi cen din harda dan tsalensa ya barta da Abdul
Ido ta zarro a hankali tana rakashi da kallo, sai kuma ta dawo dubanta kan Abdul
A hankali ya yi murmushi a saman lebensa ya furta" I love you"
Da sauro ta dauke dubanta, kirjinta na bugawa ta nemi rabe shi dan komawa wajen katifar
A hankali ya karasa gefenta kadan ya riko hannunta cikin nasa yana dan murzawa ya ce" Hajia, kin ga wai kar na taimaka mata"
Hajia ta juyo , daidai Amina ta yi tsuru tsuru ta ce" Amina zaki karaso ki basu hakinsu ne yaren nan ko sai sun fara galabaita?"
Amina ta gala masa harara tana turo baki a hankali ta karaso din ta zauna saman kujera ta zuba masu ido yadda suka zuba mata tana jira kowa ya fira sai ta ba yaran nonon ko? Ai ja za'a sakata tubewa a cikin jama'a ba ko?
Hajia ta sauko wajen katifar tana duban Fido ta ce" Kawota ita sarkin kukan a sakasu tare kin ga shima ya fara gajiyawa bawan Allah
Gyara zamanki mana Amina?"
Ido ta zarro tana kallon Hajia muryarta a sanyaye ta ce" Hajia, ba sai na shiga ciki ba zan basu?"
Hajia ta kalleta da mamaki ta ce" Cikin ina?, Amina bude rigarki ki ba yara nono mana?"
Da ido da baki ta sake budewa da mamaki tana kallon Hajiar, kasa kasa ta ce" Hajia da maza fa a dakin"
Hajia ta juyo tana neme nemen mazan, maza dai hudu ne a dakin, Mijinta, yarenta biyu, sai shi dan jaririn dake cikin tsuma
Abdul kuwa ya gyara zama daria na son kubce masa, so yake sai ya ga nonon, shi fa nonon zai gani da kuma yadda za'a ba yaren, ya san sai an yi wannan rigimar, shi kuwa abinda zai saka shi nishadi kennan
Hajia ta kama abayar ta yayeta har ta hada da dan kwalin, hakan ya bayanar da lalausan gashinta mai cika da baki da daukan ido
Hajia ta fara fada tana cewa" Kai ku ji min yarinya, yaren nan tun a asibiti suke rarume rarume kina kallonsu kina sada kai kamar gaki a gaban sirikanki, ki bude ki badu kalaci tun muna mu biyu"
Amina zata yi magana tana tare hannun Hajia da zata ciro mata nono aka yi salama
Risala ce, da mahaifiyarta, da auntynta suka shigo cikin shiga irin ta kece raini sa nan suka ja suka tsaya sunna jiran gannin idan wajen ya isa su zauna ko su gaisar da su daga tsaye su juya?
Juyowar da hajia ta yi , ganninta da suka yi, a irin wajen da suka ganta a zaune, da kallon da ta masu ta fauke kanta, bama kamar Risala da take jin haushin sai yanzu ta shigo gannin yar uwarta da ta haihu? Haihuwa fa? A fitarta ana iya dawowa da gawarta fa? Ama ko ta lekota? Ita bata tsoron itama ta sameta ne? Idan ta sameta daga ita sai ita a gidan fa? Ko ta isarwa kanta komai ne ita mai iyaye?
Kusan kimuwa a kasa Maman Rislaa ta yi gannin kamar goshin Amina da na hajia zai hadu ana kiciniyar ciro nono ta ce" Kamar Hajia Hauwau a nan?"
Hajia ta sake juyowa bayan ta ciro nonon ta amso yar, shi Kuwa ABDUL daga zaune har dadage yake yana leka nonon da mamakin ya karun kuwa ya ji Hajia na fadin" Eh nice wai ba zaku shigo bane kunna tsaitsaye a kan dokin kofa?"
Mamakinta kasa boyuwa ya yi, ta ce" Ke ce? A nan? Hajia?"
Hajia ta juyo da Yar a hannunta tana dan zizigaTA ta dubeta da mamaki itama ta ce" Eh nice hajia nace ku karaso mana kun tsaitsaya a bakin hanya?"
Maman Risala ta dafe haba, irin mamakin nan, da tarin abin al'ajabi ta ce" Ikon Allah, abin mamaki baya karewa, yau ga hajia a dakin mai waina rike da y'arta"
Ba kalacin Hajia ba, yau harta Risala sai da ta juyo a zabure, dan ta tabata maganar mamanta a ciki ta so yi ta fito waje
ABDUL kuwa kallo daya ya mata ya sake maida kansa kan Amina dake ta kare nononta yana murmushi, shi fa Allah yana ganni matar du ta sare masa walahi
Hajia kuwa sai da ta mata kallon anya kinada hankali? Sannan ta ce"
Hajia ta tabe Baki tana gyada kanta tace " Nifa kwata kwata ban fahimci inda kika dosa ba, me kike nufi ne?
A hankali Abdul ya e hajia ki saka yarinyar a nono mana kar ta mayar?
Hajia tace ko ina zuwa
Ta sake gyara Amina da kyau ta ciri nonon duka biyu ta tallaba hannunta ta nuna mata ta saka macen a hannun dama, sannan ta saka namijin a hannun hagu ta saka gizo tallabe mata shi kafin ta iya da kanta tana fadin sai kin jure fa akoi zafi
Amina ta guda kanta tana rantse idanunta domin namijin kamar jira yake yayi rage dashi macen ce ma ake ta koya mata a hankali a hankali
Karasa wa tayi tana kallon Risala ta ce" Ke tun jiya kina ina har mu na waje muka shigo muka raka yar uwarki haihuwa bakya wajen? Sannan har aka sakomu yau sai
ciro waya ya koma ya gyara zamansa yana daukanta hotuna a dabarance yana murmushi
bata san kin sauko daga kiyayar da kike yiwa matar jikan naki ba shi yasa ta yi mamaki har ta furta, kin san ita batada munafurci ko cem, takan fadi abinda take tunani komai muninsa ne sai dai ka yi hakuri idan ya maka ciwo"
Hajia ta gyada kanta ta ce" Hakane, ba mamaki, halaya ne ai na mahaukata, gashi ita kuma cikin kyakyawar shiga"
"Hajia nice kike zagi da mahaukaciya kuma yau?, Hajia nice mahaukaciya? Walahi ni ba mahaukaciya bace, ai ba karya aka yi maki ba, da baki nuna mata kiyayar ba ai da ba zan zo na fada ba, ko kin ga na maki kage a nan ne? Maman risala da itama ta harzuka ta fada har tana cire hannun yar uwarta dake mayar da ita baya dan bata so ko kadan Maman risalar ta zubar da mutuncinta a idannuwan sirikinta, duda aikin gama ya gama sunne basu sani ba, a hausa ai ba'a haka, bahaushe da kunya da kara aka sanshi ba shirme ba
Rai bace ta ce" Dan Allah adda ki daina turani haba dan Allah, ita komai ya tashi sai ta wani nemi ta wulakanta mutane , ai nima ba yar talaka bace bale a zageni da arziki, ita yarinyar da kika tsana din ai dan yar mai datin hula ce, ko karya aka yi? Kema da bakinki kin ce jikanki ba zai zauna da mai tuyar waina tana bi kwararo kwararo da ƴaƴan shegu a hannunta ba, shine yanzu zaki wani hade kai da ita a cutar min ya? Ba zai yiwu ba tunda aka fara haka Risalar ba zata ga da kyau a wajenki ba, Risala kuwa yar gata ce gaba da baya ba zan bari a wulakanta min yata ina ji ina gani ba, koda banida da shi ba zan yarda abinda kika yiwa wancen ki yiwa yata ba walahi!, Ke risala wuce mu tagi gida wuce min!" Sama sama take maganar danma du wanda bai ji ba ya ji, gaba daya zagin da ta juyewa su Amina da wulakanci tasss kowa ya ji haka kuma sirikinta dake murmushi gaba daya murmushin ya dauke a fatar bakinsa
A nutse ya mike cikin shigar dakakiyar shadarsa ya karaso yana kallonsu
Aa hankali ya ce" am, ku yi hakuri ku koma waje, yanzu ta fito daga asibiti hayaniyar nan ba zata haifar mata da abin alkhairi ba................"
Maman Risala ta tabe baki, bata sake wata muguwar maganar ba dan ko HAJIAR gaba daya bakinta a mace tana kallonsu ne
Maman Risala ta sake lekowa ta ce" Ke wai ba da ke nake ba dan kutumar ubanki?"
Risala ta juyo ifannuwanta sun cika da kwallah ta fara taku daya biyu ta tsinkayi muryarsa a dakensa ya ce" Idan kika fita daga get din gidana a yau ba tare da izinina ba na yanke igiyoyin aurena dake kanki"
A haukace ta ci birki tana juyowa ta kalle shi idannuwanta na firfitowa waje
Haka mahaifiyarta da yar uwarta, haka hajia ta juyo tana kallonsa zuciyarta na karra tsintsinkewa
Bakinta na rawa ta ringa nuna kanta, da shi tana son furta wani abin ama ta rasa mene
Mahaifiyarta ta sake shaka ta saka hannunta ta fardota tana fadin" Sai me, ai mai kyai baya tsawa , wuce mu je Alhamdulilah ba ciki bs goyo bale abin duniya ya isheni, menene a auren da ya wuce cusa bakin ciki da kaskantar da mutun da darajarsa da komai? Wuce mu je zaki samu sama da shi a komai, ai ba shi bane autan maza a duniya!"
Janyo hannun yar take yi , yar na tirjewa
Da karfi ta sake juyo da ita dan ta fuskanci kamar bata jinta, sai dai abinda y'ar ta yi ya sakata zuba mata ido, domin hannunta ne ta janye a hankali hawaye na zubowa yana neman bata kwaliyar da idan biya ne zasu yi a yi mata zasu iya kwararar dubu hamsin
A hankali ta ce" Risa, mu tafi mana kar rana ta yi zafi ta taba maki fata kin ji?"
A hankali Risala ta langwabar da kanta tana kallon Mamanta
ABDUL kuwa ya kama hannun Hajia da ta zama tamkar gunki ya shige ciki da ita, direct dakin Fido domin ya kula tana da bukatar dan kadaicewa ko yayane
A hankali Maman Risala, dan kar su Amina su jiyota ta ce " Me kike nufi da dakatawa a nan bayan kina gannin wulakancin da ake mana , ni uwarki da ke din kanki?"
Risala ta fashe da kukan da take rikewa ta kasa yin magana
Mamanta ta zarro idannuwanta tana nuna kanta ta ce" Risa, risa namiji zaki zaba a kaina?"
Da sauri ta girgiza kanta tana kallon mamanta ta ce" Aa mama, ba maganar na zabeshi bane mama, mama a shekara ashirin da takwas na same shi, na so shi, ya so ni, mun yi aure, yanzu na kai ashirin da tara a duniya, idan har ba zanen kadara ta fitar da ni ba zaki so na dawo na sake maki wani zaman? Mama banida matsala da shi, ban rasa komai ba, kema kin san a aurena zuwa yanzu na tara abinda ban tara ba kafin auren nawa......., Mama kakarsa ce, itace mamansa, itace duniyarsa, idan tana fada s kansa bana gannin laifinta, kamar kece da mu fa.........
, Mama, babar matsalarma ina son shi, mama ina son mijina, idan na biki muka tafi na dawo ina neman saka kanmu a uku baki dayanmu fa? Dan na tabata wata rana sai na tarda ABDUL, idan yau ya koreni, gobe ya koreni, jibi ya koreni, wata rana ina iya samun galaba a kansa, ina iya sakashi a uku, uwa uba na saka kaina...Mama ribar me zaki ci?....."
Dau mahaifiyarta ta dauketa da wani mahaukacin Mari tna nunata da yatsarta ta ce" Ni zaki watsawa kasa a ido a kan Kato?"
Risala da ta duke tana kuka tana girgiza kai, yayar mahaifiyarta na rike mahaifiyar tata har suka janyeta suka fita da ita a falon Amina sannan ta mike da gudu itama ta fita ta nufi bangarenta tana cire abubuwan kwaliyar da aka bata lokaci ana mata dan ta yi kira ta sanar kishiyarta ta haihu , mahaifiyarta ta zabo mata leshen dake da kyau da tsafa aka caka mata dauri, ama abin ya kare a haka? Yanzu yau ita da mahaifiyarta ne wannan abu ya faru? Ina zata shiga da ranta? Shin ABDUL da mamanta wane zata zaba? Idan ta yarda ta zabi Abdul din ya wulakantata da gaske fa? Shin yaya zata yi da rayuwarta?
Wayarta ta dauka ta ringa kiran mahaifinta, sai dai ya fada mata yana cikin aiki, da zarar ya zauna zasu yi magana, a dole ta kashe ta ci gaba da kukanta, domin an saba mata tana samun damuwa takan yi kiran mamanta ne ta zo inda take, ama a yau da maman nata ne damuwar a dole ta rasa inda zata saka kanta
____________________&__
A cikin daki,
Tunda ya zaunar da ita ya fice ya je ya samo mata ruwa mai dan sanyi sannan ya dawo ta wajen su Firdausi dake zaune jigum jigum yana dan murmushi ya ce" Sorry an mata mun shiga dakin cen dan lokaci?"
Fido ta yi murmushi tana fadin" Dady mu da muke nan muna dan hirarmuma"
Shima ya yi murmushin ya kalli Amina kkasa kasa ya ce" Sun sha?"
Manyan idannuwanta ta dago ta dora saman fuskarsa, a hankali ta dan masu kasa kasa sai kuma ta mayyar bakin hanyar da Fido ta bi dan basu waje
Murmushi ya yi ya