Showing 3001 words to 6000 words out of 145392 words
Chapter 2 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
sake kallonsa tare da auna irin yadda yake daukan maganar a saukake ba tare da ta rikita tunaninsa na yaro kamarsa ba, duda Hasan din nata yana da shekara takwas ne aman wasu abubuwan idan ya yi zaka dauka ya rufe goma ko ya haura ne, domin shiru shirun da yake yawan yi a yawancin lokuta yakan auna abubuwan dake zagaye da shi ne, dan uwansa ne mai zuba surutu ko ba ma'ana
Hasan ya girgiza kansa sai kuma ya ce" To ke yaushe zaki sayi taki Mama?"
Wannan karron har wani dan murmushi ya subuce mata tana kallonsa da manyan idannuwanta ta sake wara hannayenta tana tunanin in ba yarinta ba yau rigimar Hasan a kan mota ne yake yi? Ta ce" Zan siya idan Allah ya hore min , na ringa saka ka a ciki ina yawatawa da kai da izinin ubangiji, wai Jaririna kana adu'ar da nace ka ringa yi kai da dan uwanka kuwa?"
Sai a yanzu ya saki dan murmushin da ya saka fuskarsa wadatuwa da ni'imtacen ni'ima yalwataciya ya shiga kunce takalminsa yana kuma magana da yannayin dake nuni da ya sauko ya saku har ya fara wasa ya ce" Sosai fa, dan ranar har Liman ya so barina a masalaci ina ta fadawa Allah cewa, Ya Allah ka sa kasarmu ta samu lafiya da kwonciyar hankali mai dorewa, ya Allah ka saka tausayin talakawa a zukatan magabatanmu, ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani, ya Allah ka ba mamana dukkan abinda take bukata duniya da kiyama .....danma ina manta sauran "
Dariya ta yi tana jin zuciyarta ta saku da daurewar yaron ta mike tana sake kilace kulin da bata san ta yadda zata sayo man suyarsa ba ta dage labule sosai dan su samu yalwataciyar iskan itaciyar mangwaron dake basu sanyi tana fadin" Mantawa kake yi ko? Kulun ka fara da neman gafara, ka yi fatan gamawa da duniya lafiya, ka roki Allah ya kareka da dukan sharin abin ki, ka kuma fadawa Allah ya hanneka cin haram da cin zalin bawansa....., Sannan sai ka kawo sauran bukatun duniya domin........"
Daga bayin da Useini ya fito da dan gajeran wandonsa da bokicin wankan da kwondon sosonsa ya ajiye yana fadin" Domin duniyar ba matabata bace, lahira ce mai dorewa, dukkan bawan da ya san da haka zai yi kokarin neman lahirarsa fiye da duniya, wayo cikina Mama wollaj furar nan ta Baban nan taki ta yi gardi da yawa na koshi na koshi sosai zan shiga barci kafin ki samo na daren, ni yau da san samune na ci taliya yar murde da dan waken fulawa da man ja mai gardi walahi........"
Da ido suka raka shi ya shige ciki yana wani dan sauri kar ya bata jikinsa
Daria ta yi tana girgiza kanta tana jin dadin yadda nacin maimaita masu kalamai masu mahinmanci ya sa yaren suke rikewa harma suke maimaita mata da zaran ta dauko maganar dan sake tunatar da su,ita dai tana fata Allah ya bata ikon ba y'ayan nan tarbiya gwargwadon iyawarta, bata san hakan da take yi shine daidai ko ba daidai ba? Bata taba haihuwa ba duda shekarunta a yanzun sun kusan kaiwa talatin, bata taba raino ba sai a kansu, tana kamanta kyakyawan halaya na iyayensu da alakarsu ta shakuwa ne a kan yaren, sannan tana tambayar taimako na yadda zatana saka su a hanya a wajen malamai da manyan datijan anguwar dan samun nagartacen fahimta tsakaninta da y'ayan y'ar uwar tata, sai kuma ta shiga tunanin takiya da dan waken da ya fada ya shige barci abinsa a lokacin da Hasan ke fadin" Kai acici ko? Ba za'a dafa din ba wannan furar da muka sha ta ishemu har gobe, kai kawai ka ci ka je bayi shine kwonciyar hankakinka? Mtsssssss!"
Ita dai bata tofa masu ba domin yanzu ne zasu rikice wannan yace ta bi bayan wannan wannan yace ai shine mai gaskiya, sai kawai ta shuge cikin itama dan ta cenza suturarta ta samu wankan idan Hassan ya fito daga bayin da ya nufa
Wannan kenan.
______________________________________
🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️
_*NI ZAN LADABI*_
🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️
*NA*
*SAJIDA NIGER*
Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida
Wannan Novel na kudi ne ba free bane
Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER
Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka
*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰*
*Page 0️⃣2️⃣*
Barci suka samu wadatace har yama ta kusan yi domin har an fara kiraye kirayen sallar la'asar
A nutse ta mike ta dauro alwallah ta dawo dakin tana tashinsu ta umarcesu zuwa Masallaci da nasihar banda fada a hanya kuma kar daya ya saki ya bar daya a baya su dawo tare
Tana tsaye sai da ta ga fitarsu ta rataya sakata ta sake komawa saman nata dardumar ta kabarta sallah
Bayan ta gama adu'ar da ta saba ita ta ci gaba da yiwa naci, ba zata taba manta daren da aka shigo mata gidan nan ba, ba zata taba manta wannan rana ba, Allah ya tsaya mata ba'a cin mata ba, ama tunda daga lokacin take taka tsantsan da komai da addu'a, ta tabata wanda ya shigo mata ya nemi lalubarta ba yaro karami bane, abinda ya fi damunta yanzun gamawar da zata yi ta leka wajen mai kanti amsar kayan da zata hadawa kulin cen kar ya lalace
Buga kofar ta sakata mikewa ta zira hijabinta dogo sosai ta je ta bude masu tana murmushi hadi da fadin" Oyoyo biyuna"
Hassan ne ya fara shigewa yana cika yana batsewa, da sauri ta dan leka sai kuma ta ja baya kadan tana fadin" Au baba direba kaine ashe ke tafe"
Yar dariya ya yi yana fadin" Gaske Mai tsuntsaye ke hade min fuska daga cewa zasu dawo gidana da zama ina son na auri aminsu, yanzu Mai baban sunna nine Baba?"
Shiru Amina ta yi daga zauren bata leko ba haka kuma bata amsa ba, ita abindama ya fi damunta Husain dake tare da shi yake kuma jin abinda ya fada din
Dan murmushi ya kuma yi ya ce" Ba zaki ce komai ba maman biyu?"
A hankali ta ajiye numfashi ta ce" Uhum"
Daga wannan bata dake cewa komai ba, dama ya san ba nisa maganarsu ke yi ba, ko gidan ta je jefi jefi dan gudun kar Mai Shanu ya tako da kansa yace shi ya zo a yi zumuncin bata kula mutane irin a yi ta hira da dariyar nan, sama sama ake dan gaisawa ta yi gagawar shigewa, a gidan Mai Shanu da matarsa samarin ma'aikatan gidan na mararin mu'amalantar wannan cakwaikwai din budurwa mai yan samari, masu auren wasu na son aurenta wasu kuwa abinda ke cikin hijab dinta suke son yayewa su ga wacece ita a fili, sai dai kamun kanta da mutunta mutanenta ya sa ake shayin kawo mata maganar banza bale har a nemi haye mata fuska, a lokacin da aka diro mata Mai Shanu ne da kansa ya zuba polisawa aka kusan sati ana bincike ama ba'a gano wanda ya diro mata ba, kuma ta ki ta kaura gidan Mai Shanun kamar yadda ya so, ta gwamace mu'amalantar gidan da mai gidan da matarsa mai shekaru madaidaita da manyan mata masu aji yan siyasa na kafawa a jarida suka malaka watau shekara hamsin da hudu a duniya
Kudin dake hannunsa ya ba Husain yana fadin" Dama Mai Shanu ne yace a kawo wannan"
Kudin Husain ya shigo ya miko mata ta yi raf da hannunsa rike da kudin tana hararsa kadan dan irin yadda yake da wani hali daban da dan uwansa na shigewa mutane , shi kowa abokinsa ne ta ce" To ama baba ai kudin watan da ta bada na Waina ba karewa suka yi ba"
Ya ce" Eh sai da yace ta yiwu kice hala, yace ace maki a nan dubu goma kudin makarantar biyu ne, dubu biyar ki yi kudin adaidaita ki yi kokarin ki yi anfani da sauran yana so ki yiwa wainar hatsin nan miya ta gargajiya inaga dai ga dukkan alamu za'a samu ziyarar jikansa ne "
Kai ta gyada kamar yana kallonta sai kuma ta amsa shi ta juya tana sakawa gidan sakata ba tare da ta bashi damar shiga gidanta ba
Da dan gagawa take kimtsawa bayan ta gama yin wanka da rubuta dukkan abubuwan da tsle da bukata, sai kuma ta zauna tana tunanin inda ya dace ta je ta samo kwanuka masu sauki da kuma sauran kayan miyar da a yanzu ba zata iya samu ba gashi wainar tuyar asusuba take yi ta mika masu da sasafe
Hannayen yarenta ta riko suka fito sunna tafia bayan ta rufe gidan da ky dinta
Mijin Inar saude ne ya tsaya a gabansu da adaidaitarsa sabuwa dal sai walwali take yi ya leko kansa yana fadin" Uman biyu ce da kanta da yamacin nan? Sai ina ku shige mu je"
Dan murmushi ta yi ta ce" Aban Saudat mune, ni da kaina ban san ina zan samu siyayata ba na dai fito na san ba zamu rasa ba idan mun shiga ciki sosai wajen bariki"
"Me kike son siya ne?"
Ya fada bayan sun shiga yana kunna adaidaitar hadi da wanata kadan
Amina ta ce" Ina so na yi siyayar abubuwan da zan yi miyar gargajiya harma da kwano idan da hali"
Dan jim ya yi sai kuma ya ce" Ni kuwa na san inda zan kaiki, mu je Rahusa gaba daya abinda kike so zaki samu da rahusa a shagon"
Ita dai bata ce komai ba, hasalima bata dan inane Rahusa ba sai kawai ta yi shiru a bayan motar adaidaitar ya ja su ya tafi
Sun yi tafia mai dan tsayi gaskiya , sunna karasowa ta kalli sunnan wajen ta kalle shi ta ce" Kayan miya fa nace Aban Saudat?"
Daria ya yi ya ce" Kwarai kuwa, ai idan kika shiga nan babu ce kawai babu, komai kuma da layinsa da masu kula da layin, ki je ki gani da idannuwanki "
Kai ta gyada a ranta tana ayana'" Masha Allah mutane sunna da hikimar nema, ama a wannan waje da tun daga nan zaka iya hango bayan ACn dake jejefe ace wai kayan miya ke ciki sunna shan sanyin? Su kayan miya an ci gaba"
A hankali suke tafia, tunda ta shigo wajen ta karanta layin abinda take nema ta dauki hanyar ta nemi shagalta da kalle kalle da mamakin kayayakin dake cike a wajen
Lalle babu ce kawai babu, harta da albasa sai da ta ga kala uku , dadawa ta kasa kasa, kai harta da atarugu gashi a kilace a wajensa, gaba daya sai ta shagalta tgana tura abin tana karanta kudin abubuwan tana dauka a hankali har ta gama siyayar ta koma zagayen kwanonin ta shiga bi tana karanta kudadensu tana zarro ido da mamakin yanzu wani fa sai ya siyi wannan kwanon mai kudin gadon budurwa na aure ya zuba abinci ko? Har ta gangaro wajen kannanun masu kannanun kudi tana karantawa tana waiga manyan ta jinjina kai tace gaskiyane, da bambanci ko a kallo, tana yi ne ba tare da ta kula da kowa ba, koda yake babu wanda ya damu da wani, daidaikun matan nema wata kan alli skin dinta a fuzge ta sake kallonta a fuzge ba tare da ta kureta da kallo ba a ranta ta ayana masha Allah, bata taba gannin black beauty mai lalausan kyau irin wannan ba, bakinta mai birgewa ne da shiga ido sosai, du kuwa irin yadda ya ciza haka yske da shiga ido da birgewa
Sai da ta dauki kwano daya da miya tana duba kudinsu gabanta ya fadi ta juyo da sauri bayanta dan son gannin yarenta
Wayam din da ta gani ya sakata sake wara idannuwanta tana dubawa cikin mutanen dake bangaren kwanonin ko sunna cikin su? Ama wayam babu su babu alamunsu
Da sauri ta juyo kurar ta shiga bin bayanta hanyar da ta biyoa hankali tana furta" Fadeel? Farid? Hasan? Husain?"
Rashin gannin alamunsu ko mai kama da su jikinta ya fara rawa, lokaci daya ta nemi rikicewa tamkar ba ita ba, bata taba jin tashin hankali irin na wannan ba bayan rasuwar iyayenta, kai ko halin da kanwarta ke ciki bai taba daga mata hankali irin wannan ba
A hanzarce ta shiga tura kurar da dan gudu gudu sannan ta kara ware muryarta tana kiran sunnayensu
Da karfi ta bangaji kurar wani mutumen da ya fito yana tura tasa kurar shima , mutumen ba yaro bane gaskiya baban mutun ne kuma kasancewar tasa kurar abinda ke ciki ba wani bane sai batirin da ya zo siya da abin gyaran gashin maza kurarsa ta kifa a wajen lokaci daya ta dafe bakinta da hannayenta ta fashe da kuka tana juyawa ta saki dayan hannun nata ta dora saman kanta da da dan karfi ta shiga fadin" Wayo na shiga uku kardai an sace min y'ayana? Wayo Allahna na shigo nan da y'ayana basa yin nisa da ni yanzu kuma basa tare da ni! Hasan? Husain!?"
Ma'aikatan da suka kwashe kayan suka riko mata kurarta ne macen ta karaso tana kamota tana fadin" Calm down Madame, y'ayanki ba zasu bace ba akoy CCTV ta ko'ina a nan mu je cen baban dakin kusa da office din oga a hasko su na tabata sunna cikin nan sunna yawonsu ki daina kuka ba'a satar yara a nan"
Ita dai bata daina kukan ba, haka kuma bata gamsu da kowa a wajen ba, da sauri take bin matar tana riko fari kal din hijab dinta da ya karra haska hasken duhun fatarta suka zo shiga wajenma abin kallo ne , watau wajen sai ka tsaya nanma an cajeka da abin nan na caje mutun sannan sai an maka daukan zafin zazabin wannan cuta ta zamani mai taken covid 19
Du ta kagauta, bata taba jin tana iya zma terrorist ba irin na yau, a cen kasan zuciyarta babu irin abinda shedan la'anane baya kitsa mata, ciki harda idan har dauke mata ya'ya aka yi ta tabata mai wajen nan ne ita kuwa da hannunta zata bankawa wajen nan wuta kowa ya kone, domin ta san wannan din ba abokin gabar gwamnati bane!
Sunna shiha wani launin kanshi da sanyin daban da na baban filin sana'ar ya buso su, ama ita Amina sam bata ji shi ba, matatakala suka kama hawa sai da suka yi hawa biyu sannan suka shiga Lift ya hauda su hawa na nawa bata sani ba ita dai ta ga an bude nan da nan sun fito
Yan tafia kadan ce suka yi yanzun suka ido mamakeken ofice din dake dauke da na'urorin da ma'aikata manya manyan masu ilimin dake kula da aiki da na'urorin wajen
Sunna shiha kunnayenta suka ringa jiyo mata muryarsa da gura gura watau Husain yana fadin" To kai Hasan tsakani da Allah kaima baka ji ya birgeka ba biscuit din cen? Kuma fa ka ga yinwar yama nake ji, ni walahi dama sauran suka bani na cinye dan na san mama zata biya idan ta zo!"
Hasan da haushi ya gama cika shi na maganar da matar dake tsayen cen ta fada a kansu cewa barayi ne su ko? Sun shigo ne da wa? Wa ya bari yara kananu suka shigo su yiwa mutane sata? Yau sai ta ga iyayensu sun biya kudin biscuit din nan gobema sa saki yara sunna masu barna a waje ya ce" Ka yiwa mutane shiru! Ba zaka ci biscuit din ba! Kai baka tunanin inda Mama take ne? "
" Fadeel" ta fada a raunane tana fashewa da wani kukan da ya fito daga zuciyarta hade da dariya tamkkar wata tabarariyar yarinya lokaci daya fuskar yaren da take boyewa ta bayana a tatare da ita ta duka kasa sosai suka zo suka fada jikinta karfin soyaya da shaukin ganninsu ya debeta yana ta rungumarsu tana kukan hadi da fadim" Ashe ba'a sace ku ba? Ashe kunna nan? Me yasa kuka fita a bayana? Ina kuka je? Wa ya kawo ku nan?"
Muryar matar ne fuskarta a hade tana tsaye cikin shiga ta sweet bakake irin uniform din du wani baban mahaukacin wajen mai dogon wando ne da farar riga daga ciki cikin yaren turanci ta waiga tana kiran wanda take gannin zai fasarawa wannan mai shige da village girl din ta ce" Wannan yaron aka kama yana satar kayan kwalam da makulashe yana budewa yana ci, irinsu ne ke zuwa su yiwa mutane barna a masana'anta, muna bukatar ki sadamu da iyayensu dan su biya barnar da ya yi sannan mu yanka masu kashedin kar su kuma zuwa da yara mararsa ji masu dauke dauke wajen nan, idan sun zo da su su tsaya iya park da su ba sai sun shigo nan ba!"
Tunda ta fara maganar take kallonta, a hankali ta juya wajen yaron da aka nuna, watau Husain yana tsaye sai turo baki yake yi, Hasan kuwa yana hararar matar kamar zai fashe dan takaici da jin haushi
A hankali kunanyenta ke jiyo mata fasarar da saurayin ke bata ama yana kiyaye mugwayan kalaman da matar ta fada kamar irin su kiran Husain da barawo da ta yi, da sauransu ya dai bata maganar a dunkule ne cewa yaron laifi ya yi ba'a bude abu a ci gashi yau oga