Showing 18001 words to 21000 words out of 145392 words

Chapter 7 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8140

na sanye da suturar dake nuni su din masu ba sauran kariya ne, kamar Bodyguard haka, dayan kuwa na sanye da simple shiga ta malan bahaushe ta kama jikinsa sosai ta amshi jikinsa


"Subahanalah, subahanalah, ashe ruwan tabo ne a wajen nan bamu sani ba? Ya salam baiwar Allah ki yi hakuri mun watsa maki ruwan nan ba da gangan muka yi ba" wannan bawan Allah da ba zata mantashi ba a kampanin siyar da kayan abinci wanda ya biyosu da kayan abincin har waje ya sa suka amsa yake fada yana sake jadada hakurinsa cike da kula


Mutuwar tsaye kawai ta yi, a lokacin ne kuma yake dakatar da masu basu tsaron da suka so nufarta yana mai umartarsu da su koma mota su yi jira, lokaci daya ya shiga dan leka Husaini dake boye a bayanta sai kuma ya kalli hasan dake tsaye ya hade gabas da yama tamkar wanda yake jir a kara taku daya kusa da mamansa ya kifar da mutun


Murmushi ya sauke a sanyaye ya ce" Ashe maman twins ce?, Sorry ina zuwa"
Yadda ya fadi sorry yana zuwa din, da hakurin da ya fito ya ringa bata ya sakata sake daskarewa ta bishi da kallo tana dora hannunta na dama a hankali saman kan Hasan dan so take shima ya dawo jikinta ko hankalinta zai kwonta, idan kashe su ne za'a yi a kashe su tare


Gefen da yake ya bude a hankali ya shiga sannan ya sauke gilas din motar daga baya gaba daya yana kallonsa a hankali ya ce" Me yasa muka tsaya ne? Ka ga fa mune bamu da gaskiya duba ka ga jikinta da yaranta gaba daya datin ruwan kwatar nan ne muka watsa masu"


ABDUL RA'UF ya dan kalle shi a hanzarce ya cire dubansa ya ciro tissu din dake aljihunsa ya dan tare gaban hancinsa kadan da ya ji danshi danshi alamun habon dake masa yoyo du idan gari ana zafi ke son bale masa, kasa kasa sosai ya ce" Allah ya isa ta yi, ka kuma san bana kwonciya da hakin wani in dai na san da shi ko??"


Dama ya san rigima ce ta dawo da ABDUL RA'UF wajen nan, ya san ba dai dan ya bata hakuri ya ja ya tsaya ba, dan haka ya shiga kokarin ganin sun bar wajen ba tare da ya nuna hali a anguwar nan ba, dama duba jikin Hajia zasu je, jiya tace idannuwanta dai sunna gannin biyu biyu kuma kaffafuwanta sunna daukan mijirya, tun a jiyan ya so su zo sai Allah bai yi ba dole sai yau, sai gashi sun sake haduwa da maman yaren nan , haka kawai yake jin yaren a ransa, bai san dalili ba, yaren na matukar shiga zuciyarsa, ko dan shi bai samu haihuwar ba har yanzu ne? Ko a wancen ranar sai da kyar aka bashi hakuri ya bar maganar a cire ma'aikaciyar nan a cenza da wada ta san darajar dan Adam, sosai ya ji zafin abin a zuciyarsa, a nutse ya shiga fadin " Ban san a kan me direbobinka suke irin tukin nan ba ABDUL RA'UF, ka ga fa ai an shiga hakinta shi yasa ta yi magana fa"


Yanzun kam a kausashe ya dube shi , zai kuma yi masa magana sai kawai ya daina ya saka hannunsa ya bale marfin motar ta gefen da ba'a fita , watau hanyar da wasu ababen hawan ke wucewa bai tsaya ya duba masu wucewar ba ya fito ya rufe hankali kwonce ya zagayo ta dayan barin


Da sauri Docter Mansur ya bale gefensa shima ya fito ya karaso wajen da ABDUL RA'UF ya karaso ya ja ya tsaya kikam a kanta


A hankali yake son kwatanta masa cewa mutane fa sun fara tsayuwa kallonsu, a hankali sosai ya ce" Calm down Man, plz let's go, kar ka yi wani abin a wajen da ake gannin mutuncinka"


Amina dake rike taf da hannun Husain da ya fara kuma yana fadin" Wayo Allahna za'a zane mu"
Hasan kuwa sai huci yake zuciyarsa na yin sama tana yin kasa irin kirjinsa na daguwa yana yin kasa shima yana kallon Tsayin Docter mai kirki ko kafadar wannan mutumen bai kai ba
A hankali ta dan matsa kadan, gaba daya ji take ya yi mata innuwa haka kuma hancinsa har kamar mura zata kamata sanadiyar matsewa kanshin turaransa guri da ta yi


Bata idasa ajiye kafarta ta baya ba ta ji muryarsa for the first time a dake, sannan a rarabe, haka kuma a ajiye daidaya ya ce" *KE? BAKI DA KUNYA KO?* "


A haukace ta dago dubanta ta sauke idannuwanta cikin nasa, da matsanancin mamaki ta budi baki zata yi magana, sai dai bata kai ga yin ba ya katse mata abinda ta yi niyar fadan yana fadin" Ki tauna harshenki, ban san idan har zan iya cinye shirme yau ba!"


Ya Allah, innalilahi, ita? Yanzu yaron nan ya dubeta ya dubi tsabar idannuwanta da girmanta, da darajarta, da mutuncinta, da Ζ΄aΖ΄anta yace da ita bata da kunya? Lamarin sangartatun yayan masu kudi abin sake hauhawa yake yi, idan ba rashin kunya da karancin tarbiya ba ya dubeta ya ce da ita bata da kunya? Ai yau idan me yake takama sai dai ya yi, walahi sai ta nuna masa ita bata daukan raini!


"Kai kana da ita kunyar ne da zaka dubi idannuwan wanda ya girmeka ka ce da shi baya jin kunya? " Ta fada a tsitsikare, sannan a rarabe tana fada tana sake cire dubanta a kansa da matsawa domin tunda ta budi bakinta ya yi taku daya ya sake matse mata waje


" Dan Allah, kar ka yi, ka duba yarenta sun rikice, duba wannan yana ta kuka, kuma idan matar aure ce yau matar aure zaka biya? Plz freind" Docter Mansur ya fada da sauri yana taro shi a lokacin da ya dago hannunsa da nufin yin abinda shi kadai ya san ko menene yake shirin yi
πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ
_*NI ZAN LADABI*_
πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ




*NA*




*SAJIDA NIGER*


Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida


Wannan Novel na kudi ne ba free bane


Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER


Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai


Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka


*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°*










*Page 0️⃣8️⃣*




A hankali ya sauke dubansa a kan Hasan
Irin yadda yaron yake yi sai ya saka shi sake kura masa ido
A hankali ya damu kansa da jin kamar zai yi murmushi da yannayin yaron a cen kasan zuciyarsa, irin kallon da Hasab ke yi masa tamkar zaki yana jira ya taba masa uwa ne ya far masa
Sake kallonsa ya yi da kyau ya ga idannuwansa sun cika da kwala sosai fa, ama ya cije ya ki bari su zuba
Wannan din shine mafarkinsa, shine burinsa, idan ya haihu yayansa su zamto jarumai ba akoki ba
Yan so ya'yansa su ringa dukan yara ba wai a ringa dukansu ba


Sai kuma ya kalli Husaini dake sake jan hijab din uwar sai sake lika mata shi yake yi a jikinta dama gashinta a fili tuni, da furucinsa na bakin yara sai ihun wayo Allah za'a zane su yake yi


A zuciyarsa ya ayana' Um, Allah ya sa kar ku yi halin rashin kunyar uwarku, gwara ku gaji mahaifinku!'


Bai ce komai ba ya juya ya koma motar ya bude gaba ya shiga ya ba direban damar su tafi, dan ya ga Mansur bai gama magana da su ba


Docter Mansur kuwa Husaini ya janyo yana fadin" Haba jarumina, kai da kace min kana so ka zama likita kuma shine abu kadan sai ya rikitaka ka ringa rusa kuka kamar yar budurwa?"


Husaini da ya raka motar da kallo yana ta hakin kukan ya ce" Ba uncle din cen bane zai zane mu? Dan Allah kar ya zane mu mamanmu bata iya jifa ba ko a gida ni fa Hasan muke korar mata kyankyaso daga daki tsoronsa take yi kamar me"


A hankali ya dago da dubansa yana kallon maman nasu ya ga sai kiciniyar mayar da hijab dinta take yi kasa kasa sosai ya ce" To abanku fa? Shi ba zai korar mata ba?"


Ido ya zarro hadi da kama baki yace" Kai, mu ai bamu da Aba ya rasu akace"


A sanyaye yake kallon yaron, sai kuma ya mike ya rike hannunsa suka karasa wajen da bokicinta yake tana ta kakabar jiki ta dauki bokicin da jakarta da ta watsar du ta hade tana jan numfashi domin warin abin hawan mata kai yake yi sosai


A sanyaye ya ce" Maman twins, ki yafe mana dan Allah"


Sosai ta so jan maganar, sai dai mutumen nan tana matukar gannin girmansa, a haduwarsu sau biyu kadai alkhairi ya shiga tsakaninsu , ya kare mata mutunci sau biyu kuma ya rarashi Farid sau biyu, duda shi dinma bata tunanin idan ya girma sosai , ta yiwuma ta girme masa, ama tana gannin darajarsa, dan haka a sanyayen itama ta ce" Ba komai, zamu wuce gida"


Ya so su bari ya kaisu, ama ta kiya, a dole ya hakura ya tafi ko kyautar da ya so ba Biyu ta tubure ta kiya, da wannan ya tafi da addu'ar Allah ya sake hada su, shi kam yana son taimakawa matar nan da Ζ΄aΖ΄anta, kamun kanta na matukar birge shi a rayuwa
___________________________________


A gajiye suka dawo gidan tare da Baba lauratu, domin kasa zuwa wajen markadan ta yi sai gidan baba lauratu ta je a nan ta fashe mata da kuka tana fadin an ci mata mutunci, karshe dai Baba laurantun sai ta rufeta fa fada tana fadin ta lura a kan lamarin Biyu sai ta tube a daku da ita, ta ringa sanyaya lamarinta, ina ita ina jifan motar masu kudi, masu kudin nan da daidaiku suka san yafiya da kyaliya ? Idan aka makata a cel yayazata yi kennan? Ta san basu da inda zasu je su kama a cirota , Allah ne kadai ya isa ya yiwa abin tsawa, ta kiyaye Allah ya taimaketa ta fada hannun na kirki


Ita kam shanye abinta ta yi a ranta, ama ta san babu maganar na kirki, mutumen banza ne kawai Allah dai ya hada shi da aboki na kirki


Da kaza kazar Baba Lauratu ta hasa wutar suyar kosan ta dora kasko ta shiga soya mata da siyarwa ita kuma ta shige ciki ta ja ruwan wanka ta dumama shi ta darje Hasan da Husaini da kanta , har kawunnansu sai da ta wanke da sabulu da soso sannan ta ji dama dama
Itama ta yi wankan tamkar zata cenza fata ta fito ta gyara katifarta ta kwonta gashinta a barbaje dan ta samu ta huta, du wata kasala da bacin rai ke taso mata, ta so a bari ya mareta, da sai ta daka tsale ta shatawa jar fuskarsa mari sannan ta ciro sajensa a hannunta walahi! Karyar rashin kunya, ta rasa me yake yawo a kwakwaluwar samarin zamani


A ranar dai bata wani sake yadda ya kamata ba, Ζ΄aΖ΄anta kansu basu haye mata ba sun kula ranta a bace sai suke shigowa idan ta kama su shigo din, sunna cen wajen Baba Lauratu sunna tayata ciniki, masha Allah sai zuwa siya ake yi taa ko'ina, dama samari sun fi gane irin haka, sai ragwagin matan da basa girki a gidajensu, sai yara da kwadayin abin ke saka su amso ashirin din iyayensu su siya su laka a hakoransu




La'asar sakaliya Baba Lauratu ta gama gyara komai ta shiga ta hau dardumar da Amina ta yi sallah bata ninke ba ta shiga gabatar da sallar itama


Tana salamewa ta yi addu'a ta shafa ta waiga barin da Amina ke zaune sai cika take yi tana batsewa
Murmushi ta yi ta ce" ko dai na raka ki ki je wajen Baba Mai Shanu ki zane jikansa ne Amina?"


Amina ta kalleta jin abinda ta fada da dan mamaki, sai kuma ta sada kanta tana turo bakinta hadi da jan numfashi kasa kasa sosai ta ce" wai bani da kunya"


Baba Lauratu ta yatsina baki tana ciro kudaden itama ta ce" To ai ba'a yi abin kunya ba, ki ware uman Mijin shine kawai alkhairi, fushin bashi da dadi ai ko? Tunda dai ba ramawa zaki yi ba ai batawa kai lokaci ne, matso ki ga kuΙ—aΙ—en cinikin, masha Allah kasuwa na sonki Amina shi yasa nake ce maki ba dole sai da aikin gwamnati zaki ci abinci ba, baki taba kasawa kika kwashe ba'a siya ba, ama ke kin dage da maganar boko"


Amina ta mike kamar an tuna mata tana fadin" Yauwa Baba kin ga tunda na fara kosan ga dubu gomar nan hadeta da ajiyar wajenki, kin ga har kudaden sun zarta wanda ake da muradi na jarabawar nan, sai dai lokaci ya kure, ama ba komai zan ta ajiyewa ana adanawa kafin badi idan ina cikin masu rai sai na kuma ajiyewa na zanna , Baba ina son boko, ko dan kaina ya karra wayewa, bale boko din fa tana biya baba"


Baki Baba ta kebe, ita kam bata ga abin matsawa kai da maganar boko boko ba, a yi bokon a gama aikinma ya gagara? Ai kasarmu in dai baka da dogon hannu ko ka san mai dogon hannu ka shiga uku kennan, da zafin a kawo a kawo kawai ya isa ya koreka daga hanyar bokon, ta ce" Allah dai ya fito da miji da kudin na je na sa Lukman lafinta ya dandasa mana gado dandasheshe"


Shirun da ya biyo baya ya saka Baba Lauratu karra kallonta, dama ta san a rina, da zarar an mata maganar aure sai komai nata ya tsaya, kamar wace bakin aljani ya aura, ta dauko damuwa ta Ι—orawa kanta , a cikin manemanta mutun biyun nan tana gannin idan Allah ya yi aka yi da su ko yayane zasu kular mata da yarenta, domin a cikinsu babu na banza, daga baban Sauda har Muktar sunna da mutunci kuma an sheda sunna da riko da iyalansu da gaskiya, ba yinwa ba matsalar sutura, daidai karfinsu sunna kamantawa, bama kamar matar Muktar mai kanti, babu dashin da bata shiga na anguwa, kwanakin nan harda dashin gidan Baraka na dari uku a wata ta shiga dan tana samu, ama ita sai ture su take yi ta kasa sakin jikinta, idanma a nan take so su zauna da mijin ai ba damuwa sai su yi zamansu, duda da wahala mazan yanzu masu takaici su aminta da haka, ama ai hakan dinma ba laifi bane


Ita dai Baba sai da suka ci abincin dare ta yi masu salama ta tafi


Amina ta dawo ciki ta dage labulen dakin ta bude kofar dakin sosai, domin yau wani irin zafi take ji, biyuma da duka fara yin barci ta ga du sun rage suturar jikinsu babu mai riga a cikinsu , kowane kuma ya kama gabansa ya kwonta a gefensa dan yau basa so su likuma junna dan zafin da garin yake da shi


Sake watso ruwa ta yi ta koma dakin ta dawo baki baki ta kwonta da daurin kirjinta sai hijab dinya da ta jiko ta rufa shi a jikinta ta shiga yin adu'ar tsaro ta tofawa yaren , itama ta yi ta tofa a jikinta sannan ta kwonta tana neman barci


Barcin ne ya yi awon gaba da ita a nutse, sai dai a cikin barcin mafarki ne marar dadi ke dawainiya da ita
Mafarki take yi wai ita da namiji, mafarkin da ta jima rabonta da yin irinsa


A hankali ta ringa ji kan nononta na zafi sosai kamar ana tsikara mata allura,
Juyawa ta yi domin gaba daya abinda take mafarkin tamkar a zahiri ne


Dakatawar da aka yi na dan lokaci ya sakata sake neman barcin hadi da sauke ajiyar zuciya
Sai dai bata jima ba ta ji ana shafar kasanta an kara shafawa
Tun tana daukan abin da wasa sai ji ta yi ana mulmular abinda ke gabanta da yatsa ko da mene? Ita dai tana ji abin na sake shigarta dan haka ta kai hannunta cikin magagin barci dan kadewa, ko turewa,


Hannunta ne ya yi raf da hannun dake kasanta ,lokaci daya barcin dake idnanuwanta ya dauke sakamakon fizge hannunsa da ya yi ya mike tsaye


Wani irin razananen ihu ta saka hadi da wawurar hijabinta da zaninta tana sake ihun kwarto hadi da neman fitowa ko Allj zai bata sa'ar guduwa ta labe
Jikinta rawa yake yi, kuka take yi, bata gannin gabanta hakan ya sa ta maku da jikin garun dakin nata ta yi baya ta zice a kas ta tafi a sume


Ihun da yarenta ke yi sunna kiran sunnanta ya ankarar da daidaikun mazan dake fitowa dan zuwa masalaci


Hankali ne ya fara tashi, domin daya na girgizata ne daya na ihun kiran sunnanta, uwa uba kofat gidanta a bude ham


A hankali mazan suka fara dan taruwa a kofar gidan har suka kai mutun hudu, ciki harda yaron liman, shima magidanci ne kuma bai fi gida uku tsakaninsu ba


A nutse ya ce" Malan Innusa inaga dole zamu shiga gidan nan, kafin a tado wata macen kar aje wani ne a gidan nasu, duba da kwanakin baya hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login