Showing 6001 words to 9000 words out of 145392 words

Chapter 3 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8142

na nan basa son abinda zai kawo hankalinsa kansu na rashin kula da wani abin


Idannuwanta ta sake zubawa mutumen a hankali ta ce" Ka tabata haka tace ka ce min?"


Sake kallonta ya yi,bama kamar lebenta dake dauke da kalar kasa kuma a kallonsuma sai kyalin laushi suke yi da fari tasss din idannuwanta masu dauke da siririn kwali zuwa hijabinta da ba zai iya fadin sunnansa ba gaskiy har zuwa takalmin dake kafarta dan soso da kuma irin na kafafuwan yaren wanda ya tabata wannan shiga ce ta saka Madame yanke mata hukuncin bata fa ilimin boko harma ta mata kallon talaka futuk da sauransu dai irin na wasu masu kudin da suka raina talaka daga kallon idannuwa suke ganne kai din su ya su ne ko kuma mu ya mu ne, ta haka zasu yanke hukuncin abinda ya dace da kai su yi maka ya sake gyada kansa zai maimaita mata matar da haushi haushi ta daki table din tana rankwafawa ta janye hannun Husain da ya juya zai dauko biscuit din ya nunawa mamansa cewa ba fa sata ya yi ba wannan ne kawai ya bude ya dauki daya shine aka kama su aka ce ina iyayensu aka yi ta nemanta wajen kayan miya ba'a ganta ba shine aka ce karya suke yi su kadai suka shigo, masu tsaron kofa suka ce aa ba su kadai suka shigo ba da mamansu ama aka ki yarda aka kawo su nan, tunda aka kawo su matar nan tale fada tana zaginsu da barayi, sai dai bata bari ya fadan ba ta ture shi da tsawa ta ce" Ka fadawa wannan bagidajiyar ta kira min uwar yaren ko ubansu na dalamesu su bani waje tun kafin sir ya leko ya ji karnin da Yaren nan suke yi da ganninsu a wajen nan ransa ya bace! Yaron nan da gani barawon anguwa ne!"
πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ
_*NI ZAN LADABI*_
πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ




*NA*




*SAJIDA NIGER*


Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida


Wannan Novel na kudi ne ba free bane


Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER


Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka


*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°*










*Page 0️⃣3️⃣*








"please pull yourself together" Amina ta fada a sanyaye tana kallonta tana ta dane guguwar bacin ran da take tsoron fashewarta a irin wannan lokacin


Dagowa ta yi ta karra daukota da kallo ta watsar, yin turancinta ba shine abinda zai sa ta sasauta mata ba , ta tabata turancin an koye shi ne a boyi boyi ko a titi , watau turancin tsakiyar titi ba na makaranta ba, dan haka ta dubeta ido cikin ido ta ce" Oh kennan kina gane abinda nake fada, ohk ki yi gagawar aiwatar da abinda na fada tun kafin lokacin zuwa sallar oga ya yi ya sameku a wajen nan!"


Amina ta saki hannun Hasan ta matso daf da matar ido cikin ido ta dubeta sosai ta ce" Idan ban aiwatar ba fa?"


Matar ta kalleta da mamaki, ta kalli mutanen da suka dan fara kawo hankalinsu kansu ta dan matsa dan bata so jikinsu ya hadu ta ce" Ke, ki matsa min kadan mana baki san ana fama da cutar covid bane? Idan kika ki kuma sai ki tafi ki barsu a nan na mika su hannun masu horar da barayi!"


Da karfi Amina ta janyo atishawar karya ta maka mata sannan ta ce " Bismillah ki mika mu gaba dayanmu wajen masu horon tunda azalumai ne ku!"


Hankalinta tashe take goge fuskarta da tissu tana fadin maza a kira mata security service!


Jin haka ya kara tunzura Amina ita kuma ta shiga ihun wanda ake gudun ta gannin take son gani, da karfi ta ce" ba kina tsoron kar hankalinsa ya karkato wajenki ba? Shine zaki wulakantamu ki kirayi y'ayana barayi? Na san ke da gani baki san menene yaro ba baki san ciwonsu ba tunda ga dukkan alamu ko mage bakya ciyarwa! Na tabata shi din idan har datijon arziki ne zai maki fadan kira min yayana da sunnan barayi da kika yi!"
A haukace Amina da nake yiwa kallon ko dan yatsana na saka mata a bakinta ba zata taba cizawa ba ta shiga watsar da dukkan abinda hannunta ya kai ta nemi haukacewa a wannan waje har daidai lokacin da secirity biyu suka shigo mata da sauri suka nufota daya ta samu ta damketa sai dai juyin da ta yi da ita ta kubce mata har ta nemi yin taga taga , hakan da suka gani ya daka dayar janyo bindigar teaser dinta ta nemi kashe gaban jikin Amina a lokacin da ta danna zata dora mata shi a lokacin Husain ya gantsa mata cizo a kafarta yana kukan kokowar da ake yi da mamansa , Hasan kuwa yana tsaye wajen mutumen nan da yaren turancin dake harshensa wanda su dukansu sun yi mamakin yaron dama haka yake da turanci a bakinsa yana fadin ya hannasu taba mamansa shima yana daf da fashewa da kukan da idan ya fara ta yiwu yin shirunsa da hakurinsa sai ko zuwa gobe aka danna baban office din da ogan wajen ke ciki da bakonsa da kuma likitansa da ya zo bashi magani domin a yau ranar da ya bi sosai ta bale masa habo har sai da ya yi kiran likitan dole


Docter Mansur , likitansa kuma daya daga cikin abokinsa ne ya ga za'a jonawa yarinyar nan abin nan dake saka mutun yin bori a kasa kamar dan jaki kafin gaba daya jikinsa ya mace har fitsari ake saki fa da sauri yana fadin" stop that immediately!"


Da sauri ta dakata tana kallonsa hadi da dan ja baya domin babu wanda bai san waye shi a wajen ba, da sauri ya dan karaso yana fadin" Subahanalah, me yake faruwa haka a wajen nan , hey boys me yasa kuke kuka? Hey saketa mana, ki saketa menene haka?" Sai kuma ya juya wajen babar mai kula da harkar cctv din ya shiga tambayarta abinda yake faruwa


Kafin ta bashi amsar da zata gamsar da shi Amina dake share idannuwanta da suka cika da kwalla tana tare hijab dinta da aka yaga mata ta dube shi muryarta a shake ta ce" Dan girman Allah ina son gannin mai wajen nan, na yi rantsuwar ganninsa a yau kar kafars ta kamani, idan har ka san inda yake ko kana iya min iso ka taimaka min na ganshi"


Kallonsa Mansur yake yi sannan ya dake kallon yaren dake kuka sunna rike hijabinta , sunnan da suke kiranta da shi Mama ya saka shi sake kallonta kafan sai kuma ya juya wajen da aka yi cirko cirko, a dan hade kadan ya badu umarnin kowa ya koma bakin aikinsa, sai kuma ya dake dubanta a hankali ya ce" Ina fata lafiya? Domin bashi da lafiya ne"


Amina ta hadiyi yawu dake makogwaronta a hankali ta furta" Lafiya lau"


Kofar office din ya nuna mata sannan ya juya wajen ma'aikatan da wace ke son nuna masa bai dace ta shiga haka kanta tsaye ba, bata da damar ganninsa kai tsaye haka bale ba abin kirki ne zai kaita ba , zuwa ne zata yi ta masa rashin kunya may be fiye da haka, sa sauri ya juyo dan idan har maganar cewa rashin kunya ne zata shiga ta yi a office din cen gwara ta zo ta yi wasan kurar da suke yi da kowa a wajen nan ciki kuwa harda shi, domin idan har wata magana marar dadi ta faru a cikin cen daga bakinta bai san me zai faru ba, du inda kake neman dan zafin kai mai tsutsotsin kai idan ka zo kansa ka ja ka tsaya ka dasa aya


Sai dai ya makaro, bayanta kawai ya gani d Ζ΄aΖ΄anta dake biye da ita sun kutsa cikin office din
Juyowa ya yi dafe da gaban goshinsa ya rasa abinda zai ce, sai dai ba zai bar wajen ba sai ya ga abinda zai faru dan baya so a samu matsala ya barsu da rigimarsa su kadai


Da karfi ta bude wajen sannan ta kutsa kanta da salamar da ta zamto tarbiyar bakinta ta shiga baza ido dan ta ga abinda ta shigo nema watau mai wajen


A hankali ya dago lumsasun idannuwansa ya sauke saman kanta da Ζ΄aΖ΄anta dake ta faman rike gefe da gefen hijabinta, tunda ya mike dan takawa bakin da ya yi da sauri ya dawo sanadiyar ihun kukanta, kansa tunda ya sarra yake tare hancinsa dan yana gudun wani habon ya same shi


Wayar da yake yi bai katse ba haka kuma bai daina kallonta ba da yarenta dake kallonsa suma


Da haushi ta sake kureshi da kallon raini, a ganninta idannba wulakanci irin na y'ayan masu kudi ba ta yaya za'a maka salama kana kallon mutane ka kasa koda amsa amincin da aka nema maka a wajen ubangijinka? Baki ta tabe ta ce" Ban san ko kana jin hausa ba fan saurayi? Ama dan Allah mahaifinka ko mai gidanka nake son gani, watau mai kampanin nan! "


Kallon da yake mata da kuma dan juyar da kansa da ya yi ya waiwaiga hagu da damansa ya sakata bi itama da kallo, sai ta sake dubansa ta shiga tunanin ko kurma ne?


Da wani bacin ran ta budi baki ta ce" Bawan Allah shin kai kurma ne? Ko kana daya daga cikin masu wulakanta mutun a wannan kampani? Koda yake kasancewarka a wannan kujerar ta yiwu kai din makusanci ne ga mai kampanin, ka fada masa cewa Allah ya halice shi, shi ya halice mu, ka fada masa cewa babu wanda ya san gobe sai Allah, idan da sanninsa ake wulakanci a karkashinsa Allah ya saka min wulakantani da aka yi har aka zagar min y'ayana!, Idan ba da sanninsa ake yi ba ya gagauta yin bincike ya tace ya rauraye! Wadannan din y'ayana ne! Yayana ne ! Ba bara.........."


Idannuwanta ta rintse sai kuma ta bude ta dora da fadin" Ba barayi bane su, ina kafa kafa da abina, ina kuma fadawa Allah, yau koda sun iya hali irin na bera idan har an san ciwon haihuwa za'a kiyayi zaginsu da shi, idan kuma an san gobe ta Allah ce za'a kiyayi aibatasu da laifinsu na yanzu, domin laifin wani na iya kasancewa laifinsa na gobe!, Bai san me zai zama gobe ba, idan har shi din magidanci ne da ya san menene haihuwa to fa zai kiyaye ya saka tsari a tafiyarsa.....ka fada masa ni din uwa ce da hawayena ke zuba na ciwon wulakantamin y'ayana da aka yi, na san kai baka haifa ba bale ka sani dan girman Allah sak...................................."


Dif ta dauke wuta a lokacin da ya mike daga cikin kujerar da ya lume ya tura kafafuwansa cen kasan tabel din office din , ashe irin zaman nan ne ya yi wanda ake tura kaffafuwa karkashin table a dafe kujerar, zama ne na masu tsayi ba gajeru ba gaskiya, shi yasa sam bata gane tsayinsa ba har sai da ya mike a yanzu


Idan har ya mata magana a iffice din nan to fa takardun dake zube saman table dinma sun masa


Wajen wayar tafi da gidanka ya nufa ya daga ya karra a kunnensa dannan ya shiga dadana numbobin da yake sin kira


Cen kasan makoshinsa ya iya furta" EH " sannan ya ajiye ya kuma juyowa ya jinginar da bayansa jikin garun ya sake fuskantarta yana sauraronta


Shiru ne ya dauki wajen, sosai shiru ana kallon kallo


Kasa kasa Husain ya ce" Mama mu tafi kar ya zane mu "


Hasan dake masa kallon da yake masu ne ya sake jan hijabinta yana fadin" Mama lets go please"


Lebenta ta dantse cike da takaici, ta fa gane ba kurma bane tsagwaron wulakanci ne irin na yaren zamani, idan zata rantse ba zata yi kafara ba ta tabata wannan din ta girme shi nesa ba kusa ba, rashin kunya baya karewa a duniya!
Juyawar ta yi, ba dan komai ba sai dan ta san ko menene uban gidansa ya jita!, Ta bar wajen ne dan ta kare mutuncinta, abinda ya so faruwa dazun ba zata so ya tabata a kanta a gaban Ζ΄aΖ΄anta ba, abin nan ta ji hirarsa a wajen yan school dinsu, tabas a dazu ta tsorata da ta ga za'a dasa mata shi


Gana take sunna biye da ita har suka idasa sauka


Bata tsaya ta kula kowa ba sula nemi ficewa a baban filin kampanin har an fara kiraye kirayen sallar magariba


"Asalamu alaikum Hajia" muryar wanda ya kawo mata agaji a dazu ta daki dodon kunnenta da yannayi na ja baya ba matsewar waje ba


Juyowa ta yi sai ta ga daya daga cikin ma'aikacin wajen rike da ledoji jigi jigi kusa da likitan


A tausashe sosai ya furta" ki yi hakuri na san ke matar aure ce, ba wani abu bane dama dan na tambaya ne Ina fata ya saurareki?"


Amina ta juyar da kanta tana shaΖ™ar iskar magariba dake hurowa a sanyaye ta ce" Ban samu ganninsa ba, sia dansa, na fadawa Ι—an nasa sakon na san zai sanar masa"




Dan jim ya yi , sai kuma ya ce" Dansa kuma?"


Amina ta gyada masa kai tana dubansa


A hankali ya ce" Ai shine mai wajen fa, shi daya muka baro a ciki"


Sai da ta saki baki da mamaki, ta waiga ta sake waigawa ta kuma kallonsa, ama sai ta barawa kanta abinda ya bata mamakin a zuciyarta , karshema sai zuba ido tana kallon yadda yake ta kokarin sai Hasan ya bashi hannu ama ina, a murtuke fuskar nan du inda rigima take ta tatare a saman fuskarsa, Husaini ne ya sake sosai da shi yana amsa tambayarsa, sai kuma ta juya ta fice gannin Aban saudat ashe dai bai tafin ba ta karasa tana kawar da fuskarta gannin ya fito a adaidaitar yana tambayar lafiya kamar wace ta yi kuka?


Gannin ana miko masa ledojin ta juyo da mamaki tana fadin"








Yaya kuke gannin salon zai je? Yaya kuke hangen cakwakiyar lamarin? Ku zo mu je sistersπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜
πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ
_*NI ZAN LADABI*_
πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ




*NA*




*SAJIDA NIGER*


Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida


Wannan Novel na kudi ne ba free bane


Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER


Wa'inda suke da matsala da harkar banki zasu iya turo kati ta numberna, ko su yi pos in sha Allah, kuma a kan number nawa kamar haka 93811618..... Sai kun zo


Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka


*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°*










*Page 0️⃣4️⃣*






Da mamaki a saman fuskarta ta ce" Aa ba namu bane wannan fa"


Mutumen nan dai ne rike da hannun Husaini dan nesa da su kadan yana fuskantar Aban saudat aa tunaninsa ko mai gidanta ne ya ce" Asalamu alaikum, dan Allah na biyo bayansu dan na karra bada hakuri, sannan ku yi hakuri ku amshi kayan nan, an samu matsala ne na rashin fahimta in sha Allah hakan ba zata kuma faruwa ba"


Tsayen da take kallon bayaninsu take yi da mamakin ko menene abinda ya sa wannan mutumen biyosu mai daraja ne, shi din da kansa mai tausayi ne mutumen, a sanyaye ta girgiza kanta ta ce" Aban saudat ba zan amshi kayan nan ba, ga dai kudin a irga abinda suka kama sai a cire harda na biscuit din da ya ci"


A nutse ya ce" Ama ai Aban aboki yace ki amsa ki yi hakuri ki amsa "


Husain da sauri ya kalleshi yana fadin" Aa fa, ba abanmu bane wannan, akace abanmu ya rasu ko Mama?"


Shiru ta yi tana kallon bakin Husaini, yaron ba dai surutu ba , kuma ba rashin kwaba bace haka Allah ya halice shi da saurin sabo da shegen surutu Masha Allah


"Ay sorry ai na zata abanku ne , ama ki menene a dai yi hakuri, ni na kasa hakura ne dan na ga dan uwan aboki sai huci yake yi, "


Gannin baban mutun ba wani karamin saurayi ba yana ta masu magiya a kan abinda ba shi ya bata ba ya sakata dan rage tsayinta kadan ta yi masa godiya sannan ta shige adaidaitar ta jinginar da kanta a jikin abin adaidaitar ta yi ta lumshe idannuwanta, a haka take jin magangannunsu har ta ji ya tada babur din sun dauki hanya
Ana fitowa daga masalaci sunna karasowa kofar gidansu


A daidai lokacin ne matarsa watau innar saudat ta fito zubar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login