Showing 138001 words to 141000 words out of 145392 words

Chapter 47 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8171

nesa da ita na neman damunta


A hankali ta juyo tana dago dubanta tans kallon kyakyawar fuskarsa da cikaken sajensa
Murmushi ta yi a hankali ta dan shafa gefen fuskar tasa ta ce" Da wuri Haka Taem ruhi? ( Abincin ruhi)"


Kallonta yake yi kasa kasa, zuciyarsa na hatsiltsila.......... A hankali ya ce" Ni ne abincin ruhinki?"


Amina ta sadda kanta tana dan wasa da yan yatsunta


Murmushi ne ya subuce masa da dan gagawar magana ya ce" ki ce min na zauna..... Ni kuma ba zan ki zama ba"


Fuskarsa take ta kallo, tana yaki da son ce masa eh zauna din da zuciyarta ke ingizata
Da kyar ta iya budar baki kasa kasa ta ce" Neman na shinkafar fa?"


ABDUL ya bata fuska ya ce" Allah ba zai hannamu ba ai"


Murmushi ta yi a hankali ta shige jikinsa tana dora kanta a saman kirjinsa


Shiru ya ratsa na dan lokaci
Kasa kasa ta ce" Aa, ka je Aban Amnah, Allah ya dawo mana da kai lafiya Aban Fadeel, ai tafiya mabudin ilimi ce ko Abbansu?"


Dan makwaloton wuyansa ke sama da kasa a hankali a hankali yana sake talabo fuskarta , har sai da ya dagota yadda yake so a hankali ya shiga kissing din lips dinta


Tun sunna yi a tsaye har ya karasa bakin bed da ita ya zauna ya dorata saman cinyarsa stll yana kissing dinta


A hankali ta dan janye kasa kasa ta furta" ABDUL........"


ABDUL ya sake talabota shima cen ciki ya furta" Meenart........i ndd u"


Da kyar ta iya hannashi kaita kasa, domin du ya cire mata su dan kwalin harta da rigar, da kyar ta iya jadada masa tana hali na rashin sallah, da kyar ta iya dawo da shi a hayacinsa, hannayensa jimke da cinyoyinta ya lunshe idannuwansa kanta a saman kirjinsa, kirjin nasa na bugawa pat pat pat


Da kyar ya samu ya dawo hayacinsa, muryarsa cen ciki ya furta" Meenart?"


Amina ta ja amsar a cen cikin makoshinta


A hankali ya ce" Ki kular min da kanki, ji ringa cin abinci sosai, dubi cikinki fa ya koma ya lafe kamar ba shine bulele ba"


Yar daria ce ta kubce mata, shima ya saki murmushi yana shafa gashin kanta, a hankali ya ja numfashi a wajen gashin nata yana shakar kanshin turaran gashin sannan ya furta" Zan tafi.........."


Idannuwanta ta lumshe tana jin kamar zata yi kuka


ABDUL ya sake dagota yana kallonta, ya sakar mata murmushi ya mike yana gyagyara malunmalun dinsa da ya yakunne sannan ya dan rage tsayinsa dan ta dauko hular ne ta yi dadage ta kafa masa tana taya shi kabewa, a hankali ta ce" Allah ya tsare"


Amsata ya yi da amen, yana tafia tana biye da shi a kan dokin kofar ta tsaya tana kallo ya kama ya bude, sai kuma ya sake juyowa ya ce" I love you wife........."


Murmushi ta yi ta juya da dan sauri
Shima ya yi murmushi yana lekata har ta boye, sannan ya rufe kofar ya juyo da nufin karasawa ya yiwa Baba salama da sauran jama'ar gidan suka yi ido hudu da Baba


Wani irin kallon kurullah da Baban ke masa sai ya ji du ya dan tsargu kamar wanda ya shiga dakin matar wani jama'a


Rigarsa da ta yakune ya sake kakabewa yana dan kokarin daidaitawa har ya karaso falon ya zauna yana hade fuska danma kar a ga damarsa


Baba ya kada kai ya dan rankwafo a hankali ya ce" Ai ba zata daidaita ba sai dai ka je ka cenza wata, wannan rigar ba zata daidaita ba"


ABDUL ya kalleshi yana kankance ido ya ce" To me kake nufi?"


Baba ya dan watsa hannayensa ya ce" Aa ba komai, ama ABDUL sam bakada kunya, yaya zaka tardo yarinya har gidan iyayenta? Kai nifa sirikinka ne ko? Kar ka karra shiga dakin yata gaskiya a ringa aro kunya koda babu ita a kusa kusa"


Haba ya dafe da shegen mamakin Baban, zai bashi amsa Hajia ta fito daga kicin tana tuta abin gungurawa na yaran a hankali wanda yake dauke da abin jarirai biyu ya zamto Amna na daya , Ammar na daya sun sha wankansu kowane da abin tsotsa a bakinsa yana dab tsotsa, dan Ammar barcima yake, Ambar ce ke kallon abin wasan dake jiki yana bada kaloli da yar wakar dauke hankalin jarirai haka, gefe guda kuwa pidarsu ne da ruwa da kuma madara, domin ana hada masu da madara nonon kadai ba zai ishesu ba


Baba ya yi murmushi ya ce" ka san Hauwa kamar ita ta haifi yayan nan? Na kusa cewa jego ya karbeta "


ABDUL ya dafe goshinsa dan yau ya kula Baba ido rufe wanda zasu yi yake nema, ya dubeshi ya ce"












56




Ya dubi Baba ya ce" Allah dai ya karra lafiya"


Baba ya yi murmushi yana sake gyara zamansa daidai Hajia na ciro yaran ta fara mikawa ABDUL macen, sannan ta ba Baba namijin ta zauna tana girgiza pidan Domin Amna tamkar mai acici a cikinta ta fuskanci ABDUL ta ce" Magaji, me yasa wai Firdausi ta ki sauraron MANSUR? MANSUR ai mutumen kirki ne, na ga gaba daya baya gabanta, bawan Allah sai kai kawo yake a zamanmu a gidanka har zuwansu yau tsal yana kai kawo , ama ta yi mursisi kamar bata san me yake nufi ba, ni fa bana son iskanci a ringa wulakanta mai so domin Allah, MANSUR ya yi iya yi, gwara ta amince ta aureshi, matar nan tasa da ita da solofiyo du daya, mace tamkar irin matan da, baiwar Allah hakurinta ya cika yawa, ta yiwu da wuci zata mutu"


"Kai Hauwa, kai Hauwa, Muhamadu rasululahi salalahu alaihi Wa salam " baba ya fada yana karashewa da daria


Itama dariyar ta yi tana kallonsa ta ce" Alkali, ka taba gannin mai hakurin nan mai kwontacen ido irinta ya jima? Matar Mansur fa ko marinta ka yi kanta a kasa baiwar Allah, irin matan zamanin da ne irin yan aljannar nan, Allah ya sa mu dace baki daya"


ABDUL ya girgiza kai yana sake mana Amna a kirjinsa yana shafa bayanta, kakanninsa sun fi karfinsa shi kam, zai bisu da Adu'a kawai, dan ita suke da bukata, lamarinsu sai su,


A nutse ya ce" Eh dazu ai mun yi magana da ita,....." Sai kawai ya yi shiru ya ci gaba da dago Amna yana so a dole yar wai sai ta bude ido ta kalleshi, fadi yake dady ne ta masa daria mana?


Hajia ta shaka, barda talabe habarta dan haushi ta ce" Kai Magaji wai ba zaka min magana a mike bane?, Alkali wannan hali na menene nu Hauwa?"


Baba ya kebe baki ya ce" Ai sam Gwamna ba hali, kin ga fa soyaya ce yake nunawa ya'yan fari a gaban sirikai, ni dai na masa magana kar na kuma gannin rashin kunyar shiga dakin yata, ina dalili yo Yar da danyen jego a ringa shigar mata daki ana zaunewa? Mema za'a fada mata"


Hajia ta yiwa Baba tsuru tsuru dan kam bata san abinda zai fada ba da bata ja maganar ba


ABDUL kuwa ya tabe baki yana sake manawa Amna kiss a idannuwanta a hankali ya ce" Babyn dady ba zaki farka ba?, Ki farka mana tafia zan yi fa, bude idon ki ga dady, dady, dady ne?"


Hajia ta sake cafa ta ce" Kamarma zai fi son macen a kan namijin, kia ba'aiwa tagwaye haka, sunna iya mane maka ido"


Baba ya ce" Kwarai ko su mane masa duwawu ya gaza yin kashi ba"


A tare suka kalleshi, Hajia t ace" wai Alkali yu me na maka kake nemana da fitina ne? Tun dazu kake nemana da rigima, kuma me ya kawo magana duwawu a nan?"


ABDUL ya rintse ido, kai jama'a, Allah ya gode maka


Alkali kuwa ya ce" Kakar gwamna me yasa bakida abin fada ne ke? Mema to ni nace a tarin abubuwan fadana?, A ringa sasauta fushi dai ana yiwa tsoho hakuri, yanzu yaya maganar matar gwamnan?"


Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai ta dubu ABDUL ta ce" Yauwa, dangane da Uman biyu, za'a koya mata mota, da kuma dai dukkan abinda ya dace, idan fita ta kama zata fita"


Tsam ya dago ya sake zuba masu ido,
Kuresu ya yi da kallo ya ce" Waye yace yana so a koya mata mota, wa zai koya mata motar?"


Tsuru sukai masa su dukansu, Hajia ta kalli Baba mai Shanu ta ce" Alkali bashi amsa"


Baba ya gyada kai ya gyara zamansa yana sake rike Ammar dake barcinsa hani'an ya ce" To dai , ka ga gwamna ni din nan sunana Aliyu, ita kuma wannan hauwau, mu muka yanke zamu kai gwagwon malan koyon mota da sauransu na zamani, kai dai ka yi fata kar Hajia ta koya mata siyasa, domin ka shiga uku, ni kuma da ka gani a nan mijin kan tace ne, tunda ta fada an yarda, a lamarin Siyasa ce kawai ba dadi, bana so ta koya, ama duka kaf sauran abubuwan ka yarda da ni alkhairi za'a koyawa Matarka ka ji Gwamna?"


ABDUL ya lalubo wayarsa dake zuzuzutttt ya daga ya karra a kunnensa


Sanar masa da aka yi jirgin da zai dauki masu tafia chaina ya kusa sauka ya saka shi maida hankali ya yiwa yayansa Adu'a sosai yana ta sake rungumarsu abinsa sannan ya tafi bai idasa fadawa Hajia yadda suka yi da Fido din ba, bayan tana son ji, shi gaba dayama sun shaka masa kutu ne, ya gwamace ya tafi ya barsu da Halinsu, yana fatan Allah ya taro su, shi kam da san samu ne kar a bar Uman biyu fita, to wai dama wankan fita ake yi ne? Ya ga yau duka duka kwananta tara da haihuwa, dama sun kawota kusa dan su koya mata yawo da abubuwan da ba za'a rasa bane?, abu daya ya sani shine koda za'a fara ba yanzu ba, ta yiwu sai ya dawo, idan kuwa haka ne du zai iya da su baki dayansu!




A gidan Baba




Gata, mai sunnan gata, gatan da ko a gaban iyayenka ne da wahala ka same shi, shi Amina ke gani a gidan nan
Gyara takanas Hajia ta dauko mace tun daga garinsu ta zo ta zauna take gyara Uman biyu, a wajentaa Uman biyu ta karra daukan yadda ake gyaran mace idan ta haihu, gyara har kamar za'a juyo cikinta a zuba mata sabo, wani irin gyare gyare abin ba'a magana, ga ruwan noni da ake samu ya zamto koda yaushe ana tatsa ne a cikin pida anna kaiwa wajen Baba inda yaren ke wuninsu da Hajia a ajiye a cikin dan abin ajiyewa, idan ba dare ba bata saka su a nono, shima ba wai ta kwonta da su ta kwana rungume da su ba, no a dai basu su sha sosai su yi gyatsa a kaisu dakin Fido cikin gadajensu, ita kuwa ita ke dan motsawa idan sun motsa ta basu madara su koma barcinsu, sam basu saba masu da kwana da su gado daya ba, uwar kanta da farko a ranta ta ji kamar tana missing dinsu, sai dai tana samun wayar mijinta da ya tambayeta yarensa ta shaida masa ga abinda aka ce ya yi murmushi yace Allah ya tsare su, ai hakan kam ya yi, dan lamari na dare sai manya.....a dole ta gane yarensa ta yi shiru dan ABDUL kam sam ba tsari a harshensa


A hankali har lokacin dawowarsa ya yi, watau ranar asabar zai sauka


A wannan rana da ido kawai suka ringa bin Uman biyu yan zaman falo, domin da katon hijab dinta ta ringa shige da fice kicin, du idan zata wuce kuwa sai Baba ya ce da ita sannu, tun tana dan ja ta tsaya dan ta ji ko akoy magana ne, har ta kula kus kus suke yi shi da kakar Gwamna dan haka ta ajiyesu gefe ta zagine a kicin din nan ta yi girki mai sunan girki har kala biyu, da jus da dan abin motsa baki ta saka aka fitar da kwanuka masu kyau na kwalba aka zuba aka gyara komai, suka ringa fitarwa sunna kaiwa saman table sunna jerawa


Baba ya kalli Hajia, Hajia ta kalle shi suka yi murmushi ta sake saba Amna a kafadarta tana mata tawai


Baba kasa kasa ya ce" Hauwa, wai me yasa kwana biyu bakya zuwa taronku na manyan mata ne?"


Hajia ta yi masa banza


Baba ya yi murmushi yana kada kafarsa ya ce" Kyale miji dai ba kyau Ule"


Hajia ta juyo tana kallonsa ta ce" Alkali kai ba za'a yi makotaka da kai ba sai ka ja fada ne? Haba jama'a "


Baba ya yi murmushi ya ce" Gani na yi masha Allah kwana biyu matar aure sak kike, ga yan yayanki da suka sace maki zuciyarki, bakya zama sai da su a gefe, anya zaki iya ba Mamansu su kuwa? "


Murmushi ta yi ta ce" Zan bata mana, jarirai ne ai, amma kulun sai a kawo min su su wuni a nan, Alkali ai ka san burina na samu yan biyu ko?".............


Shigowar da Fido ta yi kamar hankalinta a dan tashe ta gaishe su zata wuce ya saka Hajia kiranta tana kallonta, domin yannayinta ya nuna hankalinta ba a kwonce yake ba


Dawowa ta yi ta duka kanta a kasa kusa da Hajiar


A tausashe Hajia ta ce" Firdausi lafiya kuwa kike?"


Fido ta dago idannuwanta da suka cika da kwallah, domin daga dakin Amina take ta wanketa soso da sabulu , a hankali ta ce" Lafiya kalau HAJIA "


Hajia ta ce" Inafa lafiya kina magana hawaye na zirara a gurbin idannuwanki? Hala Uman biyun ce ta dake ki?"


Firdausi ta girgiza kanta da sauri, Baba ya dafe haba yana fadin" Kai duka kuma?"


Fido ta sake girgiza kanta a sanyaye ta ce" Hajia, dama Dady ne yace idan ya dawo zai dauran aure da Docter....shine shine....."


Hajia ta sake zuba mata ido dan gane damuwar tata ta ce" Shine hankalinki ya tashi ke bakya son auren ko Mansur din ne bai maki ba?"


Kanta ta sada, hawayenta yaa karra balewa, hannayenta har rawa rawa suke, idan ta duba ci gaban da ta samu na rayuwa, irin yancin da ta samu da farin ciki da kwonciyar hankali na rayuwa a yan kwanakin nan, kuma ta tuna gidan aurenta takan ji ba zata taba iya yin aure da kowa ba, gwara ta yi rayuwarta haka a gefen yayarta da danginta hankali kwonce ba tare da wulakanci ko matsawar namiji ba, Mansur namiji ne cikake ma kuwa, domin ko a samfari na kyan fuska yana da shi ba mumuna bane, maaikaci ne, kuma mutun mai sauraron mutun ne, sai dai mazan ai haka suke, jira suke su malakeka a matsayin nasu shikenan su wulakantaka, jira suke ka zamto yi na yi, bari na bari su juyaka kamar ba dan Adam ba, ta tsorata da duniyar maza, yaya namiji mai mace zai zanto alkhairi a rayuwarta ita kuwa? Bata tunanin zata iya samun haka, namiji dayama ya wulakantata bale mai mace?


Zama hajia ta gyara ta ce" Fido taso li zauna saman kujera"


Firdausi ta sake sada kanta dan ba zata mike ta haye saman kujera dar ba ta jeru da HAJIA ba


Hajia ta girgiza kai, ta kula kam Fido ba dai dagewa ba, dan haka ta dubeta yanzu a kausashe ta ce" Ke zaki taso ko sai naa tsinkawa fuskarki mari ne?"


A zabure ta tashi ta hau saman kujerar tana kallon Hajia da sin gane me ya yi zafi? Baba kuwa ya yi murmushi abinsa yana kallonsu, domin so yake ya ga abinda zai faru, ya tabata ba za'a tashi lafiya ba domin Firdausi akoy sanyin hali,, Hajia kuwa da kagauta, shi yasa tafiyarsu ke tafiya da Amina, domin ita batama sake ba bale ta sha ashar din, dama ita batada sanyin hali


Hajia ta mayar da Amna cikin shinfidarta ta runguma mata dan filo tana dan shafa gashin kan yarinyar mai cika da baki ta ce" Ki saurareni da kyau, rayuwa bawa na haduwa da jarabawa kala daban daban, ki kadara mijinki wanda kuka rabu dama shine kadararki mai karfi, ki sani haka Allah ya hukunta maki, a yanzu kuma ba shi zai hannaki duban wani ba, ba shi zai hannaki auren wani ba, ba shi zai sa ki yiwa maza kallo iri daya ba, ke a kadarama Mansur dan iska ne ko? Ni da kaina zan tarda shi na nuna masa bai isa ya wulakanta min jika ba!, Ban ce zaman duniya zaki rayu kamar wata wace ta shiga aljana, ba bacin rai, kulun sai farin ciki, aa aa, ko daya, dole watarana zaki ga bacin rai, ai zama ne da iyayenkama kana haduwa da haka bale da miji, wannan shine zaman, ama fa ina mai tabatar maki idan kika auri Mansur kin samu miji, ki je ki share hawayen nan kina wani abu kamar an zare maki laka, ki yi da jiki ki yi kaza kaza bana son lalaci, tashi ki share hawayen ras ki je ki kimtsa tare zasu zo ya sauka tun dazu yana gida Mansur din zai je su zo tare, maganar aurenki an yi an gama saura idan ya zo na ji wata maganar "


Zungui zungui zungui ta mike ta tafi jiki du a mace dan Hajia batai mata da sauki ba ta bude dakinta ta shige zuciyarta cike da tunanin shin zata ba Mansur damar ne ko kuwa ta fada masu gaskiya cewar ba zata iya zaman aure da kowa ba, a barta ta rayu ita kadai shine burinta?, Idan ta tuna maganarsu da Uman biyu sai ta ji hankalinta ya sake tashi, yaushema Uman biyu ta fara cewa wai abinda dadynsu ya yi ita bata da ja? Ta yi tunanin zata ce ne aa bata cikin a yi nata aure yanzu domin ta fi kowa sannin me aure ya mata, ama da ta yi insister sai ta nuna mata ai ba zata zauna ba aure ba, shekarunta duka duka nawa? In ba fan an mata aure da wuri ba itama bata fi a raineta ba, dan haka ita bata cikin wannan maganar ta tafi kawai ta bata waje


Jiki ba karfi ta shirya itama , ta samu kanta da dan shafa dan jan baki , sai kuma ta yi murmushi da ta tuna abinda ta baro a dakin Auntynta, Auntyn nata ta dora kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login