Showing 9001 words to 12000 words out of 145392 words
Chapter 4 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
da ruwan wankin da ta yi, kasancewr anguwar ba wai mai duhu ce cen ba ya sa idannuwanta duka sauka a kan mijinta dake sauko da ledojin nan yana ajiyewa a kofar gidan Amina
Baban abinda ya sakata sake zuba masu ido gannin Aminar na binsa da kudi tana magiya ama mijinta wanda ko tau naira dari da ashirin ce ya bara mata na cefanen safe da yama nata da Ζ΄aΖ΄ansu yana nuna ba zai amshi kudin nan ba? Lalle yau abinfa take zargi ne zai tabata kennan?
Juyawa ta yi wuuuuu ta shige ciki zuciyarta cike da sake saken irin yadda zata bullowa al'amarin
Sunna shiga cikin gidan ta rufe ruf sannan ta bude baban dakin tana saka kayansu hadi da kunna wutar nepa da fatan samun wuta dan zafi take ji sosai
Du da alwallah suka shigo suka shinfida abin sallah, itama ta fice dan dauro tata alwallar
Tana zuwa ta shiga gabatar da sallarta a nutse, sai da ta gama sannan ta wuce ta bude kayan
Macaronin da ta siyo masu ta dauko ta shige kicin dinta ta kunna fitilar kwai domin kicin din bata da fitila ta shiga dahuwar gagawa ta hade komai ta tsayar da ruwan miya ta koma dakin tana idasa fitar da abubuwan dake ciki
Ido kawai ta zubawa garin kayan kwalam da makulashen da aka zuba a wata ledar shake, sai makaroni da shinkafa irin na leda masu tsadar nan kala daban daban a wasu ledojin shake summa wa'inda a sanninta dai ba ita ta saka a cikin kayansu ba
Ajiyar zuciya ta sauke ta mayar gefe tana sake duban Husaini gannin sai kallon ledar kwalam da makulashen yake
Bata bashi ba ta daure sosai ta ajiye gefe
Da wuri wuri ta gama girkin lokaci daya tana gyaran kayan miyar da danyen naman da kifin da zata yi anfani da su , so take ta gyara su tun yau kar su kai gobe su cenza warinsu domin bata da freeza bale ta saka
Juyewa ta yi a baban faranti ta ajiye masu karkashin karamar fankarsu da abin firfitu ta kama ruwan wanke hannu da na sha da yaren suka dibo ta ajiye
Hannayensu suka wanke suka shiga cin abincin bayan sun yi adu'a
Basu jima a kan cin abincin ba suka tatare ta kwashe komai da kanta ta darwaye abubuwan da suka yi amfani da shi da ruwan rijiyarsu mai kyan gaske sannan ta dawo ta zauna ta kirayi yaren
Gabanta suka zauna su biyun, ta tsura masu ido irin yadda suke kama ita da kanta ta yannayin girman jikinsu da kuma kamanin idannuwansu kawai take bambance su
A hankali ta ce" Waye ya baku izinin fita daga bayana bayan tafe muke tare da ku?"
A tare suka kwashi magana wannan na cewa dan uwansa ne wannan na nuna dan uwansa
Kausasa muryarta ta yi sosai ta ce" Ba zaku fadi gaskiya ba kennan?"
Jiki a sanyaye Hasan ya ce shine, sai kuma Husainin shima ya ce shine, lokaci daya kuma sai Husainin ya dora kansa a gefen kafadar dan uwansa ya fashe da kukan da ya kusan sakata karaya harma ta rarasheshi bayan ta dauri aniyar yi masu fada da nasiha ne, koda zata yi rarashin ba yanzu ba, dan haka ta jure sosai tana kallonsa ta ce" Kai mike daga jikinsa kuma ka kama min bakinka ka yi min shiru! Yaya nace maku a kan abinda aka bakuma bale wanda kuka gani kuka dauka? Yaya na ce maku a kan haka?"
Da sauri Husain ke rufe bakinsa dan kar ya kuma fashewa da kukan stlll yana son bada amsa ga kuka na hanna shi, dole Hassan ne ya ce" Kin ce ko bamu abu aka yi kar mu ci sai mun nuna maki, kin ce mu daina amsa bale idaan muka ga abu ko na waye kin ce kar mu yarda mu taba ko mu dandana , ba kyau, daukan abinda ba naka ba babu kyai, sata ne, sata kuwa kin ce haramun ne"
A sanyaye Amina ta ce" Ba nice nace haramun bane Fadeel, Allah ne ya haramta sata, du wanda ya yi sata a hukuncin adinin musulunci ance a datse gundugwuilar hannunsa, "
" Wayo Allahna hannuna, Mama walahi ni ba sata na yi ba, dauka na yi nace zaki biya shine na ji ina kwadayin abin na bude na diba kadan" Husain ya fada a raunane yana shirin kuma barke mata da kuka , abinka da wanda ya aikata laifin
Ajiyar zuciya ta dauke tana fuskantarsa ta ce" Farid babu kyau, haramun ne, Allah ya haramta, ko me kake so a duniya ka fada min, in dai bai fi karfina ba in sha Allah zan yi maka shi, ka ji?"
Kai yake gyadawa da sauri, hakama dan uwansa,
Sai da ta tabatar sun gane fushinta a kan wannan lamari, sannan ta dawo nasiha a tausashe sai kuma ta saka suka yi salar isha'i suka kwonta
Kamar yadda ta saba tunda ta salaci sallar asuba ta dora kaskon tuyarta a tsakar gidan ta shiga aikinta da murhu biyu da itace ba da gaz ba
Safiya na yi aka ringa buga mata gidan daidai ta taso biyu ta sakasu yin wanka d shiryawa
Zuwa ta yi ta tambayo waye, kafin ta bude
Da fara'a suka gaisa ta yi baya ta bata hanya ta shigo hannunta rike da Saudat da ko ido bata wanke mata ba
Kujera yar tsuguno ta mika mata tana mata murmushi ta koma ta ci gaba da toya wainar matar Mai shanu domin ta gama tashi tuni ta zuba a kwanon nan ta kilace
Murmushi Innar Sauda ta yi tana fadin" Oh Amina ke kam jinninki ya hadu da mai gidan abanku, bayan kasa ta birni idoma bai yada ke ba, da ba dan Baba Mai shanu ya tsufa sosai ba ai da aurenki ya yi ya cencaneki sosai, ama yanzun idanma ya aureki anya zai iya da ke?"
Amina ta dan katse zuba kulin ta kalleta da dan mamaki, sai kuma ta yi murmushi bata ce da ita kanzil ba ta ci gaba da zuba kulin wainar
Haushi ne ya kamata a ranta tana ayana ' shegiya mai shegen taurin kan tsiya, maganarma ba zata yi min ba dan bakin hali!'
Murmushi ta yi a bayane ta ce" Um, maza? Maza? Kin ga tunda na gama sallah na zo na tsaya nake jira ki gama ki bude dan na shigo na amshi wainar naj sadaka na ba yar nan, ki duba ki ga abanta a jiya naira ashirin daya da ya banu tun safe bai kuma waiwayarmu ba, wannan lamari na maza da me ya yi kama? Namiji ba kama gida, ba fara'a idan ya shigo gida bamu isa mu yi wata walwalar ba sai idan ya fice, shi kulun a babu yake, ko so yake na je wani wajen na samo mana ne?"
Amina ta zuba masu wainar isashiya ta miko mata harda miyar da ta sha kayan hadi na gargajiya sai kanshi take a hankali ta ce" Allah shi kyauta"
Maman sauda ta amsa tana ajiyewa gabansu da yin godiya ta ce" Ke kika san Allah shi kyauta, wai shine harda yin budurwa a cen bayan layi, ai nace ba damuwa ta kula shi idan har ya kawota sai mu ci idonmu baki daya"
Amina ta yi murmushi tana idasa zubawa a kwanon Matar mai shanu ta kilace shima sannan ta zauna tana gadin miyar har ta daidaita ta zuba masu isashiya a dayan kwanon ta hade komai a cikin kwondon da take mika masu ta zubawa biyu suka zauna sunna karyawa sannan ta shige wanka
Da ta fito ta shige ciki ta cenza tufafinta cikin shigar riga da sket na atampa ta zurmuka katon hijab dinta mai ruwan kasa har kasa mai hannuwa ta daka dan kwali sannan ta dake fitowa jin ana salama
Ummu salma ce ta zo tambayar gyaran amarya , nan suka yi magana suka gama ta tafi harda bada rabin kudin
Innar sauda kam kallonta kawai take yi, gata dai baka ce ita ama ko ita ta fita kyan gani, ita da kanta tana matukar kaunar kalar fatar Amina, ga shegen nutsuwa da dan uban miskilanci du yadda ka so ka daki cikinta ba zaka samu abin fada ba sai dai ka gaji ka hakura,
Tare suka fito daga gidan na Amina ta rufe komai suka yi gaba neman abin hawan da zai mikasu gidan mai Shanu, da kallo ta raka su har suka bacewa ganninta, Tsaki ta ja a fili a ranta kuwa tana ayana' Yarinya karama ba miji ba komai aman ta gaje komai na anguwa, idan gyaran jiki ne ita, kitso ita, komai ita, kowa mutunci yake da ita! To walahi baki isa ki shiga gidana ba ki hanna min zaman lafiya da kwonciyar hankali da rawar gaban hantsi a gidana!'
A hankali ta mikawa mai adaidaitar kudinsa tana kallon kofar baban get din da aka wangale ba'a rufe ba
A nutse suke tafe yarenta na rike da wasu kayan itama tana rike da wasu suka wuce baban get din sula gaisa sosai da mai gadi sannan suka dauki bangaren Baba Mai Shanu
Wani irin ja ta yi ta tsaya a lokacin da idannuwanta suka sauka a fuskar yaron nan na jiya wanda aka wulakantata a kampaninsa ta kai kara ya mayar da ita yar iska dan rainin wayo ya fito daga cikin wata galeliyar mota ya ja ya tsaya yaba karewa gidan kallo jikinsa sanye da dakakiyar shada ruwan sararin samaniya sai haska ido take fuskarsa daure yana kallon wani gayen dake masa hira yana ta nunawa yana dariya ama shi sai binsa da kallon nan na raini yake yi baya bashi amsa
Mutuwar tsayen da ta yi na yan sekwani ne da sauri ta juya da nufin komawa
Husain ya kalleta ya ce" Mama ina zamu je?"
Daburcewa ta so yi sai kuma ta juyo gannin Baba direba ya taho da dan sauri hannunsa rike da wata jaka ya wuce su fuuuuuuuu yana sauri gaisuwarma sama sama ya iya yi mata ita
A hankali ta ce" Baba ko dai yau Baban baya nan?"
Baba direba ya ce" Yana nan yana ciki fa, jikansa ne ya zo yau ai ba kanta ki taho mana"
"JIKANSA?" ta furta a saman lebenta, ta taho?
Ta sake tambayar kanta,
Abinsa ya faru a jiya ya dawo mata sak sak , irin abinda ya faru ya dawo mata, kwarai riketa da kokowar da take yi a kan idannuwansa ya koma ta kuma bishi ta dora daga inda ta tsaya
A hankali ta rike kwondon da kyau a lokacin da ta ga ya juyo barin fa suke da nufin shigewa ciki
Dan kallon second daya takk ya maka masu mai shige da harara ya dauke kansa ya shiga tatakawa ya shige ciki
Da ido ta raka shi, sai kuma ta juyo kan yaran ta ce"
πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ
_*NI ZAN LADABI*_
πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ
*NA*
*SAJIDA NIGER*
Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida
Wannan Novel na kudi ne ba free bane
Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER
Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai
Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka
*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπ₯°π₯°π₯°*
*Page 0οΈβ£5οΈβ£*
Da ido ta raka shi, kasa kasa ta ja tsakin jin haushi, sai kuma ta juyo kan yaran ta ce " Kumu je mu ba Saliss gayacen ya kai sakon Baba, yau bakine da shi ba zamu shiga mu dame shi ba"
Gaba daya yaren basu so hakan ba, bama kamar Hasan, du miskilamcinsa da rashin son mutanensa sunna shiri sosai da Baba, koda yake baban ne datijo mai datako da iya mu'amalantar mutane kala daban daban, yakan zauna da Hasan ne da irin mood din da ya zo masa, idan yan hirar ne su taba kadan ana nasarwa, idan yan a zauna a kalli junnan ne sao su wuni a haka bai ce masa ufan ba, to shi da ya zauna da jikansama suka yi zaman lafiya bale hasan jariri, ga dai jikan nasa a yanzu ya kawo mizalin da ya dace ace ya ajiye iyali shima ya yi nasa gidan da mace zata dora tukunya ta masa sannu da zuwa idan ya dawo daga nema, ama sai gidan ba macen a ciki, shi gana dayama tale takensu da kakarsa ba wani dada yardarsa da kasa suka yi ba, ya dai zuba ido ne yana kallonsu
Gaba daya sakon ta ba daya daga cikin yaren dake aiki a gidan wato Saliss suka yi tafiyarsu tare da yaren
Salis ya nufi baban falon Mai Shanu ya yi salama sannan ya ja ya tsaya daga kofa, domin ya san yau madame na wajen ba zai so ya shige kansa tsaye ba ya samu matsala
Mai Shanu dake zaune cikin sasaukar shiga ta hausa , lalausan yadi kansa sanye da hula ya sake waigowa kofar yana fadin" An amsa salama malan Salisu ka ja ka tsaya ka shigo mana?"
Salis ya daga labule ya shiga da salama a bakinsa a karro na biyu ya karasa direcy gaban Mai Shanu yana kokarin dukawa da kayan dan ajiyewa wata murya mai cike da nutsuwa, furuci kasa kasa sosai, cike da cikaken aji da wayewa ta furta" Ka kai dining mana kar ka ajiye a nan"
Mai Shanu ya dubeta sai kuma ya kalli Salis ya ce" Aa ya ajiye min a nan, wannan kamar kanshin Wainar maman biyu?"
Salis ya ajiye din kansa a kasa sosai ya karra nutsuwa ya ce" Eh itace ta ajiye ta koma tace zata mika biyu makaranta ne"
Dan jim ya yi sai kuma ya gyada kansa yana furta" ALLAH ya anfana, ya saka da alkhairi, ya yi mata albarka"
Salis ya ringa amsawa sannan ya mike ya tafi
Bayan fitarsa da kamar minti biyar Hajia ta kuma dagowa ta kalli mijinta a karro na hudu tun bayan maganar da ta yi ya take ko kallo bata ishe shi ba, ya wani kama yiwa yarinyar dake aikata aikin nan da kudin da yake tura mata godiya kamar wace ke ciyar da shi sadaka! Kanta ta cire ta maida kan Jikanta, abin kaunarta , farin cikin zuciyarta , abin alfaharinta taba cire gilas din karin ganninta hadi da ajiye jaridar hannunta ta ce" Cencenta ce ke nemanka ido rufe , ba kai bane ke nemanta *ABDUL RA'UF!*"
Sau daya ya dago daga rubutun da yake yi a wani litafi ya sauke dubansa a kanta, sai kuma ya dauke dubansa ya maida cikin litafin ya sake dasa alkalaminsa ya dora daga inda ya tsaya
Gefen da mijinta yake ta sake kallo, wannan karron abin ya taso mata daga cen kasan zuciyarta tana kallonsa ta ce" Ama ai sai ka yi masa magana ko Alkali?"
Wainar da ya ciro ya dangwala miyar taushen ya sake kaiwa bakinsa, domin tuni ya fara karyawa da ita ya juyo inda take zaunen,
Walwalin da take yi abin birgewa ne, ita din mace ce mai kwaliya, sam fatarta bata samun hutun rashin gyara, tun tana da jan sawunta da ya daukota ita din mai kwaliya ce, har yanzu da ta kawo shekaru hamsin da hudu a duniya ba zai ce ga wata macen da ta kaita iya saka kwali ba a idannuwansa, yyarintarta yake ganni ainun, a kanta ya gane bak'ar fata aba ce mai daraja da mahinmancin da ko ta zo tsufa idan da gyara sai shekaru sun yi mugun ja take nunawa, ita din ba farar mace bace, ama irin yadda ta iya daukan ado da gyara da ba kalar fatarta daraja ko farar fatar na mangarinta
Da yawa masu shekarunta sun koma sun jabge, wasu tsabar lalaci da son jiki sun fake da sun tsufa ko kunshi sun daina yi, ama ita din wannan tasan da a yanzu shi tsufan ya masa zuwan gaske ita a danya sharat yake ganninta, baban damuwarsa idan ya kwonta dama shine ya bar wannan abokiyar rayuwa tasa mai wasu halayan da yake gannin hagu a tare da ita, giyar mulki , kaunar siyasa ba yau ba suka yiwa jinninta billin da ita da kanta bata fahimta ba!, Gatanan dai a zaune a kan siyasa sai ku haura sam ku fado wuyan kowa ya karye a huta, a yanzu haka rigimar da take kokarin janyowa a tsakaninta da jikan nata da ta san mutun ne mai zaune da ra'ayin kansa, wanda ya ki jinnin wani ya nemi yin iko da shi, shi yasa ya zama mutun mai ikon kansa da kansa ta hanyar kasancewa bos din kansa yake *NEMAN NA KANSA* da karfinsa da kuma guminsa ba tare da ya jira wani ya masa ba ko ya yi jira an bashi damar yi ba, shi din mutun ne da ya ki jinnin a ja shi a kasa a kan komai, shi yasa yake nema da karfinsa da kuma lokacinsa, wannan miskilin jikan nata take so ya tashi ya nemi takarar gwamnan garin nan, tana so ta bara masa wajen da take nema a cewarta aljihunta bashi da nauyin yin farfagandi, kuma bata da matasa a damarta , shine take so shi ya motsa ya bude aljihun wandonsa ya yi zuba na kudi sannan ya riko matasan dake tare da shi su hau wannan tsani mai nauyi da hatsarin gaske, dan kawai wannan din shine