Showing 72001 words to 75000 words out of 145392 words

Chapter 25 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8148

samu tarewa a gidan bale muce ko an samu dan tayi ne na dan zaman da ake yi kafin mai wajen ta yi maki wahe rod?"


Mtssss, itafa walahi bata son wulakanci, ita kwata kwatama mutanen nan bata ga abin mutuntawa a cikinsu ba, itafa tanada sanyin hali ne ga wanda ya nuna mata mutunci


Da wani takaici ta dan juyo tana kallonta , da kakausan kallon da ya saka kowace duban tsagar idannuwanta, domin ido ne take dauke da shi mai bada umarni ba wai mai risinawar nan ba, idanma komai na Amina yanada sanyi banda idannuwan nan nata
A hankali sosai da yannayin tashin amon muryarta mai cike da kasaitar da Allah ya halita mata ba wani ba ta ce" Kila hakane, kila kuma ko dan tayin ne, ta yiwuma uban biyu zai karra samun baby ne.........tunda lamari na ba zata da bakon al'amari, ta yiwu kwon biyu da aka samu ne za'a kara samun wani...........haduwar jinsi da jinsi kuwa ai kamar maganadisu ne,........sirrin dai ne bana son fayacewa dan lokaci ke nunawa!" Magana ce ta bada a sanyaye, a lalauye, a hargitse, sai dai dukkan wata mace dake wajen ciki Harda Baba lauratu sai da ta hangame baki da mamaki hadi da zarro ido jin furucin yar baiwar Allahn dake fama da kanta batada lafiya harda jinni


A hankali ta sake juyawa ta bi bayan Umaima da suke ta shiga da kayanta wani sashen daban tana jin yadda Baba Lauratu ke basu hakuri da fadin dan Allah su yi hakuri , baki ta tabe a zuciyarta tana ayanawa' Bana tunanin zan iya hakurin wulakancin yarinya karama da danginta mararsa kunya da jin tsoron Allah, in da wata kuke kallona zan yi iya yina dan baku wace kuke son gani, mai kunya ko fitsarariya, ai ba a kanku aka fara min kallon biyu ni na haifesu ba, ko wa zai yi ya sani ina jin dadin hakan domin biyu dama nawa ne ba na wani ba, shirmen banza wai su nan a kan yaron nan ne har zasu nemi batawa mutun rai;'


Tunda ta shigo Falon sai ta kasa yin wani motsin kirki a cikinsa, domin rantsatsiyar haduwar da ya yi ita ta san ba nata bane falon ta yiwu akoy wajen da za'a ratsa a karasa nata falon


A kadan tana nan rakube ta ki motsawa du yadda ma'aikatan gidan Baba suka so ta karasa saman kujera ta zauna sai ta nuna nanma ya isa kawai, har sai da Baba ta karaso tare da mutumen nan mai kirki, mutun mai mutunci watau MANSUR da wata matar da bata santa ba


Sunna shigowa ana ta sake saka turaran wuta a dakin, Mansur din shi daga bayansu yake, docter ce ta fara shigowa da mutuntawa duka gaisa da junna
Tana kallin Amina ta fahimci itace bata da lafiyar, dan haka ta ce" Sorry Madame ki karasa ki zauna mana, keda baki da lafiya? Hajia ku zaunar da ita ko ba ita bace Madame din?"


Gaban Amina da ya hargitsa ya fatatale ya fadi ta kurawa Baba ido adu'arta daya ce Allah ubangiji ya sa ba ainahin gane abinda ya faru da ita aka yi ba, har aka turo mata matar nan da sia yanzu ta gane farar rigarta me yake nufi, haka kuma ta gane bawan Allahn cen da take ganni take gannin mutuncinsa shi dinma likita ne ashe, sai dai tambayarta daya ce tal *SHIN WA SUKA ZO GANI NE?* ,


















😖😖😖😖😖😖😖 Har yanzu bata jigatu ba jama'a da sauranta




*NZL PAGE2️⃣8️⃣*














"Amina ki karasa ki zauna mana wai me yake damunki ne yau?" Baba Lauratu ta fada tana tsatsareta da ido, domin gana daya Aminar sai wani abinda bata santa da ita ba take yima mutane a yau , kamar wata mai tashin balagar rashin kunya


Amina ta sada kanta, kunya na neman hadiyeta baki daya
A hankali ta sake dagowa a lokacin da ta ji Mansur ya yi dan gyaran murya ya shigo gaba dayansa ya dubi wajen Hajia da docter ya ce" Baba, ba saman kujera zara zauna ba, ta wuce ciki kawai, Docter ki shiga ciki ki dubata ba zai yiwu ta zauna a falo ba domin ba'a san tashinta daga nan din ba"


'innalilahi' Amina ta ayana a zuciyarta tana cire dubanta a kansa ta maida kasa
Rasa abinda zata yi cikin kin zuwa din ko zuwan ya sakata sake damkar zannin gadon dake rabe da jikinta ta juya jiki a mace ta nufi dakin da ya nuna din, domin idan akoy abinda ta yarda da shi a lokacin nan daya ne tak, shine ba zata iya hada ido da mutumen nan da tsoron kar aje ya san abinda ya faru da ita ya cika mata ciki


Du yadda ta so tafia da sauri a dole ta tafi a hankali ta shige dakin tana tafe a hankali


Muryar doctern a nutse da ta nuna mata bed din dake kasace da wata niimtaciyar shinfida tana fadin" Madame, a nan zaki kwonta dan kasa ba zai maki dadi ba" domin ta kula kamar Aminar nema take ta yada zango a saman cafet din dakin shi yasa ta katse mata hanzari


Amina ta ka numfashi ta karasa ta zauna a ringeshe tana rintse idannuwanta


Zama likitar ta yi ta fuskanceta sosai , a nutse ta ce" Madame?"


Amina ta kalleta sannan ta sake sada kanta hawayen da ya cika gurbin idannuwanta ya ringa hayewa jikin gashin idannuwan nata


Yannayinta ya saka matar sake fahimtar abinda docter Mansur ya dan kwatanta mata a gajarce


Murmushi ta yi a nutse ta ce" Kin ga, tun kafin na dubaki yannayin tafiyarki ya sheda min kina cikin halin bukatar taimakon gagawa, kin san shi wannan waje waje ne mai hatsarin gaske, babu wajen da ya kaishi bukatar taka tsantsan da samun isashen kula a duniya, kin ga idan ido ya makance zaki iya rayuwa normal, ama idan shi ya rube ba zaki anfanu ba da dadi a rayuwa, koda kin rayun tofa a cikin wahalar rayuwa ne, karshema kina iya yinta rayuwar ke daya a kauye daya dan gujewa wulakancin mutun, ina so ki yi aiki da iliminki, ki bani dama na dubaki a yi maki dukkan abinda ya dace a maki, Ni likita ce, Gynécologue ce ni, na jima a saman aiki a kadan na shekara goma sha daya, ina duba Hajia ne kawai a familly dinku sai yanzu kika shiga layi bisa umarnin SIR, zan so ki yi anfani da iliminki mu taimakeki ki ji saukin jikinki, ina fata kin fahimta?"


Kan Amina a sadden take tunani kala kala a cen cikin zuciyarta


Muryarta a sanyaye ta ce" Aunty, wanene SIR?"


Docter ta yi murmushi itama da kula tace" SIR ABDUL RA'UF sister"


Amina ta dago idannuwanta a hankali tana kallon matar
Eh lalle matar nan ta fada mata gaskiya, idan ta yi wasa da jikinta da lafiyarta itace a ciki, yau idan ta lalace a kwonce wa zai kular mata da biyu?, Kuma matar ai ba yarinya bace dimin ko a haka da take wanke jikinta ya nuna ta bata wasu shekaru goma ko sama


A hankali tace" Aunty na cire kayana ne?"


Docter ta sake yin murmushi da kula sosai ta ce" Aa ba duka kayanki ba, iya zanninku ne mu duba wajen"


Karshe dai tabas Amina ta samu kari, kuma a lokacin Docter ta hada allurar dinki ta yi mata shi, wanda saida Amina ta ringa hawaye tamkar zata summa dan azaba, domin wajen ya kwana ya sake rinewa da wahala, ana yi mata tana tunanin anya akoy wahalar da ta kai wace ta sha daga jiya zuwa yau? Sosai ta karra daukan zafi da yaron a zuciyarta, dinki? Kamar wace ta haifo kan dan mutun daga jikinta? Wannan wani irin cin zali ne?


Docter na gama yi mata tana mata sannu ta bata magungunna na zazavi da kuma na samun sasaucin radadin, cikin nutsuwa bayan Aminar ta rage jin radadin harma ta taimaka mata ta cenza wata riga yar yololuwa dan ta samu hutun mai dadi sannan ta sake bata shawrwarin yadda zata kula da kanta, ta fada mata cewa karta einga gasa kanta yanzu, ta bari zuwa jibi dinkin ya fara neman hanyar warkewa sai ta fara gasa kanta


Amina ta gyada kanta barci na fuzgarta dan ba wani isashen barci ta samu bafa a hankali ta ce" Aunty, dan Allah karki fadawa kowa cewa har kari na samu sanadiyar wannan, sanadiyar sa"


Docter ta zuba mata ido na dan dakikai, sanadiyar wannan din da ta hadiye ya dan so ya sakata a tunanin wannan me? Sai kuma ta ture tana murmushi tace" Karki damu, in sha Allah wanda ya dace ya sani kawai zai sani, ba zan sanarwa wani hakan ba"


Amina ta gyafa kanta tanai mata godiya sannan ta rakata da ido har ta fice a dakin


A hankali dan sanyin Acn na dan ratsata har barci yayi awon gaba da ita a saman lalausar shinfidar gadon , barci mai nauyi da kuma ragewar radadin wajen, hakan ya sa ta lula a barcinta har tana sauke ajiyar zuciya


Sosai Docter ta sake yiwa Baba lauratu bayanin abinda ya dace a yanzu ta ringa ci dan jikinta ya samu wadatacen kulawar da zai yi gagawar warkewa, ta sake jadada mata kar a ringa shiga ruwan yanzu, ta kuma yi nata maganar zama da hade kafafuwa da kula sosai domin kofa ba da kanta ta haihu ba idan zafin dinki ya sa a yanzu ta ringa zaman da iska ke iya shigarta sai ta shigeta ta zo tana fama da tusar gaba


Sosai Baba ta mata godiya ta rakata sannan ta dawo itama ta ringesa tana yiwa Allah godiya da sake duban falon nan, sai ta saka harshen hijabinta ta share hawayenta a fili ta furta" Mahakurci mawadaci kennan, ashe mijinki na nan rantsatse Innar marigayiya? Kinga yyau harda yan aiki ne da ke , Allah dai ya maba maganin sabon halin da ya sameki uman biyu, ki yi hakuri ki yiwa mijinki *LADABIH*"


Tunda suka fito suke dan tafe haka a hankali tana yi masa bayanin matsalar da kuma solution din da ta dauka , sosai ya gamsu da komai harda maganin da ta bata,
Har bakun motarta ya rakata yana sake yi mata godiya domin a aiki ita din gaba take da shi, kuma irin yadda rake mutuntashi da sauran ma'aikatan dake karkashinta ya sa summa suke mutuntata a rayuwa


Yana tsaye har Motarta ta fita a gidan sannan ya juyo wajen da ya hange shi tunda suka fito ya daga kansa


Yana tsayen kuwa hannunsa daya a harde a bayansa, dayan kuwa ya dafe abin madubin shima yana kallonsa


Murmushi ya yi ya tunkari part din nasa ya bude ya shiga falon ya ratsa ya shiga hawa matatakalar


A gajiye ya idasa hawa ya tsaya ya bubuga sannan ya murda ya shiga


Dafe da bayansa ya shiga yana kallon ABDUL dake zaune saman wata lalausar yar madaidaiciyar kujerar da ta yi masa kadan yana fadin" Kaikaikai, wannan idan na yarda na yi hawa goma a wata guda tabas zaunewa zan yi, wai ku yan gayun nan me kuke ji a gidan sama ne? Du ku bi ku mutu shekarunku basu kai mutuwar ba?"


ABDUL ya yi murmushi yana dauke kansa a kan Mansur ya ce" Idan ka ga ka mutun dama a rube kake man , ba laifin Upstairs bane"


Shima dariya ya yi dan yadda ya yin wai irin ya tsokale shin nan


Zaune ya kai kusa da shi kadan yana bashi hannu ya ce" Yaya kake? Ya jikinka?"


Abdul ya amshi hannun suka gaisa sosai a hankali yace" Mansur bani da lafiya ne?"


Mansur ya dage kafadarsa yace" na sani, na ga ka zama na daki kamar wani sabon ango........"


Abdul ya ce" Uhum" sannan ya yi shiru yana sake zubawa waje daya ido


Yan sekwani sun ratsa tsakani a hankali ABDUL ya ce" Wa ya dubata ne?"


Da gangan Mansur ya ce" Wace?"


ABDUL ya zuba masa ido, sai kuma ya tabe bakinsa yana kawar da kansa ya yi shiru


Yanzunma sun sake daukan lokaci Mansur ya ce" Da gangan ka yi, ko a rashin sani ka yi? "


ABDUL ya sake kallonsa, ya kuma cire kansa bai bashi amsa ba


Mansur ya yi murmushi ya ce" Ban taba tunanin zaka yi irin aikin nan ba, domin kanada ilimi"


"Ka daina magana kamar wanda kaima baka cikin mamakinta, abinda nake son sani a lamarin nan shine....mata ana yi masu halitar virginity biyu a rayuwa ne ko.......ko TWINS ba, ba ita ta haife su ba?" ABDUL ya fada a dake yana murza gaban goshinsa kadan


MANSUR ya ce" Sai dai idan Twins ba ita ta haife su ba, ama babu macen da aka halita da budurci biyu a duniya, fannin likitan mata ka karanta, kasuwanci ya kamaka ne, ya zame maka dole ne, ko kana so ka cemin akoy abinda ke iya rudaka ka shiga tunanin anya abinda ka gani haka ne ko ba haka ba?"


Da ido ya tsatsare Mansur, sai ya ga kamar wani wanda ke jiransa ya kwonkwonce masa nagangannu, to a ganninsa menene na sin titsiye shi? Me yake son fadi a maganarsa na cewa akoy abinda zai rikitashi a kan wannan lamarin ne?


A hade ya ce" Me kake nufi da na rikice na kasa fahimta?, Emotion mai karfi irin na MACEN DA AKE YIWA gagarumar soyaya, ko karfin kauna irin ta iyaye?"


Mansur ya yi murmushi a zuciyarsa, a bayane kuwa ya ce" tambaya na yi"


"Amsarka itace ba dayan biyu" ABDUL ya maida masa yana sake dauke kansa


Mansur ya dake yin murmushi yana ta kallon ABDUL, he can't believe it, ABDUL abokinsa , amininsa ne ya wayi gari da wannan farin cikin da yake dannewa karfi da yaji, ya kasa fahimtar alkiblarsa a yanzu, idan ya yi kamar ya tsani lamarinta, sai kuma ya tare mata wani abin


Mikewa ya yi yana murmushi yace" Ya dace ka dauki magani kuma ka yi sleep, ND.. .......nd ........." Ya dakatar da maganar yana kallonsa kamar tadda shima yake kallonsa


Mansur ya ce" Nd kana da tarbiya, u'r a gentle Man, ya dace ka kwatanta kula a gareta............, Kamar yadda ka fada ne, tanada shekaru kadan a saman kanta.... but tamkar baby haka take....she need ur care "


ABDUL dai da ya yi shiru baisake ce masa komai ba, dan ya kula Mansur sai wani nemansa da masifa yake yi, wai wani ya dauki magani dan kawai ana cewa ko namiji idan dai yinsa na farko ne yakan fadi rashin lafiya, ya manta ba kowa da kowa ba? Hm!




Sai da Mansur ya tafi sannan Abdul ya sake mikewa daga zaunen da yake ya karasa kusa da wayarsa ya dauka ya sake gwada number kakarsa
Sai dai still bata daga ba
Murmushi ya yi ya yi kiran mijinta suka sake gaisawa a mutunce sannan ya ce" Tsoho, ina fata ka leka asibitin wajen Hajia?"


Baba Mai shanu ya kadakai yace" Ka ganni nan a gidan gona bangaren shanu mun kada shanu ni da Rabi'u muna rakasu kiwo , ka san me Abdallah? Wannan rufe shannu da kuke yi ku yan birni bashi da wani anfani, shi yasa shanayenku basa sakin karinsu su dauki girman jiki sosai............., Abincima kulun kunna kayade masu wanda zasu ci ta yaya kuke so su yi kiwo?"




"Baba, kalli wancen farar ta ki yin gaba ta ki yin baya sai wani irin abu take yi" Muryar Husaini ta shigo cikin wayar, sai kuma muryar Baba Rabi'u yana fadin" Aliyu wancen fa haihuwa zata yi, ka ga fa ta hau gwuiwa"


Baba da dan sauri ya karasa yana sauraron ABDUL dake fadin" TWINS na tare da kai ne?"


Baba yace " Eh ai daga makarantar tasu nake na dauko su sai muka wuce nan "


Dan shirun ya sake yi, sai kuma ya samu kansa da fadin" Ina iyayensu suke?"


Baba ya dakata da tafiyar da yake yi dan tambayr ta zo masa a ba zata, kwarai ya dan zai tambayeshi hakan , dama da gangan ya boye masa dan yana so ya fara gane idan har yaron ya fara damuwa da wani abu nata , duda ya san zai yi wahala ama kuma yana tunanin idan har ta samu gurbin zuciyarsa sai ta yi fata fata da duk wani tanadinsa


Yana kallon yadda ma'aikatan ke taimakawa sanuwar dake dan fitar da kuka irin na sanuwa mai karfin nan tana ta faman haihuwar ya ce" Umansu ba tana gidanka ba? Ko dai basu je ba da na turo su ne? Likitan ya ganta kuwa?"


ABDUL ya dafe gaban goshinsa a hankali ya ce" tell me father, ka fada min abinda ka san ina son ji mana?"


Baba ya yi murmushi ya ce"






*NZL PAGE2️⃣9️⃣*














Baba ya yi murmushi ya ce" Mahaifiyarsu na nan gidan mijinta, mahaifinsu kuwa ya rasu, ita mahaifiyar tasu itace kanwar Uman biyun ai, uman biyu ta saki nono ita ta kama, su biyu kadai iyayensu suka haifa, sun rasu ne iyayen nasu kai a lokacin kana yawo da naka uban baka san ihayensu ba sam, Allah dai ya jikan marigayi da matarsa, mutane masu karamci da halaci a rayuwa"


ABDUL ya lumshe idannuwansa yana tunanin lamarin kakansa, yanzu dama maganar nan haka take sau nawa yana kawo irin haka bai taba fada masa ba? Yanaga Hajiama bata sani ba ai, kuma yanzu daga tambayarsa yar tambayar nan ya bashi amsar nan a haka kamar wanda ya tambayeshi abin a haka


Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kashe ya ce" Za'a kawo su ne?"


Baba ya kada kai ya ce" Eh to, gamunan dai, ka san yaran nan ne da shiga rai walahi, in ba dan umansu ba zara iya rayuwa babu su ba ai da na yi ruwa na yi tsaki na amshe, ama ko a yanzun dai muna shawartawa udan har yama ta yi mai halinka bai nemi umansa ba a wajena zasu kuma kwana, ka san jiya tsakuyar dare ya farka yace ina Uma? Nace ta tafi makaranta, yaron da ya mun wani kallo sai da na ji kamar na masa wani mugun laifi ne Abdallah, uhum nace kai kam kamar daga tsatson Abdullahi ka fito yaron nan"


ABDUL ya ja numfashi kasa kasa yace" Yau ka cika surutu sosai Alkali, Sai an jima"


Baba ya tabe baki ya katse yana sake kallon har Sanuwar nan ta haihu ya ce" Allah ya yankan na magana na gumtse dan nine sarkin mararsa rabon duniya? Karya ne walahi"


Sai kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login