Showing 123001 words to 126000 words out of 145392 words

Chapter 42 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8174

wace zai watsa masu a ido, domin shi ba dan siyasa bane, ba kuma zai tsaya a takarar neman kujerar gwamna ba, bashida ra'ayin hakan gaskiya


Amsa ya yi suka gaisa sosai, ya sake jadadawa , ya bada kwatance tak tak , harda na gidan ubansa , ya sake fadin irin rashin mutuncin mutanen a takaice da kuma tayarwa da ahalinsa hankali da suke son yi


DPO ya yi murmushi ya ce" Wannan aiki ai nawa ne da kaina, zamu zauna da su, idan nan ya isa to, idan bincike ya saka su a uku kuma sai mu maka su kotu, domin sai mun bincike su kaf dinsu, daga ɗan har uban Honorable"


Da wannan suka yi salama


Amina ta saka hannayenta ta talabe habarta, wani tsadaden murmushi ya kubce mata tana kallon yadda Fido ke murmushin itama tana sauke ajiyar zuciya ta mike bayan ta yi godiyar da aka yi mata fadanta ta nufi ciki, cike da gayunta




Hajia ta rakata da ido tana jin wani irin tausayinta a cen kasan zuciyarta


Abinda bata taba yi ba ne ta yi, watau shiga hurumin Amina bayan cikin dake hada su


Tana kallon Amina ta ce"






Nzl 51






A hankali Hajia ta dubi wajen Uman biyu ta ce" Na kasa fahimtar komai, twins kannenku ne? Ko kunnada wata sister din da ta haife su? Dan na ga ai Honorable ya ce min ke din............"


Ta yi shiru dan sai ta ji kamar nauyin maganar take ji a bakinta


A nutse ta idasa da fadin " Ya ce min ke yarinya ce ko?"


Baba ya sake dane kafa yana murmushi yana kallon Hauwa


Amina kuwa ta sada kanta, na farko bata taba magana haka da hajia ba, na biyu wannan magana ta sakata a kunyar da bata taba tunanin zata jita ba a rayuwa


ABDUL ya dan sauke numfashi yana jinjinawa Hajia a ransa


Baba ya ce " Ai ita din nan dai itace maman biyun , ita ta haife su ama ba'a fadi, kuma itace ta samu wasu biyun suka koma"


Hajia ta dubi baba, wani farin ciki na ratsata
Murmushi ta yi ta ce" Ama mijinta akoy sakarai Alkali, idan ba rashin mafada ba ta yaya zaka samu mace mai zubo bibiyu ka yi wasa? Muma Allah ya sa mu dace da samun biyun, Wai Honorable me yasa ka hanna a yi mata scan ne?"


ABDUL ya sake dubanta yana murmushi ya ce" Na fi so ya zamto surprise a garemu baki daya, tunda batada wata matsala a kan haka ya sa na hanna a yi"


A hankali Amina ta ciciba jin kunya zata kasheta ta mike tana dan nishi ta nufi ciki, zuciyarta cike da mamakin lamari irin na yan gayu, a zauna a waje daya ana maganar cikin fari da iyaye? Ai ba za'a kiresu kakani ba iyaye ne sak, shima yana sakin jiki hankalinsa kwonce yana bada labari? Allah dai ya sawakawa yan gayu


Gyaran murya Hajia ta yi a karto na biyu tana kallonsa


A hankali ya dawo da dubansa kanta , kallon ido cikin ido suka yi na yan dakiku ya dauke dubansa a cikin nata ya mike yana fadin" Bara na ga idan boys sun gama karatun mu dan fita"




Da ido ta raka shi har bakinta a bude dan mamaki har ya bacewa ganninta


A hankali ta dawo dubanta kan Alkali dake kallonta shima


Damuwa a kan fuskarta ta ce" Me yake faruwa a tsakaninsu?, A matsayinsu na yaran ma'aurata kula da junnansu ya dace ya zarce haka, sai na ga kamar ya fi damuwa da ita?"


ALKALI ya gyada kai yana murmushi ya ce" Hakkun"


Hajia ta zuba masa ido da kyau ta ce" Menene Hakkun Alkali?"


Alkali ya ce" Abinda kika fada ne na dafa, ai ita uman biyu sam jikanki baya gabanta"


"Ina ba zai yiwu ba, a duniya ban ga macen da ABDUL zai yi tsaye a gabanta a matsayin wace zai iya yiwa soyaya ba ta zumunci ba zuciyarta bata motsa ba, babu ita!" Ta fada tana dafe cinyarta dan ta tabatar masa


Alkali ya mayar da bakinsa gefe yana murmushi ya ce" Sai kace wanda ya yi farin jinina?, Sam bai tako Sa'a a gaban Uman biyu ba, shi ke sonmu mu baya gabanmu, ai kin ganni da idannuwanki"


Wani irin shiru Hajia ta yi, ga dukkan alamu kamar abin na dan damunta


Sai kuma ta basar a zuciyarta tana ayana" In sha Allah bama zasu raini dansu ko yarsu a rabe ba"


__________________________________




Da dare, kusan karfe bakwai da rabi,


ABDUL ke zaune saman doguwar kujerar falonsa yana rike da remot din TV yana son sake kallon maimaicin labarun da aka yi na yau wanda bai kalla ba


A hankali Risala ta karaso ta bayansa ta sanyo hannayenta a hankali tana dan murza kafadunsa ta ce" Barka da warhaka Husband"


A hankali ya saka hannunsa yana janye nata yana dagowa ya kalleta, sam hankalinsa ya tafi a wajen kallo bai ji shigowarta ba, koda yake bai kai ga rufe kofar ba ya zauna kallon


Shigar dake jikinta da ita da babu du daya, haka kuma dai ya ga after drss dinta baka ajiye saman hannun kujera


Kansa ya dan dauke yana sake maidawa saman TV ya ce" Baki kwonta ba?"


Risala ta yi farrr da idannuwanta tana zagayowa ta zauna daf da shi tana kallonsa ta ce" Ban kwonta ba, na kasa barcin, so nake na yi a nan"


Abinda yake yi ya dakatar dan kirjinsa take nunawa kuma tana son kwontawa a kai, ita fa a yanzu ba zaku gane bane, dwara da bata samu cikin ba, dan ta kula zumudin cikin kadai mijinsu ke yi, bai damu da mai dauke da cikin ba!, Dan haka gwara da aka yi haka ai


A hankali ya janye hannayenta yana kallonta ya ce" Kin san ai bama haka"


Risala ta turo baki tana cewa" Me yasa kake hannani rabarka a ranar da ita din bata gefenka?, Tunda ba zuwa take yi ta kwana ba ni na zo ai sai ka bani kulawa ko?"


"Ranakun da suke naki zan iya baki kulawa, wanda suke na yar uwarki baki da wannan damar, mu kiyaye kar ki shiga abinda kuma bai shafe ki ba" ya fada a tausashe yana sake dan matsawa kadan, domin du abinnan a idannuwan Uman biyu suke shigagu dadadu , koda ta nace ta kwana a bangarensa idan ranar ba tata bace ko daki basa hadawa, ya gwamace ya shige ya rufe ya kwonta idan ya je ya bi dare ya gano Uman biyu da cikinsa, da kuma twins ya masu addu'a


A hankali ta kawar da kanta gefe ranta na kuna, wannan jaraba da me ta yi kama ne? Bata san me yasa ABDUL ke yi mata haka ba, duda ita dadinta ne babu wanda ya san ainahin abinda yake faruwa a dakansa daga ita sai shi , sai mahalicinsu, ama idan yana mata haka sai ta ringa tunanin ba zai taba zubar da matar cen kwata kwata ba!,


A hankali ta ce" Dama zuwa na yi dan na yi godiya, kuma sai na kasa barci, shine zaka ki ko rabarka na yi ko?"


ABDUL ya yi shiru yana kallon TV din bai ce mata komai ba, dan ya gama magana ai da ita kuma


A hankali Amina ke sake rike kofar shigar zuciyarta na dokawa
Wayar da suka yi da dan gidan uncle dinsu, watau yayan mahaifinsu ya rikitata, bata san a inda ya samu numberta ba, batama san gaskiya ya fada ko karya ba, bata taba sannin idan ta ji dangin nata a wani hali zata girgiza haka ba, tunda ya fada mata maganar mutuwar zuciyarta ke bugawa da karfi, abin cikinta kuwa wani irin juyawa da ya yi ta tabata daga sama yanzu kasa yake kallo ko menene, uwa uba ciwon dake tashin mata wanda ta tabata na tsoratar da ta yi ne ya sakata haka


Ta rasa wa zata nufa da maganar, dole abin ya rikitata, gashi Fido na wajen lesson dinta, Biyu ne kawai a zaune da kayansu na masalaci sunna kallo




Sai da ya lafa mata sannan ta murda ta shiga zuciyarta na daf da tsintsinkewa
Wanda zata yiwa kuka ta ji sanyi sannan ya rakata take nema ido rufe


Da wani irin sauri Risala ta shige jikinsa lokaci daya ta nemi lalubar bakinsa a lokacin da su dukansu suka yi arba da Aminar da kana ganninta zaka fahimci hankalin ta ba a kwonce yake ba


A hankali ta sake dafe cikinta, sannan ta juya a hankali ba tare da ta furta koda A ba




Da karfi ya matsar da Risala gefe tamkar wata yar jaririya dan irin kautar da itan da ya yi da mamakinta yana mata wani kallon da ya tsoratata ya mike da dan sauri yana fadin" Aunty?"


Amina ta dan ja wani tukukin bakin ciki ya murdo ya sake murda mata cikinta


Da karfi ta duke dan har wani irin abu ta ji kamar yana bin kafarta ta rintse ido sosai tana ambaton Allah a zuciyarta


Dukowa ya yi hankalinsa tashe ya kamata yana dagota hadi da fadin" Aunty, menene? Bakida lafiya ne? Me yake damunki plz?"


Hannunta cikin nasa yake, a damke take da hannun nasa dan abinda ke mata zabtu zab zab zab kamar zai summar da ita


Gaba dayansa ya zauna a wajen yana kokarin rungumota jikinsa,
Sai da ya rungumeta sosai yana shafa bayanta a hankali a hankali yana duban wajen da Risala ya ce" Ki dauko min wayata mana "


Rai bace ta mike ta nufi ciki, ya sake rungumo Amina a jikinsa daidai ciwon ya lafa mata ta samu a hankali ta ringa janye jikinta har ta raba jikinta da nasa tana rintse idannuwanta


Cike da damuwa ya ce" Aunty?"


Amina ta bude idannuwanta ta sake zuba masa su, wannan wani irin wulakanci ne marar misali ne a rayuwa? Me ta yiwa wannan mutumen ne? Ai dole ya kireta aunty mana, tunda ya hadata da kayan nauyi ya zo yana kwakular yar yarinya


Hannunsa ya kai zai tabata, a hankali ta janye nata hannayen muryarta na rawa tana kallonsa ta ce" ABDUL, kar ka taba ni dan Allah, cin kashin ya isa hakanan, sannan ka sawake min, wanda na gani ya wadatar!"




Kirjinsa sai da ya mugun doka masa, yana kallonta da kallo mai dauke da mamakinta n kafiyarta da kuma mamakin kennan ba zata taba sonsa ba? Ya ce" Me yasa kika kasance mai furtawa miji ya sakeki bayan ba kyau? Babu kyau mace ta nemi saki a wajen mijinta haka kawai ba laifin da na maki?"




"Kake kiran ba laifin da ka yi min?, ABDUL babu laifin da ka yi min?, ABDUL tunda na dauki cikin nan ka yi watsi da ni, da ni da banza duka daya a wajenka, babu ruwanka yaya na kwana, ko yaya na tashi? Babu ruwanka da komai nawa, baka zuwa ind.................................................................." Idannuwanta ta rintse wani ciwon na sake murda mata


Cikin ciwon ta dake ture shi da dan karfi ta ce" Ka daina tabani nace, idan takamarka ni hadaka aka yi da ni, ka sani nima hakan take! Hadani aka yida kai, bayanshi ba wani abin!, Ka salameni na je na karasa haka, ya isheni haka!"




A sanyaye , jikinsa da zuciyarsa na tsintsinkewa ya sake tareta a hankali ya ce" Ki yi a hankali Plz, ki yi a hankali, ki tashi na kirawo docter dinki ta duba min ke, tun yaushe kike jin ciwo ne? Amina dan Allah ki bar rigimar nan haka kin ji?"


Fashewa ta yi da kuka tana sake tureshi ta ciciba a hankali ta mike daidai Risala ta fito da wayar tana kallonsa ido cikin ido ta ce" Ka bani waje na wuce, ka sani ko kaine autan maza kafata ba zata kuma takowa nan ba!, Idan kana so ka mayar da ita cikinka dan so, hakina da kuke shiga ku je ku kuka sani!"


Gaba daya ta rikice ta rikitashi ta hannashi rabarta ta kuma ki saurarawa


Wayar ya fizga a hannun Risala ya wuce ciki yana lalubar jalabiyarsa dan ya bita bangarensa, gaba daya hankalinsa a kololuwar tashe


Ya dan jima ciki dan bai iya rudewa ba a rayuwa, da kyar ya samo rigar da ya saka ya fito


Abinda ya sake bashi haushi da Risala, tan tsaye hannayenta harde sai jikiga take yi


Kallonta ya yi ya ce" Baki bita ba?"


Risala ta wani kalle shi ta ce"ina zan bita ni kums?"


ABDUL ya yi wani irin kwafa ya fice da sauri bai ce mata komai ba


Dorect bangeren Aminar ya karasa


Yana zuwa ya tambayi ko tana dakinta? Domin dawowar su Fido kennan , ita da Biyu sunna zaune


Yannayinsa ya shedawa firdausi ba lafiya ba, mikewa ta yi ta shige dakin Amina, sai dai ta tarar kayan aminar a watse a kasa, kamar wani abu ta dauka, ko wani ya daukar mata


Hankalinta ta ji yana neman tashi ta fito da sauri ta yi kicin,
Cenma bata sameta ba, ta dawo tana fada masa bata ganta ba, kuma ga yadda ta samu kayanta


A tsayen da yake sai da ya ji kamar za'a maka shi da kasa dan wani irin juuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu da ya ji kansa ya kwasa


Labulen dakin ya sake rikewa da dan karfi idannuwansa rintse har ya ji numfashinsa na dawowa a hankali sannan ya fita






Wasa wasa nan da nan aka tada hankalin du wani wanda ya kwana ya tashi a gidan nan ana neman UMAN biyu


Abinda ya fi komai dagawa wa'inda ke tsaron kofar gidan hankali shine, sun raja'a , a kallon ball din da ake ce ta chealsy da baban club din da suke support , ya zamto kowa hankalinsa ya dauku wajen ihun ball din da aka saka wace ta shiga a ba zata, babu wanda ya san idan ta fita ko tana cikin gidan......nan fa suka rarabu, suka haukace kowa ya kama hanyar da zai nemeta a cikin gidan, wanda ABDUL bai taba dana sannin yin ginni mai girma ba sai yau a rayuwa




Dare kara yi yake ama basu ganta ba


A hankali ya karasa wajen mota ya bude ya shiga yana danna kiran Muhammat


Muhammat ya karaso da sauri yana amsa shi


Ky din mota ya tambaya yana duban sitiyarin motar


Muhammat ya ce" Sir koma gefen cen na tuka ka"


A hankali ya girgiza kansa yana kallonsa ya ce" Ka bani ky plz"


Miko masa ky din ya yi sabban ya je da sauri ya shiga wata motar ya tayar ya dakata yana kallonsa har ya tada ya fita a gidan


Biye yake da shi a hankali har suka karaso kan kwanar da zata idasa shi gidan Baba mai shanu, yana ta dube duben hanya domin ya tabata idan ta fito daga gida ba zata tarbi kowa da bacin ranta ba sai wanda zai saurareta


Ido Muhammat ya zarro lokaci daya yana taka wani wawan birki sakamakon wani mai baban babur da ya shawo kwana a guje ya maku jikin barin da ABDUL din ke tuki, watau bangaren da yake zaune yana tuki




A haukace ya bale motar ya fito ya nufi wajen da tuni aka fara tsayawa ana son fara yiwa wajen taro


Mutanen dake wajen kofar ya kautar ya kama ya bude kofar hankalinsa tashe


Da sauri ya dago Abdul dake kwonce jikin sitiyarin motar kansa saman sitiyarin a haukace ya ce" ABDUL?"


Ido ABDUL ya rintse dan ihun ya ratsa masa kunne sosai yana bude jajayen idannuwansa ya kalli Muhammat


Muryarsa cen ciki ya ce" Ta yiwu ta shige cikin gidan Baba ko?"


Masu gadi da suka zaburo jin an ce an yi hatsari du suka nemi rudewa gannin wanda ya yi hatsarin, sai dai yadda ya ki a talabeshi ya fi komai damunsu


Cike da damuwa Muhammat ya ce" Sir buguwa ka yi fa ka tsaya mana a rikeka mu karasa gidan"


ABDUL ya juyo yana nuna masa marfin motar ya ce" Ka manta wace irin mota ce?, Muhammat nakuda take yi, ban san inda ta shiga ba"


Muhammad ya bi bayansa yana bashi baki dan motar tuni mutanen gidan Baba sun shiga kulawa da wanda ya bugun mata da motar kanta, duda shine bashida gaskiya kuma shima bai wani ji ciwo ba, babur din dai ne ya dan tatabu








A hankali ya karasa wajen da Baba ke tsaye yana jira a dawo a sanar masa Allah ya sa ba'a ji ciwo ba, an fada masa an yi accident a kan kwanar gidansa shi yasa ya fitoya tsaya kamar wani mai anguwa yana jiran dawowarsu, ai ga motar gidan ABDUL RA'UF ta shigo


Hankalinsa a kan ABDUL RA'UF din har suka zauna yana jin gabansa na faduwa, yana duban Muhammat ya ce" Muhamadu, lafiya? Me yake faruwa ne?"


Muhammat ya cire takalman ABDUL ya nufi waje yana fadin" Ina zuwa baba bara na janyo motar cen , walahi kar aje su raunatata "


Baba ya kalli ABDUL yana jin kamar ba zai iya tambayarsa ba, dan yana tsoron amsar da zai bashi


Da kyar ya daure ya ce" abdulahi me yake faruwa ne? Lafiya?"


ABDUL ya jinginar da bayansa a jikin kujera yana fitar da zazafan nishi , da kyar ya ce" Baba, ban san inda ta nufa ba, kuma dai inda ta tashi na ga har kamar ta fara zubar da ruwa, nakuda take yi"


Baba ya fuskanceshi da kyau ya ce" Kana bani magana a dunkule, ina Uman biyu? Dan na san itace da ciki a tare da kai"




ABDUL ya furzar da iskar dake bakinsa da daci ya ce"






Nld 52








Abdul ya furzar da iskar dake bakinsa da dacin harshe ya ce" Ta shigo ne, sai irin ta tarar da Risala......to yau din ba lokacin Risalar bane, sai dai abin ya bata mata rai, ta yi fushinta sosai harma irin dai ta ce sai na saketan nan, Baba damuwata ban ganta ba, bata dakinta, bata bayi, bata ko'ina "


Baba ya dafe gaban goshinsa, a sanyaye ya ce" sai da na fada maka, horon nan da kake yi mata ya isa hakanan, sai da na sanar maka ya dace ka dubeta, ka yi mata uzuri, abinda nake son fahimta a kanta na fahimta, Abdul matarka na sonka , ba bata sonka ba, ama ka ki ka bude idannuwanka ka yi hakuri ka bta kulawar da ta dace da ita, ko dan abinda ke tare da ita......, Shin idan ba'a hakuri da mata za'a zauna da su ne? Kuma ita ai na ga da saukima ko?, To yanzu da ka fito ina kake tunanin ta tafi ne?"


Abdul ya dafe goshinsa shima , jikinsa du ya dauki ja abinka da farin mutun, ya ce" Nima ban sani ba, na yi tunanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login