Showing 126001 words to 129000 words out of 145392 words
Chapter 43 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ko wajenka zata zo?"
Hajia ta idasa saukowa har tana hade kafafuwanta ta Karaso da sauri tana fadin" Macen da lokacin haihuwarta bai cika ba kace tana nakuda ABDUL hankali ka daga mata har ya kaita da fara nakuda ko menene haka?"
ABDUL ya lumshe idannuwansa ya rasa amsar da zai basu,da ace zasu iya gane hallin da yake ciki, da sun hanzarta sun gabatar masa da ita a gabansa
Hajia ta ringa kai kawo tana ji Alkali na maganar ko gidan Baba Lauratu ta nufa? Ko gidansu? Ina zata je da daren nan ga ciki ga bacin rai?
Hijabinta ta gyara a jikinta tana nufar kofa ta ce" Ba inda zata je, nakuda ai ba abin wasa bace, tana cikin gidanta"
Kusan a tare suka mike sunna mara mata baya, kowane da abinda ke bakinsa suka shige mota daya baki dayansu Muhammat ya ja su suka sake komawa gidan
Cirko cirko suka same su ana ta maganar babu wanda ya fita da waya tsakanin Muhammat din da Sir din bale a yi kiransu a fada masu an ganta
Ido Abdul ya lumshe yana jinginar da bayansa a jikin motar yana hangen kakaninsa da suka nufi dakinta kowane na saurin da Allah ya bashi ikon yi
Gaba dayansu a rikice suke a kusa da ita
A fitarsu har Fido ta yi kiran baba Lauratu dan ta ji ko gidanta ta tafi? Babar ta zo itama hankali tashe suka sake komawa dakinta a nan suka sameta a labe bayan sif jikinta na bari hankalinta du ba a jikinta ba, furucin bakinta shine ya sawake mata, ba zata iya ba, kasheta yake so ya yi ne? Ta gaji da wulakancinsa, ta gaji da komai da yake mata na wulakanci a rayuwa, ya barta ta tafi inda za'a san darajarta, tunda ba sonta yake yi ba, yana kiranta da AUnty!
Hankali tashe Hajia ta karasa tana duban Baba dake gurfane tana sake dafata ta ce" Wai a kan gwuiwa take ne?"
Baba ta gyada kai tana fadin" Haka muka sameta a kan gwuiwa take, inaga an sanar mata cewa an kashe yar gidan babansu ne a dakin saurayinta, kuma gongonsu da ta ga gawar itama ta rasu, shine kuma ya hadu da wani rikicin na Uman mallan"
Baba ya ringa kama sunnan Allah yana salatin Annabi Muhammadu Rasulullah salalahu alaihi wa salam yana gannin abin ya lafa mata tana sauke numfashi ya ce" Ni kam abin nan ya fara damuna, Uman biyu sannu kin ji? Allah ya raba lafiya, an zarce wata takwas abu ya isa haihuwa kam bale haihuwar fari, kin ga mijin fa da ya rikice har hatsari ya samu "
A gigice ta dago fuskarta jin abinda Baba ya ce
Hajia kuwa ta kalli Baba bayan ta cire hijabinta tana kiran docter ta ce" Haba alkali ya yaka kuma?"
Amina kuwa daga zaunen sai gata ta ciciba ta mike tsaye , Fido da baba na tareta ama faman sumewa take yi
Tana kallon Firdausi muryarta na rawa, daidai Abdul ya shigo a hankali dan kar ya yi hayaniya aje bata son ganninsa ya karra rikitata ta ce" Firdausi, Ab Ab Aban biyu ne ya yi hatsarin? Fido yana ina? Innalilahi wa inna ilaihi rajune..........."
Ta idasa fadi tana daf da idasa zubewa dan gaba daya kafarta ta nemi gaza daukanta
Da fido da Baba sun saka iya karfinsu dan talabeta, Haka hajia dake amsa kiran Docter tana fada mata sosai abin ya matso itama ta karaso ta talaba....uwa uba mai gaya mai tafiar shi ya fi kowa talabota a jikinsa a hankali ya zauna da ita a jikinsa yana ci gaba da shafa bayanta a hankali yana kallon yadda du ta rikice ya kama hijabinta ya ja ya cire mata shi domin du ya jika da zufa haka kuma ya janye ribom din dake kanta ya kasance gashin kanta ya saku ko zata ji saukin zafin nan, ya kai dubansa kan Fido da suka sakjar masa kuma suka kawar da dubansu yana fadin" Karra mana ACn cen Fido, kuma ki bude min dakin cen na ga idan zata iya zaman mota mu wuce asibiti ,......Hajia kirayi numbar Mansur plz ki sanar masa" ya idasa yana kallon Hajiar dake ta kai kawo kamar wace ke shirrin kwasawa da gudu, du ta rikice abinta kamar itace mai nakudar
Da sauri ta shiga lalubar number Mansur din tana buga masa kira
Baba kuwa kofi ya zuba ruwa masu dan dumi kadan ya zauna yana tofa Adu'a
A hankali ta kwontar da kanta saman kirjinsa dan hakan shine baban abinda ta ji tana bukata a zuciyarta
A hankali ya ci gaba fa shafa bayanta yana shafawa a hankali ya ce" Amina? Zaki taimaka min mu shiga cikin dakin cen na duba ki? Plz zaki iya?"
Amina dake galabaice tana sauke ajiyar zuciya a hankali ta dago idannuwanta tana kallon fuskarsa
Muryarta a raunane ta ce" ABDUL, wai nice auntyn ko?"
ABDUL ya zunawa fuskarta ido, shi kam idan za'a nada sarakan rikici na duniya zai fara bada sunnan Mina, bashida tantama ita zata ci walahi
A hankali ya girgiza kansa, dan bai san eh ko aa zai ce ba, hasalima bai san fadin sunnan take so ko kar a fadi ba
Numfashi ta ja tana sake maida kanta saman kirjinsa a sanyaye ta ce" Haka kake ce min aunty mana, kai ga mai yar yarinya mana, Abdul baba yace ka yi hatsari? Ka ji ciwo ne?"
Wata irin bugwa da zuciyarsa ke yi, da Amina ta sani, da ta bi shi a hankali kar ta halaka shi
A hankali ya mike ya samu ya dagota da taimakon Hajia sannan suka kaita dakin
Daga kofa hajia ta koma ta tsaya tana ta zufa, ita kam ta fi kowa rikicewa, kuma a yanzu kam haushin Honorable take ji, me yasa shi ba zai yi hakuri ba ko me ta masa ne sai ya ringa nemanta da rigima ne? Haba dan Allah
Da kyar ya lalabata ta yarda ya dubata,
Ai kam nakuda take yi sosai da sosai, ama idan suka maida hankali zata haihu a asibiti
Cikin gagawa yake bada umarnin maza a hada kayan haihuwa, maza a yi kaza a yi kaza, sannan suka kamata suka sakata a mota Muhammat ya ja suka nufi asibiti a lokacin dare ya tsala sosai aka bar Bab lauratu da tsaron Biyu, domin Fido kasa zama ta yi ta shige motar su Baba mai Shanu
A asibitinma gwagwarmayar ake sha, fama take baiwar Allah, nakuda sai sake nuna take ga likitoci a zagaye da ita
A hankali bakin rikicin da mita ya mutu , ta dawo sai ido sai adu'ar da take yi a cikin zuciyarta
Bata taba gannin namiji a hausa, a dakin haihuwar mace ba sai a kanta,
Mijinta na zaune rike da hannunta a lokacin da ta zo kan gaba haihuwarta ta salamo gabanin asubahi, domin haihuwar sai da asubahi ta sanyi kai sannan ta samu ta sulube ƴaƴanta kwaya biyu, mace da namiji
Yayan ake gogewa dan dora mata su a saman cikinta kamar yadda aka saba, ita kuma tana sake rintse ido da maida numfashin jin kamar an cire mata kaya zafin radafin na tafia yana barinta
Jikin ABDUL gaba daya rawa yake, ya rasa yayan zai kalla, ko ita dake damke da hannunsa bata saki ba?
A hankali ya rankwafo saman kanta yana shinshinar dukkan inda hancinsa ya kai, bama kamar wajen idannuwanta, da su hancinta, da sauransu, sai sinsina yake hannayenta cikin nasa a hankali yana kama sunnanta har ta bude idannuwanta tana kallonsa , shima yana kallonta
A hankali ya sauke numfashi mai sanyi a saman fuskarta yana kallonta, muryarsa a bayane ya furta" I love you, I love u so much Minah, i love u, i love u meenah"
Idannuwanta ta lumshe kirjinta na dokawa a hankali tana sauraron yadda yake lashe lebunnanta da suka bushe mata kayau kafin ya kame harshenta a hankali ya ringa tsotsa a yadda yake a rankwafen nan ta saman gadon tamkar zai cinyeta danya
...........
Ido Docter ta zarro tana juyawa daria na kubce mata ta ce" Docter ka bari ta sauka daga saman gadon mana mu kimtsata ka ga mun mika yaren , Hajia kuma so take ta shigo ta ga yannayin jikinta"
Da kyar ya iya barinta yana son jin amsa daga gareta, fuskarta yake kallo yadda idannuwanta ke lumshe
A hankali ya ce" Ba zaki ce min kema kina so na ba?"
Amina ta sake lumshe idannuwanta wani irin abu na ratsa ilahirin jikinta
"Kai yau na ga abu, ABDUL me kake yi haka ne wai? Ka matsa a idasa fitar mata da gudan jinni mana a gani idan da dinki a yi a kimtsata jama'a, wannan haihuwa mai wahala ka tare mata numfashi idan ta summa fa?" Hajia ta fada tana karasowa , a yau harta da rawar nan ta tsofafin da ake janyowaa kiiiii sai da ta yi, kuka kuwa risris ta rusa shi ana bata hakuri, ƴaƴan nan da kyar ta ba alkali da Firdausi, ta rasa ina zata tsoma kanta dan farin ciki, ta rasa me zata ce me zata yi? Ashe Amina itace uwar ƴaƴan jikanta? Biyu? Namiji da mace? Haihuwa da ta masu karanci a familly dinsu? Ai su lamari yana da zafin gaske a zuciyarsu, a yanzu bata san me zata yi na nuna farin cikinta ga yarinyar nan ba, to ita arzikin ya'yan nan ai ya ninka maganar hawa kujerar gwamnati sau million a wajenta
Haka ya saki hannunta ba dan ya so ba ya mike da kyar, domin a rankwafen nan a kadan ya dauki awa biyu, ita na nakuda ne shi yana nishi, kuma sai a yanzu ya ji kamar idan an jima jikinsa tsami zai yi har ya fadawa yan garinsu
Murmushi ya yi bayan ya sake juyowa ya ga yadda Hajia tta shiga taimakawa Docter da nurse din dake kan Amina dan gyarata
Hannunsa ya kai daidai zuciyarsa a hankali ya furta" Allah ka bani ikon haukatata a so na, domin idan abin ya kasance na zuciya daya ne tak, dayar bata ra'ayi, kwarai zan cutu"
Yana fitowa ya ga wani shagalin, Fido na rike da Yar, Maansur na rike da yaron, Ita fido yar take ta karra budewa cikin lulubinta hakoranta a waje tamkar gonar auduga
Shi kuwa yana rungume da ɗan a kirjinsa yana binta du inda ta yi, kuma yana kallonta kamar zai dauke idannuwansa ya lika mata
Baba kuwa ya tafi masalaci domin hawaye ya ringa yi kamar ba baba ba, ya tafi yace ya tafi ya hantse a masalaci ya godewa wanda ya basu,
Tsayawa ya yi yana kure Mansur da kallo, irin kallon nan na kankance idannuwa da dage gira guda ya ce" Kai ya haka?"
Sai da Mansur ya zabura, dan bai san ana kallonsa ba, ya juyo yana rike dan da kyau ya ce" Man ka fito?"
ABDUL ya karra kankamce ido ya karaso yana fadin" Ka ga bani na ga magajin ya ganni, kuma ka dan dawo daga nan bana so ana matsewa y'ayana waje haka, yaya yarinya na kwana kana binta?"
Ido da baki Mansur ya saki yana kallonsa, irin yadda ya sha murr kuwa kai kace baban na Fido ne sak
Fido ta karaso ta kawo masa macenma ya hade yana kallonsu
Murmushi ya dago yana yi zai yi magana ya sake gannin Mansur Fido yake kallo,
Fuska ya sha ya ce" Kai ba nace ka daina kallon yar ba?"
Mansur ya dube shi yana fadin" Dan Allah wai meye haka? Ba za'a yita ta kare ba?"
Firdausi ta yi gaba da dan sauri, dan bata kaunar abinda ke fitowa daga bakin Docter mai kirki
Sam bata so, bata tunanin idan har tana ra'ayin haka a kurkusan nan
Mansur yaa kai zaune yana fadin" Me ka yi kennan? Haba Man, yaya ba zaka kama min ba bayan ina so?"
ABDUL ya tabe baki ya ce" Yaren nan ka tabata basa bukatar kwalba?"
Da haushi haushi Mansur ya ce" Kai dan Allah ka rufa min asiri, kwalbar me yayan masha Allah babu na kasa da kilo 3?, Ina maka magana ta a bani na raya sunna kana kawar min da zancen?"
ABDUL ya yi murmushi ya ce" Man, sai ka bita a hankali.....idan kace zaka takura ba zaka samu abinda kake so ba.....ka ga tanada tabo na maza a rayuwarta, sai ta gamsu da kai a aikace ba a furucin bakinka ba........so kawai ka yi ta kanka, domin nima ta kaina zan yi da rigimamiyata"
Mansur ya yi murmushi yan saka yaran a irin gadon nan na turawa ya lulube su ya mika masa hannu yana yi masa congratulations
A nan dai suka hantse aka kimtsa Amina sosai aka kaita dakin hutu bayan ta sha dinki aka barta tana hutawa, domin awa shida zata yi a saketa, ta haihu lafiya bata samu matsalolin haihuwa ba sai na kari kadai
Ana dawowa daga masalaci aka mayar da baba gida, ama HAJIA tace aa sai sun je ta daidaita masu harkar Ac da sauransu dan kar a yi wasa a kama masu mura, yaran ta masu hoto fiye da a irga, hawaye kuwa daukewa take yi tana karrawa
ABDUL ya nemi waje zai zauna da jalabiyar nan da suka sha kokowa da komai da ita, HAJIA ta nuna Aa, kawai ya wuce gida gasunnan, ai zuwa karfe goma za'a salameta a fara shirya zuwansu gida
Har ya yi gaba ta sake kiransa ya dawo ya dan zauna yana kallonta
Fuskarta a hade ta ce" ABDUL, matarka bata san y'ar uwarta na asibiti bane?"
ABDUL ya yi dan tsai, sai kuma ya gane inda ta nufa, a nutse ya dan yi yannayi na bai sani ba
Hajia ta tabe baki tana gyada kanta ta ce"
Nzl. 53
*KU JI?, KUNNA JI? KU JI......KUNNA JI? KU GARZAYO DAN SAMUN NAKU, ZAKU SAME SHI NE DA FARIN CIKI, ANNASHUWA MUTANENMU, KWATENA CE, ALKALAMINTA NE, AKOY ZAKI, GA FARASHI MAI SAUKI 300 KADAI, TAKENSA TASBIWUL DABE, WATAU CARBIN KWAI...... SAI KUN ZO*
Hajia ta tabe baki tana gyada kanta ta ce" Ok, idan ka koma ka sanar mata, idanma wani abu ke bin bayan kanta ta warwareshi, dan bana son iskanci?"
Da dan mamaki ya kalleta, sai kuma ya yi murmushi ya mike ya fice
Ko a cikin mota sau uku Muhammat na masa magana irin ta yanna taya shi murna, ama baya jinsa sai da suka tsaya bakin danja Muhammat ya yi murmushi ya ce" Su oga soyaya ta yi raf da su"
A hankali ya dawo da dubansa wajen Muhammat, wanda sai da ya zabura, dan bai san zai ji shi
Suka yi ido hudu, ya janye dubansa da sauri, shi kuma yana dan kallonsa, sai kuma ya yi murmushi kasa kasa yana dauke dubansa ya sake komawa cikin kujerar ya zauna yana tunanin yaya zai yi da tafiyarsa? Gaskiya ba zai je ba, ba zai iya zuwa ba, idan ya tafi yaya zai yi da tunaninsu? Ya tafi ya barsu su kadai? Aa zai ba kowa hakuri taron da zasu yi a China na wani aikinsu kan harkar kasuwanci da kofar shigo da kayan order wanda zai daukar masu sati guda ba zai halarta ba, dama ya zata zata karra wata guda da sati biyu kafin ta haihu da sai ya je ya dawo, tunda ta haihu yanzu shikenan ba zai je ba
A haka suka karaso gida, suka tarar da gidan sai murna ake, babu mai ba dan uwansa hakuri kowa murna yake, bama kamar ma'aikatan su mata, mutanen sunna matukar jin dadin zama da ita, ba ruwanta, bata takuraka, bata wulakantaka, bata cin zalinka, idan kuma ta yi wainarta du mai rabo sai ya more, ya zamana har jiran juma'a suke ta zagayo a yi waina, domin yanzu yan tuya wainar sunna da yawa da ake taimaka mata, ga tsufa na ciki ga kuma yawan da aka karrawa wainar dan yan amsar sadaka, su kam uwar gidansu sunna alfahari da ita fiye da tunanin mai karatu
Murmushi kawai yake yi na yadda ake masa barka, sannan ya shige bangarensa ya haura sama dan yin wanka , ko su Baba bai leka ba dan harda jini jini a kasan rigarsa, ko sallah bai yi ba saboda babu abin sakawa sai yanzu zai gabatar da ita a nutse
A cikin bangaren Amina kuwa gyare gyare ne aka tada ba ji ba gani, sababin labulaye aka fitar aka kafa , harta da cafet sabo sai da aka saka, bangaren ya dauki kanshin turaran wuta komai sai haskawa yake yi,
Biyu sun kasa sun tsare sai tambaya suke bin Baba da ita kan wai mamansu ce zata zo da baby biyu? Gaba daya murna da farin ciki ke tare da su sun kasa koda cin abinci har karfe goma sha daya ta gota sannan bakin asibiti suka dawo
A hankali Hajia ke rike da ita dan taimaka mata, haihuwar ya'ya biyu ba wasa bane, sai a hankali karfi zai shigeka, shi yasa aka talafeta har aka dorata saman katifa madaidaiciyar da aka shinfida mata a falo dan ba zai yiwu a wuce ciki da ita ba ko dan baki, idan hutu take so ba zata rasa ba za'a fita da kowa ta huta
Hajia ta dubi Baba ta ce" Laure, a dora ruwa dan a mata wanka sannan ta koma barcin"
Baba ta dan risina ta ce" Hajia ai ruwan nan ya jima yana tafasa"
Hajia ta ce" Masha Allah, maza a juye, ke Hindatu ke kuwa a juyo zabin da nace a dafa mata da ruwa ruwa ina fata baku zuba magi ba?"
Hindatu ta amsa HAJIA itama ta tafi dak zubowar
Hajia ta sake cire hijabinta ta zauna tana dauko macen dake tsala kuka har lebenta na kasa rawa yake yi karkarkarkarkar irin alamun zata yi kukan nan
Ruwan zamzam ta dauko ta ringa diga mata tana murmushi ta ce" Firdausi wannan baki na yarki anya ba gidan rigima ba kennan?"
Fido ta yi yar daria tana ajiye bokicin kunnun kanwa da Baba ta bata ta kawo ta ce" Hajia ai fa wannan baki na prncsss nima ina kallonsa da idannun basira, yana bani tsoro"
Hajia ta ce" Nono take so, sai mamanki ta fito daga wanka zata shayar da ke kin ji amnana?"
Fido ta yi murmushi tana talaba Amina suka nufi dakinta da aka kai ruwan wankan zuciyarta fesss da tarin farin ciki
Sunna shiga ta taimaka mata ta cire hijabin da aka luluba mata sannan suka karasa wajen bayin
Amina da muryar wadda ya sha wahalar nakuda ta ce" Fido, hala yi mini wankan za'a yi?"
Baba dake