Showing 12001 words to 15000 words out of 145392 words
Chapter 5 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
*Burinta!*
Sai da ya taune ya hadiye ya yi dan murmushi yana fadin" Watau yarinyar nan Allah ya kara mata lafiya, a kulun abinda ke bani mamaki da wainarta bata konewa, bata yin yami, bata cika siga, idan kuwa ta rangada mata miyar taushe sai na ji du duniya babu miyar da ta kaita dadi, mahaifiyarta ta mata horon arziki, ita kam ta huta idan ta yi aure ba zasu samu matsala da miji ba wajen girki, mu kuma maza dama a kware wajen girkin kadaima ya wadatar"
Wani irin tukuki ke turnikar zuciyarta tana kallonsa, lalle ta yarda bashi da kiyar kama mata a kan maganar nan, bayan ta san yaron na girmama maganarsa koda da salon wasa ya yita?
Mikewa ta yi ta dauki jaridarya da gilas dinta ta maida a idannuwanta ta juya ta nufi ciki cikin takun nutsuwarta ba da fuuuuuu ba dan ranta ya baci, no, da salo irin na wayayiyar macen da ta gane idan ranta ya bace gwara ta yi shiru da ta daga muryarta ya zamto an samu mumunan furuci daga tsadafen bakinta ba!
Da ido du suka rakata, sai kuma suka yi ido hudu shi da kakansa
Goshinsa ya tatare sosai yana kallon kakan nasa
, Dubansa ya maida wajen agogon dake bango ya duba ya sake juyowa wajen da yake ya ce" Sai yanzu kake karyawa bayan kana fama da ulcer?"
Fuskarsa ya yatsina ya ce" Ka san kuwa tunda safe nake jin yinwar, har mafarkin wainar nan na yi, yau maman biyu ta yi rana shi yasa"
Takardar ya mayar gefe gaba daya yana fuskantarsa , sai da ya gama ayana abinda zai fada masa a zuciyarsa sannan ya ce" Bana so,......"
Ya yi shiru jin saukowa daga sama ya maida dubansa yana kallo, kakarsa ce ta fito cikin tsadaden shiri da abayarta mai walwali ga kanshinta dake sanar da zuwanta tun kafin ta iso
Karasa saukowa ta yi daya daga cikin yan aikinta na biye da ita rike da jakarta ta tsaya tana kallon table din ta ce" Ki tatare breakfast din cen, a yi masa na rana, kar a cika mai sannan kar a saka masa magi da yaji a ciki, a dafa masa cuscus da miyar lambu......nd a tabatar an saka turaren wuta a ko'ina idan ya gama cin abincin"
Cike da ladabi take amsata , sai da ta tabatar da cewa ta gane komai sannan ta sake juyowa barin da suke zaune
Idannuwanta suka sarke da na jikanta, tarin damuwar dake tatare da ita ya fara karanta, sai kuma juyawar da ta yi ta wuce ba tare da ta ce da su komai na, uwa uba ko tambayar izinin fita bata yi ba a wajen mijinta ta kada ta yi tafiyarta ya saka shi rakata da kallo, sai kuma ya dawo da maganar da ya fara ya ce" Bana son kana zama har wannan lokacin baka karya ba, Waina, waina waina, na yi na yi na kawo ma'aikatan da suka kware wajen sarrafa waina su ringa sarafa maka ka kiya"
Sosai jikan nasa ke saka shi a hali na kwonciyar hankali da farin ciki, uwa uba idan ya ga yana magana a kan abinda ya shafi lafiyarsa ko kwonciyar hankalinsa, tamkar wanda ya take shekara hamsin a duniya, rashin hayaniyarsa da tauna hharshensa wajen magana da matukar son girmansa na sakashi manta shekarunsa a duniya
Murmushi ya yi masa ya ce" Babu mai wainar da zata fi Maman biyu iyawa a duniya, bayan wannan na yarda da tsaftarta ne ai"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ja bakinsa ya yi shiru yana kallon abincin da kuma irin cin fa kakansa ke yi
Mai Shanu ya ce" A zuba maka ne?"
A hankali ya girgiza kansa harda yatsina fuska, kwarai shi din mai matukar son abincin gargajiya ne, ama ba zai taba iya cin wanda bai yarda da shi ba!
" Me yasa ba zaka yi mata biyaya ba ka shiga farfagandin da take da bukata?" Mai Shanu ya fada a tausashe bayan ya wanke hannunsa , ama bai sha ruwa ba , domin idan ya ci abinci baya shan ruwa a lokacin sanadiyar ulcer dinsa
Yatsarsa ta tsakiya yake dannawa a hankali har sai da ta bada kara sau biyu sannan ya juyo gefensa a hankali ya ce" Saboda da na rintse ido ban ji ba dadin makanta"
Mai Shanu ya girgiza kansa yana fadin" Ka bani a bude yadda zan fahimta"
A tausashe, ba da yannayi na raini ba, ko isa, ko haikewa a kan maganar kakan nasa ya ce" Ita din misali ce a kan kalar rayuwar da ba zan so ta gabata a kaina da iyalina ba, ita din aya ce mai karfi da nake kokowa da ita dan burina ta farga ta zubar da dabi'un da ba adininta ba!"
Mai shanu ya sake fuskantarsa ya ce" Wadine daga cikin dabi'un tawa matar ne baka so su zamto abin koyi a wajen naka iyalin?"
Dan murmushi ya yi, domin ya fuskanci kakan nasa na son jan maganar ne kawai, ya gane komai ama sai takewa yake yi, yau hira yake ji sosai shine yake so ya yi ta jansa a kasa dan fin karfi, sai dai shi din kansa yana so yau Mai Shanu ya fahimci siyasa ba ra'ayinsa bace, ya yiwa matarsa magana ta barshi haka, idan maganar kudin ce zai zuba mata ta je ta gwada sa'arta, ama zai yi ta adu'ar kar Allah ya dafa mata a burin zamowarta gwamnar garin nan!
A tausashe ya ce" Ni fa ba nufina matarka nada matsala ba Elhaji"
"Aboki, ka yi maganarka sak, idanma iyalin nawa kake nufi da wata sirfar sai na baka amsa daidai da bayaninka, ai ka san baka kam ba tsami " mai Shanu ya fada shima yana murmushi
Kafafuwansa ya tankwashe yana fuskantarsa ya ce" Bana tunanin zan iya jure wace Allah yace na kilace na bata kulawa fita yawon farfagandi dan ta tayani samun duniya koda babu izinina ba!, Zan so a wata ta yi fitar da bata fi uku ba dan sada zumunci da ta'aziya, bana tunanin zan iya fita na saurari maganar kowa da kuwar kowa dan na samo mana na gero , itama ta fita ta yi gogayar dan ta samo mana sunna ba! Na fi daukan haka a matsayin halaka da bacin sunna !, Damuwar ba zai yiwu na zama gwamna babu matar gwamna a gefena a jaridu da gidajen talabin ba, kowani kato zai kalleta kyauta harma ya aibatata, kowace katuwa zata nemi wulakantata dan kawai bata cikin tsarin wace ke birgeta! Matsalar kuwa itace ba'a gane shekaru na tafiya furfura na gama kai har sai ciwon ajali ya kama wanda ake tunanin stress ne kamar yadda aka saba jin dan damuwa na stress sai an tsinci kai a kabari!"
Shiru ya yi yana kallon yannayin kakansa da gaba daya yaa cenza, duda irin karfin halin da yake yi dan ya nuna yana cikin nutsuwarsa , ama kana kallonsa zaka gane ya afka a hali na tunani,
Kwarai ya so dakatawa haka, ko dan shima ya numfasa, sannan ya bar kakansa hakanan, sai dai bai dire abinda yake son sanarwar kakan nasa, ko yace tuntarwa, dan haka ya dora da fadin" Sai an tsinci ki a cikin kabari, daki matsatse mai duhu, wanda bin umarnin ubangiji ta hanyar bauta masa ne kadai zai sa ka samu wadatarsa da kuma haskensa, sai ka zo a panpanpan , watau biyu babu .....ukun lala, ba uwar ba ribar........me zai hanna k hadu da abokin *UKUBARKA* har a busa kaho ba?"
Sake duban idannuwansa Mai Shanu ya yi, gaba daya maganar ratsashi take yi tamkar wanda bai san hakan ba, tunatarwar nan cikin hikima ta saka shi a halin rudu da karyewar zuciya
A sanyaye ya ce" Tana sallah, tana azumi, na tabata ita din mai tsoron Allah ce, hali ne ya cenza a lokacin da ban yi aune ba, ni da kaina naa sake talafa mata dan samun farin cikinta da ci gabanta a rayuwa, arzikinta ya shiga, lokacinta ya shiga, lafiyarta ta shige, sosai an shiga fannin wasa da gobenta!, Kwarai ba haka ba nake hango tsufana, tsorona daya kar sai ta dawo wata rana ta tardo gawata bamu yi salama ba"...................
A hankali ya saka hannunsa cikin na kakansa yana dan murzawa a lokacin da kakan nasa ke fadin" itafa ba rashin damuwa da ni bane matsalarta, kuma idan yau na daure fuska tana min biyaya, shi yasa nake saka ran koda kwana daya ya rage min a duniya na ganta ta dawo matar dakana, ta zubar da mulkin nan! Domin dama ni ba ra'ayina bane"
Dan murmushi ya masa, bai amsa shi a kan wannan ba, har sai da ya kula ya saku da damuwar da ta shige shi farat daya sannan ya cika hannunsa ya sake komawa gefe ya dora da aikin da yake yi, wanda ya tanadeshi dama sai ya zo gaban Mai Shanu, domin ya fi shi sanni a wannan fannin sosai
A hankali suke zantawa kan albarkar kiwon da ake yi wanda ya zuba masu kula masu ilimin abin da kuma yan mun gada, sosai suke zantawa kan shannin dake kim amsar abincin birni idan an sayo su daga jeji, a nan ya nuna masa cewa sunna iya sakinsu a baban filin wajen kiwon, su nisanta su da babura da mota da kwaramniyar bayan magariba, su yi kokarin rage masu hasken zamani na fitilu da sauransu , su barsu da hasken wata da kyalekyalin taurari, ya zamto sunna ji a jikinsu kamar a wajen da aka haifesu ne suka tashi, a hankali a hankali ake koya masu bakin lamuran birni sai ka ga sun saba daa sababin abubuwan sunna cin abinci sosai kuma basa ramewa da firgicewa
Sosai sula zanta har sai da karfe goma sha dayan rana ta yi suka mike dan karra shiryawa su fita masalacin juma'a baba
A cikin mot su biyu ne a baya, yanzun babu mai yiwa dan uwansa magana kowane na hailala a cen kasan zuciyarsa
Sunna isawa suka tarar ana huduba dan haka suka ajiye carbi sunna sauraron hudubar har aka gama aka tayar da sallah suka yi suka gama
A wajen sadakar da ya saba ta du ranar juma'a ta goma goma sababi kal kal yara sun zagaye shi, shi kuwa sai fara'a yake sosai yana basu sadakar nan cike da farin ciki har ya gama suka kuma shiga motar suka nufi gidan gona
Sauka ya yi ya zagaya ya bude masa da kansa, ya kamo hannunsa ya fito da shi suka nufi wajen da suke hutawa da kuma hira da tsofafin dake zuwa su wuni tare
Bayan ya gama gabatar masa da komai kasa kasa sosai ya ce"
πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ
_*NI ZAN LADABI*_
πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ
*NA*
*SAJIDA NIGER*
Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida
Wannan Novel na kudi ne ba free bane
Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER
Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai
Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka
*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπ₯°π₯°π₯°*
*Page 0οΈβ£6οΈβ£*
Bayan ya gabtar masa da komai kasa kasa sosai ya ce " Ka hanneta yi min maganar siyasar nan, domin banna ra'ayi"
Da ido ya raka shi da kallo domin bai tsaya ya ji amsarsa ba ya wuce ya nufi cen bangaren da zabi da su kaji dai da sauransu ke nasu kiwon cike sunna ta ihu irin kukansu ya tsaya ya harde hannayensa yana kallon yadda ake dauke kwaya kwayansu da irin kulawar da suke samu
____________________________________
Tunda Amina ta shigo gidan kanwar tata dukkan kuzari da farin cikin da ta riko na Ζ΄aΖ΄anta suke neman barinta sakamakon irin halin da ta samu kanwar tata a ciki
Firdausi ta yi duhu sosai, ta rame, ga rashin fara'a dake damunta wace ta kasa boyewa du irin kokarin da take yi dan boyewar
Tunda ta shigo ruwa wannan na rijiya da Allah ya basu kyauta Firdausi ta gagara tashi ta debo mata ta sha, hasalima hankalin kanwar tata na yawan duban kofar shigowa gaba daya ta kasa samun nutsuwa, ga cikin wata bakwai da ya nuna kansa sosai ya yi tirtsitsi sai rinjayarta yake yi, gaba daya ba nutsuwa a tare d Firdausi, kamar ba fido dinta ba
Dan murmushin yake ta yi , ta ciro dubu biyun da ta kawo mata ta miko mata a sanyaye ta ce" Fido, dama jiya zuwa yau ne Allah ya kawo budi sosai, shine nace bara mu biyo mu kawo maki kya kara jarin kayan miyar da kike siyarwa a gida"
Firdausi ta yi shiru tana kallon kudin, a sanyaye ta ce" Aunty ni ban kai maku talafi ba sai naku zan amshe? Aa gaskiya aunty ba zan amsa ba, babu kowa a wuyana da nake ciyarwa, iya bakina ko yayane ba zan rasa na sakawa bakin salatina ba"
Amina ta girgiza kai tana fadin" Karbi mana, tunda kika ga na zo na kawo ai kin san muma mun samu ne, bale keda kike da wannan abu a gabanki ai sai da tanadi komai kankantar abin batarwar"
Jiki a sanyaye Firdausi ta ce" Aunty yanzun bana siyar da kayan miyar fa, dama daidaiku ne ke zuwa siya irin wa'inda suka san halinsa suke da niyar talafa min, to gaba daya sai ya rikice mutun bai isa ya turo yaronsa amsar koda dadawa ne komai kankantar yaron , idan ya ci karro da dan mutane sai ya daka, nima na shiga uku kulun cikin fargaba da tashin hankali, kawai sai na daina siyarwar dan ba wani anfani"
Ido Amina ta tsura mata, zuciyarta cike da damuwar wannan lamari, yanzun kayan miyarma ya salwantar mata da siyarwa? Ashe dole ta lalace har haka, dama da yar sana'ar ake samu ana kaiwa mai dan dadi baka, ta rasa ta inda zata bullowa al'amarin kanwar tata, ta ce ta je ta yi dinki ta koyi sana'ar dogaro da kai ya kafa kai da kasa ya kiya, ta nuna mata ta gwada siyar da awara ya kiya, ta ringa sana'ar kitso da gyara jiki domin itama ta iya nanma ya kiya, komai bawan Allahn nan idan an kawo na karuwar Firdausin sai ya kiya....wai sai ace kishi ne ke damunsa, wannan wani irin kishi ne bakin kishi? Yanzun dai ba'a kai Ζ΄aΖ΄an cikinta da ta haifa ba, ya yi masu katangar karfe wai hasan da husaini shekara shida shida a duniya yace sun zama samari su daina shigo masa gida, yanzu haka wannan rashin nutsuwar ta tabata tsoro take yi kar ya dawo ya tarda su a soron gidan da ta dakatar da su cewa tana zuwa, yaran kansu a yanzu idan ba ita ta kawo masu maganar Firdausin ba sun daina yi mata maganarta, shin yaya zai yi da haki da girman soyaya irin ta uwa da Ζ΄aΖ΄anta? Sam basa shiri a duniya , zata iya shiga gidansa ta fita yana nan basu gaisa ba, domin har akoy ranar da ya zageta ido da ido yace tana yawon banza ta ki fitar da miji baya son mu'amalarsu da matarsa, ita kuma tace sai ya dauki wuka ya yanka hannun matar ya tsiyaye jinninta dake gudu a jikinta ya cenza da wani, a ranar har ashariya ta kusa yanka masa dan bacin rai sai da Firdausin ta yi ta kuka da bataa hakuri ta hakura ta yi tafiyarta
Amina ta sauke gauron numfashi ta ce"ki zauna waje daya mu yi magana, tsoro kike ji kar ya dawo ya tardo biyu a soro?"
Firdausi ta zauna din tana jan numfashi ta ce" Aunty ai idan ya tardo sun ban san yaya zamu kwashe bane, kin sanshi da kulafirci da daukaka gaba da rigima"
" Y'ayanki? Fido bakya missing dinsu? Bakya jin kamar zaki haukace dan rashinsu a gefenki? Bakya jin rashin dacewar hukuncinsa ? Ba zaki iya dakatar da shi ki nuna masa martabarsu da darajarsu ba? Shin bakya gudun shiga hakinsu?" Amina ta fada a sanyaye har idannuwanta na neman cika da kwala
A hankali Firdausi ta dora kanta a kafadar Aminar kuka na kwace mata
A kasa kasa sosai take kukan tana mai sake dora kanta a gefen kafadarta ta ce" Nakan wuni, na kwana da tunaninku, da matsananciyar kewarku baki daya, Aunty ina son su sosai fa, walahi ina son su, rikicin cenjin Rayuwar da na samu ne ke makani a kasa, Aunty bana iya tsalake maganarsa ko yi masa jayaya, ina ji ina gani ya haramtawa y'ayana shigowa gidansa bayan musulunci ya yi nuni ne idan D'a namiji ya balaga kana iya ware masa wajensa da sauran yayanka mata sannan ka saka ido sosai a kansu baki daya, shi din ko dan ba shi ya haifi nawa bane yake ki? Marayu ne.....yau da bani da ke yaya zan yi a rayuwa?"
Sosai fushin dake zuciyar Amina yake narkewa yana komawa tarin tausayi da jinkai na yar uwarta
A hankali ta ci gaba da dan bubuga bayanta a sanyaye ta ce" *KI YI MASA LADABI*, na tabata babu abinda yake dawamame a duniya dadi ko wahala, watarana zai cenza halayarsa ko Allah ya canza maki da wanda ya fi shi zama alkhairi"
A hankali take amsata, Amina ta saka mata dubu biyun a hannunta ta ce" Ki adana wannan, du ranar da baki samu abinci ba ki