Showing 60001 words to 63000 words out of 145392 words

Chapter 21 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8155

ta ga Baba ya nuna kayan da suka zuba da sunnan RISALA yace wai su ya zabarwa Amina!


Murmushi ta kakaro tana mikewa ta ce" Lah alkali, ka ga ai kowace da sunnanta a jikin nata, ka ga na uman biyun nan, wannan kuwa ai na Risalar ne ko? Duka kaf komai iri daya ne aka zuba ai"


Baba ya yi murmushi a ransa yana ayana' Na san a rina'


A fili kuwa ya ce" Kai masha Allah, ai kin ga nima kawai kalar ce wannan din ta fi birgeni, shi yasa na daukarwa uman biyun ita, ai tunda komai iri daya ne menene a ciki?, Kin ga Lauratu ga fa kayan uman biyu sun sauka ni kamar a saukar mata da ni mu sha kallo wannan kaya ai sai mu bude shago da su"


Baba Lauratu wani irin farin ciki ya sakata fashewa da kuka a lokacin da Hajia ta tabatar da gaske Alkali yake kayan da ta zabo classs, masu dan uban tsada da tsarin kalar na yan gayu ne ya daukarwa bagidajiyar yarinyar nan ta juya da sauri domin ko gabanta bata ganni da kyau ta shiga sauka tana hade matatakalar da bibiyu tana rike kukan dake ciyota ta saka hannunta ta murda kofar amina ta bude da karfi ta shiga ranta bace, hankalinta tashe ta kai dubanta kan Amina ta ce"


























Rikicin cikin gida.....da mai rai ake yi 😍😍😍😍😍😍


Cmmnt dinku ya saka ni sakowa da sasafe jama'ata 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍








*NZL PAGE2️⃣3️⃣*








Kalaman da ta fara jifan aminar ta su ya saka Hasan dake samn gado yana daga kafafuwansa tashi zaune ya zuba mata ido


Rai bace ta nunawa Amina hannu ta ce" Abinda nake so da ke shine, idan ya kawo kayan nan kar ki saki ki bude, ki bari idan aka kai wadincen din zan saka a kawo maki su ki bata nata, wa'inda yace a baki ba naki bane nata ne, kar ki saki ki kaini bango yarinyar nan!"


A sanyaye Amina ke kallonta tana son fahimfar inda kalamanta suka nufa, domin ita dai bata san da maganar wai za'a karra mata lefe ba, wadinnanma da ko anfani bata fara da su ba dan gani take yi sun fi karfinta bale wasu?


A hankali Hajia ta dafe gaban goshinta tana mai fashewa da kuka ta ce" Wannan wace irin masifa ce?, Da na san zan riski ranar nan da na shirya mata, ama ki me kike tunanin kin tanada ki zubar dan walahi na shirya maki tsaf zan yake ki da dukkan karfina!, Amina ki..........".........


Maganarta ce ta katse a lokacin da ta kai dubanta kan hannun da ya rike mata hannu


Fuskar yaron har wani huci take fitarwa ya rike hannunta taf ya zubawa fuskarya ido


Hannunta ta janye da sauri tana sake kallonsa


Hasan haka kirjinsa ke sama yana kasa,


Da sauri Amina da hawaye suka fara wanke idannuwanta ta karaso ta janyo shi jikinta ta rungume shi sosai tana kallon Hajiar itama haka kuma tana shafa bayansa


Muryarta na bari ta ce" Hajia , na yi wani laifin ne kuma?"


Hajia ta mata shiru itama tana jin zuciyarta na dokawa da daci da bacin rai


Amina ta lumshe idannuwanta hawayenta suka gangaro sosai a hankali ta ce" Hajia, walahi walahi baya gabana, Hajia kudinsa basa gabana, Hajia asiri kuka rufa mana da kuka ajiye mu a nan, tabas asiri kuka rufa mana kuma Allah ne zai saka maku da alkhairi.......ama dan Allah ki yi hakuri ki daina yi a gaban yaron nan, ki yi hakuri Hajia ......." Sai ta fashe da kuka ta sake rungume yaronta wanda shima ya shiga nasa kukan, wanda dama ba zaka ji yana kuka ba sai idan abin ya shafeta ne


Hajia ta rintse idannuwanta, fushinta bai sauka ba, haka kuma bata ji wani tausayinsu bama sai fitsararsu da ta gani ta juya ta fice a dakin ta bar gidan gaba daya, dan ta san da wahala a kai kayan nan a kuma dauko su


Kayan aka fara shigowa da su , Baba Lauratu da sauri ta karaso tana kama Amina da mikar da ita hadi da fadin" subahanalah ke meye haka? Lafiya? Tare muke da Mai SHANU fa, menene? Lafiya?"


Amina ta fashe da kuka ta fada jikin Baba tana kukan ta ce" Ki ce a sakeni mana, walahi na iya talaucina kuma na iya rike mutuncina, ki ce a sakeni nima fa ba sonsa nake yi ba, a kan me zan zama wulakantaciya har a gaban dana, a gaban Fadeel zata ringa wulakantani? Kin fi kowa sannin kowa zai hadiye banda Hasan ko?, Ki ce ta saka a bani takardata ni bana sin kayan nan, na je ina da su? Nace ni yar waye? Na saka na doshi ina wai? Haba haba wayo Allahna ni ba zan iya wannan rikicin ba walahi!"


A hankali Baba ke kiran sunnanta dan bata so Baba ya karasa saukowa ya tarda wannan lamari, bata san me zai faru ba


Amina ta ringa jan numfashi ta ce" Baba yaya ba zan yi kuka ba, kin ga fa hankalin Hasan take son daga min, abinda ba zan jura bafa, ni fa ban ce ina son yaron nan ba"


Baba ta ja numfashi ta ce" Ya isa haka, kin ga fa da Baban muka sauko yace so yake ya zo ya ga murmushin marainiya da kansa, kina so ya ganki a haka ne hankalinsa ya tashi? Kin sani sarai fa yadfa yake daukan lamarinki da mahimmanci, ya dace ki sasauta ki yi masa adalci shima kin ji? Dan uwan mijin kuwa ki barni da shi zan rarasheshi kin ji? Maza share hawayenki ma yi maganar daga baya maza share kin ji?"


Amina ta gyada kanta tana share hawayen ta dauko hijabinta ta zurma Baba ta juya dan gannin ko baban ya sauko?


A hankali Baba ya juyar da bayansa ya dan matsa dan baya so su fahimci ya san wani abin


Bismillah ta yi masa ya biyo bayanta yana murmushi


Tunda ya shigo bai zauna ba, haka kuma bai idasa shigowa gaba dayansa ba, ya ja dai daga baki baki ya tsaya hannayensa a Harde a bayansa ya dan saci kallon Hasan da aka kwontar aka mayar da gabansa wajen bango dan basa so Baban ya fahimci ya yi kuka


Murmushi ya yi yana fadin" Uman biyu, kin ga lefenki nan, zan je falo na dan jira dukan abinda yake na da naki ki tarkato ki hadawa Lauratu ta fito da su ta kai ta ba mabukata, ciki harda wannan hijabi naki da kuma takalmin dake kofar dakinki kin ji? Ni kam kayan nan kamar na tayaki dubawa kin gansu kuwa?"


Amina ta tsatsare Baba da ido, murmushin yake ta kakaro tana sada kanta muryarta a cen ciki ta ce" Allah ya karra budi Baba, ama baba a bari a hankali idan na cire na yi wanki da komai sai na bada ko?"


A dake, kansa tsaye , yana dan kama hanyar fita ya ce" Baki gane Ba Uman biyu, ina jiran hakan yanzu, ina nufin harda saitin akwatunnan cen gaskiya basu min ba, ai wanki ba damuwa bane idan ta kama nima sai na wanke fa, ke kuwa kina amarya kuma uwar gida ran gida ai ba'a isa a saka ki wanki yanzu ba"


Da ido suka raka shi su dukansu


Amina ta kai zaune muryarta a raunane ta ce" Baba ki bi shi dan Allah ki rarashe shi kar na taba kayan nan, kin ji abinda tace fa, bana son abinda zai taban mutuncina"


Baba ta yatsina bakinta ta ce" Ke ki je ku yi maganar mana Amina, mutunci kuma ai kece mutuncin jikan da take tinkahon da shi, a dai juri zuwa rafi, watarana tulun zai fashe, tashi ki ban na je na aiwatar da abinda aka sakani, ai daidai yake da ku indai mai SHANU ne, kaya kuwa ta je ta same shi yadda suka yi sai mu ji idan ya zo ya dauke dama shi ya bada damar a kawo"


Tana ji tana gani aka kwashe tsofafin kayanta Baba lauratu ta fita da su


Baba gaba daya kayan nan ya umarci Baba da ta ware wa'inda ba'a dinka ba kala uku uku ma kanta, sauran kuwa ta je ta kai gidan Firdausi ta yiwu ta samu na anfanarwa kanta a ciki


Sosai Baba ta fita da wannan farin cikin, da ta samu Firdausi har kamar nakuda zata taso mata ta farin ciki, kuka kuwa ta sha kamar zata hadiyi zuciya, daga baya tace Babar ta je da su gidanta dan idan ta bara mata a nan ba zata anfana da su ba zai kwashe, idan Allah ya sauketa lafia sai ta ringa dauka da kadan kadan tana anfanarwa kanta
________________________________
Hajia kam na fita gidan Uma ta je ta wuni a ranar, sun yi kiran wani gagarumin malamin adini ya zo da kansa Hajia ta gabatar masa da damuwarta, ta dora da fadin" Malan, wannan lamari idan ba aikin sihiri ba me zai haifar da shi? Mijina gaba daya ya birkice min ? Dan Allah a duba lamarin nan"


Sosai Ustaz Laminu ya nazarci maganarta
A tausashe ya ringa yi masu nasiha baki dayansu sannan ya dora da fadin" Da farko shi sihiri ba abu bane da ido bude ke ganninsa, haka kuma ba'a hawansa da hasashe ko zargi, kwarai zan baki adu'o'in da zaki dage da yi da fadawa Allah, idan har alkhairi ce yarinyar nan Allah ya kwontar maki da hankalinki a kanta, idan kuwa ba alkhairi bace Allah ya raba ba tare da hankalin kowa ya tashi ba, Shi Kuwa Alkali ki ci gaba da yi masa biyaya in sha Allah ko menene Allah zai warware mana baki daya"


Sosai Malan ya basu adu'o'in da suka dace na karya sihiri, ya hada masu da na kariya kala daban daban sannan ya masu salama


Umma ta ja numfashi ta ce" Kai kawata abin nan na damuna, wannan lamari sai hauhawa yake yi fisabililahi kuma ace ba sihiri bane? Kinsan fa shi malan Laminu dama haka yake, ko bincike fa baya yi kwata kwata, ko me ka kawo masa damuwarka a haka din nan ne zai durfafi abin, bi abinda yasa nake nace masa gaskiya abu da yawa da na saka a gabana na fada masa ala tayamu da Adu'a ina gannin hasken abin, ama yanzun kam na fi gane mu samu gagarumin malamin da zai buga mana kasa ya gano mana sirrin dake boye dan mu haye abin ta inda ya dace"


Hajia Hauwa ta sauke ajiyar zuciya ta kurbi jus kadan tana kallon kawarta ta ce" Hajia Uma, kin san fa ni gaskiya ban cika son irin abubuwan nan ba, na fi so ko menene din na bi ta hanyar da ta dace, ina dalili sallar mutun ta lwana arba'in ba'a karba, idan halin mutuwa ya riskeni a haka fa? Kai ina tsoron bin bokaye wai sai ace malamai, wani malami ne zai aikata irin haka?, Ni yanzun abinda ya fi damuna kalar akwatunnan ne da muka dauka damuwata, ai ba classs a cakuden da muka yi, dan kayan dake ciki bani da darr da su, kayan nan ko uwar ta samu ai ta haye bale yar, balema ABDUL din yace zai min transfer na masu ranar da za'a kai kayan dazu da na kire shi ina kukan wani wulakancin na Alkali, ABDUL fa yanada damar ya bijirewa abin nan aman ya kyale alkali yana ta zubar masa da mutunci da sunna a kan banzar yarinyar nan mai manyan idannu!"


Uma ta girgiza kanta tana tsaki ta ce" Ni kam abin nan na dauren kai, koda yake ai shima ba zata barshi banza ba, wainar da ake kawowa alkali ba kince wani sa'in tare suke ci ba? Ke dai dan kawia baki yarda da maganar boka bane da mun nemi mai kaifin wuka ya nuna mata ita karamar kwaro ce, ama walahi idan muka ga zata zame mana dan hakin da muka raina har ta kai ga tsole mana ido ko kw baki je ba ni zan je, domin ba zan yarda a wulakanta lamarin Gwamnana ba!"


Hajia aka wani cira kai da isa an kira dan albarka da gwamna


Uma ta ce" Kuma fa Hajia ke kika damu kanki da maganar kalolin akwatunnan nan, yanzun ba haka na ga ana yi ba sai ki ga an hada su red, su blue, su black, su fari du a tafia daya dan gadara ba, ba wani damuwa fa"


Hajia ta tabe baki tace" A kalolin wannan yelow din mai kama da zawon baby ne ke ci min tuwo a kwarya, ke kika ce mu daukar mata ita kalar kalarta ce"


Hajia Uma tace" Ni fa Allah itama bata da wata matsala, ke dai ba da kudi ba? Ki barsu ai sai mun nunawa maman Yarinyar nan mu ba sa'aninta bane, transfer din za'a yi mata ranar da mazan suka kai kayan a mata shiru, ta ga kudin ba bayani ta haukace, ita karamar yar bariki!"


Hajia ta yi murmushi tana hango wulakancin yadda zai bada kala




Shirye shirye ake yi ba kama hannun yaro


Tunda maganar nan ta zauna har aka je aka kai lefe Hajia ta yi gadarar nan yan siyasarsu suka dauka garima ya dauka, saitin akwatunnan kayan ke yawo ta ko'ina, da hoton screen shot na transfer millioyin kudaden da aka dora wai na dinkin Amarya, kudin da sai a bude shagon dinkin na kasa da kasa da shi




Daga kowani bangare fa aka mike kowane ya shiga shirye shirye


Bangaren amarya kaya ake shirin zuba mata na garari, mahaifinta da mahaifiyarta da dangi sun hadu taf sunna bada himma
Ta bangaren Hajia kuwa ta je da kanta gidan da za'a saka amaryar ta ga tsarin gidan , da kanta wannan karron ta ware bangaren da ya fi kyau din ma ABDUL din, ta gwamace hakan dan a yadda ta ga take taken mijinta idan har ta zabi nan ma Risala zata kwashi bakin ciki ne


A event din auren diner daya jal ce za'a yi ta amaryar da ango bayan daurin aure da wunin biki
Diner ce ta garari ta taron manya wace harda su davido mawakan yan gayu da manya manyan mawakan hausa aka gayata, tuni takardar gayar ta samu kowa harta da gagarumin Hl din da za'a gabatar da bikin Hajia ta tura kudinsa


Kan Madame fa ya dau caji, bata da lokacin kowa, jikanta dake spain kawai take tabowa a kai a kai dan yan cenji, shima a gobe take sa ran zuwansa kasar domin daurin auren bai fi da saura kwana hudu ba a yau
















Happy juma'at yan uwa


*NZL PAGE2️⃣4️⃣*














Bangaren Amina, a lamarin yau da gobe na rayuwarta ta mayar da komai a kan tsari
A cikin akwatunnanta tsararun hijabai irin na yadikan turkish kuka dinkin cen har kasa masu samfari kala daban daban da tsari na gayu take cakarewa da mora hankali kwonce
Bata taba dinkunnan atampopin da sauran manyan kayan masu shegen kudi ba, ama ta taba irin dogwayan rigunna masu laushi da tsararen kyau


A haka ta samu gyaran wata amarya wace take a tsohuwar anguwarsu, yarinyar a cen yar gayu ce kuma yar gata ce, ko a yanzu ta yarda Aminar ta gyarata ne dan ta ganewa idannuwanta idan har da gaske wai zaman da Amina ke yi a gidan nan a matsayin matar Hon ABDUL RA'UF ne? Domin maganar na zaga layi, yan mata kai ya dauki caji, kowace so take ta gazkata maganar nan dan ABDUL RA'UF din ba boyayen mutun bane, bale yawancin yan matan sunna jin maganar sunnansa ne a bakunnan samarinsu irin yadda suke koda shi da halayensa da kyautarsa da daukan wankansa da ajinsa tamkar wani saraki


A yau sansanyar safiyar Alhamis, ya rage saura kwana uku a daura auren mutumen dake amsa sunnan miji a gareta, hakan ya sa gidan ya dinke da jama'a dangi da yan uwan dangi, wa'inda aka gayata da kuma Mu (😌😌😌😌 ni da kwate ai mun kusa wata a gidan)


Bakin manyan mutanen sun rinjayi ya mu ya mu din , domin kuwa gidan kansa ya dauki motoci har ya zamto an cike wajen ajiyar motocin an fara ajiyewa a balbalin gidan
Dafe dafe ake yi ta ko'ina ana ci ana wanke kwanoni, wata tukunyar na sauka wata take hawa


Kayan aikinta ta kai cen baya wajen gardin din nan, hasalima itama tunda gidan ya fara daukan haramar mutane take guduwa domin har daki ake tardota ace an zo a gaisa ne a ringa kare mata kallo, ita kuwa hakan na damunta ainun, ga gyaran nata jikin da karara ta fadawa Baba Lauratu cewa ya isa haka in na so take yi fatarta ta cenza kala gaba daya ba, yanzu haka kunshin nan na gargajiya irin na gam din nan da aka yi mata ya hudo ya yi maroon sosai sai daukan ido yake yi a kan fatarta da ta dawo milk color tsabar gyara da anfani da su ruwan kwai da madarar ruwa, ita da kanta takan ji wani iri idan ta kalli fatarta , dan Husaini cewa yayi Mama ashe kema fara ce ba'a sanu ba?, Hasan kuwa sai ya kalleta ya yi murmushi irin ta birge shin nan


Murmushi ta yi lokacin da Suraya ta ce" Oh Aunty Amina baki ga yadda hutu ya kamaki ba, ni kam dan Allah ki min irin gyaran fatarki Aunty, subahanalah dubi da kika cire hijabi, wai aunty harda gyaran Mama kina yi ba?"


Kunya ce ta kama Amina, domin rigar dake jikinta ba wata mai dogon hannu bace, kuma ta cire hijabinta ne dan yanada haske domin kalar ash color ne mai haske idan har ruwan hadin gyaran nan ya taba shi zai lalace ne da kalar, gashi ko kanta babu wani abin kirki da ya rufe kan, batada kitso a kan dab kwalin wani mai sara sara ne ta dan yafa shi ta lauyo shi haka kadan a jikinta


Dan murmushi kawai ta yi ta kasa bata amsar gyaran mamar da ta tambayeta ta shiga fadin" Surayah, kin ga hadin nan da na maki na hada kurkum ne da man ja da lalle na gargajiya, ana kwaba su a waje daya ne a shafe jiki gaba daya da shi sai a hau kujerar nan ta tsuguno mai kofa a zuba garwashi isashe a rufa wannan abin rufaf mai nauyi a bar fuska a waje ya yi ta bugun jiki, a kadan zaki dauki minti talatin a sama, dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login