Showing 99001 words to 102000 words out of 145392 words

Chapter 34 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8175

bude lumsasun idannuwanta tana kallon fuskarsa muryarta cen ciki ta ce" Abdul, meye haka wai? Ni akoy zafi fa, kuma ka daina tabani ni, a nan a wajen nan, kuma a cikin mota baka gannin m......................"


Hadiye maganarta ta yi domin bakinsa ya kafa a kan maman nata a hankali ya ringa lasa
Da karfi ta ja numfashi tana rike fuskarsa ta dagota gaba daya tana kallonsa ta ce" Tana dakin tiyata fa, ka bari mana meye haka wai"


A hankali ya ce" to kin ki yin shiru bayan nace ki daina kukan sai yi kike yi fa, idan na bari zaki daina yin kukan?"


Kai Amina ke dagawa sai hadiyar yawun wuya take yi


Murmushi ya yi ya saketa ya daga yana kallonta ta mike da sauri ta gyara rigarta ta mayar da hijabinta sai sada kai take uwa tana gaban sarkin garinsu kunya cike da cikinta da mamakin yaron nan!


Sai da ya ga ta samu nutsuwa sosai sannan ya ce" Kin ji an ce abin cikin ba rai ko?"


Amina ta gyada kanta jikinta a sanyaye


Ya sake fadin" Hakan na nufin za'a cirosu ba rai, za'a bamu su ko?"


Amina ta sake gyada kanta tana kallonsa yana mata magana kamar ya samu mai shekara biyar


Abdul ya ce" Ba maganar kuka, kin ji? Haka Allah ya hukunta, idan an ciro za'a nuna mata abinda ta samu suka koma dan ta samu dangana sannan a kaiwa mahaifinsu su ya masu sutura domin shi yakeda ikon hakan kin ji?"


Amina ta kalleshi gabanta na faduwa, a hankali ta ce" ABDUL, kuma harda Fidon zaku mayar masa itama ya kashe min?"


A hankali ya girgiza kansa ya saka hannu ya bude kofar yana fadin" Ai ba aure tsakaninsu ya saketa "


Allah yana ganni wani farin ciki da sanyi ne suka ratsa zuciyarta, Astagfrulah, ance an yi saki maimakun hankali ya tashi? , Sai ta ji wata nutsuwa na shigarta, ko ba komai Allah ya raba kanwarta da wahalar mutumen nan, abinda ya fara dawo mata a rai shine to yanzu Fido ita daya zata je gidan nan da ake shigo mata ta zauna kafin su dawo ko me?????, Da wannan ta bi shi wajen zaman jiran har a fitar da su daga dakin tiyatar suka zauna su biyu kowane da abinda yake rayawa a ransa, bama ABDUL da ya tsareta da ido har ya zamto ta kasa samun nutsuwa tana ta gyara hijab da sauke ajiyar zuciya, Biyu kuwa sun bi direba Muhamat sun tafi kaiwa baba Wainarsa da kuma sanar masa halin da ake ciki.............




Docter Mansur ne ya fito , jikinsa a matukar sanyaye ya tunkaro inda suke zaune


A tare suka mike sunna kallon abinda yake rungume da shi, shi da docter Umi


A hankali ya saka hannunsa ya bude abinda ke rufen yana kallo, hakama Amina dake gefensa a hankali ta dora kanta a gefen kafadarsa tana kallon baby face din yarinyar da cikaken gashin dake kwonce a gaban goshinta, fari fat da ita domin ba rai a jikinta


Wani numfashi ta ja, gaba dayanta ta ja wani irin abu ta .........




40😍😍😍😍😍😍








Wani numfashi ta ja mai zafi, gaba dayanta ta sake lumshe idannuwanta a saman kafadarsa tana kallon fuskar jaririyar
Jikinta babu karfi ko kadan, muryarta cen ciki ta ce" Ka ga, mamaci sai fuskarsa ta yi fari fat haka, ko baki ne sai ka ga ya kara haske irin hasken rashin jinni"


A hankali ya kalleta, hakama doctors din


A sanyaye ya ce" Haka kamanin mamaci ke yi?"


Amina ta dago tana kallonsa, a sanninta shima ai nasa iyayen sun rasu ko?, Gaba dayansu


Idannuwansa ya lumshe yana sake duban fuskar namijin ya ce" Kin san ni ban samu gannin haka ba.....ban ga komai ba"


Sai da wani irin abu ya soki zuciyarta, a hankali ta kai dubanta kan fuskarsa tana janye hannunta daga jikin abin rufar yaran
A saman lebenta ta furta" Allah ya rahamcesu"


Shima a saman nasa leben ya amsa da "Amen summa amen "


Da kansa ya rakata dakin da aka kai Firdausi
Idannuwanta biyu, dama ba na dogon barci akai mata ba ta tsurawa waje daya ido tana kallo tamkar kurma , idannuwanta a soye tass babu hawaye, ciwon dake cikin zuciyarta da na jikinta ji take yi idan ta bude baki da nufin yin kuka tana iya yin aman jini......bata tunanin idan har zata iya yin kuka normal irin na mai fama da wani miki a zuciyarsa


Hannunta ya saki ya juya ba tare da ya cewa Firdausi komai ba ya tafi......itama a hankali ta karasa kusan Firdausin ta zauna tana kallonta


Sun dauki kusan minti biyar a haka , muryarta cen ciki ta iya budat bakinta ta ce " Aunty, gidansa zan koma ko?"


A hankali Amina ta girgiza kanta hawaye na zubo mata kamar ruwa , muryarta na rawa ta ce" Koda zan rasa raina a kan yaki da dukkanin ahalinsa, ba zan yarda a mayar da ke gidansa ba......kuma Abdulma ya ce ba zaki koma ba Fido"


Firdausi ta gyada kanta tana sake mayarwa ta dora a hankali saman matashin da aka saka mata mai laushi tana kallon sama, kennan yanzu mutun biyar ta birne a rayuwarta..............
A cen kasan zuciyarta ta ringa maimaita adu'ar da Amina ke karanta mata kasa kasa sosai tana lumshe idannuwanta hawaye na diga a gefe da gefen kumatunta


Tsayuwa ya yi ya yi kiran gida , ya samu Baba na sanar masa yanzu zai taho da suka zo ya dan fita ne


Baba na kashe kiran ya kai dubansa saman kular da Hajia ta kawo masa waina mai sunnan waina, waina irin ta yan gayu ta sha su yankakiyar albasa da komai da komai , a kala yau an yi sati da take wannan abin dan ya kulata, bata san cewa bashida lokacin haukanta bane, a garin da take dakawa ta kara kaimi ta daka sama da shi, tsaf ya shirya mata ko me take takama da shi


Mikewa ya yi bai ce komai ba ya ja hannun biyu zasu tafi


Jiki a sanyaye ta ce" Alkali, ina zaka je kuma baka ci wainar da na yi ba?"


Gannin da yara dole ya dakata ya juyo yana kallonta ya ce" Zamu tafi asibiti ne, uman biyu ke cen da kanwarta an mata aiki"


Hajia dake neman shiri harda dan mikewa tana fadin" To ko na zo mu je ne?"


Sosai ya ji sasauci a guguwar fushin da yake yi da ita a zuciyarsa, sai dai ba zai yarda da ita haka kai tsaye ba , dan haka ya ce" Aa, ki yi zamanki, idan tsoro ya fita tsakaninku kwa yi zumunci"


Daga haka ya fice da biyu yana tunanin sai sun biya an dauki Baba Lauratu su je tare ko dan ta kula da biyu , domin asibitin ba'a barin yan jinyama sam, ko kwana nawa zata yi ba zasu yarda da yan jinya ba, zadai a ringa zuwa ganninta ana dawowa har a sake su


Kofar ta zubawa ido na lokaci da dama a tsaye
Ta rasa ta inda zata kamo tunanin mijinta
Koda yake, ta fi kowa sannin waye Alkali a kan kafiya kan abinda ya nacewa


Zama ta yi tana maida kiran Maman Risala a ranta tanaa ayana ' matar nan kiran wace jarabar kuma take min tun jiya da yama!'


Gaisawa suka yi a mutunce, maman Risala tana basarwa ta ce" Na ji shiru ne Hajia tun jiya na zatama zan ganki?"


Hajia ta dafe goshinta dan ta tabata wata jarabar aka yi ta ce" Lafia dai ko?"


Maman Risala ta ce" Lafia kalau hajia, na ga abin alkhairi ya samu haka kuma na ji shiru?"


"Hajia ni du ban fahimta ba, wani abu ya faru ne na alkhairi bani da labari?" Hajia Hauwau ta fada a dan kagauce dan dama zuciyarta du a cinkushe, yanzu du irin yadda ta sa aka koya mata tuyar waina ta siyo tanda irin ta jonawa da wutar lantarki ta sa aka yi mata hadin waina naa karshe na manyan yan gayu ama Alkali ko budawa bai yi ba ya tafi wai asibiti ko kanwar uman biyu ko me? Ashe har kanwa gareta yarinyar!


Maman Risala ta yi murmushi ta ce" Au, na san kunya ta hanna masa sanar maki ne Hajia, ai jiya raga raga muka daukota mun kusa kai isha'i a asibitima, sai da muka ga likita baba, ai lamarin kai budurci kan zo da salo daban daban , ita kam ta jigata baiwar Allah, kin san abu da wace bata saba ba, a kilace a tsaftace shi yasama na dawo da ita nan dan ta yi jinya"




Tsuru tsuru HAJIA ta yi da mahaukacin mamakin maman Risala, du wayewarta bata kai cen ba walahi
Yanzu dama wannan maganar matar nan zata fada mata ta saka ta nutsu take sauraronta?, Wata irin kunya ta kama Hajia, harma ta rasa amsar da ya dace ace ta bada


A hankali Hajia ta iya furta " Uhum"


Maman Risala bata dauki hanya ba, bata gane ba, ta ci gaba da yamadidi da maganar tana karra jadadata, har ya zamto Hajiar ta fahimci inda ta dosa, watau kyauta da ake yiwa amare idan sun kawo daki, shi matar ke son nunawa


A nutse ta ce" Allah ya bata lafiya, zan hau sama "


Maman RISALA ta yi dan murmushi tanaa sake fadin" To na damuwa HAJIA sai an zo dubiya, ai yar gidan naki gatanan sai nishi abu da rashin sabo mijin sam bai saurara mata ba ai in fada maki kwata kwata bai........"


"Kai lahaula wala kuwata na shiga uku , dan Allah maman Risala bakya jin nauyin maganar nan ne?, Haba dan Allah manan Risala wai wasu irin mutane kw zagaye da ke basa baki shawarar da ta dace ne tunda ke ai na kula sam ma bakya tuna irin haka, Maman RISALA ace kin je kin dauki yarinya daga dakinta dan kawai abin daukakawarta ya sameta?, Ke na kula ina yaki kina kuncen hanyar yaki ne gaba daya walahi, ama ba komai idan alkhairi ne ai zaki gani kwana kusa Maman RISALA, wannan kamari har ina wani abin ai ba sai an fada maka ba tsakani da Allah, a kanta aka fara? To bari ki ji itama dayar ai budurwar ce du yadda ya ki kar na ji sai da kika kwasheni kika kaini shi kuma ya fada min idan ya so na ji da shi ko? Ni kam kin ga bafa cen na dosa ba, mu irin wannan abin boyewa ake yi ba abin a yi yawo da shi kowa ya ji bane ba fa Hajia, ni kam kin ga kamarin kyautar wannan abinma idan ya yi niya ya yi tsakaninsu, idan baya irin haka kuma ra'ayinsa ne ba zan tofa komai a kan wannan ba, haba , yaya ina yaki dan yarinya ta samu wurin zama kina kunce min? Yanzu da kike kwasheta kika kaita gida ai fili na Amina ne, sai ki yi ta yi tunda ke bakida masu fada maki a kusa da ke" Hajia ta fada da bambami tana katse wayar hadi da ci gaba da masifa kamar zata ciki kasa, ita abin ya bata mamaki Walahi meye a su budurci da ake fada da wani isa, to hala yar ta yi yan yawace yawacenta ne da ake cika baki dan bata barar da budurcin ba?, To da me take tunani ne? Budurcin banza budurcin wofi idanma ta barar da shi ai gata ga ABDUL din, batama san waye ABDUL bane, ta dai rike y'ar ta tabata ba zai lekata ba tunda ba wani ciwo mai dalili bane , ciwon iya shege ne, yo ko fafarketa ya yi ai abin kunyarku ne yamadidi da shi bale da ace ya farketan na tabata sai kakansa mai SHANU ya ji , mutane sai shegen iyayi da dan banzan nuna kai bayan ba komai kowa ba!, Shirmen banza da ita da budurcin sun ci kaniyarsu. ( To fa)


A bangaren Maman Risala karma tana jin an katse kiran ta shiga zage zage tamkar zata hadiyi harshe, har sai da Risalar ta fashe mata da kuka tana fadin" Mama, sai da nace maki dan Allah kar ki yi kiran hajia, ki bari na daidaita tsakanina da ita, kin ga dama ba wani yin wancen matar take ba, idan na samu na sake sayeta ko menene sai aa yi, ama mama kece ki yi fada da ABDUL, ki yi da Hajia? Mama yaya kike so na yi da raina?"


Da takaici uwar ta ce" Ki hadiyi ran mana Risala? Shashashar banza da wofi, sam ban ga anfanin wannan aure ba, ace ya fatatakeki haka ama bai biyo bayanmu ya yi mana magiyar a bada ke yaa mayar da ke? Wai HAJIA ni zata cewa wancen guzumar tasamaa budurwace? Ina ruwana ni, tsohon budurci da sabo ai ba daya bane, ke da ita ba zaku taba kasancewa daya ba har abada, shirmen banza da wofi wai ita a komai sai ta wulakanta mutun"


Ita dai Risala kukanta ta ci gaba da yi da wayarta a hannu tana sake buga numbar Mijinta


A daidai lokacin sun karasa gidan iyayen Mudi sun kai masu gawarwakin yaren, sannan Baba ya sanar masu duka kaf abinda ya faru
Ga mamakinsu Mahaifinsa ko a kwakar rigarsa, vawarwakin yaren kawai ya yi gargadaf yana fadin su zasu birne , ba zasu bayar ba, tunda yaro ya saki kuma ai shikenan, dama shi sam yarinyar bata wani yi masa ba, abinda yana saurayinsa danye shataf ya je ya wani lakewa bazawarar da miji ya mutu ya bari da cikin gardawa har biyu, ai kawai an gode uma ta gais da asha


Baba mai SHANU baki da hanci ya bishi da kallo a lokacin da ya mike yana mai ci gaba da balakinsa ya shige da nufin kiran Ι—an nasa dan ya fada masa ya zo su je ko su biyu ne su birne yaren


Yana shigewa mahaifiyarsa dake rame baiwar Allah tana share hawaye ta duka gaban Baba tana fadin" Dan Allah Elhaji ku yi hakuri kun ji?, Ku yafewa yaron nan, ban taba dana sannin aurena irin haka ba, ba sauki ba alamun sauki, hali zanen rai ne yake dawainiya da su, mugun hali marar amfani, yarinyar nan tunda ya aureta sau biyu kawai na ganta, ita bata samun fita, bale ni da a wajen ubansa ya gani ya gada, Elhaji ba zan taba manta bawan Allahn nan ba, mahaifina ya rasu har aka yi suturarsa bai sanar min ba, an zo daga gidanmu dan a fada min yace zai fada mij, sai da aka yi sati mahaifiyata ta zo da kanta take fada min, a ranar na yi kuka kamar raina zai fita, kuma bana iya fita nan da kofa, idan na saka kafata zan fita kamar zan mutu nake ji, ina rokon Allah ya nuna min bayan wannan wahala domin abin ya wuce tunanin bawa
Dan Allah ku yi hakuri ku bata hakuri itama sannan ku yi mata barka , domin ko ni na samu haka ina so Elhaji"


Kai baba ya gyada cike da al'ajabin wannan ahali, yana tsinkayo wayar da uban ke yi da Ι—an nasa, waya ce mai amo mai karfi, baki dayansu sun ji ihun fadin da Mudi ke yi cewa an kashe masa ya'ya dai, ba zai taba hakura ba, ba zai yarda ba sai ya kai karansu


mikewa Baba mai Shanu ya yi yana dafa kafadar ABDUL da ya yi wani iri alamun rikici sun bayana a fuskarsa ya ce" Mu je Magaji, mu tafi , Allah ya sa masu ceto ne"


Mikewa ya yi shima ya bi bayan Baba suka fice a gidan




Ko a cikin motar shiru ne ya ratsa motar, babu mai magana a cikinsu


Sai da suka shigo farfajiyar asibitin Baba ya dubi ABDUL gannin bashida niyar yin magana ya ce" ABDUL, ka yi hakuri ka ji? Haka Allah ya hukunta, ita kuma Allah ya sa karshen wahalarta kennan, Allah ya shirye su su kuma idan masu shiryuwar ne, idan ta warke ka ga sai ta koma gida ta zauna tare da mu har Allah ya fitar mata da miji ko?"


A hankali ya dago kansa da idannuwansa da suka yi ja yana kallon Baba yana ta cije lebe da saki kadan kadan ya ce" In sha Allah"


Ya yi shiru, sai kuma ya sake duban Baban ya ce" Amma idan ta fito daga nan tare da Uman biyu zasu zauna dan idan ta je nesan ba zata daina kuka ba"


A hankali baba ya ce" Aya, ita Firdausin kau? Kuka take ta yi ko? Baiwar Allah ai ko ba'a fadan komai ba yarinyar ta wahala, Allah ya saka mata da mafificin alkhairi a cikin alkhairan duniya da kiyama "


A nutse ya ce" amen, amma ba ita ba, ni ita har yanzu bamu yi magana ba, ita Mom twince din ce ai idan aka tafi babu kanwar tata zata yi ta yin rigima ne"


A hankali Baba ya kalli Muhammat da ya dago shima ya juyo yana kallon Uban gidan nasa
Ya sake juyowa ya ce" Ita dai Uman biyun ce mai rigimar?"


Kansa ya gyada yana budewa ya fita yana fadin" Bara na leka Mansur na ji kwana nawa ya dibar mata"


Da Baban, da Muhammat din basu daina binsa da kallo ba sai da ya bacewa ganninsu


"Allah mai alkhairi, ka ga rashin rabo , saifa da kakar gwamna ta ce min zata zo na kiya, da na san hakane da na zo da ita ta ji batun gwamna......kai jama'a" Baba ya fada yana kame haba


Muhamat ya ringa dariya kasa kasa


Baba ya ce" To ka ji,, Muhamadu kaini dakin yarinyar nan na sake ganninta baiwar Allah na yi mata nasiha, Allah dai ya shiryi wasu mazan"


Yana murmushi ya bude ya shige gaba Baban na bin bayansa suka nufi ciki




A office din MANSUR


"Man, na jima ban shiga wani hali a rayuwata irin na yau ba, na jima ban ji zuciyata na girgiza irin na yau ba, Man wannan mutumen yana nan a raye baka babalashi ba? Namiji uwar yaren nan tsabar abu ya dira mata zuciya ta kasa koda kuka, yaran ta amsa ta kalla daya bayan daya ga ciwo CS a hankali ta masu addu'a ta mana masu kiss a goshinsu ta miko mana, du yadda muka so gannin hawayentama bamu samu ba.....Man dan Allah kar ku yarda ta koma gidanta idan har baku zaunar da shi kun ji meye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login