Showing 15001 words to 18000 words out of 145392 words
Chapter 6 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
yi kokari ki siya ki ci, in sha Allah zan dawo "
A hankali Firdausi ta amsa ta mike ta boye tun tana zaunen sannan Amina ta tashi ta fito daga dan tsakuraren dakin Firdausin tana yi mata salama
A hankali Firdausi ta ce" Aunty, dan Allah ki ce da su ina gaishe su, Allah ya yi masu albarka, ki ce masu kulun kulun ina yi masu addu'a sosai"
Murmushi sosai Amina ta yi mata a sanyaye ta furta" Allah ya saka da alkhairi, zan sanar masu in sha Allah"
Da wannan suka yi mata salama, basu hadu da mijinta ba sai a lokacin da suke tsayar da mai adaidaita sahu, ido cikin ido suka kalli junna da ita, ama sai ya cire kai tamkar ya ga wata abokiyar gabarsa
Itama Aminar bata gaisheshi ko ta nuna ta sanshi ba, domin ta sani ne idan ta yi masa gaisuwarma da kyar ya amsa, koda ya amsa a kayade take zai ce da ita "Lafiya" yana cire kai, gaba yake yi da ita , yana jifanta cewa ta ki yin aure ta zauna zaman banza har tana neman tsofewa ta fake da nufin bata samu miji ba, to wa zai fito ya dauki ya'yan wani ya rike sannan ya kwashi sauran karti? Wannan kalamai nasa suka saka ta daina gannin mutuncinsa, dama mutuncin nasa kadan ne take gani domin mutun mai irin halayar mijin Fido sam baya cikin tsarin wanda zata iya yin zaman minti uku da shi a waje daya ba a rayuwa
Firdausi dake gida zaune bayan tafiyar yar uwarta ta yi shiru ta zubawa waje daya ido zuciyarta cike da tunanin rayuwa da aune aune da sake sake ta yi firgigita tana mikewa tsaye da sauri sanadiyar jin rufe gidan mijinta ta hanyar saka sakata da komai sannan ya shigo gidan fuskarsa a hade sosai yana karewa ko'ina kallo da son gane abinda yake zargi
Gannin bai fahimci komai ba ya fuskanceta fuskar nan a hade tana masa sannu da zuwa hadi da miko masa ruwan da ta ja a rijiya ta tanadar masa tunda ta gama dafa dukan taliya yar murdi ta adana
Ruwan ya bi da tsinanen kallo ya sake dubanta fuskar nan a hade ya ce" Na tabatama ta zo gidan nan , domin na hadu da ita a bakin layi, abinda nake son sani shine ina fata bata shigo min gidana da kartin maza ba, kuma baki dauki ruwan gidana tsaftatace kika bata ba?"
Kai Firdausi ta sada, zuciyarta na dokawa sosai, ciwon magangannunsa na ratsa zuciyarta, ita din ba mutun mai fitina bace, du irin sanyin Amina ta dameta ta shanye, ama duda haka wani lokacin sai ta ji tamkar asararen zama take yi da mai gidanta, sam bai san darajarta ba, bata tunanin gabar da yake yi da danginta dangin nata ya tsana, ta fi tunanin matsalar a kanta ne, itace damuwarsa, itace abikiyar gabarsa, takan yi tunanin da ace tafiyarsu bata dauki salon tsarce tsarcen yawu da tashin zuciya ba, da ta nema masa sauki itama ta samawa kanta , wani lokacin tana yin biyayar ne dan tsoro da tsoron Allah ba dan tana ji a ranta ya cencenci ta masa biyayar ba!
A sanyaya ta ce" Sun zo, ama bata shigo da biyu ba, kuma ko ruwan gidanka ban bata ba"
Daga haka ta juya ta shige cikin daki ta dauki carbinta ta zauna gefen gadonta ta shiga hailala da salatin annabi, domin shine kadai abinda take lazumta ta ji sauki a zuciyarta dangane da zamanta da mai gidanta
Baki ya tabe ya daura alwallah yana ta mita da fadace fadacen shi da ya isa da gidansa da Amina ta daina shigo masa gida!
Ita dai daga wannan bata ce masa ufan ba, sai da dare ya tsala ya sake biyota saman jigatacen gadonta ya yi mata turmusar da baya tsalake rana, kulun fa wannan sai ya biya shi baya tsalaken rana, da yinwa ko ciki koshe, da yardarta ko babu yardarta , idan ya tashi zuwa zai zo ne babu dan aike zai turmusa da dukkan karfinsa ya mike ya barta da wahalarta!
Bayan kwana biyu
Kasancewar amaryar gidan aunty Rukaya yarinya ce mai dan haske sai take yi mata gyaran hadin kurkum da zuma, sai kuma hadin dilkar tubawa tsumamiya wace a kwana na biyun nan da ta fara yi mata aikin fatar yarinyar har wani kyali take yi tsabar gyaran na kamata (gaba daya hadin zai zo da zarar na rufe free page)
Yau gashin kanta ta raba gida hudu ta yi hadin gyaran gashi kamar haka : Nescafé, Kwai, madara, man shanu: ta kwaba shi sosai ta ringa bi daya bayan daya tana shafa mata har ya gama hade kan ta sakata saka leda sannan ta daura dan kwalinta a sama da zumar ba za'a wanke ba sai nan da kwana biyu domin yarinyar na fashin sallah ne, ta sake jadada mata kar ta damu da karnin kwan, idan bata kunce bama ba zata ji ba, domin turaran wutar da take yi mata kadai ya isa ya hanna karnin ya dameta
Kamar yadda ta saba tataka mata , hakan ce ta faru yauma har kan kwanar gidansu sannan ta ja ta tsaya tana hangenta har ta shige gidansu
Juyowa ta yi da zumar komawa gida, da sauri ta ja baya kadan tana kallon Muctar mai kanti dake tsaye daf da ita sosai
Hade fuskarta ta yi kadan domin ta tsorata sosai bata san da mutun kusa da ita har haka ba tana sake dan matsawa hadi da fadin" Aa, Malan muctar kaine tsaye kusana har haka?"
Muctar ya yi murmushi yana kallonta gannin tana sake jan kasan hijan dinta tana kokarin rufe fuskarta ya ce" Ba dole na ringa dakon hanyar fitowarko ba tunda na je zance sau uku kina kin fitowa? Amina shin kin dauka da wasa nake ne ko ba zaki iya auren talaka irina ba?"
Kanta na kallon kasa take tunanin amsar da ta dace ta bashi, ita ko daya ba maganar talaka ko mai kudi ke gabanta ba, ita burinta ta samu datijo ko yayane wanda zai juri zama da ita da ƴaƴanta, idan ta auri Mutari ina zata kai biyu? Mutari kansa nada nasa ya'yan hudu da matarsa, matarsa sau biyu tana mata tataki da habaice habaice da komai, sai dai ita ba tsoront take ji ba, ba kuma wannan zai sa ta bar Mutari ba idan har ta yi niyar aurensa, matsalar daya ce zuwa biyu, wace ta fi karfi ƴaƴanta, sai kuma shi din kansa, mutari ba wani baba bane in ya yi nisa ya bata shekara hudu, irin saurin auren nan ne na mutanenmu na gida har ya tara ya'ya hudu, ita yanzu ta auri wanda ya bata shekara hudu ai ta auri yaro, salon su kama gardama a gida ya wanka mata mari ko? Ko ya kamata da kokowa? Bata tunanin hakurin da ta ji da shekara ashirin da tara zata cike talatin a duniya zata zo kuma ta dsa rayuwar wahala da wani namijin, ko kamaceceniyar rayuwar kanwarta, ba ztaa iya jurar a wulakanta mata yan bayin Allan ƴaƴanta ba
A sanyaye ta ce"
Ku zo fa mu je mata💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻, barkarmuda safiyar litinin
🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️
_*NI ZAN LADABI*_
🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️
*NA*
*SAJIDA NIGER*
Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida
Wannan Novel na kudi ne ba free bane
Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER
Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai
Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka
*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰*
*Page 0️⃣7️⃣*
A sanyaye amina ta ce" Ka yi hakuri Muctar, zan karasa gida bana son tsayuwa a bakin layi"
Da dan sauri ya daga kafarsa yana biye da ita dan har ta juya ta fara tafia,
Bata yarda sun jera ba, ama idan ka gansu zaka gane tare suke, a tafiyyar da suke yi kuma kasa kasa maganar ya ci gaba da yi mata har suka karasa kantinsa
Da mamaki yake tambayarta dama nan din zata zo ta ki bashi sako?
Amina ta yi murmushi kawai ta mika kudi tana zayano abubuwan da take da bukata na kayan kosan da take son farawa na safe bisa shawarar inna lauratu
Dagewa ya yi kan sai ta amshi kudinta, a dole ta fuskance shi a nutse ta ce" Muctar, ka san bana kulaka dan wannan, ka san ba yau ba ka nuna mu ringa amsar cefane na nuna maka aa, ka yi hakuri ba zan iya amsar kayan sana'arka ba, nima sana'a zan fara da wannan din, inada na jarin, ba raina maia na yi ba, na fi so na saka gumina dan na fi gane gaban nemana"
Shi kam gaba daya irin yadda take zile masa na matukar damunsa, du yadda ta ki amsar wani abin sai da ya zuba wani ba tare da ta gane ba, sai da ta isa gida ta ringa cin karro da abubuwan da ya karra mata, sosai ta ji ba dadi domin dukkan abinda zai taba mata mutuncinta ko kwonciyar hankalinta takan yi iya yinta dan kiyaye alakar da zata taba mutuncinta, shi yasa a rayuwa du tsakaninta da kai bata yarda da kyautuka irin na yau da gobe koda na saurayi da budurwa ne
Kilace komai ta yi ta gyara wakenta da nufin kaiwa markade gobe da karfe tara , domin kosan na yan gayu ne na masu karin karfe goma ne zuwa sama
Washe gari da sasafe ta gama dukkan abubuwan da suka zamo mata jiki, yau din Alhamis ce tun kusan karfe takwas har rana ta fito ta fara kwalar kawunnan mutane, Su Amina na daya daga cikin wa'inda ranar ke kwala a bakin titi daf da kwata sunna jiran dan adaidaitan da suke wahala yau
Husaini kan buda ruwansa ya didika ya rufe ya maida a jakar makarantar, yau fa basa yin karatu ama mamansu ta ki yarda tace ita jiya ba'a fada mata ba yau ba makaranta, shi kam gaba ta kaishi domin an saka masa bota a boredinsa ga kuma naira ashirin dinsa a jaka, kwanakin nan gidansu dadinsu kawai suke ci, sunne taliya, sunne shinkafa da miya ta gwamnati mai dadin hadiya, sunne biredi da bota, jiya harda alewar tsinke yar goma goma mamansu ta siyo masu, sun zama yan gayu , cin dadi suke yi ba kama hannun yaro, shi yasa shi kam fara'arsa har kamar zata yi yawa , baya fada da kowa baya jin haushin kowa, Hasan ne hali baya barinsa, du dadin nan ya ga damar ya tashi yana fushi ya ki kula kowa a gidan
Ajiyar zuciya Amina ke saukewa lokaci zuwa lokaci tana sake hangen titin a zuciyarta tana karra ayana' ikon Allah, yau kamar an yi ruwa an kafe ? Basu da yawa yan adaidaitar kuma du a cike? Gashi har lokaci zai shige na makaranta gashi ban kai markadan ba, Allah la turo mana dan sahu na mika su na dawo'
Gali mai ruwa ne ya karyo kwana da kurar ruwansa shake yana turi, Gali kan kaiwa Amina ruwa lokaci zuwa lokaci, bama kamar in zata fara sana'a domin ruwan pampo ne yake siyarwa sosai an yarda da tsaftarsa ga kuma sauki, Gali dai saurayi ne mai zuciyar nema, yana zaune ne a gidan mahaifiyarsa tare da mahaifiyar tasa da kannensa uku yan mata, gali shine komai nasu, jajircewarsa ta sa basa zama da yinwa, mutane da yawa na mamakin irin yadda Gali ke samun kudi, sandar ruwan dai gaba daya naira ashirin da biyar ce duka duka, a cikin kurar gali bai fi sanda goma ba, kuma a wuni in ya yi zagaye mai yawa ya yi zagaye hudu, domin harka ce ta ruwa kusan mutane da yawa nada rijiya a gidajensu, yawanci masu sana'ar shayi ne da kuma masu halin siyan na pampo dan sha a gidajensu yake kaiwa ruwan, ama yanzu haka wayar da Gali ke anfani da ita a kadan zata doshi dubu hamsin, kaf anguwar nan an san gali da gayu da ba naira kashi, abinda ba'a sani ba shine shin a ina Gali yake samun kudade zafafa haka? Da yawa abokansa sun fada sana'ar siyar da ruwan suma, harma sukan yi fita fiye da tashi a wuni, ama abinda aka fi karfi cimar kaiwa baka ce, bayanta du wata rigimar da kudi zai warware sai dai a yi kamo nan kama cen a yi wace idan ba'a yi ba ana iya mutuwa ko a jigatu, sukan kalli Gali a matsayin wanda ya iya sana'a fiye da su, basu san wanene Gali ba!
Tunda ya shanyo kwanar ya tsaya dan kusa da su kadan yana dariya ya ce" Hajia Amina ikon Allah, yan matan jiya yan matan yau, kun ci zamaninku kun haye na kannenku har kun fi su kyan kamani"
Amina ta sale tamke fuskarta, a duniya ta ki jinnin dukkan wani furuci ko lamari da zai saka yan ƴaƴanta dago kai su yi mata kallon Mama ke da kanki? irin kallon nan dai na mamaki da wasu lokuta zaka ga danka ya nuna a kan wani lamari da ya ga ya faru da kai ko a gabanka baka dauki mataki ba,
Bata san dalilin da yasa Gali idan zai yi mata magana yakan saki jikinsa ya ringa yi mata tsokanar da ta wuce misali, ita dai sa'arsa bace, ita ba wani wasa take yi da maza ba irin da zaka ga budurwa tana shigewa maza da son yin wasan banza da su ba, hasalima samarin anguwar nan na mutuntata ta hanyar kuranta da aunty, ko wani ka ga zai mata ba daidai ba to fa bako ne kuma idan wani ya ji zai masa magana, kare mutuncinta da girmamasu da take yi ya sa suke girmamata itama, ama bata san shi me yasa yake yi mata irin haka ba, sam bata jin dadin irin wasan nan
Bata bashi amsa ba, ama bai karyar masa da gwuiwa ba yana kare mata kallo yauma dai cikin hijab, ita dai kulun a hijab ya ce" Makaranta ba za'a kai biyu? Hajia Amina ai yanzu malan Muktar ke fada min yau fa akoy kosai, na ajiye jarka biyu ta ruwa a wajensa ya biya kudin, shine nace ko dai da yayan namu za'a shige daga cikin ne?"
Da takaici ta juyo zata yi masa magana sai ji ta yi shaaaaaa ruwan dake kwonce na jikin kwatar nan an maka masu shi daga ita din har biyun, da Galin gaba daya
A haukace du suka bi bayan motar da ta aikata haka, walahi bata san lokacin da ta saka ihu ihu ta daga hannunta da ya wawuro dutse ta daga kafarta daa dan gudu ta cila dutsen nan da dukan karfinta da karfi kuma ta ce" Allah ya isa mugu ko muguwar dake cikin la'annaniyar bak'ar mota! Allah ya isa rainin hankalin banza da woffffffffffi dan ba'a dan zafin haihuwa ba ina tsaye da y'ayana za'a watsan ru.......................!"
Dif maganarta ta dauke, sakamakon abinda ya rubtu a idannuwanta, jifan da ta yi bata taba tunanin hannunta zai kai bayan madubin motar ba, dutsen kansa bata taba tunanin ko goshi ya daka zai fashe ba bale motar, itafa a da sai ta jima tana jifan wajen da kadangare yake ama da kyar take iya korarsa bata samunsa, sai gashi a yau wani tashin hankali jifan nan daya kamar ita fin jikar mahalba ce ya sauka a bayan motar nan da ta tabata ko kudinta aka yi ba zata kai kudin motar ba ya fasa madubin bayan motar
Bata ji cikinta na neman hautsinewa ba sai da ta ga motoci biyun sun tsaya, lokaci daya kuma ta ga sun shiga yin baya baya a hankali
A tsayen da take ta yi mutuwar tsaye, bata yi aune ba ta tsinci muryar Gali yana fadin" Kan uba, motar Jikan Mai Shanu kika daka yau Amina? WALAHI na tafi ni kam na yafe watsa kwatar da aka yi min, menenema a su kwata Allah na tuba"
Da sauri ta sado dubanta jin Husaini yana jan hijabinta da karfi , bata yi wani aunen ba hijabin ya janye gaba dayansa ya sauka a wuyanta domin dama wuyan ya mata yawa dabara ta yi da tudun gahinta ta zaunar da hijabin dan ta san babu abinda zai kawo fitar hijabinta daga kanta lafiyar Allah
A kidine, zuciyarta na dokawa ta dago jin innuwar motar da hucin tsayuwarta a gabanta
Walahaula wala kuwata ila bilahil aliyul azim, Hasbunnalahu waniimal wakil, Wannan wani irin tashin hankali ne? Kudin jikinta dududu basu fi naira dubu goma sha hudu ba, a haka jinta take tamkar biloniya kwana biyun nan, ji take yi idan da waye zasu iya karawa domin aljihunta da nauyi, shagwaba ƴaƴanta take yi da kayan dadi dan idan ta laluba ta ji cukus sai ta ji hankalinta ya kara kwonciy, itace shinkafa rabin buhu, makaroni kwali, man kuli da na ja, harda su katihun kayan makulashe na biyu alewa da tuwon madara , sai ga mai samu ta sameta rana tsaka
Motar dake gaba ce aka bude aka fito da sauri aka zagayo wajen motar dake daf da itan
Mutane hudu ne suka fito din, ukun