Showing 54001 words to 57000 words out of 145392 words

Chapter 19 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8159

MAI SHANU banda matarsa, yau ace Hajia da kanta ce ta manta waye mijinta? Lalle abin da matukar mamaki, wai har Mai SHANU ya dora doka a take? Uhum, ta manta ita din wacece, koda yake dadi kan sakawa a manga wuya.........'


A bayane kuwa sai ta yi murmushi ta ce" Aa, ba zaki ki yin anfani da kayan cen ba, haka kuma ko kai kayan amaryarsa da ke za'a yi in sha Allah, dan ai ba zaki so mai Shanu ya irgaki cikin amsu bijire masa ba ko?"


Amina da bata yi tunanin amsar nan daga Baba ba ta tsareta da ido tana son karantarta


Baba ta dora da fadin" Wani nacinma bashi da anfani, ama ba zamu daina komai ba, haka kuma zaki ci gaba da yan shige da ficenki da ci gaba da kare mutuncin kanki, janyo kayan mu gani mu ware na dinkawa idan ba a dinke ba, mu yi sauri mu gama na je na hado maki kayan wainar ta Mai SHANU ko?"


Wata ajiyar zuciya ta farin ciki ta saki ta mike ta shiga yin abinda babar ta ce hankali kwonce , cike da farin ciki


Babar kuwa ta yi murmushi irin na manya a ranta ta ayana' Aya, ta yaro kyai take yi, bata karko, Amina...zaki saka kanki a ramin nan da kanki ne, haka shima zai zurma a lokacin da bai aune ba, ita kuma zamu ga irin nata hukuncin............sannan sai mu sake aunawa mu gani a cikin taron nan *WA ZAI YI LADABIN?!* ( TOH FA)


haka suka sake wuni, koda yama ta yi dukkan abinda ya dace kafin dare ya shigo yrenta suka dawo suka dinke a ciki, abinci baya gafce masu haka kuma a yau bayan muryar baban harda ta hajia ta ringa tsinkayowa a falon, ta yi murmushi abinta watau ta samu solution hankalinta ya kwonta ko? Rayuwa kennan




Kamar yadda Baba ya saba zaman sasafe idan ranar juma'a ce, hakan ne yauma


Sai dai zaman nasa na yau tare da uman biyu, da biyu ne ga wainarsa a gefe sai turiri take yi kanshinta ya gama cika masa hanci so yake yi su gama magana da Uman biyu wace ya gama fahimtar da magana a bakinta ya kama wainar nan ya ci iya cinsa


Tsai ya yi yana kallonta, maganarta gaba daya dai ya ji bai gamsu da ita ba, yannayinta kansa ya tsargu da shi, furucin bakinta kuwa ya fi komai bashi mamaki


Amina ta sake sadda kanta tana sake kamo ayoyin samun galaba tana ta yi da addu'ar da ta shiga bakinta, dan idannuwan Mai SHANU kaifin tsiya ne da su yana iya saka ka fadin gaskiyar da ka boye a cikin karyarka


Murmushi Mai SHANU ya yi yana girgiza kansa a tausashe ya ce" Waye ya tsatsaraki ya tsara maki magana irin haka Uman biyu? Waima yaushe kika lakanci karya haka ne?"


Da sauri ta dago tana kallonsa hadi da kai hannunta mai dauke da yelow din kurkum da bata wanke ba abinta ta ce" Lah🫒"


Mai shanu ya yi yar dariya yana fadin" Fadi da kyau, Lah, to wai wa kike tsoro da za'a fara sako ki a gaba da tsararen zance ni kuma ki tardoni dan bakya jin tsorona?"


Fuskarta ta takwakwabe ta sadda kanta tana ta rubububi da kalamai dan samun galaba a kansa


Dagowa ta yi tana kallonsa a raunane ta ce" Ama Baba, ai ba haramun bane yin hakan ko?, Bayan wannan shi ABDUL din ai ya yi biyaya da ya yarda da zabinka ko Baba? Dan Allah a tura mana......"


Baba Mai Shanu ya kada kai murmushinsa ya ki ya kau, hikimar yarinyar na kayatar da shi, sai dai du yadda ta so da boye masa gaskiya a bayane yake karantar gaskiyar lamarin, abinda dai yake son fahimta ABDUL son da yake yiwa yarinyar cen har ya kai ya yi maganar da uman biyu? Lalle da kuwa ya sarawa lamarin, dan kuwa ga dukkan alamu ba karami bane


A tausashe ya ce" To ke kuwa wace irin mace ce za'a maki kishiya kike taya roko? Bakya kishi irin na mata ko kuwa Mai shanun birnin ne bakya so?"


Kunya ce ta kamata, dan walahi baba har wani kasa kasa yake maganar da wani salo na tsokana irin na jika da kakansan nan, dama sun saba irin haka tsakaninsu sukan sha hira , dan dai a da yakan yi ta tsokanar ne ita kuma kanta a kasa tana murmushi da jin kunya, ama a yanzu ita ke ta magana dan tana so a saurareta


Salamarsa a cen cikin makoshi kasa kasa da shigowar daya daga cikin masu aikinsa ya kawo kayan marmari na anfanin gonarsa da ya je kaya kaya ana ajiyewa ana sake shigo da wasu ya saka Baba kallonsa da fadin" Dan halak ya ki ambato, kai dan ka ga ina hira da amarsun ne ka wani diro kana huci? Yaro sha kuruminka ni da uman biyu mutu ka raba"


Dan satar kallon gefen da take zaune ya yi kadan, sannan ya dauke kansa ya maida wajen Hasan da ya mike yana murmushi yana kallonsa, ama bai karasa wajensa ba, jira yake yi har ya ga fuskar yin hakan, duda rabonsa da shi da dadin rai suka rabu, ama shi din ba irin yaren nan bane masu shegen zakuwa da nacin abu ba, dan uwansa kuwa tuni ya labe a jikin babarsa dan shi tsoronsa yake ji


Hannunsa na dama ya mika masa , hakan ya sa ya karaso inda yake tsaye ya saka hannunsa cikin nasa
Basu yiwa junna magana ba, ama a hankali da hannayensu dake cikin na junna ya dan matsa kadan shima ya dan matsa nasa hannun , daga haka ya wadatar


Cen gefe ya karasa ya zauna yana karra kallon sumar yaron, daidai lokacin da baba ke fadin" Lalle, hali da hali, Uman biyu wai kin ga mijinki da yaronki kuwa?"


A tare suka kalli Baban, sai kuma suka kalli junna
Wata hararar tsinin ido ta maka masa ta turo baki hadi da dauke kai, shi kuwa ya girgiza kansa a dan takaice ya dubi baban yana fadin" Na sameka lafiya?"


Baba ya ce" Gani kuwa garas muna zantawa da uman biyu, kai ka yi mata nasiha ta san ciwon kanta da kishi irin na mata, wai ace uman biyu ke min maganar kun tsayar da maganar a karo mata abokiyar zama? Ko tarewarku fa ba'a yi ba, uwa uba ta dage wai karshen watan nan dan sun shirya dangin amaryar? Jama'a ni kam ka bani sirrin nan na aikatawa Hajia ko za'a dace, dan inaga da na gwada aure nan da shekara ashirin da hudu ta kusan wata a asibiti!"






Sai da baba ya dire maganarsa, sannan ya sake kallon ABDUL da son gane yana sauraronsa kuwa? Kuma da son gane ainahin maganar uman biyu


A hankali ta ciciba ta mike daga zaunen da take dan karara baba ke so ta dauke fuskar yaron nan da mari ta shiga uku, yaya zai ringa abu kamar na neman rigima ne? Ina hadinta da yaron nan?


"KE DAWO NAN KI ZAUNA" ya fada a dake bayan ya mata kallo daya ya gane nufinta tafia ce zata yi bayan ta dauko maganar da shi bai san yaushe suka yi ba?








Lah ha ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam ku kirawo hajia ABDUL zai ballo mata ruwa jama'a πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–πŸ˜–




*NZL PAGE2️⃣1️⃣*








A hankali ta juyo ta sauke dubanta a kansa, kai innalilahi walahi walahi jama'a da ita yake, subahanalah me yake yawo a kan yaron nan ne wai? Menene wannan lamarin na zubar da kima haka?


A kaikaice ta sake dauke shi da hararar da tsaf Baba ya gani, haka kuma ya saka shi boye murmushi ya gyara zamansa tsaf yana son gannin karshen wasansu, dan ya tabata sunna daf da falasa kansu a wajen nan


Juyawa ta yi da niyar sake yin tafiyarta dan ita ai ba sa'ar yara kanana bace


A nutse Baba ya ce" Uman biyu mijinki yace ki dawo ki zauna fa"


Innalilahi wa inna ilaihi rajune, inama zata iya fashewa da kuka a wajen nan? Da ta yi kuka har kamar zata haukace


Wai mijinki, wannan kalma na tsaye mata a wuyanta kamar zata kumeta ta sumar da ita


Jiki a mace ta dawo ta zauna tana sake sada kanta tana hadiye bacin ranta


"Ke baki iya gaisar da mutane bane?" Ya sake fada , dan kawai fitsarar yarinyar dariya take bashi, yauma kuwa warin nan na abin nan take yi dan gayanan a hannayenta , ko menene anfaninsa? Bai taba haduwa da ita ba bata wari, bau san menene take kwabawa jikinta ba sam!


Idannuwanta da suka cika da kwala ta dago ta zuba a saman fuskarsa, numfashi ta ja tana fitar da kyatu ta dantse lebenta na kasa dan bata so ta fashe da ihun kuka


Baba kansa dariya ke tikarsa, sosai abin ke titikarsa a ransa, gaba daya sai suka zamto wani nishadi nasa na sasafe, dan haka da kula yace "Uman biyu baki ji ba?"


Amina ta sake kallon Baba, sai kawai ga hawaye tarrr ta bude bakinta ta ce" Baba wai na gaishe fa yake cewa fa?"


Baba ya yi murmushi yana fadin" Eh haka, to ba shine gaba ba?"


Kai kawai ta soke tana hakin kukanta


Baba ya sake yin murmushi a hankali yace" Allah shi kyauta"


Hijabinta ta saka tana dan goge hawayenta a hankali dan dagowar da ta yi ta ga Hasan ya kura mata ido so yake ya gane kuka take yi ko me? Idan kuwa ya gane haka ta san shima zata daga masa hankali
Danta kuwa tuni ya yi waje, shifa mutumen nan da baya dariya ba tafiyarsu daya ba gaskiya, dan shi baya son bulala


Baba ya sake yin murmushi gannin wani sirri da ya gani gannin idannuwansa a cikin lamarin
Kai ya gyada ya ki yin lididddigar da ya yi niya
Da kula ya ce" Yaushe kuka tsayar da mijin naki za'a tura maganar auren? Sannan yaushema kika ce za'a saka ranar daurin auren?"
A hankali ta dab karra satar kallon yaron, ita baban takaicinta kar ya yi mata wata fasarar daban
Ajiyar zuciya ta sauke ta sake maimaita masa abinda Hajia ta tsara mata


Baba ya dubi ABDUL RA'UF ya ga shima shi yake kallo, so yake ya gani wai hala da gasken sai da ta roka zai yarda? Kai ama kuwa da ya sha mamakin baban, yaushe ya saka wata a wajen da yake da power ne? Lalle da an wulakanta shi shi kam!


Kai ya gyada ya ce" Allah ya nuna mana, zamu je ni da Rabi'u, sannan za'a saka yadda kuke so, maganar tarewarku ne ban ji ba"


Da dan sauri Amina na yiwa ABDUL kallon kasa kasa da turo baki ta ce" Wannan ai mun fi so idan aka daura natan sai mu tare baki daya Baba"


Shiru ya ratsa wajen, na lokaci mai dan tsayi, domin Baban kawai kallonsu yake yi


"Uhum" ya fada a cikin makoshinsa
'idan da raina ta yiwu na raba abin kunya' ya ayyana a zuciyarsa


"Allah ya doramu a kan daidai, tashi ki bashi ruwa sai ki koma ki gama tuyarki na san Lauratun na cen tana fama da rigimar gaz, gaskiya Hauwa bata kyauta min ba, ai sai ta bari a min abina a itacen kamar yadda aka saba wai kar garu su dauki bakin hayaki, in ba Hauwa ba shekarar ginnin nan nawa? Itama dake namalakiyar ginnin bata ga ta yi furfura ba balle wai garu? Gaskiya Abdallahi ka yi mata magana ni kam in dai Uman biyu na nan du juma'a a toyan wainata da itace"


Ruwan ta zuba ta kai daga cen barin dan so take ta yi masa maganar da bata so sai an jima dan gudun mantuwa ko ya bar gidanma bata sani ba


Kasa kasa sosai bayan ta ajiye ruwan ta ce" Kake wani ce min ke zo nan gaskiya bana so kar a maimaita, kuma da kaji ana wata maganar daban nima so nake na yadda kwalon mangwaro na huta da kuda, Allah ya sa baka mance hausa ba!"


Ajiye ruwan ta yi ta mike ta yi gaba


Da ido ya rakata har ta bacewa ganninsa, ya dawo da dubansa Kan Baba domin shi yana kallonta ne shi kuma Baban na kallonsa


A hankali ya ce" Tana fama da yarinta sosai yarinyar nan"


Baba ya yi dariya harda dan kama haba ya ce" Ka ji da shi Abdallah"


Shima murmushin ya yi ya karra duban kan Hasan ya ce" Inaga zamu je aski mu dawo kafin mu tafi masalaci da yaren nan"


Wani farin ciki ya lulube zuciyar Baba, ya san cewa ABDUL zai kula yaran nan ne dan sun shiga ransa ba dan wani abu da yake da burin ginawa ko kulawa da uwarsu ba, dadin da ya ji shine Halayar ABDUL din kwata kwata sun yi nisa da na sangartacen yaro da kudi, halinsa na datako na sakashi a nishadi da kwonciyar hankali, ya tabata idan har suka samu sasantawa da Uman biyu sai ya fi kowa farin cikin hakan
Sai dai tsoro kan kama shi
Ya kula Uman biyun ma fa bata son hadin nan, domin a yadda ta yi wani abin kamar wace ba zuciya a kirjinta na kishi? Kishi ai halal ne, shi da kansa ABDUL din ya kula ya yi mamakin abin


Salamarsa Abdul din ya yi suka fice, wanda Husain ya ki binsu sai da baba direba sannan ya shiga motar yana labe a jikin Baban yana hangen ABDUL da ya hade gabas da yama ya wani yi zama a hakimce cikin lalausan milk color din yadi yana wani basarwa irin na masu kudi
Shi kuwa Hasan a haka ya ga wajen zama, dan kuwa shima ya yi zaman ne ya wani dauke kai yana kallon titi kamar wanda ya jima yana shuga mota, bayan ko kwarewa da bude motar basu yi ba, to a cenma su yan yawace yawacensu da mamansu a adaidaita sahu ne, bale a yanzu




____________________________________


Dukkan yadda suka yi da Baba ta sanarwa Hajia a yanzu da ta fito tsaf cikin lalausan shirinta da nufin tafia gidan yar uwarta


Kanta ta sadda cikin shiga ta blue din Hijab mai tsayi har kasa sosai ta ce" Hajia zan tafi gidan Firdausi ne na dawo dn Allah in ba damuwa?"


Hajia dake murmushin abin nan da mamakin yadda aka yi ya saurareta bai fatataki kowa ba, dan ita fa a shirye take tunda safw jiran ihun sunnanta take yi da balbalin balakin fadan ba'a isa ba, sai ta ji shiru , kuma gashi har yanzu bai dawo ba daga fitarsu juma'a, ita da kanta tana sin fecewa ama har yanzu bata fara fitan ba tukunnan, so take yi sai komai ya idasa lafawa


Hajia ta ce" Kina ji, kina iya tafiya ai ba wani damuwa, ama ba zaki shiga taxi ba saboda Alkali gaskiya, ki je zan yi kiran direba daya ya kasance direbanki ne"


Amina ta yi dan jim, sai kuma ta rage tsayinta kadan ta yi godiya sannan ta juya ta fice


Hajia ta sake rakata da kallon da ta saba na harare harare da kuma haushi haushi a fili ta ce" Allah ya wadaran naka ya lalace, wai Alkali wannan ce zai sa ta juyani ni Hajia Hauwau? A dai daura auren zaka gani"


Tare da Baba Lauratu suka je gidan
Sun tarar da Firdausi tana sharar dan tsurut din balbalin gidan nata da wata tsintsiyar da bata fi a irga tsinken dake daure da yaloluwar leda fara ba


Tana jin muryar Amina ta mike a zabure tana wara idannuwanta hadi da amsa salamar


Da sauri ta daga kafarta dan ta zo da gudu ta rukunkumeta, sai dai amsawar da bayanta ya yi ga daskarariyar yinwar da take ji ya sakata dafe bayanta a hankali ta furta" Wash Allahna "


Da sauri Amina ta karasa tana rikota ta rungumeta a jikinta a hankali tana fadin" Fido? Sannu ki yi a hankali mana"


Firdausi ta yi yar dariya tana ji abin ya lafa mata a tsayen nan ta shiga dariya da murna da son dole sai ta yaye hijabin Aminar tana fadin" Uman biyi kece haka? Uman biyu kanshi kike yi wannan turaran fa? Uman biyu cirw hijabin nan na gani hannayenki bake ji wani santsi hakama jikinki ya dauka? Wayo Allahna farin ciki kasheni zai yi ni kam yau, Uman biyu kin ganki kuwa? Wayo Allahna da ke nake kwana ina tashi, damuwa ta cikan cikina, idannuwana kulun a kan kofar gidan nan, sakata yake sakawa ta baya du idan zai fita wai karma na saki na fita bai san tunda yace Allah ya isa idan na je ba na yi hakuri na biki da Adu'a, Uman biyu kuma da biyu kika tare? Shi mijin naki bai koro su ba! Uman biyu wai dan Allah........."


"Fido wai ba zaki yi shiru ki huta bane?" Amina ta katseta tana ririke hijabinta, dan walahi ita kunya take ji irin yadda jikin nan nata ya dawo, kamar ba jikinta ba, wani irin santsi da yake yi har mamaki take yi, ga wani haske da fatar tata ta dauka har tana neman zarce fuskarta haske, ita kam wannan gyara ya fara damunta , gashi Baba tace bata ga ranar dakatar da gyara ba wai sai ta tare, hahahaa ta tare a ina? In ba rikicin Baba ba?


Firdausi ta dan sasauta din, sai kuma ta sake rungumeta kadan saboda tirtsitsin cikin dake hannata motsin kirki ta fashe da kuka tana fadin" Uman biyu, aka daura aurenki wai babu ni? Innalilahi wa inna ilaihi rajune, ya Allah idan wani mumunan laifi na aikata ka jabaceni da wannan jarabawa mai tsauri bayan rasuwar mijina mai sona da ta iyayena , Allah ka sasauta min ka yafe min ka bani ikon cinye jarabawar nan, Allah kai ka haliceni kai ka dora min, Allah ka bani ikon cinyewa ya ubangijina"


Baba Lauratun ce ke amsawa, Amina kam janyewa ta yi a hankali ta dauko wata yamutsatsiyar tabarmar firdausin ta shinfida a nan tana kaiwa zaune da kafafuwanta dake cikin safa


Baba Lauratu ce ta ce" Dan bani jakar nan mana?"


Amina ta miko mata jakar da kudin nan yake ciki, Baba ta fice a gidan


A hankali suke hira hannayen junnansu a rike da junna


Amina ta yi iya yinta dan kar ta yi kuka, ta yiwa kanta alkawarin in sha Allah ba zata kuma yiwa dan iskan nan kuka ba, ba Firdausi bace? Tunda ta nuna idan ta fito zata karra zama karin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login