Showing 30001 words to 33000 words out of 145392 words
Chapter 11 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ki jinnin taren nan ta Mai Shanu da yarinyar nan da walakin goro a miya
Takalmin dake kafarta slipars ne, hijabin dake jikinta baki ne sidik mai hannu, sannan ya kai mata har kasa tamkar zai kwasheta ya kifar, sai dai cizawar bakinsa ya sa fatarta haskawa ya zamto duhun fatar tata ya ragu sosai, danma ta yiwa kanta tanadin gyara ne idan ta tashi yin aure, da kalar fatarta mai hasken duhu ce sosai
Manyan idannuwanta take karra zubawa a kan Hasan dake kyakyata dariya yana bin bayan Husaini da gudu, sakewar yaron a yanzu na bata mamaki, sosai yake sakewa yanzun bayan shi din mutun ne marar dariya a da, ko a yanzun ba wai cencen bane, ama da sauki sosai da sosai
Suturar dake jikinsu ke karra shiga zuciyarta, yau bama ita ta shirya su ba, kuma sun je makaranta tana barcin asarar da ta aura, sai yanzu ta ga shirinsu, masha Allah sai haskawa suke yi cikin shigar gajerun wandunna daidai gwuiwa masu tauri watau gins daya blue, daya baƙi, sun ciza sosai da rigunnansu masu kyau masu dogwayan hannuwa, sai takalma kito kafa ciki blue da baki, masha Allah twins dinta har wata sabuwar kaunarsu ke karra bin sasan jikinta, saima idan sun juyo sun kirayeta da Mama, a zaune a wajen nan da take kamar ta yi ta taka rawa, ita kam wani kwonciyar hankali da jin dadi zata nema sama da wannan?
Baba Lauratu da ta samu kebewa gefe da Baba tunda suka zo suka tatauna ce ta fito, fuskar nan tata kamar gonar auduga ta ce da Amina"
🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️
_*NI ZAN LADABI*_
🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️🙇♀️
*NA*
*SAJIDA NIGER*
Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida
Wannan Novel na kudi ne ba free bane
Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER
Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai
Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka
*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰*
*Page 1️⃣2️⃣*
*Asalamu alaikum wa rahamatullah, karshen FREE page kennan yan uwa🥰🥰🥰🥰🥰, na gode*
Fuskar nan tata kamar gonar auduga ta ce da Amina" Tashi maza ki je Mai Shanu na son magana da ke, Uman Mijin ki sani Mai shanu uba yake a wajen marigayi, Allah ya jikansa ya sa yana cikin rahamar ubangiji shi din mai biyaya ne a gareshi, bale marigayiya, ba zan taba tuna lokacin da na ga rashin kyautawa a tsakaninta da matar Mai Shanu ba du irin baudadan hali irin nata!, Dan haka ki je, ki yi kokarin yi masa biyaya, ko ba komai yanci yake kokarin kwata maki da rufa maki asiri, kasa zai tara maki ba wulakanci ba"
Ita dai a tsaye take tana dauraron Baba har ta gama maganarta, haka kawai sai ta ji fargabarta na neman karuwa a kan tunanin abinda ya da suka zo nan, tana jin dadin yannayin wajen sosai, ama jiki sukuku ta karasa ta karra dukawa tana sake gaishe shi
Mai Shanu yana murmushi ya ce" Uman biyu rabonki da ki min waina tun ta ranar juma'a, yanzun kikan ki yi min wainarma , bayan ni din ina son waina sosai"
Murmushi take yi kasa kasa ta ce" A yi hakuri baba zan yi mai yawa , har sai kace ka koshi "
Shima dariyar ya yi yana sake gyara zamansa ya ce" Yauwa, dangane da maganar wajen uncle dinki ne, yau kwaba uku kennan da na je na same shi ni da Malan Liman "
Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi, a hankali ta kai zaune zuciyarta na saka mata abubuwa kala daban daban, baban fargabarta kardai yayan mahaifin nata ya yarda ta koma gidansa, shin yaya makomar rayuwar biyu? Tsoro da fargaba irin ta uwa ke darsuwa a zuciyarta, tunaninta ya kafe ya tsaya a kan murmushi da dariyarsu da ta barsu sunna yi yanzu, idanfa ta koma kuka a gobe?
Baba Mai Shanu ya sauke ajiyar zuciya bayan ya hada abunda ya dace ta sani, ko ba komai ba zai saki baki ya yi ta yi mata bayanin abinda babanta ya fada ba, koda tana yarinya ba zata taba jin dadi ba, sam bai ga anfanin aikata hakan ba
Dan haka ya ce" Sharadinsa daya ne tak a kan maganar zamanki a wani wajen, shine ya kasance kuna daure da auren wani a kanki , ki tare a dakin mutumen"
Yanzun kam da sauri ta dago ta kalli Baba, dara daran idannuwanta masu dogayen gashin ido take ta kiftawa tana kallon Baba, sai kuma ta sake sada kanta
Baba na hankalce da dukkan yannayinta ya ce" Harma ya bamu adadin kwanakin da ya diba bisa adalcinsa cewa nan da sati daya tak, watau nan da kwana hudu, Amina idan baki manta ba na yi ramtsuwar cewa ba zaki koma gidan nan ba, ban sani ba ko ni zan yi ta yin azumin kafara? Ko kina da tsayaye ne?"
"Tsayaye?" Ta fada a hankali still tana kikifta ido tana kallon Baba
Baba ya gyada kansa ya ce" Kwarai kuwa tsayaye, wanda kika tsayar a matsayin mijin da zaki aura, wanda ke zuwa wajenki kika ji kin aminta da son aurensa"
Gaba daya sai ta afka a duniyar tunani, Aure? Ita? Nan da kwana hudu? Mutanen da suke tsayen da alamun sunna sonta biyu ta sani a duniya, Aban saudat da kuma Muktar, su din nan su ra sani a sanninta, sai dai bata karasa tunanin nan ba baba ya ce" Lauratu ta min maganar manema aurenki biyu, tun a washe garin da rigimar nan ta faru, Malan Liman ne da kansa ya tuntube su, su dukansu sunna da ra'ayin hakan, sai dai shi daya lokaci ya kure masa duda an nuna ba yanzu tarewa ba, dayan kuwa mahaifiyarsa ce ta yi karan tsaye kan lamarin, bayansu akoy wani ne?"
Yanzun kam da hannayenta take dan watsawa, naman gaban goshinta na cakudewa a birkice ta ce" Aa, dama, dama su kadai ne suka ce, suka ce zasu aureni koda da biyuna, suka ce sunna son biyu, bayansu babu kowa"
Dan murmushi ya subucewa baba, domin ko a yanzu baba cewa ta yi ba sai ya ji ra'ayin ko tana da wani ba kawai abinda ya yanke a zartar, shine yace da ita lalalala, ko daya ba zai so ace tana son wani ya katse hakan ba, ya fi so ace bata son kowa idan ya so su shirya kansu a gidansu
A tausashe ya dubeta ya ce " Amina, idan babu, shin kin yarda ni na zaba maki miji, mai nagarta, wanda zai kula da maraicinki, ya rike yan biyunki, da ke kanki? Ina nufin zaki amince ki yi min biyaya kuwa? Idan har bakya jin zaki iya yin hakan ba zan ga laifinki ba, zan je na fara daukan azumin rantsuwar tun gobe, na san zan jure, ulcern tawa ai zata yi hakuri na yi ibada kar tsoho ya mutu ya je da bashi a kansa"
Idannuwanta da suka cika da kwallah ta zuba masa, nazartarsa take yi , karara ta ga lalle da gaske yake, magangannun Baba suka fado zuciyarta, tsoro da fargaba suka shigeta, ta yi shiru ta rasa amsar badawa, hankalinta ya ringa neman karra tashi har sai da Baban ya kuma budar bakinsa a sanyaye ya ce" Amina, shin zaki iya yi min biyaya kuwa?"
So take ta tambaye shi waye zai zaba mata? Ko baba direba ne? Ko mai ba shukoki ruwa ne? Ko Usman dan albarka ne? So take ta ji ko wanene, ama girman kunya irin ta cikakiyar budurwa ya danne curiosity dinta, kanta na kallon kasa a hankali ta daga kanta, sai kuma ta bude muryarta bakinta na rawa ta ce" Baba, zai, zai kular min da biyu? Kar kar ya min irin na mijin mamansu, kar sai ka daura auren yace ba zai rike yayan wani ba"
Tausayinta zallah ya kama baba, ya kuma yi mata murmushi ya ce" Bari ki ji, bi izinillah zai rike biyu, ke da da hali harta tarkardunsu sai sun koma da sunnansa a kai, ni nan bani da haufi a kan haka, burina dama ki amince, domin na yanke hukuncin a gobe da yama zan daura aurenki bisa wasu abubuwa da suka bilo da take dokata da wace nake tunanin na isa da ita ta yi, ta manta cewa itace a kasana, *ITACE ZATA YI MIN LADABIHHH!*, dan tsufa ya kama ni, sannan na kasance mai son bata damarta na dan Adam mai daraja, har take son wulakantani da yi min bazawar sirri a kan abinda yake *MALAKINS?*, inada iko da dukkan *BAIWAR* da Allah ya bamu, bata san na fi mai rike da bulalar iko ba!, Tashi ki je Uman biyu, bana son kuka ko damuwa, ki shige dakinki ki yi alwallah ki fadawa Allah, yau Lauratu a wajenki zata kwana, Allah ya maki albarka"
Idan ta iya budar baki tace ufan to fa takalmintama da ta saka a jirge ta nufi motar ya yi godiya ko ya yi magana, tunda suka shiga motar kuwa kanta a sade yake bata iya dagowa ba har suka karasa ta kuma ficewa ta nufi falon
Tana budewa ta ga wasu mata biyu zaune sunna zantawa
Ido hudu suka yi da junna, hakan ya sa ta duka har kasa ta gaishe su sannan ta mike ta nufi ciki
Tana nan zaune Baba ta iso itama dakin ta zauna ta fuskanceta ta shiga tambayarta yaya maganar gyaran jiki?
Da mamaki ta kalli babar, gyaran jiki? Wani irin gyaran jiki? Na me? Lallema baba ta iya hade hade a rayuwa
Bata ce mata komai ba, dan ta san ta gama sannin komai, abinda ta so ta ji wanene a cikin ma'aikatan gidan? Dan a yanzuma da ta fito ta ga baba direba sai kallonta yake yi yana murmushi, ko dai shine? Ama ba zata iya tambayar ko babar ba, kunyarta take ji walahi
Alwallar ta dauro ta dawo ta shiga gabatar da sallar magariba , a kan salayar bata tashi ba har aka yi isha'i, kai na takaice a nan harta abincinta nan ya iskota ta dan tsakura ta rufe shi ta ajiye gefe domin burinta ta dauki azumi goben! Ko menene ke shirin tarban rayuwarta Allah ya sa alkhairi ne, ta kasa gaskatawa, ashe itama zata yi aure? Aure fa? Gobe gobe? Shikenan shi babanta bashi da ta cewa kennan? Idanma waye a bata? Anya Baba dan iya zai iya bada y'arsa haka?
Cire komai ta yi a ranta ta ci gaba da adu'arta
Masu jiran Baba kuwa kowa sai kama wajen kwonciya ya yi ya kwonta, domin bai shigo gidan bama bale su hadu da shi
___________________________________
Washe gari
Jirgin karfe tara ya sauka da shi a kasarsa ta haihuwa
Yana samun ntwrk din kasarsa ya shiga kiran numbar baba da layinsa na gida
Abin mamaki tana yin ringin aka daga, kuma muryar baban ce
A tausashe baba ya ce" Ga dukkan alamu ka sauka Baban mutun?"
Abdul Ra'uf ya sauke ajiyar zuciya jin muryarsa ram ya ce" What happened with u? Shin me yake faruwa ne? Ina Hajia?"
Baba ya ce " Tana gida"
Abdul Ra'uf ya ce" Kai kuma kana ina?"
Baba ya ce" Yanzun dai na fito daga kasuwa ni da Malan Liman siyan goro, mu hadu a gidan dan nima cen na nufa ai"
Yana gama fada ya katse kiran yana ta adu'ar da Liman ya karra bashi har suka karaso gida
Gannin motocin Abdul Ra'uf din ya tabatar masa cewa ya karaso, lalle ya zaku ya ga kakarsa yar rigima
Murmushi ya yi yana gyara babar rigarsa dake baza kanshin misk hannunsa rike wayarsa da kuma carbinsa ya doshi falon kansa tsaye
Yana shiga mutanen da ya gani sai da bin ya so bashi dariya, haka kuma irin yadda ake nuna jimamin ba'a ganshi ba ya sake bashi dariya, kamar ya bace din nan?
Shi dai da mutunci ya gaishe su, sannan ya karasa wajen abokinsa da ya sake zuwa da sasafe dan jin idan ya dawo gidan
Hannunda ya kama yana fadin" Mu je saman mana Elhaji, na san Abdullahi ya karaso ko?"
Du yadfa suka so dan fara dannarsa kowa sai ya yi shiru suka haura saman
Tun daga kofar dakin nata yake jiyo muryoyi na mata da kuma nata, ita tana magana da kuka ne, matan kuwa sunna irin abin nan na zigi zigi da nuna sam idan aka yi haka ai wulakanci ne da tozarci,
Hajia ta sake dubansa hannunta cikin nasa ta ce" Kar ka yarda Abdallah, ka tuna kana soyaya da yarinyar nan, yarinya yar gata gaba da baya, ga ilimin boko rututu a kanta, ga kyau ga kwalisa, aljannar duniya ce ita din, idan har ka yarda ya dauki y'ar fa ta gama yawace yawacenta kwararo kwararo ya aura maka ya cuceka, zai aura maka itane dan yana tausayinta, wai ita uman biyu, kulun tana tafe da yara sunna rike da hijabinta, bari ka ji ifan har ka aminta da haka ya wulakantar da girmanka da darajarka, da wahala Honorable ya yarda a makawa yarsa kishiya jahila!, Me take da shi na classssss? Me take iya yi na nuna halin girma? Zata bata sunnanka da nawa, kai ka ga duhun fatarta? Kar ka yarda da wannan hadin ka ji yarona?"
Shi kam abin gaba daya wani iri ya zo masa, kallon kakar tasa yake yi a tsanake yana nazartar abinda take son fadi, shi fa idan za'a yi masa bayani da hargagin nan ba ganewa yake yi ba, ga kawayenta sun ki su yi shiru kowace sai fada take yi,
A tausashe ya ce" Uma ku yi shiru mana daya ta yi magana, nu na kasa fahimta, aure ne za'a yi min?"
A kusan tare suka amsa shi da eh
Da mamaki yana jin murmushi zai subuce masa ya ce" To fah, sai kace yar budurwa? Shi mijin naki bai san ba an daina yayin auren dole ne ko ga yan mata?"
Hajia ta ce" magana nake maka ta gaskiya fa son, ba maganar wasa bace, nufinsa aure zai daura maka nan da kwana uku kennan yau!"
Ido ya dan zarro sai kuma ya dafe habarsa yana dan tunnani, a hankali ya ce" To yanzu kukan da kike yi a waya kika ce zaki mutu baki da lafiya ne? Jikin ne ya motsa?"
Wace yake kira da Uma ce ta karbe maganar da fadin" Aa abin ne ya daga mata hankali mana Gwamna, ni da kaina sai da na ji kamar hawan jinina zai tashi , ka kuwa san me hakan yake nufi? Tun jiya take kuka baiwar Allan nan, duba ka ga yau ko dan kwalin kirki ban daura ba na fito daga gida , soma na yi na kwana sai kuma dai na koma gidan"
Dan kwalin da tace ya bi da kallo, da magangannunta yana aunawa ya ce" Uma, kardai daga ke sai wannan abin na kanki kika fito?"
Uma ta ce" Eh kana gani dai son, ai a mota ne da kyar na iya yin barci jiya, kar ka yarda da auren nan kai kadai ka isa ka bijire masa!"
Mai Shanu da abikinsa, amininsa , datijon arziki da a jiya matar Mai Shanun ta rikita suka sake kallin junna
Mai shanu ya saki murmushi ya dan ja shi gefe ya ce" Yarinyar nan ta wajen mai gadina ce ake magana a kanta, ka san bata samu aure ba.........."
Gaba daya ya kwashe ya fada masa komai, ya dora da fadim" Shine Ni hauwau take neman tozartawa da tara kawaye ana yamadidi da korawa yarona bayani kan kar ya mik biyaya? Ashe basu da hankali? Ashe basu da kunya? Basu san sun girma ba? Kawunna cike da furfura basu gane a kusa suke da rami ba? Inace ba'a yi sati uku ba da daya daga cikinsu ta rasu , basu gane ana masu dauki daidaya ba suke neman izgili da lamarin ubangiji? Matan nan sunna da hankali kuwa?"
Shima da madaukakin mamaki da takaici ya ce" Dama abinda ya sa Hauwau tara jama'a tun jiya har yau kennan? Hasbunnalahu waniimal wakil, hauwaun haka ta zama? Kai kace karfe nawa daurin auren?"
Baba mai shanu ya ce" Shi dai uban yarinyar yace daga azahar har isha'i sunna sauraronmu
Baba Rabi'u zai yi magana sai ga Abdul Ra'uf ya fito daga dakin yana dan tare gaban goshinsa, fuskarsa dauke da murmushin rikicin kakarsa da kawayenta, to rikici mana, wannan maganar ta wuce a zauna a tatauna tsakaninsu su uku a kashe wutar a wuce wajen? Shine take kukan nan? Uhum shi yanzu baima san inda zai lalubo Docter Mansur ya zo ya dubata ba, ya ga du ta kode abinka da farin mutun ido ya jeme mata ba kwaliya wai ita ta shiga tashin hankali za'a yiwa gwamna aure, shi idan sunna kiransa da gwamnan kamar ya fashe da dariya walahi
Hannu ya fara mikawa Baba Rabi'u yana rage tsayinsa , sannan ya kalli Babab yana nazartar irin daure fuskar da ya yi ya ce" Ashe kana nan angin uley"
Sukan yi haka da junna , yace da shi na bar maka shima yace aa aa tasa ce, ama yau sai ba'a bashi amsa ba, hasalima Baba Rabi'u ne ya shiga yi masa nasihar da ta saka shi zubar da dukkan wani yannayi