Showing 132001 words to 135000 words out of 145392 words

Chapter 45 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8154

sake fadin" kins da kyau, jan ajin kuma ya amsheki Hajiar ABDUL"


Yanzuma baki ta dan tabe bata ce masa komai ba har yaa mike ya nufi ciki yana jin dan damuwa na rashin kulashin da take yi


A hankali ya zubawa HAJIA bayan ya bude ya mika mata sannan shima ya zauna a gefenta ya yi shiru yana sauraron hucin dake fita daga bakinta


A hankali Hajia ta sauke numfashi tana girgiza kanta ta ce" Ka san a duniya, babu wulakantace sai wanda ya wulakanta kansa ta hanyar daukan duniyar nan a wani abu mai dorewa, bayan tunda aka haifeka kake gannin jariri, yaro, saurayi, mai aure, uba, tsoho, mace ko namiji na mutuwa sunna zuwa wajen da ba'a katse rayuwar sai dai ka yi ta girban abinda ka shuka na dindindin, ama a haka muke manta komai muna aikata abubuwan da suka fi karfin kawunnanmua........"


ABDUL ya sake dubanta a hankali ya ce" Daj Adam din kennan, alkhairinsa ya kasance mai rokon gafarar ubangijinsa sannan ya tuba da gaskiya da daukar niyar ba zai kuma maimaita laifin da ya aikata ba"


Hajia ta gyada kanta tana sake sauke wani numfashin ta ce" Yanzu ace da furfurata, na wulakanta kaina har yarinyar bayana tana irin haka da ni? Gaba daya na manta darajata ta shekarun da Allah ya bani, na manta mutuncina , da girman darajar da Allah ya luluba min,na wulakanta marainiyar Allah,na wulakantata bata taka min ba, bata kashe min ba, du a kan son kai, gashi yanzu an zageni ko budar baki na kasa yi dan gaskiya aka fada min, a kan son kaina da rufewar idannuwana................"


Abdul ya sake fuskantarta bai ce komai ba yana kallonta


Hajia ta sake girgiza kanta ta ce" baka sani ba fa, ita fa siyarma du haka take, ka ga zamu hadu da yayan cikinmu, wasu mun yi jikoki da su mu yi ta abubuwa kamar ba zamu mutu ba, a yi ta iface iface da manyan da kananan, mu yi ta tsare tsaren yadda zamu samu mu ci kudade ko na waye, mu yi ta shiga hakin junna, uwa uba ABDUL RA'UF kulun bama koshi da abinda muke samu, kulun burinmi mu samu sama da abinda muka samu, ba ruwanmu da wa zai ritsa ko wa zai jigata, idan dai kawunnanmu suka wucewa jifa to ya fada kan kowama......, Abdul bama kaunar a rabamu da talaka, ba ruwanmu da talaka, mun manta mu menene tushenmu, da yawanmu sun rasa aurensu a haka, wasu a cikin haka sun rasu, wasu sun dimiya basa tuna komai irin Allah ya kyalesun nan..... Abdul yau nice na jawa kaina wulakanci irin haka? Wai a kan dan cikinka ake gannin bak dace na taba ba dan kawai na nunawa yarinya tsana? Bata min komai ba dan kawai bata kwaliya irin ta yan matan zamani, bata gwali da abubuwan yan matan zamani shikenan ni ga kakar Gwamna dole gwamna ya auro matar gwamna ko? A haka idona ya rufe na dauko yar mararsa kunya na hada a cikin ahalina, idan da haihuwa itama ta haifo ta kuma bada tarbiya irin wace ta damu a gidansu.........."




A hankali ya kama hannunta yana murzawa


A tausashe ya ce" Hajia ya isa haka kin ji? Ki kwontar da hankalinki, abinda ya faru ki kadara wani mataki ne na samun cenji a rayuwarki, ke mutun ce, baiwa ce ke, ba zai taba yiwuwa ki rayu ba laifi a rayuwa, baban laifi shine na daukan alhakin bawa, Allah baya yafe wannan, ki yi kokari ki gyara mu'amalarki da kowa, ki kokarta ki daidaita mu'amalarki da jama'a, ba wai Mom twins kadai ba, kowama, bama kamar Alkali, a kusa kusa ban ga namiji mai hakuri da iyalinsa irinsa ba, ki yi kokari ki gyara hakan, sauran du saura ne marar karfi, domin kamar yadda kika ce, dama kika bada har yau aka ci maki zarafi haka, idan ba wannan damar dole a mutuntaki, mutun dama shi yake fara mutunta kansa , sai ki ga ana mutunta shi, hakan kuwa ta yannayin mu'amalarsa da mutanen dake zagaye da shi ne........."


Hajia kai take gyadawa har ya dasa Aya


A hankali ta yi murmushi ta ce" Ban taba tunanin zan ji kunyar Amina ba a rayuwa irin na yau"


Shima murmushin ya yi ya ce" bata rike ki ba, koda ta ji haushi ba zata wulakantaki ba"


"Hakane, tanada hakuri sosai, ta jima tana bautawa mijina , ama ba abinda ke shiga tsakanina da ita sai mugwayan kalamai..........na yi dana sannin wasu halayana, kuma in sha Allah sai na gyara abinda zai gyaru idan har inada sauran numfashi a duniya" Hajia ta sake fada tana kallon ABDUL


ABDUL ya ce" Allah ya aminta"




A nan dai suka ci gaba da dan zantawa, harta da masu girki da komai sai da ta sanar masa ga yadda za'a yi, uwa uba kayan da Amina zata yi anfani da shi na sunna, a gangaro kan irin kular da za'ana badawa na uwar da ƴaƴanta baki daya, abubuwa dai wanda shi da kansa sai da ya samu kansa da yin murmushin jin dadin hakan a zuciyarsa,
Ya san Uman biyu zata dube shi, ya san zata amsa shi, ya san yanzun da bata son Aunty hakan na nufin tana iya amsarshi a matsayin miji, idan kuwa ba haka ba bai san yaya zasu kare rayuwa ba, tunda shi dai ya san ita din kaunarsa ce, zuciyarsa ce, soyayarsa ce, jarabawar da zata rabashi da ita mai zafi ce, baya fatan ganninta, kai da ba dan kar ace wani abin sai yace gwara ta mutuwa da ita, wace ya san ya bar duniyar ne kwata kwata da ya yi wani tunanin daban




___________________________________




A hankali aka ci gaba da samun baki, aja amsar baki tare da alkhairansu
Kwonci tashi har ranar sunna ta zagayo yara suka dauki sunnan iyayensa mahaifa , ama suke masu kiranye da Ammar da amna dan kare sunnan


Taro ne aka yi na mamaki, taron da ya tara al'uma masu yawa, masu dauke da position din rayuwa kala kala


ABDUL RA'UF mai mutane ne, matasa da datijai babu wanda babu, masu hannu da shunni da mu du gamunan, taron da ya yi niyar cenza sutura sau uku irin na Uman biyu, tun ta farko da ya saka bai sake zaunawa bama bale ya cenza
Yana waje tare da jama'arsa ana shan sunna


A cikin gida kuwa tunda Risala ta bar bangaren nan sai a yau wunnin biki ta fito, shima a zuwan mahaifinta fatiha ya sameta ya yi mata wankin baban bargo da fada mata gaskiya mai dacin gaske, ya fada mata cewa idan ta yi wasa tana iya yin biyu babu, gwara ta sauke kanta ta yi zumunci da uwar gidanta su zauna lafiya
A dole ta shirya kanta cikin rantsatsiyar shada da gwala gwalai da rantsatsen mayafi ta je ta samu kujera ta kame tana dan dane danenta da dan kallon abinda ke faruwa, taron cike yake da manyan mutane jama'ar hajia da na ABDUL, wai abin arzikin da ake shigewa da shi dakin da aka ware dan kar a rikita dakin mai jego du na wannan matar ne? A dole ranta ya ci gaba da kunna na rufewar ido sai da ta yi da gaske sannan ta hanna kanta kuka tana biye da motsin kowa
Gani take yi kowa ya tsaneta
Gani take yi kowa a bayan kishiyarta yake
Gani take yi kishiyarta ta asirce mijinsu da danginsa ne
Gani take yi ba banza ba, wannan abin ba banza ba
Ba zata iya amincewa cewa matar da aka yi auren hadi da itane take da wannan taron a kanta da soyayar dangin miji, ita matar da aka auro dan soyaya an maida ita gefe ace kuma lafia ne
Sai dai ita ba zata iya wulakanta kanta haka ba
Babu wanda zata lashi kafarsa dan ta samu fada walahi
Kuma bata san kofar boka ba
Haka kuma.malami ba zai ci kudinta dan a karya ba
Ita kam ta bari da Allah kawai!, A ci gaba da nuna mata fifikota bari da Allah kawai!




Alhamdulilah taro ya ci lafiya ya tashi lafiya, jama'a na nesa da na kusa kowa ya kama gabansa an bar ma'aikata da gyaran gidansu,


Tun karfe bakwai yau Amina ta kwonta
Yaren kansu bata tsaya nemansu ba , sunna wajen Baba lauratu da ta dora ruwan zafi zata gasa masu jiki, idan sun gama tace su goya su, kanta tarwatsewa zai yi tsabar gajiya da ciwo




A hankali ta kwonta saman lalausar shinfidarta tana jan abin rufarta ta maida shi gefe ta kurawa waje daya ido ta afka a duniyar tunani


A yau ta ga abubuwan da bata taba tunanin zata iya gani ba a rayuwa na arziki da kauna da kwonciyar hankali


Kuma duka sun tarun mata ne dan ABDUL DINTA!,


Dan murmushi ta yi tana juyowa da dan karfi dan ta gyara kwoncintsa, sai dai me? Ido hudun da suka yi da shi ya sakata dan zarro ido tana dan mikewa tana kallonsa ta ce"










A hankali ta dan gyara rigar barcin dake jikinta, mai hasken fari da mannewa a jiki tana dan son wara idannuwanta dake shanyewa dan kansu tamkar wace ke masu haka da gangan, muryarta a dan shake ta ce" Hi "


Idannuwansa ya lumshe, hannunsa daya a cikin aljihun wandon barcinsa irin budaden nan mai dan kauri mai ruwan blu , watau hasken sararin samaniya, sai rigar ciki singileti da kuma ta sama ta wandon wace bai balla boturan ba haka ya ratso al'uma ya taho , hannunsa daya kuwa a saman kirjinsa yana dan shafawa a hankali, yana son dauke yar damuwar dake tattare da shi wace bata wuce rikicin da suka yi daa Baba da Hajia kan maganar Amina, cewa Amina gida zata je ta yi wanka, wai gidan Baba, bayan shi yana niyyar fasa tasa tafiyar dan ya sake raya duniyarsu shi da ita da ƴaƴansu hudu? Shikenan sai a wani ce za'a tafi da ita?




Bakin nata da ta ce Hi, da amon muryarta ya nemi cenza tunaninsa


A hankali ya karasa inda take zaune, ta yi irin zaman nan da ake matsewa a cen saman gado, ta dan hade bayanta da jikin abin gadon , kafafuwanta kuwa ta dan dago su ta dora hannayenta samansu


A hankali ya haye gaba dayansa saman gadon ya yi zaune yana kallonta


Bai san a yadda zai fasarta lamarinta a tare da rayuwarsa ba
Tanada girma mai girman da girma bai isa ya kayade ba
Yana gannin mutuncinta, kimarta, da dumbin soyayarta a zuciyarsa
Bai taba tunanin zai samu wannan jarabawa a kan Amina ba


A hankali ya kamo hannunta ya sakaa cikin nasa, sannan ya shiga murzawa kadan kadan yana kallonta, muryarsa a ciki ciki ya ce" Ba zan iya barinki ki tafi ba "


Amina ta bude lumsasun idannuwanta ta zuba masa su, ba zai iya barinta ta tafi ina ba? Ina yake tunanin zata tafi? Hala a tunanin ABDUL tana kan bakanta na neman saki? Lolz lalle




Iska ya furzar daga bakinsa mai zafi ya ce" Shi wankan, a nanma ba sai ki yi ba? Idanma babu mai maki ba gani ba?"


Sai a yanzu ta dago zancen, kuma sai abin ya bata kunya
A hankali ta dan cicira idannuwanta gefe na alamun kunyar, wanda tsaf ya karanceta bar ya samu kansa da sakin murmushi, domin dama yana tunanin gannin haka daga gareta, Aminansa ba dai kunya ba


Ni tuni na ce masu ba zaki tafi ba, suka ce sai kin je, shi wancen Alkalin harda fadin da kansa zai zo ku tafi sai kin yi wankan jego a gabansa, baya ciki da cin amana.....Wifey Ni ai ba dan cin amana bane ko?"


Ya salam, gaba daya nema yake ya cenza duniyarta da dukkan wani tunaninta


A hankali ta janye hannunta taana kallonsa da lumsasun idannuwanta ta ce" Yanzu zamu tafi ko gobe?"


Shiru ya yi sshima yana kallonta, sai kuma ya budi bakinsa a hankali ya ce" Binsu zaki yi?"


Da idannuwanta ta bashi amsa tana masu luuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu sannan ta dage su


Jajayen lebunnansa ya dan cije yana kallonta ya ce" Tafia zaki yi ki barni ni kadai?"


A hankali ta dan sake matsawa dan matsota yake yi kasa kasa ta ce" Dama ai ba tare da ni kake ba, ko na tafi ba kai kadai bane"


"Meenart" ya fada aa hankali yana katseta


Amina ta sake bude idannuwanta aa hankali ta ce" Aban Amnahhhhhhhh"


Abinda zai fada ya samu kansa da mantawa har ya dan daburce, wannan ne karron farko da ta budi baki ta ce masa Aban Amnahhhhhh, ba ABDUL ba ko kai ka bari fa
Murmushi ya dan saki a hankali ya ce" Bakya tausaya min ko?"


Baki ta dan tabe, sai kuma ta dannawa gefe harara kasa kasa ta ce" Aban Amnah kai ka tausaya min ne?"


Ido ya zarro har yana dafe habarsa , da madaukakin mamaki ya ce" Lah hararata kika yi?"


Amina ta bude idannuwanta tarr tana kallonsa, ta turo bakinta hadi da shagwabe fuskarta ta ce" Ni aa, gefe na harara fa"


"Umum um um Uman twins da ni kike " ya fada yana sake matse mata waje


Amina ta dire kasa hakan ya bayanar da iya tsayin rigar barcin nata da kwata kwata duwawunta kadai ta dan dara
A hankali ta duka tana bashi baya ta dauki takalminta na kusan bed ba dan sai ta yi haka zata saka ba, aa , kawai hakanan ta yi hakan har tana wani irin dan girgiza ta saka takalmin sannan ta mike ta dan gantsare tana yin hammar da ba ta gaskiya ba sai kuma ta janye ribom dinta ta dan girgiza kanta kadan, hakan ya sa gashin kan nata bajewa ya dan watsu gefe da gefe sannan cikin tafiyar izgili ta nufi bayi kasa kasa tana fadin" ABAn Fadeel, bana ciki da rigima, kawai Allah ya bamu alkhairi, yo Allah na tuba yau ka fara cin amana kuwa, ka je kawai wajen dayar na san tana cen tana kyarkyara" da gangan da zata ce kyarkyarar har sai da ta kama kofar bayi ta juya duwawunta son ranta sannan ta shige ta datse kofar tana zarro ido hadi da dafe kirjinta dake dokawar tsoro ta rufe idannuwanta da hannayenta biyu wata mahaukaciyar kunya na son halakata ta rufe bakinta dan kar ta kurma ihun kunyar da ta rufeta




"Dady?, Dady?" Muryar Husaini da ya shigo yiwa mamansa sai da safe ya yi ta salama shiru ba'a amsa ba sai da ya karaso ya taba gefen hannun babansu da ya tarar a zaune tamkar matacen mutun ya kurawa kofar bayi ido ko kiftawa baya yi ya ringa ambaton sunnansa ama shiru, dan haka ya dafa shi yana sake kiran sunnan da karfi


Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, a zabure ya kalli Husaini, sai kuma lokaci daya ya kalli jikinsa


Cikin dabara ya dora kafa daya kan daya yana kallon Husaini muryarsa a cen kurya ya ce" Son, ?"


Husaini ya sake kallonsa a hankalin sshima ya ce" Dady baka da lafiya ne?"


ABDUL ya dan fitar da idannuwansa irin bai san me yasa ya ce haka ba ya ce" Rashin lafiya? Me ya sa kace banida lafiys?"


Husaini ya shafo gaban goshinsa da zufa ke tsatsafowa ya ce" Dady kalli fa goshinka?"


ABDUL ya ringa sauke ajiyar zuciya a boye cikin dabara ya kakaro murmushi ya ce" No lafiyata kalau Boy, wai mema kake so?" Ya karashe yana dage masa gira daya


Husaini ya yi murmushi yana kallon gashin girar babn nasu kamar wanda ke gyaran gira, ga cika gaa tsari ya ce" Mama ne ni ban mata good night ba, shine na zo"


ABDUL ya yi murmushi ya shafa kansa yana fadin" Mamanka tanaa bayi, zan sanar mata ka tafi ka kwonta saboda school fa gobe"


Husaini ya gyada kansa ya juya yana masa byby


A hankali ABDUL ya yi masa by din shima sannan ya sake maido dubansa kan kofar


Mikewa ya yi ya karasa ya kama abin budewa ya murda, ama a garkame ta rufe ruf




A hankali ya dora hannunsa saman kofar ya dan shafa kofar yana sauraron ciki ko zai ji motsi, ama baya jin komai


Wata ajiyar zuciyar ya sauke kasa kasa ya ce" Na san kina jina............."


Amina dake like da kofar tana jinsa ta sake lumshe idannuwanta tana sauraronsa, domin bata iya motsawa daga jikin kofar ba tana jin maganarsa da Husaini


ABDUL ya sake sauke numfashi a hankali ya ce" I'm sorry, plz ki yafe min kin ji?"


Amina ta sake lumshe idannuwanta tana dafe gaban kirjinta dake doka mata


A hankali ya ci gabaa da fadin" Ni ban taba rainaki ba a matsayinki ko nasabarki, u seee ko da na ga kece aka bani na yi niyar idan aka zauna aka tatauna zan ga na yi abinda ya dace a lamarinki.............."


Ya sake dan cije bakinsa ya ce" Meenart a namiji ko mace babu wadda ya taba min ihu ban dauki mataki a kansa ba, haka kika min son ranki a ranar ina ciwon kai, ama na kasa kwakwaran motsi sai dai kallonki.............."




ABDUL ya dan dafe gaban goshinsa ya dora da fadin" A lokacin, ba maganar so, kyau, ko halitar jikinki ta sakani kafeki da ido ba, kawai haka na samu kaina da yi har kika gaji kika yi tafiyarki.....................u know kin takani sosai fa Madame"


A hankali ta ringa bude idannuwanta kamar yana gabanta , ta samu kanta da yin dan murmushi still tana sauraronsa


Ya ci gaba da fadin " Ko da maganar tsoron Hajia, ko ba so, Ko ba jin kunyar ido, ko ba jin nauyi , ya dace ki tausaya min, a lokacin na jima ina jan farin cikina na samun cikinki sai kawai kika ce ke ba sona kike yi ba, ke a zubar da cikina dake jikinki?.......kin kuwa san matsayin girman kalaman nan..................
Amina sun raunata ni, sun jigata ni, ba dan a lokacin kika fara nuna min baki zo dan zama da ni ba......no dan a lokacin kin fadi abinda ke cikin zuciyarki ne da dukkan gaskiyarki.........."


Amina ta zubawa kofar ido tana jin wani irin abu kamar tuhumar kanta, kamar zata ji haushin kanta


ABDUL ya ce" Tell me, idan kece ba zaki bani space ta yadda zan duba na gani idan zan iya rayuwa da ke ko akasinsa ba? Na tabata a yadda meenart kike da zuciyarnan kin barni har abada!"


Amina ta sake turo baki tana dan kai kawo tana sauraronsa


Ya ce" A haka na ringa naci , du dare sai na leko na tsotsi dan abubuwan tsotsa na dan shafa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login