Showing 84001 words to 87000 words out of 145392 words
Chapter 29 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
sun fi karfin kowama? Ciki harda shakikan nasu? Dama maganar ce muka ga ya dace a kawota gaban wace ta isa da shi , shine muka zo "
Hajia ta koma saman kujerar tana sake buga masa waya, sau hudu kennan bai daga ba a ranta tana ayana' ramawa kake yi ko?'
A hankali ta yi salama a lokacin da ya daga, sannan ta saurara har ya amsa mata a nutse
Hajia ta ce" Zan zo gidan ne, ina fata baka fita ba"
ABDUL da dawowarsa kennan daga kampani ya dawo ya dan huta ne ya fita gonaki domin tunda duku dukun ya fita ya je Kampanin ya amsa hajia cewa yana gida
Bata ce komai ba ta kashe ta juya ta fuskance su ta mike tana kallon Hajia Umma da izar hajiar ke birgewa kamar ace itace ta ce" Uma zamu je, ta yiwu daga cen na wuce gida ko na dawo yadda hali ya bada"
Umma ta mike tana yi masu Rakiya, Hajia ta shige motarta direbanta ya ja , suma suka shiga tasu Maman Risala sai masifa take yiwa yayarta da yaren turanci kamar zata ari baki ta ja masu motar suka bi bayan ta Hajia
Tunda Hajiar tace masa gatanan dama ya gane ba lafiya ba, shi yasa ya kimtsa kansa ya dawo falonsa na kasa ya zauna yana jin kamar hayakin Turaran wutar da aka saka ya dan yi yawa, ko kuwa dan ya fito daga cikin kura ne ya shaki kurar da yawa? Ga kayan karinsa saman table ko tabasu bai yi ba suka karaso
Tunda suka zauna ya gaishe da wa'inda ya dace ace ya gaishe da su ya dan kalli Risala sau daya ya dauke dubansa ya maida kan kakarsa dake cicin magani ita a dole fushi take yi da shi
A hade Hajia ta ce" Meye gaskiyar maganar da matarka ta fada?"
ABDUL ya sake fuskantar Hajia yana rage sanyin ACn domin sanyin ya yi yawa sosai a nutse ya ce" Dangane da me fa?"
Hajia ta dube shi, ta dubi Risala ta ga sai sake sinne kai take, ta sake dubansa tana tunanin ta inda ya dace ace ta yi bayanin ta ce" Kan maganar tarewarta"
ABDUL ya lumshe idannuwansa yana komawa saman kujerar gaba dayansa yana jin nauyi da kunya na son kama shi dangane da maganar, sake dagowa ya yi idannuwansu suka sarke da matarsa, yar budurwar matar da ya dauko wace a tunaninsa ko wata ya yi bai taba hannunta ba zata yi kawaici har sai abin ya zarce misali, sai gashi a kan kishi ne ko wauta ce, ko sabo da yi ne ya saka har ta fitar da maganar cikin gidansa a jiya tsal zuwa yau?
A dake yana dan fara cenza yannayinsa ya ce" Gaskiyar kennan"
Daga Hajiar, har iyayen na Risala sai da suka zuba masa ido
Hajia ta dan so daburcewa, sai dai ba zata yarda da haka ba, komai hardewar fuskarsa gaskiya ce ta zo sanar masa sai ta fada
Da kuka ta ce" A kan me zaka dauki kwanakin wata ka ba wata bayan ita ta rigayi dayar shigowa gidan nan?"
A dakensa ya ce" Dan aka hukuncin yake, ke kin san Uman biyu ta rigayeta tarewa...............kuma an rigayi daura aurenta a kan na Risala"
Ido Hajia ta shiga kiftawa, watau ABDUL dan rashin kunya yana so ya nuna mata cewa ita ta dan ya kwonta da uman biyu ko me?
Mahaifiyar Risala ta ce" Ka yi hakuri Abdul, ai ba haka tsarin yake ba, inaga ya dace ka bi gaskiya dan gudun wasu fitintinnun, inm ba abinka ba ina kai ina tsohuwar macen da ta girmeka nesa ba kusa ba?, Sannan matar nan harda ya'ya menene abin bata har sati guda fisabililahi?"
ABDUL ya sake jinginar da bayansa yana dan ciciza lebensa a lokacin da yayar mahaifiyar matarsa ke fadin" Ai abin ba wani bane son kai ne irin nata, ita tana gannin ai idan ta gaskiyar za'a bi bata da riba, shi yasa zata fara hada shi da bokaye da sauransu da kuma kirsa irin ta tsohuwar mace, Allah ya sa Risala ba marainiya bace tanada iyayenta zasu tsaya mata, na san an jima ana sonka dama ana dabonka yanzu da aka samu za'a yi aiki irin na zalunci, ina anfanin haka?"
"Bata SONA fa" ya fada a hankali yana duban agogon dake hannunsa
Ya sake dagowa gannin kowace ta masa tsuru tsuru tana kallonsa
Murmushi ya yi ya ce" Ita soma take yi na saketa, ko jiya sai da tace na saketa ta koma gidansu......ina nazari ne a kan abinda ya dace, tunda kun ga ai AMINA MARAINIYA CE, ina matukar kwadayin samun ladan rikon Marainiya da marainun ƴaƴanta "
Hajia kamar ta kurma ihu, idannuwanta kamar ta ciro su ta lika masa haka take ji
Maman Risala takaici kamar zata hadiyi zuciya ta ce" Ta yaya zaka ringa maganar cewa bata sonka? Idan ka saketa ba sai ta shiga uku ba a duniya gaba daya?, Ai ana yi maka haka ne dan kara damkeka a bar yar yarinya karama da ciwon zuciya na wulakancin d'a namiji, tunda tana so ka saketa ka saketa mana, babar banza kawai"
ABDUL ya fuskanceta, a nutse ya ce" Hajia, itafa du yadda ake dan hasashe a kanta bama haka bane, twinsma ai na kanwarta ne, ita dinma yarinya ce karama fa sosai, kuma maganar bata sona da gaske ne, bata da ra'ayin zaman itama"
Hajia da kyar ta iya budar bakinta da rarashi dan ta fara yarda da maganar yayar maman Risala cewa an hada danta da malamai, in ba malamai ba fisabililahi ina bakin ABDUL ina kiran Amina da yarinya karama? Yace wai bata sonsa kuma har yanzu bai rabu da ita ba? Ai an gama da jikanta tana wasa da yawon siyasa
A hankali ta ce " SON, ka saketan mana?"
Risala ta gyada kai da sauri ta ce" Eh, dan Allah ka saketa mana?"
ABDUL ya ringa kallonsu daya bayan daya yana tunanin anya sunna da adalci kuwa?
A tausashe ya dubi Hajia ya ce" Idan na saketa yaya zaki yi da Alkali?"
Hajia ta kalle shi tana kure shi da duba ta ce" Kamar yaya, ni kuma ? Kai dai"
Murmushi ya yi yana kowama ya zauna da kyau, a nutse ya ce" Zan so ace, ko menene tsakanina da su dukansu, mu iya zama mu sasanta mu fuskanci junna, zan so ace idan na dora doka a gidana koda ta son rai ce ba wai ta gaskiyar da ake son takewa dan wasu dalilai daban ba a zauna da ni da iyalina mu yi maganar mu sasanta komai........."
Ya saurara , ya kausasa muryarsa sosai ya sake dubansu ya ce" Da wahala na iya daukan jeka ka dawo ga kuma kasuwa da jama'a, sam a cikin neman na abinci wanda dole sai da shi za'a rayu , da wace ya dace ace ta zamto wajen hutuna wajen nutsuwata, wajen da na fi komai farin cikin zama mu zanta ko mu yi shiru a waje daya.....uwa uba wajen da.........."
Ya dauke maganarsa yana dan murza hancinsa kadan ya ce" Wajen da nake da ikon ajiye hudu, koda wa'inda ke nan mun kasa zaunuwa ba dan na kasance mai sake sake ba, sai dan ba zan iya jurar RAINI ta WATA FUSKAR ba!, Su zamto hargitsina, kwonciyar hankalina ba, .............kwarai zan so ya zamto na farko hakan, kuma na karshe, ba dan raini ba, ba dan na raina manyana ba, sai dan gudun abon rainin ya shiga tsakani....domin farawar hakan tsakiyarsa cin mutunci ne, karshensa kuwa bakin ciki............."
Yana dire ayarsa ya sake bude idannuwansa ya zuba a cikin idannuwan mutane hudun nan da kowace girman nata idon ya fi gurbinsa dan kowace da irin fasarar da ta ba maganarsa a dunkule, kowace da irin abinda ya shiga kwakwaluwar a maganar jikam Hajia
Maman Risala da mamaki ranta bace ta ce"
*NZL PAGE3️⃣4️⃣*
Maman Risala da mamaki ta ce" ABDUL, yanzu a kan wacen matar ne zaka sakamu a gabaa ka nemi rainamu har ka nuna kana iya rabuwa da RISALA yau daya kwana daya?"
A zabure Risala ta kalli Uwar hankakinta tashe ta ce" Mama sakina kuma?"
Abdul ya sake sauke ajiyar zuciya ya mike gaba daya bai kuma cewa dayansu ufan ba , ciki harda kakarsaa ya haye sama
Mikewa Hajia ta yi harta jakarta da wayarta ta bari a nan ta shiga binsa saman da dan sauri, inda gaba daya suka rakata da kallo
Yana shiga tana shigowa ta bude kofar da karfi ta jiga ta kamo shi ta juyo da shi yana dubanta a rikice ta ce" ABDUL, yau ni zaka wulakanta? Abdul ni zaka watsawa kasa a ido a cikin mutane ka wulakantani?"
Abdul ya ja numfashi a hankali ya kama hannunta ya nufi bakin gadonsa da ita ya zaunar da ita, sannan ya tsuguna a kusa da ita kadan yana dubanta a nutse ya ce" Hajia, me yake faruwa ne? Me yake damunki ne haka?"
Hajia ta ce" Ni za'a tambaya abinda yake damuna ko kai Abdul? Kai za'a tambaya abinda yake damunka da har ya rufe maja ido haka"
ABDUL ya yi shiru kadan, sai ya sake riko hannunta yana dubanta ya ce" Menene abin daga hankali acikin abinda Allah ya hukunta?, Du da ake wannan rigimar idan Allah ya yi sai mun zauna zaunawar fa zamu yi, idan kuwa Allah bai yi ba muna kallo sai dai mu yi hakuri fa Hajia"
"Dama kanada niyar zama da ita ne Abdallah? Dama kana soyaya da ita ne?, Dama ka jima da sanninta ne ko menene? Abdallah ta girmeka fa?" Hajia ta fada tana tarar numfashinsa
A hankali ya ce" Hajia , halal ne, kuma sunna ce mai girma wace Ma'aiki ya raya SAW, ita shekara daya ce tsakanina da ita wace idan za'a zauna a duba yarintarta sai ace na bata shekara takwas ko goma a haife............, Hajia shekarunta be matsalar ko mene?" Ya idasa a sanyaye yana kallon Hajiar............
Hajia ta ce" Magana kake yi a kan shekarunta kadai?, Kosai fa take saidawa, kwararo kwararo tana yawo da yayanta da kake cewa wai ba nata bane"
"She's virgin Hajia" ya fada kasa kasa sosai wanda hakan ya saka su dukansu yin shiru kamar an yi ruwa a dauke, domin shi din da kansa ya zame masa dole ne fadin hakan, ita kuma hajiar wata irin kunya da nauyi ne suka zo lulubeta, gaba daya ta rasa kallonsa zata yi ko sada kanta zata yi kamar tana gaban sirikanta?
Dan tarin karfi da yaji ya yi kadan yana cire nauyin da ya tsaye masa a gaban idannuwansa a sanyaye ya ce" Kin san cewa ba kyau tsananta kiyaya ko soyaya ko?, Kuma kin sani wannan hadi na Alkali ne.........a kan haka kin ga irin fushin da Alkali yake yi da ke ko?"
Hajia ta lumshe idannuwanta ta ce " ABDUL, sam ita din ba tsarinka bace, shin ka manta burina ka tsaya a takarar gwamna a sabon zabe ne?, Ka san me ake so a matsayin matar gwamna uwar gida, nifa ba wai wani damuwata Risala ko iyayenta ba, no, ni damuwata kai, ina wannan yarinyar ina amsa kiran sunnan matarka a gaban manyan mutane?"
Murmushi ya yi a hankali ya ce" Ki kwontar da hankalinki, in sha Allah lokaci zai nuna mana komai Hajia"
"Ni so nake ka salameta" hajia ta sake nanatawa, wanda hakan ya sake bashi mamakinta, bai taba sannin haka Hajiarsa take ba gaskiya
Murmushi ya yi bai ce komai ba, har Hajia ta gama saukowa, domin shi ya san hanyoyin sauko da ita koda tana cikin fushi ne, a nan ya yi mata abinda ta fi kauna watau ya tura mata ƴaƴan banki yana fadin" Ina so a koma gida yanzun daga nan.....Hajia, ina mamakin irin yadda har yanzu kike yarda wasu na shiga tsakaninki da Alkali, bayan kin fi kowa sannin wanene shi"
Shiru ne ya biyo baya mai dauke da tunani kala daban daban daga Hajiar har shi din
Cen ta mike tana yi masa salama ta sauka
A lokacin da ta sauko basa nan gaba dayansu dan haka itama bata tsaya nemansu ba ta fice da gagawa ta shige mota aka nufi gidanta da ita
ABDUL kuwa wayoyinsa ya kashe gaba daya ya kwonta dan hutawa
__________________________________
Kwanaki uku da suka biyo baya ABDUL bai kuma komawa dakin Amina da nufin tabata ko kwonciya yin barci tare da ita ba
Hakan da ya yi sai ya samar mata nutsuwa da ragewar faduwar gaba har ta zo ciwonta ya fara yadda zare dan haka ta shiga gasashi sosai har yanzu ya zamto ta saka Baba turo mata Asma'u dan su gama gyaranta sannan tace biyunma su fara zuwa ta yimasu nasu zata iya
A bangaren ABDUL kuwa wata irin shakuwa ce ta shiga tsakaninsa da Biyu, a yanzu haka a cikin tractation din cenza masu makaranta yake , ama bai sanar mata ba, domin makarantar tasu gaba daya bata yi masa ba, ba dan tana makarantar gwamnati ba, aa, dan matsalolin da ake fuskanta na irin bambance bambance karara ba tsawatarwa ya saka shi neman takardunsu da komai ya rubuta su a wata babar makaranta ta ƴaƴan manya, yanzu haka lesson da aka ce sai an masu na wata daya kafin su ci gaba da cen din ne ya dan dakattar da su, idan aka dauke su akan mikasu wajen lesson din ne da kayansu na makarantarsu a dawo da su gida, ko a wuce da su gidan gona su sha kiwo da Baba, ko a tafi da su Kampani a sake su, su sha yawo da ciye ciyen kwalam da makulashe ana dubansu ta camera ana gannin mouvement dinsu da komai ciki harda ma'aikaciyar da ta kirayi husaini barawo, sai dai ta ringa binsu da kallo bata da bakin magana, domin a lokacin da ya zo da su sakon da ya bada a fadawa duk wani mai ruwa da tsaki a wajen a matsayin mahaukaci cewa ya kula tikiten karshen shan ruwansa a kampanin ke yawo a kusa da shi, dalilin wannan suka zama yan gata a wajen ma'aikatan, da masu yi dan kar a kore su, da masu yi domin Allah
ABDUL ya tatara du wani abu dake iya zamowa damuwa ya ajiye shi gefe, duda abin damuwar ya kula shigarsa ne yake yi da karfi da yaji koda baya so, ba wai shawararsa yake nema ba, a tsakakanin iyalinsa yakan ji bugun zuciya mai tsanani na yawo da shi
Ya bata fili, ya bata damar da zata yi mu'amalarta da dan kai kawonta yadda take so, idan ya shiga sun hadu da farko takan daure fuska tamau ta nemi rurufe jikinta, shi kuwa sai ya yi mata murmushi ya kireta da AUNTYNA sannan ya tambayeta idan ta tashi lafiya? Hakan ke sakata rakashi da kallo har sai ta tuna wa ta bi da kallo sai ta cire dubanta tana tura lebenta da tunanin yanzu haka da yace mata Aunty ba har zuciyarsa ba.........sosai take so su zauna ta amshi takardarta, ama du idan ya shigo sai ta ji bara dai gobe ta masa zancen har ta cike kwana biyar cif a matsayin mace cikakiyarta a karkashin ikonsa ya zamto yai zata fara gyare gyarenta bayan ta dan yawata a gidan da yamaci tare da Baba sun samu wajen da ya dace ace ta fara din Baba Ta fuskanceta ta ce" AMINA ya dace ki ga ABDUL RA'UF ki sanar masa da maganar nemanki, kafin ki fara, domin yanada yancin sani a yanzu da yake mijinki......"
Wannan magana ta tsaye mata a kahon zuci har yanzu da take kan murjewa Asma'u gyaran da ta yi mata tana tunawa
Sunma gamawa ta rako Asma'u har bakin get, daidai an wangale get din motoci har biyar suka shigo
Daga ita har Asmaun raka motocin suka yi da ido har suka kulewa ganninsu , Asma'u ta gyada kai tana yi mata salama ta tafi
A sanyaye Amina ke nufar Bangarenta ba tare da ta kalli kowa ba
A hankali tafiyar taya ta fara yin nauyi sakamakon jin kamar ana kallonta
Da dabara ta dago dubanta ta sauke a wajen da ta fi kyautata zaton a nan ne ake kallon nata
Tsaye yake kikam Hannayensa duka biyu zube cikin aljihun wandonsa yana kallonta da kallon da ya saka gaba daya ta tsargu da kanta
A hankali ta cire idannuwanta daga kansa ta sake daga kafarta ta yi taku biyu ta ji ta kasa yin na uku, a dole ta sake dakatawa ta juyo gaba dayanta ta tsaya tana kallonsan itama
Rabonsu da su yi irin kallon nan gaskiya har ta manta
A hankali ta nufo inda yake tsayen, hakan ya saka shi dan sake waigawa dan gannin idan umarnin da ya ba garadansa sun tafin ko sunna nan, sannan ya sake zubawa Uman biyu ido har ta karaso inda yake tsaye ta ja ta tsaya tana harde hannayenta biyu a saman doguwar rigarta wace ta dan lafe kadan a jikinta ta dan bi shap din jikinta kadan ta matukar kayatar da halitar jikinta
Kanta ta dan langwabe ciki ciki ta ce" Hi"
Fuskarta ya zubawa ido da yadda ta yin, kamar in Husaini na son abu yake yin haka, Hasan dama shi halayansa kamar na wani baba ne
A hankali ya dan matso kusa da ita, ta yadda sosai ya sake kerewa tsayinta yana kallonta cem ciki ya ce" Yanzu fa kin girma......ina hijab dinki?"
Idannuwa ta wara, sai kuma ta kausasasu tana kallonsa ta ce" Me yasa idan kana yiwa manya magana baka tausasawa?"
Murmushin gefen baki ya yi kadan ya zuba mata tsaurarun idannuwansa a kanta a hankali ya ce" Kin tabata kin warke?"
Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi......, A hankali ta dan cire idannuwanta a cikin nasa kasa kasa ta ce" Hala murna kake ji dan ka ci zalina?"
Kansa ya girgiza yana kallon yadda ta turo bakin ita a doke amsa take so
Baki ta karra turowa tana kawar da kanta ta ce" Baba Lauratu ce tace nace maka wai, wai ina yin sana'ar gyaran amare, zasunna zuwa nan ina yi masu kafin mu tashi daga nan"
Baki ya tabe ya ce" Tashi zamu yi daga nan din Aunty?"
Har sai da ta kama habarta ta ce" Kai, harda kai kuma?"
Ya dage kafadunsa irin ya sani?, Sai kuma ya ce" Ba damuwa, ama idan muka zauna na ji million nawa ake baki dan