Showing 117001 words to 120000 words out of 145392 words
Chapter 40 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ido,da tambayar kanta shin a amso mata ky din ne?
Zuciyarta na zumudin a amso, wata na gargadinta
A hankali ta girgiza kai ta juya tana sake maimaita sunnan wajen a cikin zuciyarta ta koma cen bangarensu
Tun daga nesa ta hango Risala ta yiwa wata cencadediyar budurwa rakiya, hakan ya sa ta dan rage tafiyarta gar suka gama matar ta shige motarta ta tafi, ita kuma ta juya ta nufi nata bangaren
A hankali ta dauke dubanta a kanta, dan da farko ido ta dan zuba mata sannan ta shige bangarenta
Sai bayan magariba Baba ta tafi, watau sai da ta yi jira ABDUL ya dawo ta samu ganninsa da kanta ta sanar masa komai, domin ita kam ba za'a yi haka da ita ba walahi, yadda yaron nan ke mutuntasu ba zata kasance cikin shiritar Amina ba
Ai kuwa, halayansa na girma ne ya gabatar
A yadda ya dauki abin da irin yadda ya yi maganar sai da ta ji kamar ta fasa kukan dadi
Bayan sun gama maganar duka kaf abinda za'a yi wanda sai da kyar ya yarfa aka dan rage ya fuskanci Baba a nutse ya ce" Baba, dama a kan maganar Firdausin nake son mu zauna da ke, sai gashi yau kin zo"
Baba ta gyara zamanta a saman kujerar falonsa da ya yi ya yi da kyar ta zauna , domin da farko a kasa ta so zama gannin yana sama, ama firr ya nuna shima ai kasan zai sauka idan har ta sauka
A hankali ya ce " Kasancewar ba takaba bace take yi, tana da damar fita, shine nake son sannin a fannin makarantar boko da ta islamiya a daidai ina ta tsaya? Domin ina so ta je ta ci gaba da karatu dan ta karra warwarewa ta manta komai"
Sai da idannuwan Baba suka cika da kwallah, harda tarin jin kunyarsa tana sake sada kanta kamar shine baban , itace karamar ta ce" Oh, Elhaji da wannan wahala haka, Allah ubangiji ya saka da alkhairi, yadda kake talafin marayun nan kaima Allah ya dubeka ya ji kanka, ya kareka a duk inda kake, Allah ua saka maka da mafificin alkhairi ka ji? Allah dai ya karra rufa asiri sannan Allah ya shiryi Uman biyu ku yi zamanki lafiya lau"
Da farko shiru ya dan yi, sai kuma ya sadda kansa a hankali ya furta" Amen summa amen"
Baba ta sake fadin" A yi ta hakuri, a yi ta hakuro, ka san mace da namiji yannayin hankalin ba daya ba, a dauka yarinta ce da kuma hankali irin namu na mata, a yi ta hakuri da komai dan Allah"
Yanzuma kasa kasa ya amsa da" In sha Allah " yana lumshe idannuwansa sannan ya sake bata damar yin magana
Baba ta ce" To dai, a sanina ita Fido karatun nata sam bai yi wani nisa ba, dama Aminar itace mai nacin makaranta ko a lokacin da ran marigaya, ita Firdausi ta taso da irin gyare gyaren nan dai irin na Aminar, sai kuma son koyon aiyuka irin na hannu da burin kasancewa babar mai girke girke na zamani , dan takan ce idan ta samu haki zata je ta biya ta koya ta bude wajen siyarwa, to ama duka wannan yanzu ban san yayane ba, ina iya zuwa na kirawota sai ku tatauna lamarin"
Zai ba Baba Amsa Risala ta shigo ta sha wata mahaukaciyar kwaliya sai baza kanshi take ta ko'ina da salamarta sannan hannayenta dauke da wani faranti mai shegen kyau da jug mai dauke da jus mai haske ta yiwuma na aya ne ya sha hadi
Kansa ya cire bayan ya amsa salamarta a nutse ya dubi Baba dake gaisheta ita kuma tana amsawa ya ce" Baba?,"
Baba ta dube shi
Ya ce" Aa ba sai kin kirawota ba, in sha Allah zamu yi maganar idan na leka su"
Baba ta amsa ta mike tana karra risinawa tana yin godiya ta fice a falon tana karra kallon Risala da kwaliyarta
Falon Amina ta koma da salamarta
Daidai Amina na kora ruwa masu sanyi a cikinta tana lumshe ido dan dadin da take ji na koshin da ta yi ta ce" Uhum, mata na kwaliya a duniya"
Amina ta dubi Baba tana fadin" Sosai fa Baba, wata amarya ba kika gano ko me?"
Baba ta ce" Hakkun, ai amaryar Elhaji ce kar ki so ki ga kwaliya kamar aljana a kyau, sai baza kanshi take"
Daga ita har Firdausi sai da suka dago sunna kallonta,
Ita Firdausi dariya ta danne dan ta gane inda Baba ta dosa
Ita kuma Amina baki ta tabe bata tanka komai ba
Baba ta aniya sake zuzuta abin har fiye da inda ya kai, har sai da Amina ta kai iya wuya, a ganninta meye a ciki yo? Yau ta fara gannin kwaliya ko kawai ta shiga hakkin wa'inda basa son hayaniya?
Mikewa ta yi ta nufi dakin Biyu tana fadin" Bara na ga dana, Ke kuma Fido walahi kar ki kuma dungurinsa, ki bar min abina kar ki rikita min yaro, kin ji na fada maki"
Baba ta dan daga murya ta ce" To Uman biyu ni fa ba zaki tardoni ba, zan wuce, kai ni dama Amaryar Elhaji ta dan tsakura min turaren cen , baki ji kanshi ba"
Turus Amina ta yi, ta juyo a kufule tana kallon Baba ta ce"
Nzl. 49
Turus Amina ta yi, ta juyo a kufule tana kallon Baba ta ce" Ke kuma yaushe kika fara kaunar turare haka? Inace du turaren da nake hadawa sai kice aa bakya son turare kinada cutar turare, idan kika shaka yana hadasa maki ciwon hanci da wuya?"
Baba ta karkace zamanta tana kantsar goronta ta ce" An yi haka, sai dai ai turarenma sunna ya kama, wannan nata ai inaga ba na kasar nan bane"
Yanzuma da haushi haushin da ita sam bata san ya kai cen ba ta ce" Du turare dai turare ne, Allah na tuba ai ba'a kai turarukan Madina ba, ni kuma da su nake aiki , da su nake hada turarukana, ko menene dai na Madina ya fi kyau da karko da komai, kuma sai maganar kwaliya kyau kyau kyau ai Allah na tuba du kyanta idan ta ga wata sai dai ta ja gefe ta yi shiru!, Kuma ai farin ne ta fi mutane ba dai kyau ba walahi!, Fari kuwa a me? Ai fari banza ne ni nan Amina na fada!" Harda buga kirji da sake kallon Baba irin tana jira ta ji ta bakintan nan
Firdausi tamkar zata saki fitsari a zaune yanda take mutsu mutsu da kafarta dariya na tukarta, a dole ta shiga tarin dole dan kar ta fashe da dariyar ta shiga uku
Baba kuwa ta sake gyara zama ta ce" haƙa ne kuma, ama fari ai karshen kennan, wani fa cewa yake yana son fara ko maya ce, kuma ni banma ga me yasa abin ke bata maki rai ba, bayan ba layin abinda ya shafeki bane uman biyu, sai na ga kamar fada ne muke yi a kan maganar ABDUL "
Turus ta sake yi tana kallon Baba
Sai kawai ta cire kai ta kama kofar dakin yarenta ta shige a fusace
Tana mako kofar Firdausi ta kama ciki tana kakaba dariya har fadowa take yi daga saman kujera
Babama dariya take yi bilhaki ta ce" Walahi idan ta tarar da su sunna rashin ji zasu ci kakansu a dakin cen"
Firdausi na dariya ta ce" gwarama su ci kakan nasu yaren cen sai ita, kim ga wai yadda Hasan ke cika yana batsewa, ni kuwa na gaura masa mari , shegen yaro kai ba dan kowa ba sai shegen hobara?"
Baba ta ce" Kin ga, ki rufawa kanki asiri da dukan ƴaƴan nan walahi a kansu sai mamansu ta zaneki tsaf idan ya so in me za'ai mata a yi mata"
Firdausi ta ce" Na ga kat, dan walahi da ya je ya rukunkumeta harda tara hawaye a idannuwanta ta min kaca kaca tace aa bata son wasan duka in daina dukansu, in masu nasiha in masu addu'a ya isa, fadama ba'a yarda na yi ba"
Baba ta ce" Kadan daga soyayarta da ƴaƴan nan, Allah dai ya biyata sannan ya shiryeta, dan baki ga yadda maganarta ke cenza yannayin mijinta ba, muna magana da karsashinsa da na kamanta hirarta nan take yannayi na rashin jin dadin mu'amalarsu ya bayana a tatare da shi, na tabata abinda ke zuciyarsa dangane da ita mai girma ne, bana so wannan firgitaciyar y'ar ta kwace komai, Uman biyu kuwa na shirme"
Firdausi ta sauke ajiyar zuciya mai zafi, ta ce" Baba, walahi tana sonsa, rikicinta ne ya fi komai karfi a cikin lamarin, ama ai wannan hanya da ya dauko zamu gani ita ko shi wanda zai saki ya nemi sulhu"
Baba ta amsata ta mike tana mata salama dan so take ta yi ta je ta gayaci makota su tayata aikin nan tun yau a rarage
Yauma hakan ta kasance, sai da dare ya tsala ya shigo ya samu Firdausi na karatun Alkur'ani mai girma
Ya zauna suka gaisa sosai, ya karra yi mata nasiha da rarashi a kan lamarin rayuwa, sanann suka tatauna a kan lamarin abinda suka tatauna da Baba
Sosai Firsausi ta ringa kuka tana sake dukawa tana yi masa godiya, har sai da ya nuna bacin ransa ya fara fada sannan ta share hawayenta ta shige kamar yadda ya umarceta
Tana shiga bayi ta wuce ta dauro alwallah ta haye saman salaya ta shiga Adu'a a kan wannan mutumi da yayarta da dukan alkhairin dake tare da su
Shi kuma abinda ya saba ya yi, yaransa ya yiwa adu'a sosai sannan ya karasa kofarta ya tura a hankali ya shiga
A hankali ya karasa bakin gadon ya tsuguna yana kallonta
Kumatunta yake kallo da ajiyar zuciyar dake masa nuni kamar ranta a bace ta kwonta
A hankali ya dora hannunsaa saman mararta ya shafa yana dan sakin murmushi
A hankali ya kai bakinsa ya manna mata kisss mai zafi a wajen sannan ya dago ya sake zubawa fuskarta ido da gashin kanta dake waje wanda ke wal wal wal wal na hasken duhunsa da kyansa
A hankali ya dan shafa shi yana sake kallon fuskarta zuciyarsa na dokawa da mugun karfi
Kasa kasa sosai ya furta"u'r sleeping like a baby"
A hankali ya sake shafa fuskarta ya kuma furta " U'r a baby , my baby, Wifey" ya idasa yana dan sakin murmushi kadan yana kallonta
A hankali ya ci gaba da tofa mata Adu'a har ya yi ya gama ya mike ya fice ya rufe mata dakin
Ta baya tmya rufe ya duka ya tura masu ky din ciki sannan ya koma nasa bangaren cike da bege da jin rashi a cikin zuciyarsa, sai dai kamar yadda ya kudurta ba zai takurata ba, idan dai hakan shine burin Amina zai hakura, ko menene ai in sha Allah ya tabata Allah zai sanyaya masa, balema ba wani abu mai karfi da ya wuce tarin kaunar abinda ke cikinta!
Sosai suka raya daren nan, bayan Risala ta yi masa rantse rantsen cewa ba zata kuma bari wani ya ji abinda ya shiga tsakaninsu ba, ta bashi hakuri na wanda ya faru, sun karra tataunawa a kan furucinta na gidan Baba mai shanu sun ganewa junna
Ta sha wahala a yauma , ta sha wahala sosai, domin ya kwana biyu da abin shima, a dole ya barta daga karshe domin irin nishin da take fitarwa kar ta summe masa
Da kyar shima ya samu barcin bayan sun tsaftace jikinsu yana jin yadda mararsa bata sakar masa yadda yake so ba, ama ba halin sake koma mata dan shi ba makaho bane ya gane kwarai ta yi hakuri ta jure kuma ta gaji dole ya tausaya mata ya barta ta huta
___________________________________
Washe gari ta kama asabar, ranar da ya ware ta hutu ce tunda ya tare da matansa, ya kasance yana gida ne tunda safe har wata safiyar, sallah kawai ke fitar da shi sai ko idan ana wani abu mai mahimmanci irin zuwa taaziya, ko zuwa wajen daurin aure, ko zannen sunna, da zarar an gama yake dawowa gida dan ya ware ranar ne dama wa iyalinsa
Kusan karfe goma bayan an kai Biyu wajen aski ta fito a nutse ta nufi bangarensa ba tare da ta yiwa Firdausi salama ba, dama ko da ta tashi a cike ta tashi kamar yadda ta kwonta a kufule, kamar zata tashi sama dan haushi da take ji na kowa da kowa
A nutse ta tsaya bakin kofar tana dan bubugawa kamar yadda ya zame mata jiki, bata fadawa waje ba tare da ta nemi izini ba sannan ta yi salama a amsa mata
A karro na biyu ta sake yin salamar , sannan ta ji muryarsa, duda bata yi tunanin samunsa a falo ba, dama ta tsaya a falon ne da nufin idan ta yi salama uku ba'a amsa ba ta shiga ta haye sama ta same shi a samansa
A hankali ta tura ta shiga tana baza dubanta dan ya lalubo shi a cikin kwayar idannuwanta
A hankali ta karru da kujerar dake gabanta wace bata san ta kawo inda take ba sakamakon kallonsu da ta shagalta da yi dan mamaki dake ciciyar zuciyarta
"Be careful please, don't injured ur ur self " Ya fada yana dan son tashi da dan karfi daga zaunen da yake kan Risala na saman cinyoyinsa yana dan shafa hannayenta dake waje sanadiyar karamar rigar dake jikinta, idannuwansa kuwa tarr a cikin na Amina
A hankali ta dauke idannuwanta ta dan juyar da kanta tana gyara tsayuwarta dan kar ya karaso ya tabata
Shima dan dakatawa ya yi bayan ya tuna da Risala a samansa ya koma ya zauna yana lumshe idannuwansa hadi da lalubo hannunta a hankali ya jimke dan abinda zai rike hakan yake so dan samun kwarin gwuiwar fuskantarta
Yawu mai dacin gaske Amina ta hadiye ta sake juyowa tana dan kallonsa, a ranta tana ayana' Namiji kennan, buhun kaya, watau ga Maina kaya ko? Har ka hau ka jida mata aiki ka sauka ka rike yar shila?, Shine ina fama da ciye ciyen cikin da ka dura min babu ruwanka na rayu ko na mace kana nan ka labe a jikin yar yarinya kamar a karyata dan shegen kasusuwa a wuya ko? Ba damuwa ni ba makashiya bace, zan haife maka na dire maka dan walahi babu wanda zai sakani zawarci da malulun yaro, an jima baa zageni ba!'
A fili kuwa , a dake ta ce" Wajenka na zo, ina son zamu yi magana"
Fuskarta da ta hade da cire kan da take ya saka shi shima a dan hade ya ce" Bismillah"
Juyowa ta sake yi gannin kadangaruwar tasa sai sake dago kai take kamar ta sha rana tana son innuwa kadan ko jin ƙishirwa, sannan ta sake kallonsa ta ga ita yake kallo da idannuwansa dake daf da kasheta dan kaifafan kallonsa sam ba risinawa a ciki
A hankali ta sake juyawa da nufin tafia, dan ta ga soyayar irin mai hawa kan nan ce tanada bukatar a basu waje
A hankali ya dubi Risala kasa kasa ya ce" Bab, dan bamu waje kadan kin ji?"
Sai da ta dan dago yana kallon idannuwansa ta mana masa kisss wanda tsaf a idannuwan Amina sannan ta mike taa nufi ciki firki firki tamkar zata karye biyu
Ita amina Al'ajabinema ke neman kasheta, oh yaren zamani jarabace cike da cikinsu, yanzi wannan yar ita kuma halin da ta saka kanta kennan a rayuwa? Jarabar maza? To Allah ya sanyaya
Zamansa ya gyara yana nuna mata wajen zama dan nesa da shi, a tsare ya ce" Bismillah"
Kujerar ta kalla, tana nesa da shi ainun, sannan ta kalli ta dan kusa da shi
Haka kawai sai ta ga harda rashin adalci a lamarinsa
Ama sai ta kyale shi ta barshi da halinsa ta je ta zauna a kujerar, itama ai gani take ta fi mata alkhairi fiye da kowace
A nutse ta ce" Dama, dama dangane da maganar makaranta ne, jiya twins ke ce min ashe ka cire su a wancen makarantar tasu, ni ban sani ba, kuma har ka saka su wata ta kudi duka ni ban sani ba, shine nace dama zan zo na ganka a kan hakan"
Sai da ta dire aya yana kallonta, shima a hankali ya ce" Eh an yi haka, ashe ban nemi izininki ba Amina, na cire su ne baki yarda ba?"
Idannuwanta ta dago cike da jin wani irin abu marar dadi, tana kallonsa a hankali ta ce" Aa ba haka nake nufi ba fa"
Gannin ya yi shiru ya sakata ci gaba da fadin" Dama na zo mu yi maganar ne, saboda na ji wace makarantar ce suka koma, saboda halin rayuwa idan bata yi mugun tsada ba, kuma na yi godiya"
Yanzunma jin shirun ya yi yawa a dole ta dago idannuwanta dake sade ta zuba masa ido
Sai ta ga ita yake kallo, ama ba da kallon nan na kamar zai cinyeta danya ba, kallo ne normal kawai wanda zaka yiwa irin wani wanda baka sani ba haka
Basarwa ya yi yana kauda kansa ya ce" Allah zai badaa yadda za'a yi in sha Allah"
Amsar tasa a dunkule, kuma yua ja ya tsaya, kamar ya gama maganar yake nufi
Ta dan jima tana cicira maganar, har dai ta rasa abin bilowa a kan maganar sai ta ce" Kuma, Kuma fido yau take ce min an ce ta shirya gobe ta fara zuwa, ta fara tafiya makaranta da kuma koyon girki da.........."
"Amina, abinda ya Kawo ki kennan?" Ya fada yana katseta
Tsuru ta masa da ido
ABDUL ya ce" Idan shine kina iya tafia it's ok"
Sake zuba masa ido ta yi zuciyarta na kunna da tafarfasa, watau ta tafi ta basu waje su dora daga inda suka tsaya ko?
Rai bace ta mike ta juya zata yi tafiyarta tana dana sannin zuwa yi masa godiyar nan, farin cikin da ta tsinta a fuskar kanwarta ya sakata nufo dakinsa, sai gashi yana wulakantata
"Zaki fara awo gobe, dan ya kai wata daya da sati biyu , zaki je wajen Mansur ya hadaki da doctern da zara ringa maki awo in sha Allah" ya fada yana kallonta
Rai bace ta juyo ta ce" Awon me zan je?
A dake ya ce" Awon ajiyar dake tare da ke "
"Ni babu awon da zan je, kuma da kake fadin adadin lokacinsa wani ya fada maka ne?" Ta fada cike da neman a yita ta kare
ABDUL ya tabe bakinsa