Showing 75001 words to 78000 words out of 145392 words
Chapter 26 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ya karasa yana fadin" Masha Allah Masha Allah ashe an sauka, to Husaini maza jeka ka amso mana kwano a bamu sabuwar tatsa mu je mu yi dakashi, kiwo kennan alkhairainsa yawa ne da su"
_________________________________
ABDUL kuwa baki ya tabe ya koma wajen gadonsa ya cire rigar da ta rage masa ya kwonta a saman gadon
Rashin Sa'a ya taka a lokacin da ya kai dubansa saman zannin gadon ya yi arba da kalar zannin gadon mai ruwan peak mai haske ne sosai, kuma harta da fan kwaliya kwaliyar jikin sak irin zannin gadonta ne na jiya
Wani irin yarrrr yarr yarr da jikinsa ya dauka a lokacin da ya hasko irin rikon da ya yi mata itama ta yiwa zannin gadon har kamar zata yaga shi da hannunta , da idannuwanta da suka girmama wajen kallonsa irin ya zo mata fa bidiar nan
Idannuwansa ya rintse da dan karfi yana jan hannayensa ya yi mika sosai a hankali ya furta" YA SALAM" sai kuma ya hade kafafuwansa ya rufe jikinsa da kyau yana ambaton Allah kamar yadda ya saba a irin lokutan nan idan ya samu kansa a irin wannan yannayi mai wuyar fasara wanda ke sako shi a gaab lokutan da ya ga dama
Nan da nan jikinsa ya gama karba, a yanzu maimakun ya dan lafa sai ya sake murde masa
Idannuwansa ya bude hana jin lalle ba damar samun barcin fa a yanzu ya dan zubawa waje daya ido
Haka kawia ya samu kansa da sakin murmushi a zuciyarsa yana ayana' Ga rashin kunya, ga tsoro kamar farar kura......wai kaida baka san ciwon haihuwa ba, ashe ita dinma bata san komai ba, jaririya ce , kofarma a matse kamar kofar hanci sai iya rigima'
( Maman jariri inaga ya dace yanzu kam ki makashi a kotu, wai fa da kawarki yake😭😭😭😭😭😭😭😭😭🤣).....
Wahala ya sha da kansa kafin ya samu barcin shima ya yi awon gaba da shi, domin shi din kansa ba wani barcin kirki ya damu ba , dan tun a jiyan yake cike da tunani harma da tuhumar kansa irin yadda ya jema wace bata san komai a kan lamarin ba
Amina na farkawa daga barci da yama sosai Baba Lauratu ta sakata a gaba sai da ta ci ta koshi ta sha maganinta sannan ta shige wanka ta sake yin wanka ta dawo ta saka wata rigar yanzuma irin ta zaman gida mai laushi kuma marar nauyi ta zauna tana fuskantar Baba dake yi mata hirar Irin rikicewar da Firdausi ta yi kan sai ta zo wajen taron bikin nan
Amina ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana ayana' gwarama da bata zo ba, da fa wani ido zan kalleta?'
A fili kuwa ta girgiza kai da takaici ta ce" Mijin Fido, Allah ne kawai zai saka mata wulakantata da yake yi Baba"
Baba Lauratu ta ce" Allah ya shirye shi tun kafin lokaci bai kure masa ba ya gane matar rufin asiri yake tare da ita su hadu su rufama junna asiri su talafi junna, ama lamarin yaron akoy ban haushi"
Haka suka yi ta zantawa har Babar ta mike da nufin tafiya
Amina ta shagwababe fuska tana kallonta ta ce" Baba, kuma ki barni da wa a wannan katon dakin? Ni walahi tsoro nake ji"
Baba ta yi murmushi ta ce" ke kuwa tsoron me Allah na tuba ga katuwar tvn nan kadai ai ta isheki hira, ai dai ba zama zan yi mu yi ta labari a gifan siriki ba ko? Ko yanzu ai an jima a zaunen ke dai Bara na tafi, zan fara biyawa gidansu Asmaun da kika ce na masu kwatancen nan din ko? Kuma fa kin ga su Rabiama sun ce sunna son gyaran amaren gidansu watau biyu, kuma auren fa saura sati biyu dudu, shine nace anya zaki iya kuwa?"
Amina ta ce" Zan iya sosaima, ko gobe suke son fara zuwa su zo kawai mu fara Baba"
Baba ta dan zuba mata ido, sai kuma ta yi murmushi ta ce" Sa zo, ama ba gobe ba, nan da kwana biyar in sha Allah sai su zo ku fara, idan suka samu wadatacen gyara abinda sati guda ya isa su yi fess da su, ke dai ki dauki maganinki yadda aka ce kin ji ko?"
Kai ta gyada ta dauki hijabinta tana tafe a hankali wai ita a dole sai ta yiwa Baba rakiya
Ita dai bata hannata ba dan lalabata take yi, karma ta tubure tace sai ta bita gidan, babu abinda ya gagari uman biyu yanzu
Tana kallo aka ja Baba a wata mahaukaciyar mota aka tafi da ita
Ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe ido da shakar iskar waje mai ni'ima da dadi, ga shuke shuken mangwaro da sauransu balbalin gidan ba karamin kyau ne da shi da dauke hankali ba
A nutse ta koma dakin ya rufe bata saka sakata ba ta wuce ciki ta sake shiga bayi ta dan wanke dan danshi danshin da ya hannata sallah ta sake fitowa ta dauko akwatin kayayakin hade haden HUMURARTA ta koma falo ta baje kayanta bayan ta shinfida wata leda ta shiga ciciro kayan hadin BAK'AR humura kamar su:
*Hadin BAK'AR Humura*
*Ruwan turare irin na jarirai mai dadin kanshi, irin kanshin dake birgeka*
*ALKAMUS*
*TURARE Na madara MAI KAURI , CONCENTRÉ MAI DADIN GASKE*
*Garin sandal*
*Musk, musk ba muski ba, musk shima murje shi zaka yi ka hade a ciki*
Yadda ake yin hadin kawai zaka harhadasu a cikin butali guda mai dan girma ne suma ka girgizasu su hade jikinsu sosai, shikenan sai ka barta ta jiku, domin Humura ta fi dadi idan ta tsumi sosai komai ya hade jikinsa.....Wannan itace sasaukar Bak'ar humura, kana iya yin hadin karamin kudi ko baban kudi, ya danganta da murdinka ko muradin mai siya a wajenka
Turaren ta hada kunnayenta na jiyo mata salamewar kiran sallar magariba, sai kuma ga daya daga cikin ma'aikatan bangarenta ta fito da karkon turaren wuta ga dukkan alamun turaren ne zata saka
Gannin Amina a falon a zaune sai da ta duka har kasa tana gaisheta cike da ladabi da biyaya sannan ta ce" Hajia zan saka turare ne dare ya yi kafin na koma bangarenmu"
Wani irin banbarakwai Amina ta ji kuma ta ga lamarin, sai dai bata ce komai ba illa gyada mata kai da ta yi tana kallonta ta sasaka ta ajiye sannan ta ja ta tsaya sai da dakin ya dauki kanshin turaren wutar mai dadin gaske sannan ta dauke kaskon ta fita da su bayan ta yiwa Amuna salama
Ajiyar zuciya Amina ta sauke tan lunshe idannuwanta ta kau hannunta gaban hancinta tana sinsinawa dan son jin kanshin humurar a hancinta sosai
Budewar da aka yi ya sakata sauke idannuwanta a kan kofar
Hasan ne ya fara shigowa, yana ganninta a guje ya karasa itama ta ajiye dukkan abunda ke gabanta tana kyakyata dariya ta rukunkume shi a jikinta tana fadin" My son, my boy"
Hasan na rukunkumarta shima ya ce" my mama, my mom, mama i misss u so much........."
Itama harda son ta fashe da kuka tana fadin" Ina dan uwanka? Ina Husainina? Ina fata bai yi kuka da ya ga bana nan ba?"
Hasan ya yi dariya yana danewa saman cinyoyinta ya zauna abinssa ya ce" Mama ya yi mana sosaima, kuma da aka bashi madara sai ya yi shiru, yanzu haka yana wajen DaD yana masa fadan shan nonon Sanuwa da ya yi ba'a tafasa ba, wai kawai dan ya ga Baba tsoho ya sha.....Mama yanzu a nan kuma zamu zauna ne?"
Mamansa ta yi gagawar fadin" Aa, ba zamu jima ba a nan zamu koma wancen gidan namu , kace waye DAD kuma?"
ABDUL dake tsaye hannunsa rike da Husaini yana sauraron dukkan abinda take fada ita da Hasan ya dan karra kallon Husainin dake ta ajiyar zuciya dan ya gindaya masa kashedin daga yau idan ya kuma jin ya ci wani abu a waje sai ya yanka masa lebe ya soya ya ba mage sun cinye, shine fa ya ringa hawaye yana rantse rantsen ba zai kuma ba
Shima hannunsa ya saka ya bude kofar ya shigo
Da ba dan Hasan na daf da kasa ba da wannan mikewar da ta yi tabas sai ta hantsila shi ta yadda zai ji ciwo a wani sashe na jikinsa
A yanzunma a kwonce ya fado sai dai bai wani damu ba domin bai doku da karfi ba
Tsaye take tana kallonsa har ya karaso inda take tsayen yana kallon gefe kadan wajen da Hasan ya fadi
Ciki ciki ya ce" Ke, ki yi a hankali mana kar ki yiwa YARONA rauni, tashi son ku je ciki ku tube ku shiga wanka"
Yaron na mikewa ya nufi inda aka nuna masan itama zungwai zungwai ta juya zata bisu, ko kulashi neman masifar da ya yi mata bata yi niyar yi ba, domin bata tunanin zata iya tsayawa su yi wani dauki ba dadin da junna
Sai dai bai barta ta shige ba ya saka hannunsa ya kamo nata hannun na hagu sannan ya janyota baya kadan har sai da bayanta ya dan doku a kirjinsa kadan
A hankali maganar da ta so yi a cikin ranta ta fito fili ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, na shiga uku me kuma zai min?"
Tana fada ne hawaye na son kwonce mata
A hankali ya dan juya da ita ya shiga nufar dakinta da ita ba tare da yace da ita ci kanki ko daina kuka ba
Baki Amina ta bude tsakaninta da wanda ranta ke hannunsa ta takarkare ta ce" " Wayo, kai, meye haka? Kai Abdul meye haka?"
Dakatawa ya yi da tafiar da yake yi da ita yana kallonta kamar bai gane yarenta ba
Amina ta shiga murza hannayenta ta juya ta ji ya sake riko hannunta
A haukace ta juyo tana sake matsawa nesa da shi hadi da zuba masa idannuwan itama
Murmushi ya yi kasa kasa ya ce" Dama, cewa na yi, yaya jikin ki?"
Me Amina zata yi a yanzu da ya wuce kuka? Dukma wace zatace mata kar ta koka dan ba ita abinnan ke samu ba, dole ta yi kuka , dole ta zubar da hawaye
A raunane tana kallonsa ta ce"
*NZL PAGE3️⃣0️⃣*
A raunane tana kallonsa ta ce" Ka ga, ko a anguwarmu ni bana wasan maza, bana shiga harkar maza, dan haka dan Allah ka fita a harkata kafin ka bani takardata, ka daina yi min maganama kwata kwata"
Sake matse mata waje ya yi hakan ya saka AMINA, da girmanta da komai ta kwala ihu tana rintse idannuwanta, domin ita abinda ta yi tunani daban, sai ta ga ya tsaya yana kallonta
Tana bude idannuwanta suka sake yin ido hudu sai ta ga ya sakar mata murmushin da ko a gaban sarki aka gurfanar da ita zata iya rantsewa murmushin rainin wayo ne
Juyawa ya yi bai ce nata komai ba ya kama hanyar ficewa
Har ya kama kofar ya dakata ya juyo kasa kasa yace " Ki tabatar kin saka masu kayan barci sannan ku masu addu'a ki rufe masu dakinsu"
Baki bude take kallonsa zuciyarta na raya mata abubuwa irin na rashin kunya da ya dace ace ta yayaba masa ko zai shiga hayacinsa ya gane yarenta
Bai bar dakin ba sai da ya sake fadin" Kar ki saki ki hada daki da su AMINA"
Ido ta kwalalo tana kallon kofar da ya rufe ya fice ta karaso tana fadin" Idan na hada din sai me? Ina ruwanka da hada dakina da y'ayana? Malan sai shishigi ni zaka nunawa raini? Ka bari na warke walahi sai na koya maka biyaya wa manyan gabanka, kuma zalina da kake ci kai da Allah.....shima Hasan....Hasan? Hasan?"
Ta nufi dakin da aka ce nasu ne wanda ko shiga bata yi ba tanai masa kiran da yana ji ya yi turus dama fitowarsa kennan daga wanka Husaini kuwa yana ciki
Tana shigowa ta ja da mamaki tana kallonsa
Rigar wanka ce a jikin Hasan jama'a ya wani yi fresh kamar dan yan gayu na kasa da kasa shi kadai sai shinning yake ga abin ruwa dake nuna fitowarsa kennan a wanka
Farin cikin ganninsa a haka ya so mantar da ita abinda ta shigo yi, har sai da ta zauna gefe ta tuna sannan ta sake hade fuska ta ce" Kai zo nan, zo nan"
Fuskarta yake kallo kafin ya shiga matsowa ya tsuguna a gabanta
Tsayinta ta rage tana sake hade fuska ta ce" Waye yace maka ka ringa fadawa wancen dady?"
Dagowa ya yi da mamaki yana kallonta, sai kuma ya ce" Ba dady bane Mama?"
Amina ta yi tsuru ta rasa amsar da ya dace ta bashi
Hasan ya sake soke kansa ya ce" Dama dazu ne da yama ya je cen gidan gona, shine Baba yace ga dadynmu nan, muka ce masa akace dadynmu ya rasu? Sai yace eh wancen ya rasu, yanzu kuma ga dadynmu nan, mu je masa dady, ni dai sai nace masa dady sai yace da gaske ina so ya zama dadyna?"
Amina dake kallonsa tsigar jikinta na kwonkwoncews tana sagewa a hankali ta ce" Sai kace me?"
Sake dagowa ya yi yana kallonta, sai ya sakar mata murmushi ya ce" Mama, kin manta dama munna ce maki mune bamuda dady a school? Yanzu muma fa mun samu kennan?"
Zuciyarta ne ta ji ta yi mata nauyi, amsar da yaron ya bata kuwa ta tabatar mata lalle baban burinsa ne ya cika, domin karara take karantar farin ciki a tare da shi idan yana maganar wancen mutumen
Fitowar Husaini da saurin cin birkinshi y saka Amina da Hasan waigawa sunna kallonsa
Kiri kiri ya yi ya ce" Mama ai na cewa Dady ba zan kuma cin abin kowa ba , walahu ba zan kuma ba Mamana"
Ajiyar zuciya ta sauke ta sakar masa murmushi ta mika masa hannu, haka kuma ta mikar da Hasan din ta nufi wajen da take tunanin a nan suturunsu suke, suturun da ita dai bata san lokacin da suka samesu haka ba, batama san yaushe aka zuba su ba, kai karshe bata san wa ya zuba ba
Sai da ta tsorata da ta bude wajen kayan
Kayan gasunnan birjik kala daban daban, kuma kowani launin tufa an yi gefensa daban
Ajiyar zuciya ta dauke ta nemo wajen kayan barcin ta ciro masu wando da riga kowa da color din da ya fi so ta basu , suka shiga sakawa ta dauko masu turare ta zo gabansu ta shiga dan fesa masu
Sai kawai ta lumshe idannuwanta tana jin wani irin sanyi da nutsuwa a cen kasan zuciyarta
Sai kuma ta ji wani gefe na zuciyarta na katse mata farin cikinta ta hanyar fadin' Amina, duka wannan jin dadi na dan lokaci ne, ke kin sani, duda mafarkin da kike yiwa yaranki samu kennan, watau irin wannan rayuwar, ama hakan ba yana nufin ki ringa mantawa da komai dake gabanki ba'
A hankaki ta sauke ajiyar zuciya bayan ta gama shafa masun suka haye saman gado daya su biyun kowane na yi mata murmushi
Itama murmushi ta yi masu a hankali ta shiga yi masu addu'a tana kallon askin dake kansu mai kyau sak dai irin na yan gayu,
Murmushi ta yi , ta samu kanta da yiwa koma waye ya kular mata da ƴaƴanta haka adu'ar fatan alkhairi a zuciyarta
Bata tashi ba sai da ta ga sun yi barci sannan ta tashi da kyar ta nufi nata dakin tana ayana' Bara dai na yi wankan nima na dawo mu yi kwoncin mu , ba wani yaron da zai hannani kwonciya daki faya da y'ayana ba, idan fa suka motsa tsakiyar dare bana kusa suka yi kuka? Nima ba zan iya barci ni daya a dakin cen ba ai'
Tunda ya bude bangarenta ya ga sai hasken fitilu da TV dake yi ama bata falon ya yi tunanin tana dakinta
A nutse ya nufi dakin nata ya murda ya shiga da salama a bakinsa yana wara dubansa dan son gannin inda take
A jikin kofar ya jinginu yana kallonta, zaune take a saman gadonta da shiga irin ta sasaukan wando dogo da riga , kitsonta a daure a tsakiyar kanta, fuskarta a hargitse kamar ta sha kuka
Itama kallin take yi tana sauke ajiyar zuciyar bacin ran dake nukurkusarta, yanzu fa ta gama yanke cewar zata je ta same shi, sai kawarta tace da ita aa ta bari ya zo, kar ta manta amarya take, kuma gashi gida da kishiya kar a fara saka mata ido, ita dai ta saurareta ne ba wai da nufin zata yi aiki da abinda ta fada ba, sai gashi ya shigo
Murmushi ya saki gannin da gaske a shake take, dan haka sai ya dago ya karasa bakin gadon y zauna yana sake fadin" Amincin Allah ya tabata a gareki Risalah, ina nema maki amincin Allah kin yi shiru?"
Risala ta lumshe idaannuwanta tana rike hawayenta, domin idan akoy abinda mahaifiyarta ta yi ta jadada mata shine ta kiyaye yawan kukan nan, bashida wani anfani, idan ya kasance komai zata sakashi a gaba tana yi masa kuka to fa zai rainata ne
A hankali ta ce" Huby, yanzu fisabililahi ace yau kwana biyu da daura aurenmu sai yanzu na ganka? Kamar baka dokina? Wani irin kira ne ban yi maka ba bayan ka san kai ya dace ka neme ni? Irin kiran da ake yiwa mace ana murnar an daura din nanma baka yi min ba, nd mun ware babar ranar yin diner kace kar na fita? Why? Me yasa kake min irin haka ne?"
A hankali ya sake fuskantarta ya ce" Risala, tsarin gidanku ne sai an yi diner a kawo ki gidana shi yasa na baku dama, na hannaki zuwa diner ne dan baki saka suturar da zaki je gaban kowani kato ki wuce ya biki da kallo ba, ita diner din nan ai ba'a ce ba za'a yi ba, ama me zai hanna a yi shiga ta musulmai?"
RISALA ta tsare shi da ido bayan ta kamo hannunsa ta ce" Kishina ne ya saka ka hanna ni tafia?"
Sai da ya zubawa fuskarta ido mai dauke da kwaliya da su gashin ido, kwaliya kai mai kyau din nan , a hankali ya gyada kansa yana tunanin kwaliyar nan ai ta yi yawa fisabililahi
Murmushi ta yi tana komawa kusa da shi ta ce" Dama na sani, sai da na fadawa Mama ta daina fushi na tabata da dalilinka mai karfi, gashi kuwa da dalilin"
Murmushi ya yi shima, domin ko ba komai ya ji dadin da