Showing 102001 words to 105000 words out of 145392 words

Chapter 35 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8160

damuwarsa ba, kar aje mahaukaci ne ba'a sani ba fa" Mansur ya fada hankalinsa tashe , ko a cikin amon muryarsa zaka fahimci ransa a bace yake shima


ABDUL ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa ya ce" Man, ba zaka gane ba, ni da kaina kadan na tsinta a cikin maganar, har yanzu ban san duka maganar ba, ama in sha Allah ba zan bari haka ba, idan shi dan duniya ne zamu buga kwallon duniyancin,....... Daga shi har ubansa!"


Da mamaki ya ce" Man kana nufin mahaifinsa da rai dama ya bar rayuwar yarinya a wulakance haka?"


ABDUL ya sake cije lebensa da bacin rai ya ce






Nzl 42




ABDUL ya sake cije lebensa da bacin rai ya ce" Yana nan da ransa , ka gane abin ya wuce tunanin mutum, ya zamto talaka bashida wani gata sai na Allah, wa'inda suka isa su tsawata sun nade hannu kowa na tsoron tofawa, mahaifiyar yaron kanta a ha'ula'i take, ai ba maganar aure cewa ya yi idan na fito da ita ya mata saki uku, ni kuwa na fito da itan a summe"


"Saki?, Uku? Hasbunnalah, wannan wani irin marat imani ne? Wani irin rashin godiyar Allah ne? Ni ina nan haihuwar nake nema ido rufe Allah bai kawo ba ka gaan sameta a wani wajen ana wukakantawa? Dan Adam bashida godiyar Allah, wanin baya jin tsoron Allah sam"




ABDUL ya sake daukan file dinta ya bude yana komawa ya zauna ya ce" Allah zai yi maganinsu, kwana nawa ka daukan mana ne?"


Mansur ya ce" Na daukar mata kwana uku ne, idan komai ya tafi daidia jinninta ya daidaita in sha Allah zan salameta"


ABDUL ya gyada kansa yana duba duka kaf magungunnan da aka rubuta mata harda na kafe ruwan nono dan kar su dameta da suba da zogi


Sosai ya gamsu da komai ya ajiye yana sake zama yana ta cicira tunanin dake zuciyarsa, sai dai ba zai fadawa kowa yanzu ba, zai bari ne har ya tabatar sannan ya san abin yi, shin yaya zasu rayu bayan bata son rayuwa da shi? Idan kuwa har furen dake tare da ita ya yi tsiro har ya yabanya wace irin gagarumar rigima ke gabansaM


"Hum" yace har sai da Mansur ya dube shi yana ajiye masa jus yana fadin" Man kayanka sun baci gashi an kusa shiga masalaci, ya dace ka je ka kimtsa"


Ajiyar zuciya ya sauke ya mike yana masa salama da nufin sai sun hadu da yama idan ya dawo daukan Uman biyu




Tafiyarsa ya yi ya bar Baba da biyu dan ya san sa wuce masalacin tare , shi kuma ya koma gida


A cikin dakin kuwa Baba ke yiwa Amina nasiha kasa kasa, Firdausi kuwa ta samu barcin wahala tunda ta saka hannunta cikin na yayarta sai da barcin ya kwashetama Amina ta janye a hankali ta zauna aa gefenta tana kallonta


Kasa kasa Baba ya ce" Haka nata salon kadarar yake, kuma kin sam cewa Allah baya dorawa bawa abinda ya fi karfinsa, ki daina kuka ki bata kwaron gwuiwa, ta haka sai ta shanye dukkan wahalar har ki ga ta mike kamar ba ita ba kin ji Uman biyu?"


Amina ta gyada kanta tana sake share hawayen nata, idannuwanta har sun kumburo dan kuka, bata taba jin maraici har cikin kirjintaba irin na yau, kafin Abdul ya fito da Firdausi babu irin abinda bata tuna ba a duniyarta, ta yi kuka da boda kamar zata fasa motar


Shigowar Baba tana rike da bokici da yan kayayakin dake ciki , Husaini na yi mata surutu ya saka Baba sakin murmushi yana kallon Hasan ya ce" Yau sam ba fara'a a fuskar mai tsuntsaye, Allah dai ya sanyaya fushinsa"


Baba ta yi murmushi itama tana sake gyaraa matashin kan Firdausi ta zauna tana kyatu ta kama Hassan ta zaunar ta ce" Allah ubangiji yaa sa karshen wahalar kennan"


Da amen suka amsa, du suka ci gaba da zama har karfe goma sha biyu ta yi suka fice tare da Muhammat da ya dawo daukansu dan kaisu masalaci




Da yama da kyar Uman biyu ta fito , har zuwa lokacin Firdausi bata farka ba, kuma ance idan ta farka ba za'a bata abinci ba , sai dai ta sha jus


Ji take abin nan sam bai dace ba ace za'a rabata da kanwarta, shi dai a bayan motar a zaune waya yake amsawa , yau sam bai leka nema ba, gashi da zafin nema, suka nufi gidan Baba domin yau bai je ba, rabonsa da Hajia kwana biyar ciffffffffff




A asibiti


Tsaye suke a kanta, docter da Mansur sunna bata baki a kan kin amsar koda bakin ruwa ne ta sha, ta nuna Alhamdulilah bata jin cin komai


Docter ta janyo kujera ta zauna tana kallonta ta ringa yi mata nasiha da bada baki da nuna mata mahinmancin lafiyarta
Ama Firdausi sam ta nuna bata jin yinwa ne


Da kula Docter ta dubi Docter Mansur ta ce" Likita, inaga sai an tabo makusancinta, ka san ba zai yiwu ta ki shan jus din nan ba, shi zai taimaka mata samun karfin jikinta kafin ta samu iska ta fara cin dan salak da dai wani abin marar nauyi ko?"


Kai MANSUR ya gyada, cike da tausayi yana kallonta ya ce" Na gode sosai Docter da kika zo, zan dubata....."


Docter ta amsa ta mike ta tafi,


Mansur ya amshi jus din dake hannun Nurse din da ta shiyata da komai , itama ta fita , ya maida dubanta kan Fido da kanta ke sade tana kallon waje daya


Aa sanyaye ya ce"baki dangana ba Firdausi?"


Fido ta dago a hankali ta yi masa kallo daya ta sake sada kanta, muryarta a sanyaye ta ce" Dangana da me likita?"


Mansur ya ce" Da rashin da muka samu, ko kuma aban yaren ne mai baban laifin?"


Sake dagowa ta yi tana kallonsa, ta sake soke kaanta


Mansur ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Akoy ciwo Firdausi, akoy ciwo matuka, ama ya dace ki yi duba da jama'ar dake zagaye da ke masu zubar da hawayensu dominki, a kan laifin daya tak, kar ki hukunta kanki da hukuncin da zai damu masoyanki, kin ga wace zata fara jigata yayarki ce, a gangaro kan biyunki, mu da kanmu sai hankakinmu yaa tashi Firdausi, karma ki saka damuwar wani a ranki ki kasa nutsuwa kin ji?"


Firdausi ta sauke numfashi yinwar fa na cinta, a sanyaye ta ce" Docter, dama wata sharaar ai sai a kiyama......., Luuuu luuuuuuuuuu
Nake gani kar aje nima mutuwar zan yi na shagalta da kurbar juss, shi yasa nake ta Adu'a a zuciyata......ka ga kuma biyu ba nawa bane ba fa, na uman biyu ne"


Tausayinta, madaukakin tausayinta, shi ya fi komai rinjayarsa,
Da dabaru irin na likitoci ya samu ta amshi juss din har ta yi masa sha na mamaki


Tana gama sha ta koma barci domin akoy allurorin barci a lamarin dole sai da hutu


Ido ya zuba mata yana kallonta, kallon da shi kansa bai san ya zarce a kallon ba
Gata dai a cikin hali na rama, duhun fata du hasken fatarta wahala ta rinar da ita, rashin walwala, girman ciki irin na wanda ya sauke ciki yanzu, tarin tausayinta ya sakashi zuba mata ido yana mai cike da madaukakin tausayinta a zuciyarsa


Ajiyar zuciya ya sauke ya mike domin a lokacin tuni har isha'i ce ke shirin kawo kai ya sake duba komai na dakin sannan ya tafi ya kimtsa ya nufi gidansa dan tun karfe shida yau rabonsa da gidan nasa




___________________________________


Daga gidan Baba suke, fuskar Amina tamkar an saka balan balan , ita kafai ke hauhawa tana hucisakamakon abinda biyu suka yi mata, wai ba zasu zo ba yau a gidan baba zasu kwana a cen zasu yi weekend
Tana ji tana ganni akace wai ta bar ƴaƴanta ta dawo gida ita kadai, ita lamarinsu ya fara bata tsoro, tana janye shakuwarta da ahalin gidan Mai Shanu yaran nan na makalata




Sai da ta bacewa ganninsa ya dawo da dubansa wajen Muhammat, ya ga ya tsareshi da ido yana wani murmushi irin na saman leben nan


A kausashe ya dage girarsa daya ya ce" menene?"


Muhammat ya dora yan yatsunsa biyu daidai bakinsa ya ja irin ya yi zif din nan sannan ya sake mayar da kansa gefe yana murmushi


ABDUL ya bude ya fice yana dan mimike kafafuwansa fa fadin" Sai gobe idan A'lah ya kaimu"


Muhammat ya ce" Allah ya tashemu lafia Oga, a huta lafia"


Bangarensa ya shige ya haura sama
Ko'ina fes fes an gyara ko'ina sai kanshi yake yi, masu gyara harta da dakin barcinsa su suke gyarawa


Wanka ya yi ya dauro alwallah ya dawo saman salaya yana sake dafe cikinsa da suka sake cin wainar Uman biyu shi da yara da baba gaba daya, cikin nasa ya yi nauyi da yawa bayan baya cika kulunsa har haka da dare, a dole zai dan motsa jikinsa idan ba haka ba , ba zai iya samun barci mai dadi ba


Yana gama sallah ya dan buda computernsa ya dadana ya gama aikin da zai yi sannan ya mije ya sake fesa turare ya sauko yana kallon table din abincinsa an shake da kuloli kala kala ya yi gaba , yau ba zai leka komai ba ai ya koshi sosai ne


A Hankali yake takawa, da fara kar din jalabiyarsa a jikinsa ya shiga dan tafia a tsakar gidan, nufinsa ya fita haka ya zagaya anguwar a kafa ko zai ji cikinsa ya sauka kadan


Idannuwansa ne suka sauka a kanta, ta cenza shigar jikinta ama da hijabinta tana tsaye ta dan dafa jikin garu a balbalin kofar bangarenta tana kalle kalle


"An mata" ya fada a hankali yana kallonta a tsaye


Itama tunda ya fito ta ganshi, shi yasama ta cire dubanta a kansa take kallon wani wajen daban, da yace an mata, a dole ta juyo tana kallonsa da mamakinsa


Murmushi ya sakar mata yana kallonta ya ce" Me ake yi a waje da dare?"


Amina ta dan sadda kanta , sai kuma ta cuno baki tana fadin" to ba twins bane ba zasu zo ba, su ba ruwansu idan na ji tsoro ko?"


"Da ruwansu mana" ya fada a hankali
Sai kuma ya sake kallonta ya ce" Tsoro kike ji?"


Mazewa ta yi ta ki bashi amsa


Dan murmushi ya yi ya ce" To zo mu fita yawo a cikin anguwa"


Samun kanta ta yi da son fitar, domin ita kadai du wani kadaici ke damunta na ba gaira babu dalili


A sanyaye ta sauko suka shiga tafia, kadan kadan da dabara sai ta saba jerawar da suka yi, shima da dabarar sai ya daidaita


A hankali suke takawar har suka fita a makeken get din suka shiga tafia a anguwar dake dauke da fitillu manya a kofar gidaje, ya zamto ba duhu sosai, sannan akoy mutane jifa jifa sunna dan tafiyarsu, wasun kuwa a zaune zaka gansu nesa sosai sunna dan zantawa, harda mata kuwa, domin anguwa ce ta gayu mai dauke da yayan yan gayu da jikakun yan gayu masu son yannayi mai dan sanyi na dare haka kafin dare ya dan tsala su shige gida


"Me yasa kake son shiga tsakanina da nemana?" Amina ta fada a hankali tana kallon hannunsa daya dake saman kirjinsa a rungume


Dan juyowa ya yi ya kalleta, sai kuma ya dauke kansa ya shiga nuna mata wata shuka yana fadin" Kim ga wannan shukar, a shekara daya take girma, kuma ita bata son mai dati ya tabata, idan kanada dauda irin haramtaciya ka tabata mutuwa take yi, Aunty kin ga tanada kyau ko?"


Amina ta kalli shukar, ba shukar komai bace sai ta zogale, zogale dai zogale , ta ce" Uhum"


Takawar suke yi har suka kusa kaiwa wata kwana ,
Dan daga kafarta ta yi ta je ta gabansa tana kallonsa ta ce" ABDUL, me yasa kake son shiga tsakanina da nemana?"


"Bani da nutsuwa a kan neman ki" ya fada a takaice


Amina ta ce" Why?, Ka san kuwa shi ya rufa mana asiri ni da y'ayana da kanwata har muka kawo yanzu?"


A hankali ya dakata yana kallonta ya ce" Yanzu kuwa ba gani ba, sai na zamto rufin asirinmu baki daya in sha Allah"


"Na dan lokaci?, Na kayadadan lokaci? ABDUL na dan lokaci? Yaya kake tunanin zan yi sake da barci bayan na san ni mai nemo shinkafa ce?, Ba zan kuma yarda Fido ta fada hannun wani azalumin ba in sha Allah, haka kuma ba zan iya amincewa ka korar min wa'inda nake yiwa gyara a yanzu ba, idan ka barni kuma na koma ina nema ana kin kulla ni, tun ba yau ba sana'ata ce, haka kuma inada burin habaka karatuna ABDUL " Amina ta fada tana rage amon muryarta domin ya juyo gaba dayansa yana kallonta ne har ta dire aya


A hankali ya ce" Waye ya ce maki zan barki?"


Amina ta tsatsareshi da ido
Gabanta na wani irin dokawa
Muryarta tana kin fitowa da kyau ta ce" Me, me kake nufi ne?"


ABDUL ya juyar da kansa gefe yana basar da maganat, sannan ya sake juyowa yana kallonta ya ce" Manta "


Amina ta sake matsowa tana kallonsa ta ce" Na manta me ABDUL? Me zan manta?, Ka min magana a kan bayanin nan, ni fa bana son magana a rufe!"


"Ki ringa tausasa lafuzanki mana Aunty, mu tafi kin ji?" Ya sake fada a tausashe


Amina ta sake neman tuburewa tana kallonsa, irin ai itace baba ita ya dace ta ringa masa irin haka ba wani shi ba


Tana kallonsa ta ce" Ka ga , ba wani maganar tausasawa babe ko rashinsa, magana ce ta gaskiya, dama Baba tace na bari matarka ta tare, ta tare ai har na ga aikin tarewa kun aikata kau? Yanzu ni sai ka salameni na je na ji da rayuwata, na je na ji da ta y'ayana da ta kanwata, bana so Biyu su ci gaba da shagalta da abinda ba dindindin ba, ni kawai ka..............."




Da wata irin murya ,a mugun kausashe, ya sake matsowa yana dora dan yatsarsa daya a saman lebenta ya ce" Cewa na yi, Ki tausasa harshenki, sannan ku tauna kalamanki, bana son aiki irin na yarinta da shirme a nan"


Amina ta zarro idannuwanta ta bude bakinta zata sake yin magana ta ga ya watsa mata wani mahaukacin kallo mai dauke da namijin hatsari, mai firgice da yaren zane,
Sannan ya saka yan yatsotsinsa biyu rak ya rike lebenta da su ya ce" SHUIIIIIIIIIIIIIIIIITTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTT!"




TAKAICI, MAMAKI, BACIN RAI, TASHIN HANKALI suka hadun mata, suka hannata barkata komai,yawo idannuwanta ke yi a saman fuskarsa, hadewar fuskarsa ya girmami tunaninta,


Hannunta ta saka ta janye lebenta da kyar , ta sake zubawa fuskarsa ido, sannan ta juya da wani irin gudu gudu,sauri sauri ta koma hanyar da suka biyoita da shi tana rufe bakinta da hanna kanta kuka a gaban yaro!


Da ido Masu gadi sukabita, harda Muhammat dake shirin tafia nasa gidan


Murmushi ya yi da ya tuno furucin ABDUL na dazu yana tabatar da gaskiyarsa ashe, maman twins ba dai rigima ba




Tana bude falonta ta shiga suka yi ido hudu da Hindatu tana sake saka turaren wuta


Huci take yi na wanda ke son fashewa da kuka tana kallon Hindatun ta ce"




Nzl 43








Huci take yi na wanda ke daf da fashewa da kuka tana kallon Hindatu ta ce" Hindatu, hala turaran wutar ne? Nace maku juwa yake sakani Hindatu kin cika masa muski hawar mun kai yake yi Hindatu, wayo Allahna Hindatu". Sai kawai Amina ta fashe da kuka tana zama a kasa kamar wata yar baby


Ido Hindatun ta zarro tana yin waje da turaran ta hanyar kicin da gudu sannan ta dawo hankali tashe sai fadi take"Na shiga uku na lalace, Hajia,dan Allah ki yi hakuri ban san bakya sonsa ba HAJIA, dan Allah ki yi hakuri ki daina kukan na shiga ukuna"


Amina ta tuje hijabin, wani mahaukacin kyau da ta fara yi na daban fiye da gyaran amarcin da ta sha, da wani irin luf luf da gashinta ya karra yi sai wanda ya gani, tana tuje kafafuwanta ta ce" Ki daina ce min Hajia, ni ba HAJIA bace, hasalima filin jirgin kansa ban san a wace anguwa yake ba, kawai sai ki ringa min abinda raina baya so bayan ban maki komai ba?"


"Annabi Muhammadu Rasulullah salalahi alaihi wa ahlihi wa salam, na shiga uku ni Hindatu jikar Maryama, Hajia ki yafe mib baki daya rankatakaf laifin da na yi maki, ki kuma dauka kan ba za'a kuma ba, duka kaf abinda bakya so zan daina yi miki har karshen rayuwata a gidan nan kin ji Hajia?" Hindatu ta fada tana sake dukawa gaba daya hankalinta a tashe, ita tama manta tana sake maimaita Hajiar da aka hannata fada


Da haushi Amina ta mike tana jin juwar na daukanta, dan walahi juwa take ji sosai , gaba daya hadin turaran nan ya mata karfi shi yasa ita bata anfani da turaruka masu karfi, dan sunna cutar da ita ko cenma


Hijabinta ta amshe tana hararar Hindatu dan ganu take yi ai du laifinta ne, ta hannata ce mata HAJIA ta wani sake fada mata


Dakinta ta nufa tana fadin" Sai ki yi ai , ki yi ta cewa Hajiar Hindatu, nace ki kwana kina fada"......
Tsuru Hindatu ta yiwa kofar , sai kuma ta yi hanyar kicin har kamar zata kifa tana adu'ar Allah ya sa kar Hajia ta koreta, ita ta rasa me ta yi da zafi haka har Hajiar take kuka? Wayo duniya


Tana shiga dakinta ta yi bayi tana wurgar da abubuwan dake jikinta


Wanka ta sake yi dan zafi take ji du irin sanyi sanyin garin


Tana fitowa ta dauko yar yololuwar riga fara ta saka , sannan ta dauki hijabinta ta zurma ta fita falo


Wajen abincin ta bubude tana dubawa, gannin abubuwa irin na turawa sak ta rufe tana jan dan tsaki ta nufi kicin din da kanta ta dauko dadawa da tafarnuwa da dan kayan yaji mai kanshi sai magi ,
Friza ta bude ta babako kaza guda ta tsomata a ruwa ta zauna tana jira
Sai da kazar ta saki sannan ta yayankata ta cire bindin ta sakata cikin tukunya ta zuba dadawar nan da komai da komai sannan ta dora saman gaz ta sake hayewa tana dan balancing din kafafuwabta tana jira


Kanshin dadawar ya sakata hadiyyar yawu har kazar ta silalu sosai ruwan ya janye saura kadan, ta juye a kwano ta yi zamanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login