Showing 135001 words to 138000 words out of 145392 words

Chapter 46 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8168

shafawa na dan yi um um um sai na koma bangarena"


Ido ta zarro da dan karfi ta ce" aban amna a jikin wa?"


Murmushi ya yi mai dan sauti ya ce" Hala zaki ce min baki taba farkawa kika ga babu jan bakin da kika shafa ba? Baki taba tunanin a ina ya goge ba?"


Yanzun kam har sai da ta so budewa sai kuma ta fasa tana jin mamaki na neman kasheta, haba da farko dan wani iya yi zata shafa jan baki ta kwonta, idan ta farka sai ta ga babu, ta sha duba abin shinfidarta ko a jiki take gogewa garin barci? Sai ta ga ba komai, sai ta bar hakan a matsayin shanyewa take yi da kanta, ashe ashe ABDUL ne?


"Ama ai hakan bai hannaka daukan kwanana ka ba yarinyar cen ba har take bubude min a cikin gida ko?". Ta fada tana turo bakinta tamkar za'a saka mata ribom


Yar daria ya yi, dan a yadda ta fara amsa shi ya tabata alamu ne ta fara saukowa, a hankali ya ce" Sai kace jahili? Kina tunanin zan yi saken da zan kona kaina da kaina? Aa, ba zan yi haka ba, dan ina tsoron Allahna"


Amina ta dafe haba, gaba daya mamakinsa na isar duniyarta


Yanzun kuwa sai ta saurari muryarsa cen kasa sosai yana fadin" Meenart kasheni zaki yi, idan har kika ci gaba da wahalar da ni kasheni zaki yi gaba daya kin ji?, Ki sasautawa ABDUL dinki kin ji? In sha Allah zamana da ke zan kamanta adalci wa kaina ne ba a wa kowa ba, idan na cuta maki nine a cikin damuwa Meenart, plz ki sasauta min kin ji?"


Lahaula wala kuwata ila bilah, kai jama'a, gaba daya jikinta ne ya dauki bari, sauraro take tana mana kunnayenta kamar zata shige ta shige cikinsa ta huta
Ita da ace zata ga masu cewa ta yiwa ABDUL dogon fushi gaskiya da ta yada masu magana
Tsakani da Allah mema ya yi mata?
Bawan Allah mai halayan yan aljana😌
Gaskiya zata shirya da mijinta maki gani kuma ya rintse idannuwansa, haba jama'a, yo ita anya kaf duniya akoy wanda ya kai mijinta kuwa?, Ina ba kyauma ai gaba da daukewa miji kai da hararansa, sam ba kyau


A hankali ya idasa tsumata yana fadin" In sha Allah, zan tafi Chaina jibi, idan mun je gidan mun wuni tare zan tafi kan harkar aikina, dama ace bakya jinni Meenart, dama ace ya tsaya Meenarnahhhhh"


'annabi muhamadu Sallallahu alaihi Wa ahlihi wa Salam, Allah ya karra kusanci a tsakaninka da shi da muka ribanci sunnarka, sunnarka itace sunna mafi dadi a duniya, kai jama'a ashe auren kani shine riba? Yau ni Aminar Abanmu da ABDUL ya sakeni da na lalace, dama bana jinnin nan ABDUL, tsaf zan fito mu jone du wandama yace aa kansa ake ji' Amina ke ayanawa a zuciyarta tamkar zata summe dan tsumuwa


ABDUL bai bar dakin nan ba sai da ya gaji da rarashi da ban baki da tsuma zuciya sannan ya juya jikinsa a mace ya fice a dakin da tunanin bata yafe masa bane, Mansur babu irin abinda bai masa ba da ya fada masa tana masa fushi ne dan ya dan nuna mata tare yake da Risala harta ranar kwananta, Mabsur yace masa kai tsaya ka ji mata ba'a yi masu haka, idan ka yarda ka masu haka sunna iya tsanarkama, sam ba'a yiwa mata haka fa, shi ua karra rikita shi a wunnin yau din nan, sun koma gefe sun tatauna sosai




Jiki a mace ya shige bangarensa ya karasa wajen diner yana kallon Risala dake zaune saman kujerar dinern tana jiransa


Kwanaki ne da matarsa ke jinnin haihuwa, idan ta zo marabarta, idanma bata zo ba kanta


A hankali ya zauna dan ya dan ci salak din da yakan ci kafin ya kwonta bayan ya amsa gaisuwarta da murmushin da shi kadai ya rage masa a fatar bakinsa, jama'a wai sittin saba'in din nan na jikin Uman Biyu ba ciko? Kai jama'a mata na abubuwa a duniya, ta karkace ta masa tuka tuwon baban gida yana zaune yana kallonta? Oh tsaf so take ta kaishi kiyama




A hankali Risala ta ce"






A sanyaye Risala ta ce" Bab, ka je da ni mana Chainar, me yasa zaka tafi kai daya bayan kanada mace?"


Idannuwansa ya dan lumshe ya dauki ruwa dan ya jika makoshinsa ya kurba kadan sannan ya fuskanceta ya
ce" Risala, na fada maki , aiki ne zai kaini chaina, aiki irin mai wahalar nan, idan na fice tunda duku duku idan da rai da lafiya sai da wani duhun zan shigo, na barki ke daya a dakin hotel, chaina gari ne na aiki, ba zama , ba wasa, idan na je da ke ba zamu ribanci zuwan ba, ke me zai hanna ki zauna ne har Allah ya dawo da ni?"


Risala ta juyar da fuskarta gefe tana ta tunani, sake rage garajen muryarta ta yi sosai tana dubansa ta ce" Kennan ni kadai za'a bari a gidan? Sati daya fa ba wasa ba, ga gidan nan da girma"


ABDUL ya ce" To ko zaki je gidan Hajiar ne kema?"


Da sauri ta zarro ido tana girgiza kanta, ita kuma me zai kaita gidan hajia ? Ai har an yanka mata wuya saboda kiyaya, matar da ta tsaneta ta zabi kishiyarta a kanta? Ina ba zata je ba walahi ( Ina jiran irin wannan lokacin dan na kawo wani misali kadan a garemu baki daya, ba dan na fiku sanni ba, ko dan zan koyar da ku ba, ban kuma isa na cenza wanda ya dauki maganata da zafi ba, naci ne irin nawa ya sakani zan yi maganar nan, Yan uwana mata, mun san cewa aure abu ne dake kamawa ba dole sai an tsani mace, ko dan ta gaza ta wani fannin ake kawo mata abokiyar zama ba, ta yiwu laifin nan na mijinku ne, ko kuma haka kawai kika tankadawa kanki garin wahala mai cike da tsakuwa, kina tunanin ke kece mace ke kika isa ki kawowa namijin nan da ya auri matarsa ta farko shekara a kadan biyu, ko uku, har zuwa goma ko sama cenje cenje da jin dadin rayuwar da bai taba yi ba? Albishirinki, itama a ledarta ya daukota, yar shila sabuwa dal, ya murza ya dannan son ransa, komai lalacewarta da ita yake kwana saman gado daya, yan yayan da kike ganni nasu ai kin san ba fyade yake mata yana bata su ba ko?, Soyaya mai sunnan soyaya ta yiwu wace suka yi ba zaki taba ganninta a wajensa ba, ta yiwu lamari ne na bukatar karo ki dan karrin jin dadi na namiji, kina sane da cewa namiji na karra aure dan ra'ayi, yana karra aure dan karin gidan hutu, yana karra aure dan matarsa na kyautata masa ya karra samun kyautatawa? Yana karo ki dan yana so a cika masa gida da ya'ya, yana karro ki dan shi din mai yawan koyi ne da wanda ya isa a yi koyi da shi sugabanmu Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wa salam, ama sai ki tashi, ki cika kwakwaluwarki da abubuwa, tunani kala kala, ke kece mace kece isashiya kece matar so, wata zata shigo ne da kudurin mayar da matarsa banza ya zamto komai ya dawo hannunta itace mai waje mai tabarmar ta nade?, Wata dama nufinta waje zata yi da uwar ya'yansa bayan ita ko yayan ba zata iya rike masa da zuciya daya ba, wata da nufin lalata gidansa wargaza gidansa ya zamto kowa bai ji dadin zama ba, wata da nufin haifo wa'inda zasu gaji gida, abubuwa dai gasunnan barkatai subahanalah, ta yiwu wannan namijin da kike hobara a kansa shine asalin wanda zai kasheki kamar yadda ya kasheta, idan nace kashewa ba na kai mutun kiyama ba, yau wani namijin irin mumunan zaman da yake da wata macen kamar zaman kiyaya, kamar wace aka kawo dan ya kashe, ya daureta ya ringa yi mata kisan mumuke, bai saketa ba bai jiyar da ita dadin zama ba,sai kin zauna ki gane, idan kuwa ba haka bane kika samu macen nan a gidanta, macen da ta san kanta, take zaune da ciki daya da jama'ar dake zagaye da ita, ta samu kyakyawar mu'amala, idan bakida wayo kika kasa yin koyi da ita kika samu kema naki waje har kika gina taki rayuwar sai ki dawo kina batun cewa ta asirce kowa ta malake miji baya gannin kowa baya ganne komai sai ita sai zancenta, baki san irin wahalar da ta sha na biyaya da takewa da gannin kaskanci kafin su zamto aminan junna ita da mijinta ba, baki gane a haka dinma yakan birkice ya rufeta da fada ama kanta a sade bata dagowa ba dan haka suka saba rayuwarsu dan haka take masa biyaya, saima ki ce ai ke ba zaki dauki wulakancin namiji ba, itama matarsa kissa ce, ke baki yardaba kennan da ana iya yin biyaya domin Allah ba dan a yi kissa da kishiya ba ko? A haka da yawa zaman ya gagara a ringa cewa ta fitar da ke, a ringa magangannu, idan kuwa zaman ya zaunu a wahalce, kulun cikin cin zarafin junna? Ki sani idan da kika tardota ta dan yamuge ne, fatarta ta dan ja ne, ko kwali ta saka baya mata ram ya zauna mata dasss hakan rayuwa ce, yau da gobe ne, kwonci tashi ne, haihuwa ce, shekaru ne, Mace daman ta fi namiji tsufa, namijin nan naku da kike gannin kin zo ki ririta kema haka zai didirka maki naki cikin a hankali ki fara janyewar fatar shi kuwa ram abinsa..........dan Girman Allah mu ringa yiwa kanmu fada, mu rayu da sannin ko me muke takama zamu mutu baki daya, ban yi maganar nan dan na fi wata ko ni ba zan yi kishi da kishiyata ba idan Allah ya kadarto min ita ba, na yi be dan baki daya mu ringa tunani a kan lamuranmu, kishi halal ne, kishi akoyshi, ba karya bane, ama kuma wani kishin mu da kanmu zamu hanna kanmu sukuni da kwonciyar hankali/ Maganata ba wai iya Amaren da suka tardo iyayen gidansu nake ba, harta ke hajia uwar gida, ki sani yarinyar nan da aka kawo maki idan kika dauketa kika riketa dan ki cutar da ke Allah zai saka mata, idan dan kinada dama wajen mijinku kike anfani da damar nan kina kunna mata wuta Allah na jiranki, idan dan kin fita sannin danginsa ba zaki sakata a hanya ba kina kallonta ta ringa aikata abinda zasu tsaneta kema kin haifa!, Idan dan kece Hajia mama uwar gidan Elhaj zaki rike kambun nan ki munana mata, ki wulakantata, ki sakata labewa a daki dan tsoronki da tsoron kaidinki sai ki yiwa kanki karatun ta nutsi ki kalli fatar hannunki, na tabata zaki gane tsufa kike kara yi yau da gobe, yau ko ba mutuwa a barki da tsufan nan zaki zo shekarun da kanki ba zaki gane ba bale wani, DUNIYA AI MAKARANTA CE, du abinki ba zaki kasheta ba idan lokacinta bai yi ba, dan an aurota ne ta maki laifi sai ki bada hima a takaitaciyar rayuwar ki munana mata, idan kin je kiyama sai ki amshi sakamako daidai da laifinki!, Sai kai baba, idan ba zaka iya rike biyun nan ba ka yiwa girman Allah kar ka karro, ko ka salameta ka dauko tunda bakada adalci!, Kaine gyaran gidanka, kuma kaine mai batawa!, Idan ka yi aiki irin na munafurci ka bata daya a wajen daya dan ka faranta ran daya ka lalata gidanka da kanka!......Na gode )


Risala ta girgiza kanta tana fadin" Aa, wai da cewa na yi nima na je gidanmu har ka dawo?"


Shiru ya yi na dan lokaci yana tunani a zuciyarsa
Shirunsa ba a kan komai bane sai a kan tunanin abinda ya dace ya yanke, wanda ba zata ga an tauyeta ba, ba kuma zai tauye kansa ba


Tsakani da Allah har a cikin ransa ya ji dadin da bata bi su ba, kuma dalilin wannan shima ya daga mata kafa a kan abinda ya so yi mata na rashin kyautawarta dangane da yar uwarta, sai ya daga mata kafa dan ko ba komai ta ji naganarsa duda yana hankalce da ita ba ruwanta da harkar sunnan ya'yansa sai a wunin biki kawai ta je ta zauna a gefe tana kallon mutane tana amsa waya da dane danenta
Ama duka wannan ya yi niyar a hankali zai kwatanta hada kansu , zai kwatanta hada zumunci a tsakaninsu, ba zai dira kai tsaye ya yi haka ba dan abin ne tunda farko a rikice yake, dole ya bi a hankali


A nutse ya fuskanceta ya ce" Kina ji? Risala ki yi hakuri kin ji? Idan bakya zaman nan din ne ku je gidan Hajiar baki dayanku, ama bana son maganar zuwa gidanku ki yi har sati guda dan kawai na yi tafia, a nan dinma ai ba ke kadai bace sai idan kin so zama ke kadai din, ga masu aikinki ga komai, kuma kina iya sakawa daga gidan naku kannenki su zo su tayaki zama ko?" Ya fadi nagabar kannenta ne kawai, domin ba zasu taba zaman minti goma basu yi fada ba, sam basa zaunuwa waje daya, akoy lamari na rainin junna a tsakaninsu
Risala ta yi tsai, a hankali ta ce" Ama husband, ita fa da ka barta ta tafi gidan hajia ba zabinta bane? Sai nice zaka hanna?"


ABDUL ya dafe kansa, wai dama haka ne hada biyun? Bale idan masu jinini ne? Wannan tace wannan, wancen tace wannan


A tausashensa dai ya ce" Risala, haihuwa fa ta yi, ina zata je ta yi wanka ne? Wankan jego zata yi a gidan ai, kuma kema nace idan kina son cen din ku tafi tare ko?"


Risala ta cire kanta idannuwanta na cika da kwallah
Zuciyarta na haharbawa


Muryarta a raunane ta ce" Allah ya sa dai ba bakin uwa zan gani a zamana da kai ba, du inda na bi sai ka hanna ni, ita kuma du abinda take so ka baza mata, yanzuma daga wajenta kake, kamar wanda ke sonta bayan asiri ne, babu wanda zai ji labarinku bai tabatar min da asiri ta yi ba, ta rabani da Hajia , yanzu tana son rabani da kai gaba daya, na ce ka je chaina da ni kace aa, gidanmu ka ce aa, Allah ya nuna min karshen masifar nan, dan ni da Allah na dogara!"


A hankali ABDUL ke girgiza kansa yana kallonta


Niyar bude Salak din ya fasa ya ajiye ya juyo da kyau yana fuskantarta


Da siga ta nasiha ya ce" Risala, kin san a duniya bawan da ya saka irin tunaninki ya fi kowani bawa wahala a rayuwa kuwa?, Da yawama wa'inda ke bin bokayen suke fama da irin wannan matsalar, zaki ga kullun su cikin maganar an jefe su, an masu asiri, an shiga gabansu suke domin sun ba dan kasuwa yardarsu wanda abubuwan siyarwarsa wannan buga kasar ne ya fada maka karya dan a ciki abincinsa yake, idan ya fada maka cewa lafia kake ai ba zaka dawo neman magani ba, a haka wa'inda ke fama ke fama, sai gashi kema kina irin tunanin nan?, Zan so ki ba kanki lafiya, ki cire wannan tunani a ranki, ki rungumi abinda yske gabanki, babu abinda ya kai gaskiya dadi a duniya, domin itace raminta ba kurare ba Risala, ko me zaka yi kuma gwara ai ka yi shi a kan gaskiyarka ko? Da ka yi shi a kan hasashe ko son zuciya, Risala Amina matata ce, kamar yadda kike matata, ina sonta kamar yadda nake son ki, ke da ita ba bambanci, yadda zan kare mutuncinki haka zan kare nata, ki cire tunanin an hadani da ita dan dole an min dole, ke babu wanda ya isa ya min dole fa ? Ra'ayina ce ita , kamar yadda kike ra'ayina, ki kwontar da hankalinki, ki nutsu, ki cire komai a ranki, ki fuskanci me ya dace ki gyara ko me ya dace ki daina, zaki ga mu'amalarki da kowa dake tare da ke ta daidaita, koda ba yadda kike so ba zaki ga akoy fahimta kin ji?"




Risala ta ringa daka tissu tana goge hawayenta, domin ita dukka kaf jadadawar soyayarsa wa Amina da ya yi ta dauki haka a matsayi aiki irin na sihiri!, ABDUL dinta? Haba dai, haba!,


Tana hawayen ta ce" Kennan dai ba zan je gidan namu ba, dan kana tsoron kar a lalatani ko me kake nufi ?"


ABDUL ya kureta da ido, kennan dai ba zata gane me yake nufi ba?


Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki jug din ruwa ya mike ya nufi ciki, kwata kwata ba zai ci salak din bama, Allah kuma ya shiryeta idan tanada rabon shiriya ( kina fa da dama, kina iya tankwasashi har ya yarje makin, kina iya morar kuruciyarkin, da kyanki, ama A haka, a haka ko?, kwonci tashi, tun ana sauraronki, za'a zo a daina, zai zamto da kin bude baki ba'a ba abinda ,aki fada mahinmanci, domin an san me zaki jajanta, koda bakinki na dauke da magana mai mahinmanci......dan Allah ina anfanin kashe kai da kai? Ai gwara a hakura walahi a gabatar da kishin da ya dace, ke mu fa a kishi muna iya yin burgima abinmuπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ™‡πŸ»β€β™€οΈπŸ™‡πŸ»β€β™€οΈπŸ™‡πŸ»β€β™€οΈπŸ™‡πŸ»β€β™€οΈπŸ™‡πŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈ i com in peace)


Mikewa ta yi itana ta fice ranta a bace, ta sani rayuwar bambanci in dai da aikin asiri ai kadanma ta gani, yau zata yi ta kiran mamanta koda zata kwana tana yi ne dan su shirya, domin batada wanda zata kaiwa matsalarta sama da ita, a hankali zata kwatanta mata ba gida zata bita ba, aa ta tayata da Adu'a ko menene ya karye itama ABDUL dinta ya dawo nata ita daya.






_____________________________________






A gidan Baba mai shanu






A tsaye suke gaban madubi, ko nace ita tana tsaye tana saka dan kunne a kunnenta bayan ta fito daga wankan yamma ya shigo dakin nata harda murza ky


A hankali ya rungumeta ta baya , ya zamto malunmalun din jikinsa ta dan dagu ta kareta sosai a jikinsa


Kasa kasa ya ce" Zan tafi......"




Amina ta lumshe idannuwanta, wani irin abu mai girma irin na rashin son mutun ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login