Showing 21001 words to 24000 words out of 145392 words
Chapter 8 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ta faru?"
Na'am suka yi da shawararsa, gaba dayansu suka shiga, sai daya da ya koma tado matarsa datijuwa da nufin ko menene mace sai ta fi su karfin taimakawa dan kare hakin musulunci
A yannayin da suka same su da Ζ΄aΖ΄anta a dole suka fara bata talafin tsayar da jikin da goshinta ke yi, sai kuma Aban Saudat ya fice da sauri dan ya dauko adaidaitarsa a tafi asibiti
Innar Audu itace da yarta suka talafi Maman biyu, sai Aban saudat din da kuma biyu suka nufi asibiti, su kuwa sauran suka je masalacin dan gabatar da sallah
Bayan an gama sallah ne yaron Liman ya shaidawa Liman abinda ya faru, da yake baban masalaci ne dake cen tsalake , har sallar juma'a a nan ake yi ya saka Liman anfani da lasifikar masalaci ya dakatar da datawan da samarin baki daya ya shiga nasiha da jan hankali, da neman alfarmar kowa ya binciki ya'yan gidansa ko idan ya kula yaron anguwarsa nada irin halin nan ya fada a sanarwa hukuma su yi gagawar shiga lamarin, yaren sun ce wani ne ya shigo ya taba mamansu ta suma, an sako yarinya a gaba dan an ga miji bai fito ba kuma ba uwa ba uba ba dangin da suka yi jin kai? To b zasu zuba ido sunna ji sunna gani a salwantar da rayuwar yarinya ba, yau koda ace itace ke janyo mazan da rashin kamun kai datawan anguwa ba zasu bari hakan ya ringa faruwa ba bale yarinyar an yi mata shedar kamun kai da kare mutuncin kai!
Sosai abin ya taba zukata, ciki kuwa Harda Mai Shanu dake yin doguwar tafiya a kafarsa shi da daidaikun ma'aikatan gidansa su zo har masalacin nan dan yin sallah, idan suka fita sukan zagaya ne a kafa su yi sport sosai dan jin saukin yannayin jiki
Hankalinsa tashe ya karasa wajen Liman bayan an sake yin addu'a a raragu sosai yana tambayar wada ake magana a kanta?
Liman ya san sarai mahaifinta ya masa gadi, hasalima gidan da take cikin Baba Mai Shanu ne ya malakawa mahaifinta suka fita daga haya suke ciki, dan haka ya sanar masa ko wacece da fadin anma kaita asibitin tafasa, shina yanzu cen din zai nufa
Sosai hankalin Mai Shanu ya karra tashi,
Tatare suka dungunzuma a cikin motar gidansa da ya sa Baba direba ya je ya dauko sula nufi asibitin Tasafar kowa hankalinsa tashe, zuciyarsa kuwa cike da tsoro da zulumin Allah ya sa wannan shedani bai samu galaba a kanta ba
Baba Mai Shanu kam abubuwan dake cikin zuciyarsa yawansu da girmansu Allah kadai ya sani
Ya shirya yin gaba da gaba da dangin iyayen yarinyar nan, idan zasu mayar da ita wajensu su mayar, idan ba zasu mayar ba to fa shi zai dauketa koda kuwa bata so! Ya isa haka, zaman tarenma da aka yi ai sai Allah ya tambaye su su da kansu bama dangin na iyayenta ba, sam an yi sake, an yi wasa da lamarin yarinyar nan, shi tunda ya kwatanta ta koma ta nuna ta fi son zama a nan tana gannin dakin mahaifinta da mahaifiyarta sai ya bar maganar, bai san ba baban tashin hankalinta zama tare da Matarsa bane, bai san ba Amina tana tsoron abinda zai taba mutuncinta komai kankantarsa, shi yasa ta iya garinta take tuka tuwonta
Sun tarar an gama wanke mata goshin nata ta farfado ama tana kunshe cikin hijabi sai kuka take yi, Aban saudat ya koma gida ya dawo domin bai fito da isashen kudin da aka ce zai biya ba
Baba mai shanu ne ya fito da fari kal din carbinsa ya je direct office din baban likitan wanda ya kwana a asibitin kuma bai sauka ba ya nemi izinin ganninsa
Likitan na fitowa ya gaisar da Baba cikin mutunci, domin likitan akoy daraja dan Adam, kuma kana gannin Baba ka san akoy hutu a tare da tsohon
A tausashe, da damuwa Baba ya ce" Jikata ce aka shiga gidansu jiya, nake so a duba min ita da fatan babu abinda ya sameta"
Cike da jimami likitan ya yi gaba ya kirayi likita mace ya sa aka kirawo Amina sula shige ciki dan a dubatan
Sosai aka sha daga da ita, domin sake rikicewa ta yi da nuna ba za'a dubata ba, ba zata kunce zanninta ba, sai da Likitar ta rarasheta ta nuna mata za'a duba ne idan bai yi mata komai ba sannan ta amince ta dubata
Tare suka fito Likitar ta shedawa Baba cewa Allah bai bashi dama a kanta ba
Gaba dayansu sai da alamun nutsuwa ta bayana a tatare da su
Fuska a hade Baba ya ce" Amina Wuce ki shiga mota mu tafi gida"
Amina da har yanzu bata wani dawo normal ba ta kalli Baba hankalinta na sake tashi ta ce"
ASALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH
πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ
_*NI ZAN LADABI*_
πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ
*NA*
*SAJIDA NIGER*
Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida
Wannan Novel na kudi ne ba free bane
Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER
Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai
Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka
*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπ₯°π₯°π₯°*
πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ
_*NI ZAN LADABI*_
πββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈπββοΈ
*NA*
*SAJIDA NIGER*
*PAGE0οΈβ£9οΈβ£*
Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida
Wannan Novel na kudi ne ba free bane
Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER
Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai
Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka
*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπ₯°π₯°π₯°*
Bakinta na bari ta ce" Baba gida?"
Carbin da yake ja ya hade ya daka a aljihun doguwar rigarsa fara sannan ya juya wajen da yaren suke ya masu nuni da su je mota gasunnan zuwa
Juyawa suka yi suka nufi motar dan basa wasan musu da Baba
A lokacin ya fuskanceta sosai ya ce" Eh gidana nake nufin ki wuce mu je mu ajiyeki, daga nan yau ba dai gobe ba zamu je mu samu dangin mahaifinki, yayansa daya daa na sani wanda da shi muka salaci gawar marigayi na masa magana a kanki, daga yau in sha Allah kin gama zama a gidan nan ke kadai, idan cen din suka ce zaki koma sai ki koma, idan gidan iyalinsa zaki koma sai ki koma, ama ba zai yiwu ki je gidan nan ke kadai ki yi rayuwa ba, zuwa yanzu na fahimci kin gane hatsarin hakan ya fi jin dadin gurbin da iyayenki suke zaune, ba zaki taba damun zaman lafiya ba mudin kina zaune ke kadai, babu wanda ya san mai zuwa maki gida da nufin cutarwa, idan na farko Allah ya kubutar da ke, na biyu Allah ya kubutar da ke, na uku ba'a san da wani shirin zai zo ba, idan ya barki a iya keta hadinki da sauki sauki, wa ya san ko yana fama da wata cutar? Idanfa Allah ya yi ke din mai kwai ce a kusa?, Wannan din gardame ce marar anfani, an riga an san ke kadai ce, Yaren nan ba zasu tare maki komai ba Amina, rayuwar y'a mace abin a bata kariya ce komai girmanta, yanzun shige mu wuce"
Gaba daya tatareta suka yi suka hannata wani yinkurin bijirewa tafiyar, a hankali take tafe jikinta a mace tare da mugun tunani da tsoron abubuwa biyun dake shirin tunkaro rayuwarta
Na farko gidajen yan uwan mahaifinta biyu ne kadai wa'inda suke shakikai a gareta,
Kanninsa da yayansa
Yan magana suka ce, abinda ya koro kura daga rami ta fada wuta ya fi wutar zafi
Bayan rasuwar iyayensu babu gidan da basu gwada zama ba, suka gwamace zamansu su kadai daga ita sai yar uwarta
A lokacin da suka zauna a gidan yayan mahaifinsu karen gidanma ya fi su daraja, babu abinda duka isa su raba , kasancewar gida ne na mata uku kowace da Ζ΄aΖ΄anta a gefe tana kalar nata ikon da kalar tata rayuwar, sai suka zamto kamar kishiyoyi ne na hudu aka zubo masu, abinci wannan basa samu sai ace ya yi kadan ne ba zai isa da su ba, abin takaicin yayan Aban nasu kuwa tunda ya nuna takardar gidansu yake so ya siyar ya raba masu gafo suka nuna basa so a siyar sunna so a barsu a kwana biyu , hasalima basa so a siyar da gidan a bara masu watarana wani sai ya shiga, gida dai nasu ne gadonsu ne mata suke, a yanzu idan suka siyar da shi sunna iya kade kudin ya zamto ba gurnon, ba kudin, idan halin rayuwa ya same su ina zasu je su zauna?
To fa wannan lamari sai ya kular da shi, shi dai bai fito ya nuna ga dalili ba ama tun daga lokacin ya kawo ido ya zuba masu, in me za'a yi masu a gidan nan babu ruwansa, sau uku baban dansa na zane Firdausi tamkar zai kasheta da bulala da tatakawa da kutufo da komai, tun tana tunanin abu ne da zai wuce har ya gagara wucewar , aka zo aka yiwa Firdausi aure ko tsintsiya basu saka mata ba, a nan ta so siyar da gidan dan yi mata kayan daki mijin ya kiya yace aa shi zai yi mata, mafarin gabar family dinsa da Firdausin kennan, sam basa sonta basa kaunarta, gashi ana yin auren bai jima ba ya rasu suka tatarota suka watsar ta fito da cikin biyu Karshe dai zaman gidan yayan mahaifinsu gagararsu ya yi domin ga ciki ba zasu juri duka ba , suka koma gidan kannin mahaifinsu, wanda sai da suka gwamace kida da karatu, ashe tsohuwar gaba ke nanake a zuciyar bawan Allahn sanadiyar hanna shi auren dadiron matar da kowa ya san ba zama take yi ba, aurenta uku ana kamata da maza a gidajen, karshe dai ya bige da binta a haka aka aura masa itan suka zo suke zaune, har yanzun itace matarsa wace ta ja rantsuwar ba shi ba yayansa ko a kiyama! Ta kuwa hau ta zauna sai gasu sun fado gidansu, watau ta samu , sai da ta kai ido da ido matar nan ta nuna idan zaman lafiya suke so sai sun zama abokanan shashancinta, a ranar da kafafuwansu suka gudu , sanadiyar bak'ar wahalar ta saka Fido nakudar dole ta haihu a hannun Baba Lauratu, inda dangin mijinta suka bada abin yanka kawai suka nade hannayensu, ana gama sunna babu wanda ya kuma waiwayar yaren nan, su kuma sun daukarwa kansu alkawari zasu rike, Allah ya raya ya basu abinda zasu ciyar su shayar, su tufatar, su yiwa tarbiya!
Tun daga lokacin ya zamto sai su kwashe wata daya ko biyu basu leka iyayen nasu ba, abinda ya sake yiwa Amina mugun tabo a zuciya shine haihuwar Fido ko a leke, suka barsu da kansu sai baiwar Allahn nake dake tare da su, dan auren Fido na biyu kiri kiri yayan mahaifinsu yace tafiya zai yi bashi da lokaci, aka ce a yi jiran dawowarsa sai a daura yace kawai limamin anguwar ya daura, wannan shine silar siya mata wulakanci a wajen mijinta, domin idan ya tashi gorinsa hadawa yake yi harda wannan
Sai dayar damuwar itace Hajia,
Walahi Amina na matukar tunanin zama da matar koda na awa daya ne bale na rayuwa tare da ita
Ita dai ba zata ce ga ranar da wani abu marar dadi ya shiga tsakaaninsu ba, ama irin yadda ta san Hajiar da kyamar lamarin talaka tana tsoron zamantowa abar kyama a cikin gidan
Tana tsoron kasancewa a karkashin Hajiar dan bata san wani irin zama zata yi a gidan ba, a kadan ta shekara uku tana yiwa Baba Mai Shanu waina tana kawo masa, ama maganar fatar baki bata hadata da matarsa bale godiya ko kamanta ta dan da zamanta, daidai da yin wainar shinkafa Baban ne yace da ita Hajia na son wainar shinkafa, ita kuma sai take yi dan kara girmama shi, ta fi tsoron zama da matar a cen kasan zuciyarta dan tana tsoron mutuncinta da son kare ratuwar Ζ΄aΖ΄anta
Ama idan ta yi duba da abinda ke neman haye mata fa? Lalle da wata wahalar gwara wata
Tana cikin tunanin nan suka karaso gidan
Hankalinta du ba a jikinta yake ba ashe har Baba ya bada umarnin a kai su Malan Liman gida su kimtsa su karya zai zo zuwa karfe goma su wuce gidan iyayenta
Sai da Hasan ya sake tba fuskarta ta dube shi a zabure , sai kuma ta shiga duban cikin gidan da datijan dake kallonta da tausayawa
Malan Liman ya ce" Idan kin samu masauki, kafin ki kwonta ki tabatar kin rama sallar dake kanki , ki yi addu'a sannan ki kwontar da hankalinki, in sha Allah karshen fargabarki ta zo"
Kai ta gyada a sanyaye sannan ta sauko ta shiga tafia a hankali Biyu na rike da gefe gefen hijabinta
Baba ne a gaba, kadan kadan yana amsa gaisuwar daidaikun ma'aikatan dake aiyukansu na safe har suka shige falonsa
A babar kujera ya mata umarnin zama sannan ya nufi sama cikin tafiyarsa a hankali na baban mutun mai shekaru irinsa
A nutse ya tura kofar dakinta ya shiga da salama
Hajia dake kwonce dan yanzu ta gama doguwar adu'ar da takan zauna ta yi bayan sallar asuba har sai rana ta fito sannan ta sake watsa ruwa ta kwonta dan so take ta fan huta kafin a jima wajen karfe goma ta fita cen wajen taron da suke yi yau dan ba mata masu fama da yoyon fitsari talafi da sunnan kungiyarsu
A hankali ta dago tana kallon mijin nata
Annurin musulunci daban yake, shi annurin musulunci tausasashe ne, ni'imarsa kuwa bata da iyaka, wannan bawa mai yawan sallah da nafila da ambaton Allah ya fi mata kowani namiji kyan kallo a duniya, annurin dake fita a murmushinsa kuwa ya fi mata komai dadina zuciya, gashi dai ya tsufa, fuskarsa du yabar tsufa ta bayana abinka da dogon mutun kuma fari tsufansa na gagawar nunawa, bale shi din ya kai tsufan shekara saba'in a duniya ai an sha ruwa, ama irin yadda yake da kuzari daidai gwargwado da kokari irin nasa na sakata jin nutsuwa a zuciyarta
Murmushi ta sakar masa tana karra jan hular kanta ta rufe gashinta da furfura ta kusan hadewa tana fadin" Alkali yau kai fa kanka? Na so sauka fa sai barci ya ci karfina"
Murmushi ya yi ya karasa bakin gadon ya zauna a ransa yana tunanin yau da gobe kayan Allah, tsufa labari, gashi yanzu shine kusan ba ruwansa da wannan lamari da ya yiwa naci a da, ita dinma da ta kasance cingan sarkin nacin miji a yanzu ba wannan a gabanta , abubuwan dake gabanta sun fi wannan fado mata a rai, kuma ana zaune, ana matukar kaunar junna da kula da junna, idan daya ya ce wash dan uwansa kaan rikice ya susuce
A hankali ya kamo hannunsa tana sake fuskantarsa, duda kwana biyu sun yi yar tsama a kan maganar ABDUL RA'UF ta nuna cewa shine bai yi masa magana ba da tuni ya amshi tayinsu ya masu biyaya, sai a yau take jin ta yafe , kanshin turaran miskinsa mai taushi na mata dadi a hanci ta ce" Fari mai farin gemu ko yinwa ake ji?"
Murmushi ya yi yana kallonta ya ce" kakar Fari bana jin yinwa, zuwa na yi da magana"
Sake fuskantarsa ta yi tana sauraronsa dan ta san ko meye yana da mahimmanci a zuciyarsa
A tausashe ya ce" Magana ce a kan Yarinyar nan, yarinyar nan marainiya ce, tana fama da kanta da neman hanyar da zata kare mutuncin kanta, sai dai hakan na neman gagara, har ya zamto wani marar jin tsoron Allah na dira mata gida da yara, ina so ta dawo gidan nan ta zauna har Allah ya fitar mata da mijin aure"
A tausashe ta ce" Wa kennan?"
Mai Shanu ya ce" Uman biyu nake magana a kai"
Dan jim ta yi tana dan tunani, sai kuma ta sauke Ajiyar zuciya ta ce" Allah shi kyauta, to kuma Kakan Fari sai an nemi shawarata dan wannan? Ta zo mana ga cen bangaren su Nana sai ta zauna tare da su"
Yana kallonta ya ce" Nana kuma?"
Hajia ta gyada kai tana kallonsa
Mai shanu ya girgiza kansa ya ce" Duda suma bana zaune da su a matsayin