Showing 69001 words to 72000 words out of 145392 words
Chapter 24 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ta sameta da ta ga ya juyo sai da ta rintse idannuwanta da karfi tana dantse lebenta da korar shedan a duniyarta, dan ta san ba komai zai sakaka jin tsoron kanninka ba irin aikin shedan a duniya
Kallonta yake yi daga tsayen da yake, tarin tambayoyi ne dankam a cikin zuciyarsa, sannin cewa bashida amsosinsu a dole ya dan kara takowa wajen da take a giciye, wani irin kwonciya ita ba a kwonce ba, ita ba a ringeshe ba ta cakumi abin rufa ta cumuimuye jikinta da shi sai kikifta idannuwa take yi kamar an jijiga bera a kwano
Tsoratar da ya ga ta yi a lokacin da ya nufota ya sakashi sake dan dakatawa yana kallonta, ajiyar zuciya take saukewa ta dauke kanta a kansa bakin fitsarar a cune tana kallon gefe hakan ya saka shi sakin dan murmushi sannan ya karasa ya dauki shadar zuwa diner dinsa a hannu ya kabe ya sake juyowa ya yi mata kallon da shi kadai ya san tarin tambayoyin dake cikinsa sannan ya juya bai ce mata komai ba ya fice a dakin
Amina na kallon gefe sai da ta ji rufewar kofar ta maido dubanta a kan kofar
A hankali idannuwanta suka sake cikawa da kwallah ta fashe da wani kukan da sam batada karfin yinsa da karfi
A hankali ta shiga fadin" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, wayo Allahna na shiga ukuna, innalilahi wa inna ilaihi rajune ina zan kai wannan abin kunyar? Wayo Allahna ni Amina da girmana da darajata yaro karami ya min wannan wulakancin a kan abinda nake yiwa datijo tanadi? Allah ne zai saka min zalina da ka ci!, Me na yi maka da zafi haka da zaka rabani da prde dina bayan ka san na san aurenmu na yan dakiku ne?, Idan ka saba kaida kake da sabuwar amarya yarinya irinka ka je ka yi shirmenka a cen mana? Yanzu da wani ido zan kalli duniya ta kalle ni? ( Ah to, a dai san a yadda za'ayi ido hudu da jama'ar gidan Ni zan ladabi, inaga harda wace ta dora katuwar tukunyar gashi)
Sosai Amina ta ci kukanta mai ratsa zuciya, kuka na takaici, domin bata taba kawowa a ranta cewa haka zai faru da ita Amina ba , duda ta san an daura mata aure da shi a tunaninta ai baba sai baba , yaro kuwa sai yaro bata taba tunanin cewa yaron nan zai saka hannu daya ya rike mata nata hannayen ya keketata uwa zannin atampa ba sai yau, mema ta taba yi masa? Me na arziki ya taba shiga tsakaninta da shi? A tunaninsa ga banza ya samu ko? Ga yar talakawa marar galihu shine zai wulakantata? In sha Allah ya yi daukan fari ba zai kuma dauka ba koda adashi ne ya zuba!, In sha Allah furucin kakarsa sai dai ya kare a kansa da wace take so ba dai ita ba, zata tsaya tsayin daka ya bata takardarta domin itama bataga ado a yiwa yaro kannin bayanta *Biyaya ba*, me zata ce a gaban mutane ? Yaro dan kannnin bayanta ya sauka a kan ruwan cikinta? Wannan shi ya fi kona mata zuciyarta ya fi sakata kuka, a dole take fashewa da kukan nan ba dan tana so ba
Da kyar ta iya jan jikinta ta sake mayar da kanta bayi
Ruwan da ya cireta a ciki ta zubar ta tara wani mai zafin gaske ama hannunta na iya zama a ciki
Sosai ta jure ta rintse ido ta shiga ta zauna tana ambaton Allah a cen kasan zuciyarta, ta sani ta ji ciwo, domin tana gannin jini jinin dake fita daga gabanta
Tsuru ta yi tana kallon ruwan yana dada dafa mata wajen har ya huce sannan ta fito da jan kafa ta koma ta sake dosanuwa a bakin gadon da ya yiwa wata irin jirkitaciyar shinfida tamkar makaho ne ya shinfida
Sauka ta yi kasa dan kasa zaman gadon ta yi
A ranta ta yi tsaki tana ayana' Ko me Hajia take tunani ne a kaina?, Nima ba shine nawa zabin ba, bani da wani hurumi a cikin lamarin, *wata kokowar* ba tawa bace, *neman na kaina* shi na fi hangowa a gabana, ni da na so na auri mutun tamkar dutse bashi da gaba bale baya?, Dan kawai *alkalamin kadarata* ya ajiyeni a nan ai bai gama zannani ba tunda ba raina ya fita daga gangar jikina ba, kasancewata *BAK'A* kuwa ba dan Allah ya tsaneni ya haliceni haka ba, inma ba mutun da raina mutun ba ai kowa nada tasa baiwa kamar yadda nake da *BAIWATA* ko?, Ba zan taka rawa a wannan *BADAKALAR* ba, idan ya bani takardata na bace sai na zamto tamkar zanen rubutu a saman farin allo a wajenki bi'izinillah'
Radadin dake tsikararta ya saka dole barcin rabi da rabi ne ke surarta, har lokacin sallar asubahi ta zo ta yi iya yinta dan ta mike ta koma bayin ta dauro alwallah aman ta kasa hakan, daga kwoncen da take kafafuwanta a hade take matsar kwallah tana astagfari a zuciyarta, idannuwanta kuwa sun karra yi mata luhu luhu tana tunanin ita kam wa zai agajeta? Wa zai dubeta? Wa zai talafeta? Amare na kwonciya su tashi da miji koda ba mai kula bane yakan dan nuna kularsa a wannan dare, danginka kan kawo maka ziyara a taimakeka, ama ita gashi safiya ta waye bata da gaba bata da baya, tana jin zanninta da danshin da take tsoron ko jinni ne ama ta kasa motsin gyara kanta, kardai ace wannan yaro ya farketa ne ya sakata a uku? Lalle da saidai ta zauna a haka dan babu wani mahalukin da zata yarda ya san abinda take ciki ta tonawa kanta asiri da kanta
Karfe bakwai ta gota, a lokacin ta fara jigatuwa da dukkan wani launi na azabar dake iya saka bawa fadawa a rashin lafiya irin su yinwa, kishirwa, ciwon jiki da kuma uban garin wanda du wata cikakiyar budurwar da ta kai mutuncinta zata iya haduwa da zazabin nan , bale idan akai mata irin hakar da aka yiwa wace ake tunanin ta fitar da biyu daga kasanta a lokaci daya
Kwonkwasawar da ake yi a hankali ana dan saurarawa ya sakata bude lumsasun idannuwanta ta kai dubanta kan kofar sannan ta bude bakinta cen ciki duda ta san da wahala a jita tana amsawa da cewa a shigo
Budewa Baba Lauratu ta yi ta shigo tana salama hadi da wara idannuwanta cikin dakin tana kiran " UMAN biyu? Ina kike ne?"
Ido Amina ta rintse ta kasa amsawa
Hello mutanen.....
*NZL PAGE2️⃣7️⃣*
Ido amina ta rintse ta kasa amsawa , Babar kuwa tana kalle kalle har idannuwanta suka sauka a kan Amina
Da mamaki tace" Toh? Barci ne haka? Kefa akoy nauyin barci bale idan kika gaji, to maza tashi tashi mu tafi umarnin Baba"
A hankali ta bude idannuwanta ta sauke a kan Baba Lauratu dake kallonta
Ido Baba ta zarro ta ce" Subahanalah menene a idannuwan naki haka ne? Ko bakida lafiya ne Amina?"
A hankali Amina ta iya budar bakinta tace" Lafiyana kalau Baba, lafiya na ganki warhaka? Ko Fido ce?"
Baba Lauratu tace" Lafiya kalau, kiran Mai Shanu ne ya sameni daga direba tunda duku dukun asubahi yace a zo da ni, ina zuwa yace maza na sadaki da dakinki, nace da shi me zai hanna a bari sai da dare ? Yace aa haka yake so , baya so ace uwar gida bata gidanta a lokacin da zata tarbi amarya, ashe shi baima san bakida lafiya ba, tashi ki yi wanka ki kimtsa mu tafi ana jiranmu fa"
Murya a raunane Amina ta ce" baba wani irin gidana?, Baba wani irin gida nake da shi da ya wuce na cen gidanmu? Baba dan Allah ki saka baki a bani takardata"
Baba ta sake kura mata ido, lamarin Amina ya fara bata tsoro fa kuma, irin yadda take saka damuwar abin nan a ranta ya fara damunta itama
A sanyaye tace" Amina, ina cewa mun yi da ke ki yi ta Adu'a ki fadawa Allah sannan ki yi hakuri ta tare a hankali sai a sake yin maganar nan?, Shin akoy wani abu da yasa zaki dawo ki take maganar da muka ajiye ne?"
Amina ta lumshe idannuwanta sakamakon rashin amsar bayarwa
A hankali Baba ta kama hannunta tana fadin" Ciciba ki tashi, keda kike fadawa Allah? Muma muke fada masa? Ki kwontar da hankalinki in dan rigimar kakar ABDUL ce, yanzu haka da na tambaya idan tana nan dan na gaisheta mai aikintace tace ta tafi asibiti, irin mutane masu halayanta Allah kadai ya isa ya daidaita su idan sunnada rabon shiryuwa, shi kuwa ai mun yi da ke ki kyale shi idan kun hadu gaisuwa ta hada ku, idan baku hadu ba babu ruwanki da shi ko matarsa ko?"
Amina ta rintse ido hadi da damkar hannun Baba a lokacin da Babar ta zaunar da ita dangalgal a saman duwawunta
Kasa bata amsa ta yi sai hawayen da ya shiga bin kumatunta
Baba ta dakata tana kallonta sosai tana son gane abinda ya sakata cije lebe haka
A hankali ta sake kamata tana son mikar da ita sai ta ga tana dudukewa haka kuma abinda take sin damkewa dan karta gani sai da ta ganshi domin hijabin dake jikinta fari ne tas
Hankali tashe ta sake duban yannayinta , sai kuma ta samu kanta da kallon gadon dakin
Sosai ta ji ta girgiza da tunanin da ya shiga kwakwaluwarta, kai harma ta so karyara hakan da ajiye haka a matsayin sharin kwatse kwatse ne na tunani
Da kula ta ce" Amina ki mike da kyau mana ki shirya kina ganni lokaci na tafia?"
Mikewar ta so yi, dan kwata kwata bata so asirinta ya tonu, duda Baba ce, ama Babar ce wace ya dace ta boyea tashin farko.sai dai ta makaro domin idan tace zata mike din kafafuwanta kuwa sai dai ta wara su
A hankali Baba tace" Me ya samu kafafuwan naki ne? Kuma jinni ne kike yi haka baki sani ba ya bata maki jiki?"
Amina ta dakata kanta a kasa, a hankali ta shiga shashekar kuka, sai kuma ta kasa rikewa ta fashe da kukan har ta kusan zubewa a kasa
Da sauri Baba ta tareta a jikinta ta riketa sosai tana sauraron kukan nata, har ta tsagaita tana jan ajiyar zuciya
Baba a hankali tace" Kin ji ciwo ne?"
Amina ta cije lebenta , a hankali ta gyada kanta dan koda bata san meye ko yayane ake jin ciwon nan ba tana ji a jikinta tamkar yankan reza akai mata a wajen nan
Baba bata ce komai ba ta rakata bayin ta taimka mata da komai a kusa ta ce" ki yi wankan ina zuwa"
A hankali Amina ta gyada kanta dake sade Har baba ta bar bayin wannan karronma a ranta ji take yi ba zata iya yafewa yaron nan ba gaskiya
Dukkan abinsa yake na bukatar Amina Baba ta daure taf sannan ta je ta kirawo ma'aikatan tana miko masu sunna saukewa wajen morocin dake jiransu wa'inda Baba ne da kansa ya bada umarnin a fitar da su
Kasa inda Baba yake ta koma, cike da jin kunyar maganar dake bakinta da nauyi bayan sun gama magana a kan sauke kaya da komai, cike da kula da dan jimamin dake saman fuskarsa wanda yake nufi da ya san abinda ya faru kennan ya tambayeta Aminar?, Kanta a kasa cike da takaicin Hajia, wadda ya dace ace da ita aka yi maganar nan, ko dan kasancewarta mace, ama firrrr ta ki abin ta ture, ta ce" Alhamdulilah Baba, sai dai jikin nada bukatar gannin likita"
Da kula Baba yace" subahanalah, aya, to ko zata iya yin jimirin zaman mota har zuwa gidanta ne sai likitan ya sameta a cen?"
Baba ta amsashi da eh
Baba ya ce" Allah ya bata lafiya, ku je Lauratu Allah ya tsare, zan zaunar da su idan kura ta lafa na masu nasiha, sannan za'a kawo biyu da yama idan suka sauko daga school, kin san tau litinin ta nasara muke"
Baba ta amsa baba da biyaya sannan ta mike ta koma
Ajiyar zuciya Baba ya sauke, yana fatan fitar da Hajia ta yi da nufin a kai Risala gidanta ya zamto Amina ta fara shiga gidanta kafin Risalar ta shiga, shifa ba yana hamaya da Risala bane, ko daya, hasalima zai so ace sun yi zaman lafia da fahimtar junna, sai dai take takensu da abinda aka fada masa na bincike ya saka yake taka tsantsan da son kankarowa Aminar nata itama mutuncin, yana yaki da matarsa , rufin asirinsa dan baya so a cuci marainiya, ya zamo mara uwa kuma uba dan alkhairin mahaifinta a gareshi yanada yawa, in ba Hauwau da manta alkhairi ba har ta manta irin taimakon da mahaifin Amina ya masa a lokacin da aka jefe shi ya kwonta, suka ringa fita kasashe neman magani abu ya faskara, shi dai mahaifin na uman Biyu ne ya samo masa magani na hausa Allah ya yi ta sanadiyarsa zai samu lafiya ya mike, ai da yanzu ta yiwu ko musakanta ta saka Hauwau ta barshi ko shi ya bar duniyar idan da karan kwana, shi ai in sha Allahu so yake yi ya samu nutsuwa dayarms ya bibiyi zaman auren nan nata, a yadda ya ga ana shagalin nan kaf babu ita ya fara saka ayar tambaya a kan hakan, rayuwa kennan,
Sosai Baba Lauratu ta lulube Amina da zannin gado, wani abin kunyar tamkar wata yar yarinya karama za'a yiwa rakiya gidan wanda ya girmeta, suka lulubeta da masu aikin gidan na hannun damar Baba, domin shi da kansa ya badu umarnin rakiya ma matar ABDUL
Wa'inda fuskokinsu ke bude suke da damar haukacewa ginnin gidan nan
Amina da idannuwanta ke lumshe tana jin yadda ake santin gidan da ilimi irin na adini ba da furta Wauh wauh ba ta tabe bakinta tana sake gyara zamanta, danma ta dake shiga wani ruwan ta ji sauki saukin wahalar dake damunta, kuma jinnin ba wai zubar da jinni bane irin na mai bini ko wace ke jinnin al'ada ba, sam bai kai haka ba, ba zuba bane yake yi daga cen cikin jikinta, baki bakin da take tunanin da farcensa ya farketa dan wajen ya masa kadan ne ke dan fitar da jinnin kadan shima idan ta bige wajen dan haka nrmal bata jin zubarsa sai dai tana jinta da danshi danshi haka na wani abu mai yauki da bata san ki menene ba
Du yadda Baba ya so wannan karron bai samu ba, domin irin yadda ya so ace Amina ta fara saka kaffarta gidan hakan bai samu ba dan kuwa motocin su Risala sun tsaya mata na fita sunna nufar bangaren da aka ce masu nan ne na amaryarsu motocin su Aminarma suka iso
Mata ne, lamarinmu ne , kowa ya san ko masu nikaf watau malamanmu ne zasu dan dakata a gaisa a mutunce, bale wadinnan din dama daidaiku ne cikin zababun fitsararun makusantan mahaifiyar amaryar suka yi mata rakiya bisa jan idon mijin maman amaryar domin Hajia shi ta yi kira ta bashi umarnin a kai yarinya dakinta yanzu yanzu, shi kuma ya ba wace ya isa da uta umarnin shima
"Abin al'ajabi baya karewa, wai kallo ya koma sama shawo ya dau giwa, meye wannan a luluben tamkar wata farin ciga duniyar ey yane? Ko tantagarin bariki ne irin na wasu matan? Lalle Risala kin kwaso da zafi, " Hajia Mabaruka ta fada tana janye gilas din dake saman hancinta tana kallon wajen su Amina kuma da karfi ta yadda kowama zai ji
Dubu ta yi murmushi tana kada kai ta ce" Gane min hanya makaho ya so gulma, oh to wai inace ta jima da tarewa da gotai gotan makota ne?"
A hankali Amina ta ja ta tsaya sannan ta saka hannunta ta yaye rufar da aka maka mata ta abin gado dake neman siketa, ga wasu kalamai da take tsinta a sama kamar da ita ake
Yayewar da ta yi ne ya hadasa hardewar idannuwansu
Risala dake rike da hannun kanwar mamanta , da Amina da hannunta ke cikin na Baba lauratu
Kallon kallon da suka yiwa junna ya saka Risala cire idannuwanta tana sake kausasa fuskarta ta dubi Dubu ta ce" Momcy mu je mana, bana so wani abu na raini ya fara gitawa tsakanina da wadda ni da ita sai dai na dauketa aiki ta wanken bayi ta wanken tiles domin ko girkina bata kai wajen da zata dafa ba"
Amina dai a tsaye take tana kallon ikon Allah, ita abinda ya fi daure mata kai wai a cikinsu wacece matar ne? Babu wace ta yi rufa ta mutunci kowace tamkar zata yar da dan yalolon mayafin da aka rufa dan cikashe gayu
Wace dai take tunanin ta yiwu ko itace kuma sai ta ga ai yarinya ce karama ko menene? To wannan ai da ta yi auren wuri sai ta haifeta fa? Tunda anya zata wuce wata sha bakwai haka?, Sai dai furucin bakinta ya sakata yi mata kallon baba da yaro, watau ki yi aniya ki kama kanka kar na saka bulala na zane maki jikinki tasss, dan gaskiya ba ,zata so ta dauki rainin kannen matar tasa ba gaskiya
"AMINA, mu tafi dan Allah ko jikin ne?"
Baba Lauratu ta fada a sanyaye, dan ita kam mutanen nan sun samu galabar firgitata, wannan cakewa haka? Kowace kuwa ta sha suturar da ba dai talaka yace zai dana ba
Fuska ta kwashababe ta so cewa baba ta daina tambayarta haka itafa ta warke, duda azabar dake sukanta, sai dai ta fasa dan itama ta bude fuskar nan ne dan ji take yi kamar tana tafia sama da kasa ne ga kuma numfashinta dake son tsayawa dan sun nadeta sosai walahi
Sai kuma ta fasa cewa koman ta sake juyawa wajen babar ma'aikaciyar Hajia dake masu bayanin ga bangaren AMINAR nan, domin bayan an gama saka komai ita baba ya turo ta zo ta gane masa lamarin kicin komai ya ji?
A hankali ta ci gaba da dan takawa, wanda dama tunda akace ko jikin ne ya tsayewa Hajia Mabaruka ta sake samun abin magantawa, wani yananayi ta yi na son sai ta dizga Aminar tace" To wai wace irin rashin lafiya bayan ga dukkan alamu kema yau kika