Showing 93001 words to 96000 words out of 145392 words
Chapter 32 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
makaroni ta dafo shapshao ta juyo masu a baban plat sai turiri take ta sha kayan lambu da kifin gwongwani , kana kallo sai ka hadiye yawu koda baka shirya ba ta ajiye masu a saman table sannan ta dauki tuwonta tana fadin" Allah na tuba tuwo ai zaune yake darrr , duma wanda ya wulakanta shi zai nemeshi ne , in dai tuwo ne, karma a ci mana masu sonsa ai da yawa......yaushema in ba karyar biyu ba"
Su dai babu wanda ya tanka, hasalima ABDUL ke jujuya abincin hayakin na raguwa yana kuma sauraron habaicin da harda shi ake yiwa yana murmushi a cen kasan zuciyarsa
Tsaf suka ci abincin suka gama ta kwashe komai ta kai kicin ta dawo ta idasa tatare wajen ta kimtsa a ranta tana tunanin yanzu yaya za'a yi da sauran tuwon nan mai yawa ne? Ta tabata za'a zubar ne fa ko mene? Har ta zo zata shige ciki ta ji ya kamo hannunta ya janyota baya , bata ankara ba ya zaunar da ita darr a saman cinyarsa
A zabure ta mike tana ruruko ido ta ce" Kai"
Hannunsa ya saka ya maidata saman cinyar tasa sannan ya saka hannayensa ya rungume bayanta ya hadeta da kirjinsa
Marmar ta fara da ido gabanta na dan faduwa ta sake neman surmiyowa tana fadin" ABDUL wai menene haka ne ?, Ka cikani mana dan Allah nifa bana son abubuwan nan na rashin kunya da kyakyashewar ido haba dan Allah, ka tashi ka tafi wajen matarka kar yarana su manta wani abu su fito su ga wannan abin taba hankalin yaron"
Murmushi ya yi yana sake zaunar da ita dandar a jikinsa cen kasa yace" Ita ai an tafi da ita gida batada lafiya fa"
Amina ta yi shiru sai kuma ta juyo cike da son tsegumi ta ce" to me ya sameta ne?"
ABDUL ya murmusa har sai da kumatunsa suka lotsa ya ki bata amsa sai idannuwanta da ya kafe da kallo
A hankali ta cire dubanta tana sake som tashi
"Ita maman biyu, i mn wace ta haife su inane gidanta ne? Yaya aka yi ban taba ganninta ba?" Ya fada cen kasa yana sake kai hancinsa yana sinsinar wuyanta dake kyali zuwa kirjinta da yake jin kamar ya warto shi da karfi ya ciro..................gaba daya wunin yau haka ya wuni cikin zaburar zuciya da tunani.....ya kasa ci gaba da sharetan har cikin ransa, ya gaza samun sukuni motsi kadan sai ya saki murmushi idan ya tuno wata diramarta, Risala na kiran gidansu da ya fita sallar azahar yana dawowa ya tardota cikin kukanta ya sake kamanta rarashinta , fir ta ki sauraronsa har aka zo daukanta daga gidansu, abinda ya bashi mamaki da haushi har ya shige ciki bai ce masu komai ba mamanta ce da kanta da kanwarta suka zo daukan Risalar, ana wani fuzge fuzge irin sun gano ya kwonta da yar ne, suka nuna da ita zasu tafi dan sun yi tunanin yanzu ya fara ratsa duniyar mace ne, a tunaninsu zai kwonta ya ringa magiyar kar su rabashi da duniyar maji dadi ne, sai suka ga ya masu fatan alkhairi ya shigewarsa, da haushi uwar ta tatara y'arta suka tafi da nufin sai ta yi jinya ta warke zata dawo, kamar a kanta aka fara kai bidurci gidan miji? Kamar ita ta fi kowa gata a duniya?, Watau su nasu iyayen sun rasu ko? Itace mai iyaye...................
"Tana nan, tanada tsohon ciki ne bata iya fita" Amina ta fada muryarta na nuna damuwa ƙarara a cikin furucinta
A hankali ya dubi fuskarta yana son karantar abinda ya fahimta a muryarta
Amina ta saka idannuwanta cikin nasa ta ce" ABDUL, ina so na je na ganta ka ga kwana biyun nan sam bana barci ban yi mafarkinta ba...., ABDUL ni kadai takeda a duniya..... dan Allah kar ka zamto miki a rayuwata ta hanyar shiga tsakanina da y'ar uwata"
Ashe ta iya tausasawa? Ashe tanada baban rauni bayan Biyu? Ya zata biyune kadai idan aka taba ake cin mata koda bata shirya ba, sai yanzu ya gane bayansu akoy watansu
Murmushi ya yi yana sake kallon cikin idannuwanta da suka cika da kwalar son ta fashe da kuka, bakinta da ya tabe kamar na yar baby , fuskar gaba daya ta dauki kala na son yin rigima..........
A hankali ya samu kansa da rungumeta a jikinsa ya dora kanta a kafadarsa yana dan shafa bayanta
Sun dauki lokaci a haka Amina ta ce" Zan tashi"
Murmushi ya yi yana gyada kansa ya saketa ya bata dama ta tashi tana ta murje murjen da bai san ba shin Uman biyu wanka ne bata yi ba ko irin abin nan ne na yara idan wani abu na damunsu da zaka ga sun rikice da soshe soshe
Dakinta ta nufa tana fadin" Sai an jima"
Kai ya gyada yana kallon bayanta har ta bacewa ganninsa
Mikewa ya yi a hankali ya nufi dakin yaren bayan yaa kashe komai ya rufo ya shige ya samu kamsa da kwonciya a tsakaninsu yana kallon fuskar Husaini yar kutub da ita yaron ya karra kiba mulmul
A hankali ya ce" ko dai tanada wani da take so na tauyeta?"............
A hankali ya ce" Ko dai tanada wanda take so ne na tauyeta??????"
Sai kuma ya samu kansa da faduwar gaban jin abinda ya fada din, bai san dalili ba
A hankali ya juya a saman bed din yana lumshe idannuwansa hadi da sake neman barci
Da asuba sunna dawowa daga masalaci tare da yaren ya rakasu dakinsu domin yana son komawa nasa bangaren ya ja carbi har rana ta fito
Yana fitowa ya ringa jiyo kwaramniya kamar daga cikin kicin take fitowa
A nutse ya nufi kicin din da tunanin waye da duku dukun safiya yake kwaramniyar nan?
Gannin ba kowa a kicin din ama fes fes yake sai cokula dake zube nan ga dukkan alamu an cirosu ne, ya nufi hanyar da ya fi jiyo kwaramniyar domin ya ga kofar bayace a bude, dan haka a nutse ya fice sai ya ja ya tsaya yana kallon ikon Allah
Amina ce ta sauka kasa ta duka sosai wajen itacen nan tana hurawa da bakinta domin wutar ta mutu ne kuma du abubuwan fifitar nan Amina ta fi gane hurawa da bakinta, ga wani daurin zani da ta yi a saman wata riga mai siririn hannu ruwan copee
Hular kanta ce ta fadi , ta dakata ta dauka tana lalubar birke ta daidaita ta shiga kunnawa tana fadin" Kayan aiki du na nasaru, yanzu ace wannan abin mai ruwa a ciki ne zai bada wuta? To wai kananzir ne a ciki ko ruwan nasaru ne?, Shi yasama ya kasa hasa wutar gashi zubi daya tak na yi tunda duku dukun duhun asubahi kar safiya ta waye Baba ya yi jiran wainarsa ina nan ina gantali da itace!"
A hankali ya jingina da jikin kofar ya harde hannayensa yana kallonta fuskarsa dauke da yannayin da shi kansa bai san ya kai cen ba
Murmushi yake yiwa dukkan motsinta, ya shagala da kallonta, komai take yi sai ya daukeshi daban, ya bashi fasara daban, ya nemi waje daban ya ajiyeshi mai matukar girma da son daukaka lamarin a bayane, ita batama san yana wajen ba domin hayakin nan da aikinta ya fi komai daukan hankalinta
Hayakin ne ya fara janyo hankalin ma'aikatan gidan masu kula da gidan, maza kennan, domin ko'ina shukoki ne, hayaki dai irin haka a gaskiya basa fatan gani domin ko shara ba konata ake yi a gidan ba bale ace hayakin shara ne, dole zasu duba su ga ta inda yake fitowa
"Aminu, ka ga ka bi ta cen ni bara na bi ta nan mu yi gagawa mu ga ta inda hayakin yake fitowa, ka ga wannan hayaki haka ai ba lafiya ba" usman ya fada yana sakin hanyar ya nufo dayar hanyar, shi kuma Aminun ya nufo hanyar da Amina take
Da dan sauri ABDUL ya fito ya ratsa ya wuceta ya nufo hanyar da ya tabata ta nan za'a bilo a tardo uman biyu ta bararaje tana buga tsugunon nan a haka ita ga mai tuyar waina
Sai da ya wuce ta lura da shi
Samun kanta ta yi da yin dogon wuya tana karra tabatarwa kanta shine, sai kuma ta koma ta dauki hijabinta ta saka ta dauko mafici tana fifita wutar , Allah ya taimaketa ta tashi ta ci gaba da suyarta hankali kwonce, kanshi kuwa ya gama gidan tuni, masu kaunar waina bakinsu ya gama rikicewa da hadiyar yawu
Kusan zubewa ya yi a kasa dan gaisar da uban gidansa
Yana dan dube dube ya ce" Sir dama hayaki ne muke ta gani shine muke neman wajen"
ABDUL ya gyada kansa a nutse ya ce" Ni na hasa shi"
Kai Aminu ya gyada ya mike yana mai yi masa fatan a yi sallar juma'a lafiya
ABDUL ya dan yi gyaran murya yana fadin" Ji mana Aminu?"
Aminu ya dawo ya sake dukawa
Abdul ya ce" Kana ji, du ranar juma'a zakunna gannin hayakin nan, Uman biyu ke tuya, bana son gannin kowa a nan wajen ka fahimta?"
Aminu ya amsa shi sosai sannan ya mike ya tafi
Ajiyar zuciya ya sauke ya koma wajen da take tuyar yana kallon an saka hijabi ashe
Karasawa ya yi wajen wani kyakyawan kwano mai rike zafi an rufe shi da wani farin tawul ya dan tsuguna ya bude yana ciro guda hadi da jujuyata sannan ya yi bismillah ya kai bakinsa ya gutsura yana taunawa a hankali, sai kuma ya saki jikinsa da taunawar domin ta masa dadi a bakin nasa
Amina dake kallonsa kasa kasa ta ce" Baka tsoron kar aje na yi bade baden magani a ciki na asiri?"
Kalonta ya yi da dan mamakinta
Sai kuma ya yi murmushi yana idasa cinyewa ya ce" Uman biyu zan ci nima yau wainar, tai min dadi a bakina.....zaki bani?"
Samun kanta ta yi da sada kanta dan wollah sai ta ga kamar maganar da bata so ce ya yi mata, kawai sai maganarsa ta zai sha ta fado mata a rai jama'a,
Gaba daya tsigar jikinta sai da ta tashi, ta sake sada kanta tana dan bubuga tandar suyar dan gaba daya nema take ta rikice
Mikewa ya yi ya shige ciki ya dauko plate ya dawo ya sake budewa ya zuba kwaya hudu sannan ya koma gefe ya zauna yana kallonta tana tuyar kanta a gefe sam bata so su hada ido
Kunyarta na saka masa nishadi, bai san dalili ba
Koda ya gama cin sai da ya ga ya matse mata waje ya hanna mata motsi yadda take so sannan ya mike yana fadin" ki fa shirya karfe goma mu ajiyeki gidan Fido kafin mu wuce wajen baba"
Da sauri ta dago kanta tana kallonsa ta ce" Allah wai?"
Turus ya yi ya juyo, dan har ya kusan shigewa ya tsaya yana kallonta, to wai hala so take ya ja rantsuwa da ta tsatsareshi da ido, hm Amina kennan yanzu idan wani abin ne ta iya bude baki tace ita babace
Sharewa ya yi ya ce" Idan kika saka suturar dake lafe maki a jiki kuma sai dai mu yi tafiyarmu mu kadai"
Dariya hadi da farin ciki suka hade mata tana fadin" aa aa, in sha Allah bama zan saka ba, wayo Allahna dadi yau zan ga fidona"
Juyawa ya yi ya tafi dan ya koshi ainun so yake ya dan huta koda na awa daya ne kafin su fice gidan Baba su yi hirar safe sai su wuce masalaci tare
Da zumudi ta gama tuyar ta zubawa masu aiki , ta zubewa baba sauran ta rufe ruf ta dora miyar da yake ci da ita ta wuce dakinta
Tun a lokacin ta shiga shiryawa cike da zumudinta , yara kuwa sunna ji sunna gani barcin ya gagaresu domin kiri kiri mamansu ta hanna masu barci ta sakasu yin wanka ta ciro masu jalabiyoyi biyu iri daya da takalmansu ta koma falo tana ta aikin murmushi tana duba lokaci a wayarta
Karfe goma ta gota ya shigo da salama a bakinsa yana dan kallon falon da mutanen ciki
Zamanta ta gyara tana sake baza hijabin jikinta irin ya gani din nan bai matseta ba sannan tana washe bakinta da murmushin da sai ya rantse dai ba na Allah bane dan kawai yace zai fita da Uman biyu ne take washe masa baki har haka
Ratsawa ya yi ya shige dakin biyu, suka rakashi da kallo baki dayansu
Jim kadan ya dawo hannayensa rike da shadoji iri daya ya mimikawa kowane yana fadin" ku cenza kayan nan"
Amsa suka yi , kowane ya nufi inda zai labe ya cenza suturarsa,
Da kallo ya bisu ya juyo yana murmushi ya ce" Wai zuzuzu dinsu zasu boye miki"
Ido Amina ta zarro ta juya da dan sauri tana nufar wajen table dan dauko kwanonin wainar nan a zuciyarta tana ayana' Sam ba kunya a lamarin ABDUL'
Tana kawowa ta ajiye ya bi kwanonin da kallo ya gyada kansa ya ce" Kin san na kula yannayin tafiyarki ne yannayin nuna halitar jikinki, kawai ki daina tafiya da sauri sai bombom din su daina dancng......"
"Kai jama'a" ta fada kasa kasa ta sake yin shiru, dan dai burinta ai su kaita inda zata je , bata so ta biye shi su yi wani fadan ya sake hanna mata fita
Cikin motar suka shige, biyu a gaba su biyu, ita da shi a baya a zaune, sai sasada kai take yi tana tunanin idan aka ganta a make a wannan shareriyar motar ai ta gama siyawa kanta zunde da yagalgala, bama irin wa'inda suka nuna mata soyaya ta kiya, ai har ance dama kudi take so ba wani datijo ita kuma du wanda ya fasarata haka ya cuceta Allah ne zai saka mata
A hankali yake jansu, sai da suka je anguwani uku sunna sauka da biyu da shi kadai da direba su shiga su fito sannan suka dauki hanyar gidan Fido tana kwatanta masa yana fadawa direban kamar wani wanda aka saka dole sai shi zai fadawa direban har suka iso kofar tsakuraren gidan Fido din direban na tuki a guje kamar zai tashi sama, ta kula da direban da ABDUL din du kamar yan daba Walahi
Ido ya zubawa kofar yana kallo, sai kuma ya dubeta ya ga tana washe baki ta kama kofar ta bale ta fita harda yi masu byby abinta ta tsalaka kwatar ta nufi soron kofar gidan
Basu tashi ba domin a tunaninsa zata dawo ta yi masa iso ne su gaisa da kanwar tata, haka kuma a tunaninsa ai biyu zasu sauka su gaisar da mahaifiyarsu, sai ya ga basu motsa daga inda suke zaune ba
Da kulla ya ce" Boys ku je mana"
Husaini ya juyo ya kalle shi, sai ya juya yana girgiza kansa ya ce" Dady ai bama shiga, idan muka shiga mijin Aunty ke dukanmu , itama ya doketa, yace maza basa shiga gidansa wai"
Daga Abdul din har direban a zabure suka kalle shi,
Abdul ya sake fuskantarsa da kyau ya ce" Husaini, ba nan ne gidan mamanku ba?"
Husaini ya kalli Hasan, Hasan ya kalle shi, Hasan ya juyo yana kallon ABDUL ya ce" Dady gidan kanwar mamanmu dai ko? Gidan aunty ne nan, mu mamanmu ba a gidanmu sabo bane kace gidanta cen ne gidanta ko?"
Sai yanzu ya tuna wa suke duba uwa a duniya
Sai ya ji haka kawai ya kasa bada umarnin su tafi
Haka kawai ya ji yana so Uman biyu ta fito su tafi gida kafarsa kafarta, bai san dalili ba sai ya ji gaba daya hankalinsa na kan gidan
A hankali ya bude bangaren da yake ya fito ya tsalaka wajen mazan dake zaune sun zubawa motar ido tsuru sunna kallo
Hannu ya basu suka ringa gaisawa da kula sosai sannan ya nemi waje ya zauna a kan bancin da aka marmatsa masa ana yi masa bismillah mana
Habu mai teburin ya ce" Malan bako ne ba? Sai na ga kamar gidan Mudi kuka sauka?"
ABDUL ya yi murmushi yana gyada kansa ya ce" Eh, na kawo madame ne ta ga kanwarta, inaga matar gidan itace kanwar tata"
Saley ya sauke ajiyar zuciya yana fadin" Alhamdulilah, dama yanzu muka gama maganar yarinyar, muna yi mata ADU'A, muna fatan Allah ya amsa, ace yarinya a kan gwuiwa yau kwana biyu tana fama ama ya ki a mikata asibiti? Yanzu da kai ya waye Allah na tuba ai ba'a haihuwar gida, mata na wahala ana kallonsu har sai sun lalace a yi watsi da su, ko idan abu ya zo a mace ko su su mace sai kaji ana fadin lokaci ya yi, eh Akoy maganar lokaci,wanda idan ya yi ba tsumi ba dabara, ko a ina kake ko a karkashin kulawar wa kake zaka tafi ne, ama kuma akoy mugun hali na wasu mazan,Allah na tuba wannan asibiti ta gwamnati da yan kudaden da zaka kashe basu taka kara sun karya ba kake yiwa macen bakin ciki?"
Audu ya ce" Kai fa saley kanada matsala, aishi wannan mutumen bama maganar kudin bane inaga, wannan bakin hali nasa sam bai masa rana ba, wai sai ace maza sunnada kishi basa so namiji ya bude masu mace ya amshi haihuwarta, ni fa nan da ka ganni da innar baban gida ta jigata gwara namijin ya amshi haihuwar tata, to Allah na tuba lafiyarta ai ta fi min komai a duniya"
Saley ya amshe da fadin" Kai kace, bale yanzu fa mata ke amsar haihuwar nan,mata ilimi suke yi sun amshe abin fa, maza kuwa su duba maza yan uwansu, dama in ba mai laluwai a hannu ba ina kai namiji kato ina karatun feraye matar wani? In ba so kake yi ka ringa shiga hurumin da ba naka ba"
"Ku dai kun shiga uku da bakinku walahi, kun ga sai maganar nan kuke tunda safe matayenku sun zigo ku kun zubawa kofarsa ido kun kasa aikata komai sai saka da warwara kuke yi, inace yanzu na gama maganar mu kai kara wajen mai gari a fitar da yarinyar cen a kaita asibiti kuka nuna aa aa wannan ba huruminku bane, sai da mutun ya zauna zaku saki baki kunna cakalkalarsa, idanfa dan uwansa ne?" Mubashir ya fada da dan fada fada, domin tunda safiyar juma'ar nan ta waye suke kan maganar nan, ama da Mudin ya fito siyan garin kwakin ashirin hannu hannu suka ringa bashi sunna gaisawa shi kuwa yana wani cire kai kamar wani tsiya, wai shi