Showing 108001 words to 111000 words out of 145392 words
Chapter 37 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
sake cewa komai ba dan ta lura bai da niyyar yi mata magana, sai dai ita ai bata ga abinda ta mishi ba, kuma tunda har ya zo gidan da kanshi ya nemi ta koma, to tabbas yana buƙatarta ne a gidan, dan ta san wannan uwar biyun ta bakinshi ba abinda za ta iya tsinana masa dan ita ce sabuwa fil a leda.
Sai dai bata san Abdul ya amsa kiran mahaifinta ne ba wanda ya na girmamashi fiye da yadda a yanzu yake ganin mutumcin Mamanta, ba dan ya kirashi ba da ya so ya barta ta yi ta zama a gidan, idan an tamayeta dalili ta ce dan ya je mata ne ta zo jinya gida, aikin banza kawai! Shi bai ma taɓa ganin irin wannan rashin hankalin ba a rayuwarshi.
Sunna karasawa gida yanzu bai ciro jakarta ba, hasalima bangarensa ya nufa yana amsa waya da ta shafi kasuwancinsa
Itama fitowa ta yi tana yatsina, ita ga matar oga matar so,
Da isa ta dubi Muhammat ta ce" Kai ka daukon jakata ka kaita bangarena"
Da mamaki Muhammat ya kalleta, sai kuma ya dauke idannuwansa da sauri domin hijabin ta kwashe ta bi bayan Abdul
Tana shigowa yana gama wayar a zaune saman kujera ta shiga fadin" Bab, yanzu fisabililahi kana yi min adalci a rayuwa kuwa?, Ka duba ka gani a yadda aka daukeni aka tafi da ni, ashema kanada bukatata a gefenka ka wani shareni ba kira ba amsa kirana?, Bab soyaya fa ba karya bace, ni masoyiyarka nake ba makiyiyarka ba"
Da mamaki yake kallonta, zai bata amsa aka sake kiransa
A dole ya duba ya daga ya shiga amsawa
A kalaman da yake yi karara ta fahimci gini ne aka yi a cikin gidan nan da ya dauki sunnan Mom twins gyaran amare, wanda ta ji da kunnayenta yana maganar cewa yanada bukatar wajen ya yi fili, kuma dukkan abubuwan bukatar da aka kawo na ginawa a saka a tabatar sun shiga wajensu a tsare kamar yadda ya bada a hoto
Sun dauki dan lokaci sunna wayar dan mutumen famar da yake yi ya leko wajen, ama yace aa shi ba yanzu ba yana dai so a gama komai idan an gama zasu zo tare ta gani shima sai ya gani, abinda bai yi mata ba sai a cenza mata
Risala har idannuwanta ke neman rufewa da duhu da tashin hankali
Kallonsa kawai take yi har ya katse kiran ya juyo sashenta ya ce" Sorry, mema kika ce?"
Maimakun ta dawo kan maganarsu, sai ta sake dubansa tana fadin" Abdul, gini menene ake yi ne?"
Idannuwansa ya lumshe , sannan ya sake budewa ya ce" Wajen gyaran are ko mene, Na maman twins ne"
Sake dubansa ta yi ta ce" Kuma a cikin gidan nan?"
Shima dubanta yake dan son gane me take nufi
Risala ta dafe gaban goshinta ta ce" Bama wannan ba, wai ba kace ka hanna mace sana'a ba?, Ba kace ba zan yi aikin saloon dina ba?, Ba kai da kanka ka shiga tsakanina da nawa neman ba?, A kan me ita zata yi?"
Da farko ya so hawa ta hanyar da ta hau, watau kalubalantarta ita da kanta kafin ya tsigeta daidai da laifinta
Sai kawai ya ga ciwon kai ne zai dorawa kansa mai zafin gaske
Dan haka yana dubanta ya ce" Ba sana'a na hanna mace yi ba, bana son sana'ar da mace zata yi a waje ne, idan kema kina so sai a maki naki a nan cikin gida sai ku ringa yin abinku a cikin gida, ai nema hallal ne, ama ni na fi gane na cikin gida wa iyalina"
"ABDUL, kennan kana nufin zama zaka yi na aure na dindindin da wannan matar da har kake kirrarin iyalinka? ABDUL hakan na nufin matar aure take a gidanka mai darajar da har ta samu wajen sana'a a cikin gidanka wanda yake nufin bakada niyar rabuwa da ita?" Risala ta fada a sanyaye
ABDUL ya dago daga ringeshen da yake yana kallonta
Risala ba zata daina bashi mamaki ba a rayuwa
A nutse ya ce" Kina ji, da san samu ne mu ringa kauce irin wannan magangannun, kin ga kamar yadda kike da daraja a wajena haka takeda ita, maganar na zauna da ita ko aa wannan kuma ni ta shafa, haka kuma maganar abinda zan iya yi dan kyautatawa dayarku, Risala bana mayar da abu dole idan ba adininane ya koyar da ni ba......Amina matata ce, bayantama ban maku alkawarin auren zobe ba bale ki damu kanki, tsakaninku baki daya kuwa kowa ya yi ta kansa kawai, wanda ya iya allonsa ya wanke .....ai fili ne a gabanku!"
Yana dasa aya ya mike ya haura sama dan futa zai kuma yi, ga wayar da Baba ya masa a kan auren jikar Baba Rabi'u na yana son ganninsa dan gudunmuwar da zasu kai, ga kuma zuwa da zai yi kauye su ga wasu dabobi da aka ce magada nada bukatar kudinsu, garke ne har shida na mahaifansu, zasu raba gado
Shi kam abubuwan dake gabansa da yawa , ba zai zauna Risala ta ringa bata masa rai ba! , Tunda batada wayau ai sai ta yi ta yi.
_____________________________________
Tunda Risala ta dawo aka ci gaba da gabatar da zaman kwana daidaya a tsakanin iyalinsa, rigimarsu suke yi a cen tsakaninsu a dalilin ginin gyara, kasancewar kowa da part dinsa ba lale ka san me dan uwanka ke ciki ba idan ba zumunci kuke yi ba, ko kuma kunna yaegumtar junna
A wannan rigimar Harta baba sai da ya shiga, yace kuwa yana bayan jikansa, idan zata yi aiki a cikin gidanta ba laifi ta yi, in ba haka ba ta hakura, shima da ya yarda macen ta fita gashinan abinda ya haifar masa!
Karshe dai mahaifiyarta ta tsaya kan ya zuba mata kudin da ya kashewa Amina tunda hakinta ne ai itama a asusunta, a zuciyarta kuwa ta kudurta a dai zauna zama mai sunnan zama, da kansa zai yarda ta koma bakin aikinta ne
Kwanaki daidaya da yake masu sam Amina bata gane hakan sosai ba, domin yakan daga mata kafa ne idan ya gaza yake tarda ita da dabara da wayo ya cin mata, sai komai ya lafa ta gaza dago ido ta kalleshi dan kunyarsa da kunyar kanta, shi kuwa babu abinda yake sakashi daria irin lokacin, da ganganma yake mikewa yada ya fado duniya a gabanta ya yi tsaye, watarana har ihu take ta fice bayi da gudu tana fadin sam bashida kunya wannanba hali bane!, Ya yi ta dariarsa shi kuwa.........
Baban abinda ke saka Amina a farin ciki a yanzu idan ta daga ido ta ga irin walwalar da kanwarta ke tsinta a hankali a hankali
Bama idan ABDUL ya masu shigowar yama,
A da takan gudu ta barsu da yaren da su Firdausin
A yanzu kuwa sai kawai ta zauna nesa ta ringa mamakin tadinsu, da walwalarsu, da wasa da dariya
Bama abinda ke sake sakata dariya sai Fido ta ce masa wai wani Dady, shi kuma ba kunya ya amsa abinsa
Takan ji wani irin farin ciki idan ta ga sunna kus kus da Fido,
Sam bata taba sannin me suke fadi ba, ama a yadda suke dinkewar su yi kuskus harma da Baba idan tana gidan sai ta ji wani irin kwonciyar hankali na samunta a cen kasan zuciyarta
Da wannan ta je ta zanna jarabawarta, jarabawar da ta ringa shan wahala a kan ajiyewa kadai bama har ta samu damar zannawar ba
Jarabawar da babu abianda bata ganni ba a kanta
Har an so a wulakanta mutuncinta a kanta
Har an so a wulakanta mutuncinta a kan jarabawar nan
An nuna mata idan tana so ana iya bata hanya ama idan itama zata bayar da wani abin da take da shi kuma takeda iko da shi
Kiri kiri saboda dan cikon da bai taka karra ya karya ba aka rike mata hannunta harma aka so a nuna mata itace ta ki ci gabanta a duniya
Sai gashi ta zannata a mutunce, a kamilance, a hakimce a bayan motar da Muhammat ya ja bayan ABDUL ya yi mata adu'ar Allah ya tsare ya bada Sa'a
Suka je ta shige aji ta zanna ta fito ta samu Muhammat na jiranta, harda abin karin da ta sha mamakin yadda aka yi ya san yinwa take ji, har mamakin kanta take yi kafin ta fito fa sai da ta karya tare da Fido da ta yi dan wake tun da asusuba, ta ci dan waken nan kamar ba gobe, kuma sai gashi tun kafin a fito wata yinwar na yi mata wawushe da kayan ciki, kuma yinwar nan fa idan tana ji bata jin kunyar cin abinci a gaban kowa
Bata san tana ci hannu baka hannu kwarya ba a cikin motar sai da ta cinye tana lumshe ido tana kora ruwa mai sanyi ta dubi wajen Muhammat ta ce" Ama muhammat wannan dambu ya yi dadi, a ina ka siyo shi?"
Muhammat ya yi murmushi yana kadda kai, watau abinda ya faru ogansa ne yace da shi a ina za'a samo abincin gargajiya, dangin abinci dai na gargajiya, idanma da hali harda dadawa
Shine ya je ya samu Matarsa ita kuwa ta kaishi gidan da ake yin dambun nan suka siyo
Yana kai masa yace aa ya je daukan Uman biyu da shi zata so samunsa a wannan lokacin
Har yana mamakin dambu kuma uman biyun?, Sai gashi ta cinye tsaf
Muhammat ya ce" Mom twins ai a gidan wata kawar madame na siyo shi"
Amina ta gyada kai tana fadin" Muhammat ta iya dambu, man kulin nan da ta saka ya yi dadi sosai, mu je mu karro in ajiye da yama na ci, sai na ji ko kulun shi zan ringa ci ba zan gajiya ba, ama ka san wannan dambun ba na gaz bane ko Muhammat?"
Muhammad da ya dauke wuta tunda tace su je su siyo yana tunanin ai bama zai tarki zuwa da ita ba Sir ya nadi hancinsa ya ce" ai da itace take yi, ko man da itace take soyawa, ai bakiga ba tsaftarta, ama yanzun gida zan kaiki sai na koma na gani idan akoy na karro maki"
"Aa Muhammat, ba gida zaka kaini ba gaskiya, zuwa zamu yi na siyowa baba, na tabata idan ya taba dambun nan gobema sai ya sa an siyo masa, mu he mu sayi da yawa a kai masa nasa nima na tafi da nawa gida" Amina ta fada tana buda yar jakarta dan ta ga tanadin jakar, kar aje ba nauyi tana ta maganar aje ta sayi dambu
Waje ya samu ya parker yana fadin" to bara na amsa kira na dawo mu tafi
Daga motar ya fita ya koma gefe ya danna kiran ABDUL da fatan Allah ya sa ya daga da wuri, duda ya san da wahala ya ki dagawar , ama kuma idan aiki ya masa yawa yakan ki dagawarma
Koro masa bayani ya yi dala dala, wanda hakan ya saka ABDUL neman excus ya fito daga dakin meeting din da suke yi da bakinsa yana sake fadin" Wai kai wa ya aikeka fada mata ga inda ka siyo? Muhammat bakinka ba dai magana ba, yanzu idan babu fa?"
Muhammat ya ce" Nima abinda nake ta tunani kennan, kar dai ta yi wannan kuka nata na shiga uku"
ABDUL ya dafe gaban goshinsa ya ce" Kana ji, ka fara kiran matarka, ta je ta yi jiranka a zuba a daure, ka yi ta yawo da ita kafin ku karasa a tabatar an daure komai , kawai a miko maku , ku je wajen baban daga cen sai ka maida ita gida"
Muhammat ya ce" In sha Allah sir"
Har zai katse ya ce" Kana ji?"
Mummamat ya amsa da "eh sir ina ji"
"Muhammat kar ka yi tukin ganganci da ita ka ji?" ABDUL ya fada a hankali yana duban agogon hannunsa.
Muhammat na murmushi ya sake fadin" Bi'izinillah Sir"
Ai ko gidan suka wuce, Muhammat ya fita daga motar ya jira kaɗan matarsa ta miƙo masa dambun sannan suka wuce gidan Baba mai Shanu.
Tunda suka shiga bayan sun gaisa, bata nemi hawa wajen hajia ba, domin ba haka tsakaninsu, idanma ta je zata dauki wulakanci a hannunta ne na gori kala kala,
Da zumudi ta masa tayin shin ta zuba masa dambu zai ci?
Baba ya kalleta da mamaki yace "Uman biyu yau kuma dambu aka yi?"
Da fara'a a fuskarta tace "A'a Baba, ai a hanya ne na sa Muhammat ya tsaya muka siyo, wallahi Baba baka ji dambun ba? Na zuba maka ka ci za ka ji daɗ..."
Yar sauran harafin daya rage ne ya makale dan ita wallahi kallon da Baban yake mata kamar wanda ya ga wani abu a jikinta, irin kallon mamakin nan ne da kuma son gano wani abu........, Dan kallon jikinta ta yi , kar aje ko abincin ta zuzuba a jikinta bata sani ba?
Murmushin da ya saki tare da girgiza kanshi gefe daya ya sake tabbatar mata da lallai fa Baban wani abu yake tunani a kan ta.
Amma tunda ba tambayarshi za ta yi ba sai kawai ba ta ce komai ba aka bar zancen, amma kam yannayin nasa kamar wasu lokuta yaron nan dake sakata a duhu kuma ya barta da duhun kai yake mata shi ma.
Dake kwanan Risala ne yau kuma ba wani damuwa take da shiga harkar yarinyar ba, har fridge din falon ta zo dan daukar kakkaurar madarar da suka rage dazu ita da Fido, dan wallahi idan tana sha ji take kamar za ta tsinka harshenta
Tafiya take tana jan kafafunta dake sanye da silifas masu laushi na daki tana susar bayanta da yar yatsarta, kuma a ganinta darene ai kowa yayi bacci, shiyasa ta fito da riga da wondonta na cotton da suka dan saketa har jikinta na rawa a ciki, iya hula ce a kanta wacce ta tsaya a rabin kanta kamar za ta fadi.
Har ta buda fridge din ta dauko farin bidon ta kalli madarar mai kaurin gaske da sanyi, rufewa tayi ta juya da niyyar komawa dakinta. Hada ido sukayi da Abdul da ya fito daga dakin Biyu zai koma makwancinsa, domin Risala har yanzu bai idasa sake mata ba, dan tunda ta dawo ya kan je dakin ne ya ga lafiyarta, amma yana so ya barta tayi hankali kafin ya sake nuna ita ma matarsa ce, dan ba zai iya da wannan kwaroroton tereren tara masa dangi ba daga abinda bai kai bai kawo ba.........sirrinsa abin boyewa ne da karfin gaske ba abin watsawa bane!
Kyaɓe baki ta fara yi tana lullumshe idanu, sai kuma ta ɓoye madarar a bayanta ta zura hannunta cikin bayan rigar ita a dole kar ya ga me ta zo yi, a nutse ta shiga takawa ba ta sake kallon inda yake ba sai ma gunguni da take kasa kasa a kan me bai yi bacci ba shi din?
Shi dai yana tsaye bai ce mata kala ba har ta shige dakin ta maida kofar ta rufe, wani tattausan murmushi ya saki yana girgiza kai a ranshi ya ayanna 'Uman biyu kennan'
*Bayan kwana biyu* dukansu gidan Baba Rabi'u suka je bikin jikar tasa, duk da ba wani shaƙuwa ce tsakaninsu ba amma dai tare suka tafi bisa bukatar Baba da shi ABDUL din , harma suka kwashe awannin nan tare, ama kowa da inda ya fi karkata, domin Hajia na cen wajen tsofafin wajen sunna nasu shagali na iyaye,Amina na wajen amaren sunna nasu shagali , Risala na nata eriyar tana nata shagalin har lokacin dawowarsu gida yayi
Abdul da kanshi ne yake tuƙasu
Hajia na gaba tare da shi sai ita da Risala a baya, inda Muhamat ke tuƙa Baba da biyu, ya zamto motar sunna bibiyar junna ne, watau daya a gaba daya a baya
Motar shiru da fari ba mai wani magana, sai kuma Hajia da Risala da suka fara yar hirarsu da Abdul ma shi tsakani da Allah yana jin me suke fada amma baya gane gaban zancen, gyara zama Hajia ta sake yi ta buɗa jakarta ta lalubo dabinonta irin na kwalin nan ta fara ci, dan bata ci abincin bikin ba, sam lamarin matar Rabi'u ba classs, yaushe zata barawa mutanen gida su yi girkin abincin auren jikarta? Ga kampani na ma'aikata dake girki kala daban daban maimakun su je su dauko a yi girki a tsare da kiyayewa ...aaa, sai ta bari yan gida suka jamalmala, shi yasa ta kasa ci gaskiya, dan a matsayinta ba zata wanke goma ta durmiya biyar a cikin abincin vilagggssss ba!
Ɗan kallonta Amina tayi daga baya, dan a barin da ABDUL yake ta zauna, tana iya gannin hajiar da abinda take yi
har zata ɗauke idanunta sai kuma ta sake kallon dabinon, irin yanda ya jeru raras a gidanshi yayi ja mai kyau da alamar masifaffen zaƙi, sai kawai ta ji yawunta na wucewa ba tare da ta ankara ba
alamar dai so take yi sosai
Ba ta ankara ba, ba ta kula da ta kasa dauke idanunta akan dabinon ba har saida Hajia ta ci mai isarta ta maida sauran a jaka tana korawa da ruwan roba.
Abdul da tun fara kallonta ga dabinon ya kula, da fari ita yake ɗan satar kallo ta madubi, da ya ga ba ta ko kyabtawa sai ya maida hankali kan abinda take kallo, hakan yasa shi kallon hannun Hajia ya sake kallon idanun Aminatu ta madubi.
Yanzu kuma da Hajia ta maida abunta sai ya kula da yadda ta dauke kanta da yanayin rashin jin dadi tare da dan turo bakinta gaba ta jinginar da kanta sosai irin na yaro dai idan yana son abu aka hanna masa, murmushi kawai ya saki yana ci gaba da tukinsa
A ƙofar gidan Baba Mai Shanun aka tsaya dan sauke Hajiar da motar su Baba dake bayansu, Hajia na buɗewa za ta fita Amina ta rigata fita tare da bude bakinta ta kwaranyo aman da ya tuƙota yanzun nan ba tare da sanin dalilinsa ba
Da sauri ya fito daga motar Hajia kuma ta zagayo duk suna kallonta da yi mata sannu a tare, dan dukawa ta yi tana yi harda rintse ido
yatsina fuska Risala tayi ta ɗauke kanta tana jin kamar zata yi aman itama dan kyankyami tana duduba jikinta kar aje iska ta dauko aman ta watsa mata a jiki tace "Cussss, wata ƙazama da ita."
Da yanayin kulawa Hajia tace "Dama ba ta lafiya ne ko kuwa abuncin