Showing 27001 words to 30000 words out of 145392 words

Chapter 10 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8141

kawai sun kalubalanceta ne


Ita dai dadin da ta ji na gannin Babar ne, sosai suka wuni sunna shan hirarsu har yama ta yi baba ta mata salama zata tafi, a nan ne ta roki alfarmar ta biya ta sanarwa Firdausi, tace mata ba sai tace zata zo ba dan ta san ba barinta mijinta zai yi ba, ta fada mata babu abinda ya sameta, zata zo da kanta daga ta samu sararin hakan


A wannan ranarma idonta idon Hajia bai hadu ba, Hajiar fa tamkar babu mutun a gidan haka ta mayar da ita, bata damu da lekata ba, bata damu da ita ta lekota ta gaisheta ba, takan fita dan ta gaishetan ama bata taba cin sa'ar haduwa da ita ba, yaranta kuwa sun zama sai hange, to sai hange mana sukan tare da Baba sai dai ta ringa jiyo dariyarsu da guje gujensu, karshema wani gem ya sa aka kafa masu tafkeke ya sa ana koya masu idan suka fito daga karatun islamiya yana zauna yana shan dariyar saurin fushin Hasan da kuma saurin kulan Hisaini, kamaninsu daya ama halayarsu sun sha bamban sosai, irin nutsuwar da yake kara ji da shawarar da ya yanke a zuciyarsa ya sa yale karra shirin hakan a ransa


Yau kwanansu uku cif a gidan, a irgensa yau saura kwana hudu cif maganarsa da Dan iya, haka kuma a dazu da asuba sun sake zantawa da Liman kam maganar adu'ar da ya saka shi yi, ya sake tabatar masa shi kam alkhairin abin kawai yake gani , duda kwarai ya san akoy kalubale sosai , ama ya tabata alkhairin zai fi rinjaya idan aka tsananta da addu'a


Shi yasa ya shirya fara tarban bama baman da ya san zasu tunkaro shi, harma ya sa aka kai abincin karinsa dakinsa sannan ya aika gayatar matarsa dakin nasa dan su karya




Cikin wani rantsatswn lesh mai ruwan ash Hajia ta shigo falon mijin nata na sama da salama a bakinta


Tafia take yi da classs, harufan manyan mata na yi mata wasali a goshinta


Daurin kalabinta na wayayiyar mace ce, AC kuwa ya kara kwontar mata da kalar fatarta


A nutse ta gama serving dinsa abinci ta ajiye a gabansa cikin plate a ranta tana ayana' Allah ka sa na ji alkhairi, wannan hade fuska haka a wajen alkali ba lafia ba'


Baba Mai Shanu kuwa bai taba abincin ba, abinda le cikinsa ya fi cin abincin mahimmanci a yanzu

Dan haka ya fuskanceta a nutse bayan sun gaisa sosai da sosai ya ce" Hajia Hauwa, dangane da maganar Abdallah ce, na yi masa Mace, kuma ina son daura auren nan da kwana hudu bi'izinillah, idan ya so a hankali kya yi taron bikinkkkkkkkkkkkkkk"




Kwarewar da ta yi da ruwan jus din da ta kai bakinta zata surba ya saka shi saurarawa yana kallonta


Tari ta ringa yi a hankali tana dan fifita fuskarta har ta daidaita, sannan ta dube shi da idannuwanta da suka dan cenza launi domin ba taron gangan bane ta ce" Sorry Alkali, na kwaru ne, to ama yaushe aka tsaida maganar auren da gagawa haka? Jiyama fa mun hadu da Honorable din a wajen taron yaye yan makarantar bording da suka samu shiga Universityn Kasar Spanish"


Baba Mai Shanu ya ce " Aya, Allah ya sanya alkhairi, ai bama da y'ar gidan Honarable Alhasan Kwongilar bace, wannan sai daga baya, idan luwa ya zama wajibi sai a hade, yanzun da *MAMAN BIYU* ne nale magana......."










Kaka kara kaka, lamarin fa ba karami bsne, rigimar ba ta nan bace, wai cakwakiyar idan kin san ba zaki jura ba karki fara bi, wannan rigima ta ina zata bile? Ba ga mahadan ba , ba ga wa'inda za'a hadan ba..........Rigiji gabji


Dankaro da gudu ki turo naki katin ko shedar transfer ki same ki tsundum a gidan NI ZAN LADABIHHHH, sai ki min ladabi ki bi alkalaminsa, domin nima ladabin nake yi masu dan su bani danar fahimtar *WA ZAI YI LADABIH* a kokowar!


Barka da yau😌😍😍😍😍😍








πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ
_*NI ZAN LADABI*_
πŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈπŸ™‡β€β™€οΈ




*NA*




*SAJIDA NIGER*


Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida


Wannan Novel na kudi ne ba free bane


Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER


Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai


Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka


*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zoπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°*










*Page 1️⃣1️⃣*




Furucinsa, har zuwa kafiyarsa da yannayinsa, da suturar dake jikinsa , kai harta da kalar fatar jikinsa sai da ta shiga aunawa da idan yana cikin hayacinsa, a hankali da mugun kula ta karra dubansa kasa kasa sosai ta ce" NA'AM?"


dukkan yannayinta yana kula, yana kuma hankalta, murmushi ya yi mata wanda ke tabatar mata da kwarai abinda ta ji shi yake nufi, ba gizo kunnenta ke yi mata ba, ba kuma a cikin hali na fitar hayaci ya yi bayani ba


Da sauri ta saka hannayenta ta dauke farantin dake ajiye a gabanta ta kawar gefe ta zauna tana tataro dukan nutsuwarta da hankalinta ta ce" Alkali, wasa kake yi da furucin nan ama ko? Ka kuwa ji me ka fada? My big son , My hero, Uban gidan yan siyasa! Uban gidan masu mulkin! Dan yanada baban kowa a banki, shine zaka dauko auren fari kace zaka hada da macen da ta girme shi, macen da ta gama yawonta, macen dake fama da ya'ya, macen da bata waye ba, macen da take tuyar waina da kosai tana siyarwa, macen da bakin fatarta sai ya makanta mutun idan ya matsawa kallonta? Plz ka fada min cewa wasa kake yi da furucinka!"


Mamakin abinda bai taba kawowa kansa cewa zai ji daga bakinta bane ya saka shi dora yan yatsunsa biyu saman lebensa, kwana uku da suka shige wanda ya yi maganar nan ya yi masa uzuri ya ajiye shi a matsayin wanda bai yi dogon karatu ba, yana fama da jahilci ya da ya yi aikin dana sani, a yanzu kuwa a wani bigiri zai ajiye iyalinsa? Shi dai sheda ne a kan irin karatun da matar gidansa ta yi, na bokon da na islamiya, shin jahilci shine sani a take sanin ko kuwa wannan din son kai zai kire shi da shi?


Turw komai ya yi daga cikin zuciyarsa ya ce" Shin haramun ne aikata hakan?"


Hajia kam abinda nema yake yi ya girmami tunaninta, har so yake ya ji idan haramun ne? Kennan so yake yi ya zauna a kan bakansa?
Dan kwalin kanta ta cire ta ajiye gefe , lalausan gashin kanta mai dauke da furfura ya bayana a tufke a bayan keyarta da dan karamin ribom ta ce" Ba maganar haramun, shin ina hadi a nan? Idan miji kake son yi mata ka sama mata daya daga cikin ma'aikatan gidan nan mana, in ka raina su ka duba cikin ma'aikatan ka masu takardar gwamnati ka bata mana, ama sai ka dauko jirgi ka hada da mota? Ai ya fi karfinta walahi! Ita kuma ta girme masa a shekaru ai hadin sam bai yi ba, a cenza shi!"


Kai ya gyada yana murmushi da tunanin lalle ya yi sake katon raini ya riga ya shiga tsakaninsa da iyalinsa, yana wanzar da rayuwar yanci da ita da shawara a dukkan abinda ya taso masu dan yana girmamata da darajata a rayuwa domin shi a ganninsa mace tana da damar zabi itama a tata rayuwar ba wai sai dai a ringa yanke mata hukunci da an yi niya ba, sai gashi tana neman maida hakan iko da isarta? Tana so ta manta yana raye kuma bai shirufce ba? Tana son take komai ta murje komai ta manta nata usulin?, Koda yake tana iya mantawa, domin halin rashin na dan lokaci ne suka yi kafin Allah ya warware, sai dai zai ji mamaki ainun idan ta ci gaba da nunawa talaka haka , takan manta Allah ya haliceta da ita da wanda bashi da shi, yana iya amshe dukkan abinda take gannin ta malaka ciki jarda jikan nata a lokaci daya kuma ya barta da ranta da hankalinta ta gani da idannuwanta?
Kai Allah ya wadaran naka ya lalace!


A tausashensa ya ce" To tunda dai ba haram bane ai an wuce wajen, nima da na aureki ai tserayar shekarun dake tsakaninmu nu har kunya na ringa ji a lokacin kar ace na auri yar cikina, gamu kuwa an yi tsayin rai du kanmu ya cika da furfura muna tare, wannanma ai aya ce Hauwau"


"Alkali" Hajia ta fada tana tsareshi da manyan idannuwanta gannin ya mike tsaye yana shirin yin gaba ya bar mata dakinsa da itace ta tardo shi


Juyowa ya yi fuskarsa a hade sosai ya ce" Look, ki saurara abinda kike shirin yi ko menene! Ki tausasa muryarki a kan tawa, ki saurareni da kunnen basira, Ni Alkali na ce na yanke hukunci Daura auren jikana da Maman Biyu nan da kwana hudu, na baki dama idan kina gagawar a hade da wace yaron ke kulawa matsayin soyaya ba damuwa, idan baki gagawa kuwa lokacin da kila shirya sai a daura masa ita, shi din ai mijin mace hudu ne a sanina, so bana son yawan surutu a kan lamarin nan, kuma na hanneki tarda yarinyar nan da wata maganar da zata zubar da mutuncinki a idaannuwanta, ki sani ya zama wajibi *KI YI MIN LADABIHHHH* , Idan ba haka ba lalle zamu bar abin kunya mai girma a duniya kafin kasa ta birni idannuwanmu!"




Yana gama fada ya fice ya rufe dakin ya sauka kasa




Hajia kam sai da ta yi summan hucin gadi kafin ta zabura tana sallalami da dora hannunta a saman kanta tana fadain" Walahi talahi ba zai yiwu ba, ni zaka wulakanta? Walahi ba zai yiwu ba, in ni ka fi karfina ai akoy masu yi maka magana, haka kawai dan tsufa ya zo maka sai ka hada yaro da abinda ba shikenan ba? Wani irin zaman aure ne zai iya yi da yarinyar nan? Ko hannunta zai iya tabawa ne? Kuma walahi ba za'a daura auren yar gidan honorable da gagawar nan ba, ni da nake shirya wannan rana ta yadda zan gayaci manyan yan siyasa su zo mu hadu a kashe koren arziki? Ba zaka taba sakani a jarida da yamadidin abin kunya ba, sauran titin zaka ba yarona? Haka kawai marayan Allah zaka wulakanta? Ba zai yiwu ba!"


Tana fadan ne kuka na neman kubce mata tana dadana numbobi


ABDUL RA'UF din ta fara kira, har sau biyu kafin ya kashe ya maido mata kiran


Tana dagawa kuka ta fashe masa da shi tana fadin " ABDUL ko me kake yi ka zo gidan nan a yau yau, walahi Alkali ba zai kasheni ba, walahi ba zai kashe ni ba, bai isa ba, *Ba zan yi masa ladabin ba!*, A kan wannan bukatar tasa ba zan taba sada kaina kasa ba!"


Du yadda ya so ya fahimci abinda ya hada su a yau kuma ya kasa, takan yi kiransa da korafin kakan nasa ya yi mata kaza ita kuma ta rama da kaza, ya yi mata nasiha ya hannata maimaitawa, ama bata taba kiransa tana rusa kukan nan haka kamar zata mutu ba, kuma kukan ba wai na wasa bane , irin yadda take yinsa zaka gane daga cen zuciyarta abin ke fita
Hankalinsa ne ya yi mugun tashi, ya tabata ko kudi take so ya hannata, ko ya hannata yawon siyasa, a tunaninsa wadinnan ne kawai damuwar da zata rikita Matar Alkali, shi kam yaya zai yi da tsofafin nan ne fisabililahi? Sam basa girma, kulun cikin rikici suke, kuma shine a tsakiya, tsoronsa daya kar ciwon hawan jininta ya tashi, to wai inama shi Mai Shanun yake ya barta tana kukan nan haka? Ko menene ai sai ya rarasheta ya yi hakuri tunda ya fita girma kuma shine namijin ko?
Kiran wayar Mai SHANU yake yi ba'a dagawa, ya shiga kiran yaronsa da fada masa maza ya sama masa waje a jirgin da zai juya gida, nanma aka sheda masa a yau dai sai jirgin yawo wanda a kadan zai iya kwasar awani ashirin bai je gidan ba, domin kasa kasa zasu sauka , baban jirgin Ethiopia ne, ya gwamace ya yi hakurin jirgin karfe bakwai din kawai da wahalar nan
Sake kiran numberta ya yi ya sameta tana cikin waya
Kansa ya girgiza ya jefar da wayar yana adu'ar samun saukin rigimar nan tasu, sunna daga masa hankali, sani ne basu yi ba, bashida damuwar da ta wuce tasu a duniya, yau ko rikicin neman kudi baya daukan hankalinsa irin wannan, shi fa samun kansa ya yi dumu dumu a cikin nema, kuma ya san da kudi da babu rayuwa zai yi normal, ama wadinan biyun da suka rage masa a cikin makusantansaa mafi kusanci da shi sunna taba kwonciyar hankalinsa


Jin kukan wayarsa har gagawa ya yi ya dauko, a tunaninsa daya ne cikinsu, sai dai yana dubawa ya ga budurwarsa ce, wace bata san ya yi tafia ba, ya tabata ta samu labarin inda ya zo da numbersa ta nan din ne a wajen Hajia domin bai yi kiranta ba, fushi yake yi da ita, ya rasa rashin sannin ciwon kan nan nata da me ya yi kama, ba zata gane ba, shi fa baya son wulakantar da kai, ita ta dage wai ita yar kasuwa dole sai ta bude saloon? Tace aikin gwamnati yace sai dai ya dauketa aiki ta kiya, yanzu tace saloon ya nuna aa ta je ta bude, shi fa ba zai fita nema ba iyalinsa ta fita nema, idan karatun ne ba zai hannata ba, ta yi har ta ga makirkirin bokon, ama kuma ta yi zamanta, walahi ta fi karfin bautawa wani, kuma ta fi karfin wulakanta kanta a titi kulun tana yawo tana kama gashin wannan tana cudanya da karti wai ita mai saloon!, Yayan bankin yanzu haka na bankinta karamar mai kudi ce ita, idan sun mata kadan ya sake jibgawa, bahi da damuwa da hakan, ba kudin ne damuwarsa ba, a zauna masa a gida *A yi masa ladabi* sannan a tarairaye shi shine damuwarsa, a yadda ya jima da lamari mai girma rike da arzuzumin wandonsa ai dole ya bude filin sukuwa a gidansa ta kowani lungu da sako!, Ama shine dan raini yarinya karama ta ki bin umarninsa? No shi ba zai yarda da raini ba walahi! ( To fah, llale akwoy gwarama, to mu da muka saba da neman na kanmu fa? Ka zo da izala yaro!)


Kafin yama ta yi tuni gidan Mai Shanu ya dauki haramar baki, na nesa da na kusa, duk wani wanda Hajia Hauwau ta dan yana jin kunyarsa ko nauyinsa ko sunna abotakata ta kud da kud sai da ta yi kiransa ta dora masa kukan mutuwa da fadin zai sakata a uku ya tona mata asiri, ciki harda Ɗan zumunsa, yaron da yale rayuwa a waje tare da iyalinsa, wanda a kusa kusan nan shine daya kwal yake laluba ya ji sanyi, dangi ne su mararsa yawa dama, sai ga lamari na dauki daidaya, sai ko taron dangin dake nesa sosai wa'inda sai a yi shekaru ba'a ga junna ba, kowa ya labe da iyalinsa yana toyawa yana kwashe abinda zai fishe shi, yau ta gigibo masu iya tasowa a ranar ta kawo su, wa'inda kuwa basa iya zuwa a ranar sun shiga shirye shiryen zuwa, domin ko ba zumuncin haduwa da junna , akoy na waya da kuma hannun Mai Shanu da na jikansa dake samun kowanensu, idan har da gaske ne Mai Shanun zai dauko ruwan dafa kansa kamar yadda Hajia ta fada za'a hafu a yi masa nasiha sannan a fadawa Allah ya kade lamarin, domin babu wanda ya isa ya yi masa dole, sai dai rarashin




Tunda Mai Shanu ya fuskanci abinda yake faruwa ya yi murmushi ya kada kansa ya sa Direbansa dauko biyu suka wuce suka bar gidan


Bayan sun tafi gidan gonar ABDUL RA'UF Baba Mau Shanu ya saka aka je aka dauki Baba Lauratu aka bata waya suka yi magana, dan haka aka wuce da ita gidansa kamar yadda ya umarta cewa a kaita direct dakin da Amina ta mayar da kanta yar kuryar daki a zo masa da ita


Hakan ce ta faru, domin har suka fice a gidan Hajia Hauwau bata sani ba, rana sama kawayenta na danarta da rarashinta da nuna mata cewa lalle hadin naj sam ba zai haifar da alkhairi ba, ai bambancin shekarun ya fi komai daga hankali ga kauyanci, ba zai taba yiwuwa ba matar Gwamna ta kasance a haka ( uhum, su gwamna manya), idan aka yarda aka aurawa Honorable mace irin haka ai za'a samu matsala wajen zabe, ba matar gabam mota bace sam! Dole a cenza ra'ayin mai Shanu, wannan ke daga mata hankali, mijinta mutun ne mai masifar sanyi, a cikin sanyin nasa yake tafka maka abinda zai hadaka da juwa, ko a yanzu irin yadda ake buga masa waya baya dagawa ta tabata yana kallo, baban burinta shine a sakashi a tsakiya a tankwasa shi, idan ya daura auren nan mutuwa zata yi! Kai ama Allah ya tsinewa wata jarabar walahi, tana zaman zamanta, ita ta san tunda ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login