Showing 33001 words to 36000 words out of 145392 words

Chapter 12 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8149

na farin ciki da daukan maganar a shirme yana kallonsu baki daya, har suka gama suka dire Aya


A hankalce ya ce" Ama, baba ka san ai inada wace na tsayar a matsayin wace zan dauka ko?"


Baba ya fuskance shi da kyau ya ce" Ban hanna ka ba, ama a yanzu na cenza shawara sai na ga yannayin zamanka da yarinyar nan sai ka karra aurenka, ABDUL RA'UF na riga na sayi goro na kuma tsayar da magana, idan mun dawo daga daurin auren ma shigo mu zauna da iyayenku da ita yarinyar da kowa da kowa"


Idannuwansa ya wara da mugun mamaki, a san kagauce ya dubi kansa, farar shada ce a jikinsa dinkin tazarce, simple bata da adon komai a jikinta sai hular dake kansa , kayan tunda asuba ya saka su, kai bama wannan ba sai kace mutuwa wannan abu a kagauce?


"Ba zaka yi min ladabin ba?, Ba zaka bi umarnina ba? Nace ba zaka amsa maganata ba? Kana da damar bijirewa kamar yadda suka ce, kana da damar kiyawa tunda ai dama kaine mai kudin, hausawa kuwa suka ce mai kudi uban iyayensa!, Zamu yi gaba da jama'ar da na gayata, idan mun je cen din zamu daura auren, kafin nan kafin azahar ka yi kirana idan ka ga ba zaka iya ba kace da ni kar na saki na daura, domin ba zan so na yi maka auren dole ba, ai kai ba yar budurwa bace!, Rabi'u mu je" Baba ya fada a hasale ya fara yin gaba da tafiyarsa ta tsanake dan baya oya mugun sauri jikin tsufa


Sosai baba Rabi'u ya dan kara tausarsa da nuna masa ya yi Ladabi wa kakansa, ya isa da shi kar ya bashi kunya, sannan ya bi bayan tsohon ba tare da ya yi masa tambayar waima wacece ne? Shi gaba daya gani yake yi ai mafarki ne wannan din, wani irin almara ce wannan? Aure? Aure fa? To da bai zo Bama za'a daura masa auren ne? Wannan wani irin abu ne? Wacece wai yarinyar nan da kakarsa ke ta fadin ta gama yawace yawacenta? Kuma shine shi za'a daura masa? Ya salam


Jikinsa ya ji na damunsa da gajiya da kuma kasala dan haka sai ya koma ya dauki darduma a dakin hajia da ta daina kuka hankalinta kwonce ta san am gama tunda ta yaron ya kuma yarda da maganarta


A hankali ya fice baya ya shinfida dardumar ya karasa wajen pampo ya daura alwallah ya koma ya zauna ya dauki carbinsa ya shiga ja, ko yinwar baya ji, ya fi irga lokaci da duban hanya, y kula samarin gidan sai ficewa suke yi a motocin gidan, har gidan ya dauki shiru , aka fara kiraye lurayen sallar azahar


Kasa fita waje ya yi ya kabarta ya shiga bin sallar daga nan,, har aka salame ya sake Ubbawa wayarsa ido da tunanin in dai da gaske ne yanzun ana cen ko an daura masa aure da bakuwar da bai san ko wacece ba ko za'a daura masa
Kai yau shi ya ga masifa lukuta walahi


Sannu sannu har karfe biyu ta gota, dan haka ya mike ya dauki dardumar da nufin yin tsakar gidan
Sai dai hango mnai gadi ya wangale kofa ya saka shi cenza akalar tafiyar ya dauki doguwar hanyar wajen mangoro dan burinsa ya dan labewa hayaniyar da ya tabata za'a yi a gidan nan a yanzu ,,. Dan baya so tta summe idan ta ji an daura masa auren nan, shi su bashi dama ya fahimci abinma sun kasa bashi, uhum wani abu sai hausa!


Tunda ya taho tunani ya cika kwakwaluwarsa, haka itama dake tahoha dan ta koma dakinta ta kicin kamar yadda ta biyo ta zo ta wuni a karkashin mangwaron nan dan ta gujewa abinda Baba Lauratu a sakota a gaba da shi wai wani gyaran jiki har ta kama ta murza mata man ja da kurkum a jiki sai karnin man jan tale, shi yasama ta ki saka hijabinta ko daya dan bata shirya lalata hijabi ba a kan shirmen gyaran jikin auren da bata san da waye ba, kawai ta fito da doguwar rigarta sai dan kwalin rigar ta yane kanta da shi, kanta a kasa tana ta tunanin a wace ake ciki ne? Ina baba yake ne bata ganshi ba tun jiya? Shin yaya maganar da ya mata ne? Allah ya sa an fasa
A zuciyarta ta ayana' Allah ya sa baban yace aa an fasa ba yanzu ba , ba zai bayar da................." Kim, kum duskarta mai dauke da man ja da kurkum tana kyalin mai ta kumun masa a gaban kirjinsa da farar shadarsa


A rikice ta saka hannunta da ya dauki yellow din kurkum din ta damuki rigar tana furta" Aushhhhhhhh subahanalah wa........."


Dif maganarta ta dauke a lokacin da ta yi arba da sajjen fuskarsa da kuma hasken fatarsa da kamaninsa


Shima da hanzari ya rike damtsen hannunta ya janyeta baya yana yatsina fuska da binta da kallo da son tuno wacece wannan a ina ya san fuskar wanann, bale dan kwalin da ya yaye sak sai ya so tuna masa wata fuska daban


Dan tsakin da bata dan da shi bane ya bale mata ta shiga jan hannunta, sai kuma da dan karfi ta ce" Malan cikani mana meye haka!"


Idannuwansa ya wara a kanta, nan take a ransa ya ayana 'Fitsarariyar nan ce!' ,
A hankali hankali ya shiga dan nitsa mata hannunsa a damtsen da take gannin na mai karfi ce ita yana kallonta sai kuma ya dan matse hannun yana tsaye kikam yana kallon yadda ta kawo dayan hannunta tana zarro ido hadi da kokowar son kwace kanta a haukace ta ce" Kai baka da kunya ko? Ka cikani ni sa'arkace wai da zaka matsen hannu ? Kai ka...........










Wai wai wai wai wai wai wai gwarama in ji kawata


Nace ba, kin kuwa turo naki katin? Nan na tsayar da free, kuma in sha Allah shi din babu na aunty sajida a taimaka min da NI ZAN LADABIHHHH, domin a cikinsa zan baje basira na bada maganar gyara na sana'a ba cuta ba cutarwa .........garzayo yar uwa mu je da ke rikicin mai karfi ne.......wai yaya tafiar zata tafi ne? AMINA fa baba ce bata son raini, ga kuma wanda ya fita gannin shine baba , a samanta yake, uwa uba su din mata da miji suke a yanzu....wai yayane , *WAYE ZAI YI LADABIN?*,
GA kuma hajia a gefe, kun tanadi ruwan watsa mata dan ta farka idan ta summa?, Wai yayane maganar yar gidan honorable? Iyayen gida mune da kambun wannan karo, tafiyar tamu ce! Ku buga mana tamburan aunty, hajia sannunki yah mama, kece uwar gidan gidan oga, kece za'a yiwa ladabin fa!


Maman jariri nace ba? Yayane๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ๐Ÿšถ๐Ÿปโ€โ™€๏ธ










Sai kun zo




*NZL PAGE1๏ธโƒฃ3๏ธโƒฃ*
















Kokowa take neman tafkawa da shi dan ta kwaci kanta, wani irin takaici da haushi suka hadun mata suka tsaya mata a wuyanta, so take ta fashe da kukan takaici na irin kusancin dake tsakaninta da shi, tunda take ko maza masu sunnan maza da suka girmeshi hakan bai taba faruwa tsakaninta da su ba sai a kan wannan? A kan me zai kama mata hannu? Ko ya zata yar iska ce ita? To ko iskanci zata yi ai ba da kannin bayanta ba walahi
Kasa amshe hannunta da ta yi , ga ido ya cika da ruwan hawaye sai zuru zuru take ya sakata dago hannunta a haukace da nufin kifa masa abinda ta tabata idan har ta aikata din sai ta kulle kanta, dan bata tunanin in za'a kyaleta ta ci bilis, ta tabata Allah ne kawai zai tsaya mata ya kwaceta a hannunsa da kakarsa, ama ta yi niya a kan mutuncinta babu abinda ba zata yi ba


Da karfi ta nufo fuskarsa da hannun nata, sai dai kasa karasawar hannun nata ya sakata neman kara dukewa da saurin kai dayan hannun da ya sakar mata ta damki gaban rigarsa wajen cikinsa tana haki hadi da kallonsa, domin da hannunsa daya ya tare marin yan dan zarro idon mamakinta


Zai yi magana madaukakin salati da salalamin da duka fito daga falon nan du irin nisansu da falon ya sakasu a tare juyawa suka kalli hanyar falon


Gabansu faduwa yake yi a tare,
Ita dama taron jama'ar nan ya tsaye mata a kirji tans tunanin na menene, shi kuma a kasan zuciyarss fadi yake yi lalle ta faru ta kare


Da dan karfi kadan ya yarfe mata hannun, wanda sai fa ta yi taga taga sannan ta iya rike kanta tana zarro ido


Fuskarsa ya yatsina, domin ji ya yi ba zai iya buyar da ya so ya yi ba, ya san wace kakarsa a duniyar yan rikici, bale yau zagaye take da fadawanta yan zigata, baya so a yi abinda zai shiga uku
Dan haka dole ya juya a nutse ya dake daukan hanyar cikin


Amina dake haki tana hararan bayansa itama dole ta dauki hanyar falon, sai dai nesa take da shi sosai tana mamakin irin yadda yake tafiya da wani dan bubudewa kamar wani uba, uhum yaten zamani? Sai su


Labulen dakin ya kama ya daga gaba daya ta yadda haske zai karru a dakin
Dan tokarewa ya yi yana kallon ikon Allah, du an wani yayume kakarsa ana tausarta, shi kuma oga kwata kwatan yana zaune yana kallonsu a saman kujerarsa da yakan zama lokuta da dama, shi sai a yanzuma ya ga cousint dinsa hakan ya saka shi dan zarro ido sai kuma ya dauke ya shiga falon da salama a bakinsa ya ja ya tsaya yana kallon wajen kakar tasa a hankali ya ce" Hajia?, Hajia?"


Hajia dake kuka ris ris ta dago da sauri jin muryarsa, sai dai wace ta gani a kusan daf da shi ya sakata dagowa tana nunata ta ce" Ke? Uban me kike min a nan ? Ko kin ga sa'anki a wajen n......"


"Haba hajia, Haba hajia, wannan din ba girmanki bane, kar ki yi abinda zata rainaki tun yanzu mana" daya daga cikin kawarta ta fada, Amina kuwa ido ta zarro bayan ta waiga dan gannin da wace ake ta tabata da ita ake sai dam ta nemi juyawa dan barin dakin domin dama ita tsoron da ta ji kar aje mutuwa aka yi a gidan, kar aje wanda ya daure mata ne ya mutun, to wannan ihu da salalamin bakunna da dama ai ba dai karamin mugun abu zai saka su yi ba


"Uman biyu, zo nan, dawi ki zauna cikin mutane" baba mai shanu ya fada a tausashe , sannan ya maida dubansa wajen da aka rike Hajiar ya kare mata kallo daga sama har kasa, da wa'inda ke ta tarotan


A kausashe ya ce" Alhamdulilah, Allah ya saka da alkhairi, mun yi magana da Issuhu an fitar da motoci za'a maida kowa gidansa, wa'inda ba na gari ba kuwa za'a sakasu a hanyar da ta dace su koma gida, idan an tashi yin bikinsu kowa zai ji sai a dawo da dadin rai, wannan dai itace iyalinsa, gatanan in sha Allah mutu ka raba"


Yanzunma gaba daya dakin aka bi inda Amina ke dan tahowa dan ta zauna a wajen da ya nuna mata, domin dan kusa da kafafuwansa kadan ya nuna mata kan ta zauna


Itama ja ta yi ta tsaya da sauri , sannan ta kalli gefe da gefenta har bayanta da kujera ce kadai ba komai sai da ta waiga ta kalla,
A dan rude ta kalle shi , hadi da salalamin da Hajia ke yi ta kai zaune a wajen da take tsaye tana faman fadim" Ban san irin girman laifin da na yi maka ba da kake wulakantani har Haka Alkali ba , ko menene ai sai ka fada min na nemi yafiyarka ko? Ina hadin aure tsakanin Abdul Ra'uf da yarinyar nan? Alkali shine ka je ka daura kuma kake son korar min mutanen da nake gannin sun isa da kai?"


" Ki min shiru Hauwau tun kafin na saba maki! Idan ke baki da hankali baki gane kin kai wajen da zaki fara tsawatarwa ba maimakun a ringa tsawatar maki to ki iya bakikinki ki tausasa kalamanki, kar ki saki garin shirme irin naki ki yi furuci a abinda Allah ya boye maki sirrinsa!, Ke baki san waye zai rike hannunki idan kin kai gajiyawa ba! Kaf mutanen dake wajen nan da kike fadin sun isa da ni, ni Aliyu dan gidan Umar faruk karya ne a kan gaskiya, kai ko akoy wanda zai tirsasani yanke hukunci dan na yi abinda yake alkhairi ya saka a yanke igiyar auren nan? Bari ki ji Hauwau zaki yi sanadiyar da zan hanna maki siyasa, watau na haramta maki ita har duniya ta nade!"


Baba Rabi'u ne yake son maida shi zaune, dan har rawa jikinsa yake yi, gaba daya ya fizge hannunsa yana juyowa wajensa ya ce" Ka barni da ita, me take takama da shi ne? In ba rashin godiyar Allah ba fa kudin zaki je kiyama? A kasarmu mace na mulki ne? Yaron nan da kike ikirarin ya hau kujera ya nuna baya so, na maku shiru ne dan na san idan Allah ya hukunta tabas zai yi mulkin kuma bi izinillah jinina ba zai kasa samu ba domin waye bai san sarkin matasa da kyakyawar mu'amallarsa da mutane ba?, Ama sai wani jahiltar siyasar kike yi kina wani irin abu tamkar kin kauro duniya da zama!, Hauwau idan daga zaunen nan baki idasa sauka kasa kika suma ba ke ba cikakiyar yar gayu mai kyamatar jinin talaka bace, Wai sai ikirarin bak'ar fata kike yi , ke kin manta yadda taki fatar take ne?"


Da sauri Ya daga kafarsa ya karasa wajen kakansa da ya ki sauraron kowa ya saka hannunsa ya damki nasa hannayen ya shiga murzawa a hankali yana kallonsa , du irin halin da shi ya shiga a yanzu wannan da yake ciki ya saka kafa ya shure yace kau bani waje!, Muryarsa a tausashe ya shiga fadin" Aba....Abahnah, abah da baki fa a gidan"


"Ka barni na yi, ka barni na tuna mata ita din mutun ce kamar kowa, bakin ai ita ta gayato su dan a hadu a taro ni, na haukace ko? Ita ta harhado su dan a yi min magana zan tafka sabo ko? Ai bakin makusantanta ne da nawa, idan summa sun haukace sai na gani, idan tunani take yi saukin halin da na dauka na zubar da komai nake rayuwa da ita dan samun sukunin zuciya tsoro ne ko dan ta fi karfina ne ta farka, Son ka barni a gaban bakin nata na tuna mata bata isa ba ta hanna wani abu a kan wannan, na daura maka aure zaka zauna da matar ko ta ki ko ta so, kuma sai matarka ta aminta zaka dauko ta biyun da take fada, maganar siyasa kar Allah ya sa su hau in dai son zuciya suka saka a gaba!, Hauwau kema zan iya haramta maki zumunci da kawayen nan dake mance abin rufa dan su zo su yi zigi a kan aikim lada da gyaran rayuwar wani, ki saurareni da kyau Hauwau, nace zan iya haramta mu'amalarki fa Uma, idan har ta fini a wajenki kuma sai ki bita, ki bita Hauwau!"
Baba Mai shanu fada yake yi tun karfinsa, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, gaba daya hakuri ake bashi ana fatan ya yi shiru ama ya gagara, zuciyar Aliyun Umar Farukun a kusa take yau, yau a kai kan gaba ya amaye abinda ya girgiza kowa, da yawaa yanzu suke kuka na tsorata da tashin hankali, ya jima rabonsa da rigima irin haka, ya dauki girmansa da hannu biyu ya zubar da komai tunda ya rasa dansa kwalin kwal da matarsa, ya daina saka hancinsa a wajen da ba'a saka shi ba, yana aiki ne dan ubangijinsa ba dan wani ba, yana kyautata mata ne da zuciya daya dan burinsa ya mace a hannunta ta yi masa takaba a gobe kiyama ta zamto uwar gidansa a aljannah idan Allah ya aminta, sai gashi lamarinta na kulafircin mulki na son haifar mata da ษ—a ba ido, a fadansa da ya furta furtaciya fa? Wace koda da kome da kunya fa? Da sun dawo kowa ya yi dana sani, ABDUL RA'UF gannin abin zai zarce misali ya saka shi shiga kafadunsa ya rike shi da kyau ya shiga tafia da shi a hankali ya nufi sama da shi kasa kasa sosai yana fadin" Ka yi ta hailala, ka maye gurbin maganar da ambaton Allah, ka daina maganar haka, ka bar maganar haka"


Sosai kirjinsa ke dokawa, bai taba tunanin da girmansa zai ga irin haka ba sai yau, tun ana yara ba'a yi haka ba sai yanzu? Gaskiya ta zo masa da sabon lamari a cikin rayuwarsa, wannan wace irin masifa ce? Tun jiya zuwa yau ta hannawa kanta kwonciyar hankali saboda abinda yake daidai da kuma alkhairi? Shi ba gori ya yi mata ba, ba kuma wulakanci ba, ya daki abin da karfi ne dan harta masu ririketan su gane bai zo da wasa ba a kan lamarin nan!


Zaunar da shi ya yi a bakin gadonsa, a hankali ya dora masa kafafuwansa a samn bed din ya cire masa sabon takalmin da ya dandasha na amarci, sannan ya cire masa safarsa harda hularsa ya kai komai ma'adaninsa ya dawo ya janyo kujera ya zauna ya zuba masa ido yana kallonsa


A hankali fushin ya fara sauka, har ya dawo yana ajiyar zuciya carbinsa a hannunsa yana ja


Kasa kasa ya ce" Na kira Mansur ne?"


Baba Mai Shanu ya bude idannuwansa ya sauke a kansa, shi yama zata ya fice ashe bai fita ba, tausayinsa ya ji ya kama shi a cen kasan zuciyarsa, ya sani sarai shima a cikin wani hali yake mai girman gaske, sai dai kamar yadda ya kasance mai saka bukatar wasu a gaba da taa, damuwar wani a gaba da tasa damuwar halaya kamara wani mai manyan shekaru ya sa ya dane nasa balin da ya sa zai masa ne a lokacin da ya fuskanci ya dace ya yi masan, a yanzu da ya ga yana fada ya cinye ya kawo shi dakinsa


Kai ya girgiza a hankali yana bin shadar dake jikinsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login