Showing 66001 words to 69000 words out of 145392 words
Chapter 23 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ya ki fitowa, a dole ya sake riƙe Amina dake fatan farkawa ta samu kanta a summe ace da ita ai summan kwana biyu ta yi har ta yi mumunan mafarkin nan, sai dai tana jin ya daina gana mata azabar da bata taba tunanin yaro dan tsurut haka zai aikata ba ya aikata mata ya ci gaba da motsi a jikinta ne ta sake gwada sa'arta ta hanyar sakw kiran wanda ya kawota gidan tana ihun ya taimaketa ko Allah zai sa a dace ya jita ya taimaketan, sai dai kashhh, karshema kukanta ya zamto tamkar busar sarewa da karin kaimi wajen taka rawarsa, tun tana jin gaban jikinta a jikinta har ta daina jinsu kwata kwata, tun muryarta na fita da karfi har ta disashe gaba daya
Jiki a mace baba ya dawo matatakalar hawan ta kusan hudu ya zauna ya rafka tagumi yana Adu'a a kasan zuciyarsa da jiran tsamanin aikin yaro😭
Da sauri Hajia ta ringa tafia ta rasa number ya dace a yanzu ta yi kira
Tana komawa ta tarar da Mahaifiyar RISALA ta dage sai fada take yi da fadin magangannu tana kallon kawarta kamar haka" Ke Hajia ki bar maganar nan, an yi ci gaban da namiji karyarsa ta sha karya yace zai yiwa mace haka, na tabata yaron nan wani salon raini ne da nuna isarsa a kan wajen da bai isa ba, a kan wani dalili zai saka min ya ta yi kuka?, Walahi kin ji na rantse bai isa ba, shi din banza shi din wofi, a kan yata zan iya aikata aikin da kare ba zai ci ba, dole ya fito a je a yi dinen nan a gama, du irin kwaliyar nan da Risalah ta sha za'a fito min da wani wasan na rainin wayo? Ai ni kaf a dangina babu talaka, in dan wannan ne, dan takamarsa kudi ai gidan ya tarar, walahi walahi karya yake shi karamin dan duniya yace zai zageni, shi da ya garwayu da talakawanma har yanzu talaucin ke bibiyarsa ya je ya dauko mace yar talakawa ba gaba ba baya futuk kamar beran masalaci? Idan har ABDUL RA'UF ya yi wasa da ni, tabas zan yi wasa da shi!"
" Ke dillah rufewa mutane baki!" Hajia ta fada a kufule cike da matsanancin mamaki tana kallon maman Risalar
Takowa ta yi ta karasa shigowa tana kallonta tamkar zata dauketa da mari a kausashe ta ce" Ke?, Har kin isa ke ki budi bakinki mai tsami ki zagi ABDUL RA'UF?"
Hajia ta dire maganar tana sake bin dakin da mutanen dake ciki du da aka mike ana son basu hakuri baki dayansu
Hajia ta mika hannunta ta dakatar da Uma ta ce" Ina yake kudin? I said ina yake kudin dan Uban Ubank.............."
"Subahanalah Hajia zagi kuma da girmanki? Dan Allah kar ku yi haka a yanzu da kuka zama daya ai ba maganar haka ta fara shigowa a tsakani, maganar Diner kuwa idan wanda ya aurwta yace ya fasa ai inaga aljihunsa ne sai a ba baki abinci su ci su watse ai ba yau ba aka fara taro ba ango da amarya ko?" Auntyn Maman Risala ta fada tana son katse rigimar domin falon cike yake da yan zubawa wuta essence su hasata maimakun su kasheta, duda zagin da maganar ina kudin itama sun tsaye mata a rai harma tanada amsar ba Hajiar sai dai ba zata so a tafi da su haka a baki ba, uwa uba idan har mahaifiyar RISALA ta yi wasa da lamarin soyayar da y'arta ke yiwa ABDUL zata shiga uku ne da kanta, domin abinda take gudun ne zai faru, y'ar tata ce zata zama abin tausayi, babu wanda bai san cewa Risalah ta fi Abdul karfafa soyayarsu
Saukowa take yi da gudu gudu daga sama, kuka take ci na maganar ABDUL, sai dai ana fada mata abinda ke shirin faruwa ta ji hankalinta ya karra tashi, Umanta ta zagi Hajia? So take yo a saketa ne? A haukace ta mike ta cakumi rigar amarenta ta shiga saukowa da gudu gudu tana fadin" Mama, mama dan girman Allah me kuke yi haka? Mama!" Ta idasa fada da karfi tana gurdewa a abin hawa na biyun ta rike karfen da ake dafawa ta fashe da ihun kukan da ya sake daukan hankalin jama'ar wajen dake ta bada hakuri sunna ririke Hajia da umanta tamkar zasu daku
Hajia ta janye hannunta daga na wata datijuwa dake bata baki a hankali ta ce" Its ok Hajia"
Sai kuma ta sake juyawa wajen da maman Risala ke tsaye ta ce" Ki gwada min aiki irin na isasu ki je ki dauki yarki ku je wajen diner ku raya daren nan, ni kuma a yau zan nuna maki aiki na wace ta isa na baki sakamakon hakan, ABDUL yace kar ta je na ga Ubanda zai taka dokarsa! Yarinya baki san maza ba sai kin ji kanki baya jikin wuyanki!"
Daga haka ta juya ta nufi waje tana kokarin sake kiran number Umaimat dan hankalinta gaba daya ya yi gidanta irin yadda gabanta ke faduwa a kan lamarin ya fi komai daga mata hankali, bata san waye wannan mai kuka haka ba, koma waye Alkali na tare da shi, bata san wacece ke kiran mijinta haka ba, wacece ke neman ceto haka ba, loma wacece wani baban lamari marar dadi ya tunkarota............
Bayan motar ta bude da kanta ta shiga ta rufe tana fadiN" KAINI GIDA"
A KAIKI INA? 🧐😫😫😫😫😫😫😫😫😫🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢
*NZL PAGE2️⃣6️⃣*
Janta direban ya shiga yi cike da kwarewa sannan a hankali dan gudun tala dokar ABDUL RA'UF kan kar a ringa gudu da kakaninsa a cikin mota
Hajia ta daga kiran Hajia Umma ta saka a kunnenta tana amsawa
Abinda Umman tace ya sakata dan tabe baki a hankali ta ce" Uma kin gane, kuna iya yin dinern a tsakaninku, ku salami baki.ku ce masu wani abin urgent ya hanna mana halarta, sannan idan ta ga dama ta baku yarinyar ku mikata gidanta in ta kiya ta zaunar da ita a nan, indai ni HAUWAUN ALKALI ce zan je na daukota ta jima bata tare a dakin GWAMNA ba, !"
Sosai Uma ke rarashinta dan ta bata hakuri ama Hajia ta katse kiran tana duban direban ta ce" Ka daga kafa mana"
Da darajata ya amsa sannan ya ci gaba da tukin da gudu kadan
Fitowa ta yi yanzuma tana dan jan karamin mayafinta dake saman kafadarta ta shiga nufar part dinsu
Ja ta yi gannin Umaimat na kai kawo du a hargitse tana dubanta da haushi gannin ta sake firgicewa ganninta ta ce" Umaimat tabas a yau zan salameki daga gidan nan ba sai gobe ba tunda baki da wani anfani sai hauka da shashanci, wai nace ki kaiwa ABDUL waya sai ki kaima Alkali!"
A rikice Umaimar ta ringa binta tana fadin" Hajia dan Allah ki yi hakuri, sir dinne nake ta nema nake ta nema dan ALLAH hajia karki koreni"
Tana biye da ita tana bata hakurin ne har suka shige falon tana rike da jakarta Hajia bata tsaya ta kulata ba
Turus Hajia ta yi gannin Alkali , Alkali nata zaune dangalgal a kasa wajen abin hawa, watau saman upstairs hannayensa biyubiyu a dafe da gefen fuskarsa yayi wani zuru zuru da shi kamar ya sha tsinanen duka
Gabanta ne ya fadi domin abinda ya fadar mata da gaba a lamarin shine ABDUL RA'UF ne wani abun ya same shi,
Gwuiwoyinta na rawa, hannayenta na rawa ta saki mayafin ta karasa gabansa jiki ba karfi ta ce" Alkali? Ina ABDUL din?"
Tsakani da Allah ko a zamanin samartaka ba karamin abu ke hadasa masa faduwar gaba ba, bale a yanzu da tsufa ya zo ko wace wace baya wani shayin komai, ama ganninta a wannan lokacin kusan awa biyu kennan da Abdullahi ke dakin Amina baiwar Allah bai fito ba, sai ya ji gabansa ya kwonci kwonci ya fadi
Fitinar Hauwau daukaka take yi a kulun safiyar Allah, hakan ya sa yake jin shayinta a cikin ransa tamkar itace mijin idan wani abin fitinar ya tashi
Kokarin fashewa take yi da kuka ta ce" Ni na san ba banza ba jikana zai tayar min da hankali a kan maganar diner din nan, Alkali dan annabi Muhammadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam ka fadan inda yaron nan yake, me ya same shi ne? Me yake damunsa ne? Ina yake ne?............................"
" Dan Allah ka fita, ka fitar min a daki nace........" Gajiyayiyar, shakakiyar sanyayar muryarta ke tashi a hankali, da yannayi na kamar a tsorace take da jin muryoyin dake tashi a kusa da dakin da take wa'inda a dazu bata ji ba sai a yanzu, haka kuma kamar an nufeta ne da wani nufin da ya sake dan hargitsa yannayinta,
A waje kuwa, amon muryar du laushinsa kunnaye na jiyowa domin dare ne ya fara rabawa ba takun jama'a a gidan ba wata hayaniya, gashi ba wani gini bane mai sirrin nan dan irin gidin nan ne ko tsaki ka yi a dakinka ana iya jiyo shi a dakin makocinka
"Ki bari mana " muryarsa shima tamkar bajimin zaki ta shiga kunnan kakarsa a lokacin da ta dago kanta ta kai dubanta dakin da aka saka yarinyar nan
Da farko a rudu ta shiga na tunanin meye haka kuma? Daga baya sai ta zabura daga kusan mijinta ta sake kallon hanyar, lokaci daya ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi rajune Alkali? Ina Abdul? Me me me ABDUL yake yi a dakin cen? Ka cemin wani ne ya fada mata daki alkali kace min wani ne ya diro mata kamar yadda ta saba fada ba ABDUL dina bane"
Da sauri Umaima ta bar falon hankalinta tashe, ta sani ne in ba ALLAH ya tsaya mata ba shan ruwanta ya kare a gidan nan,
Gannin kallon da Baba ke yi mata ya sakata juyawa ta shiga hawa a haukace tana fadin" ABDUL? ABDUL? ABDUL?"
Mikewar baba ya yi shima ya bita dan ya sani sarai Hauwau na iya afkawa dakin cen
Da wani irin sauri ya mike daga saman gadon da yake zaune, domin yana ajiyeta ya zauna shima yana son warwarewa kansa abinda ke damunsa a kwakwaluwarsa
Da takun cikaken namiji mai ji da karfi da girgizajen balagagen shiga hantsi ya karasa ya saka hannunsa ya dana kofar da tuni Hajia ta murda ya saka sakata sannan ya bar ky din a jikin kofar ya tsaya a jikin kofar ya rintse idannuwansa yana jin irin dokawar da ta fara yi da karfi tana kiran sunnansa, mamaki na neman kashe shi da tunanin wai idan da ya barta zata bude dakin nan ta shigo ne? Lalle da yau ya yiwa kakarsa abinda mamakinsa zaya kasheta, aa yana tunanin ya dace ko me zata yi ta ringa kiyaye limit, akoy abinda idan ka yi Allah ne zai kamaka da shi, da ta tardo su ba suturar kirki fa? Duda ko a yanzun shine mai suturar a jikinsa ita mai hararansan cen ta ki pantma ya maida mata bale a kai ga suturar
Wani ihun kuka hajia ta barke da shi mai cin zuciyar nan ta kama abin budewar tana jijigawa a haukace ta ce" Abdul ka buden kofar nan kafin na tsine maka albarka! Ka buden kofar nan kafin ka kasheni"
Baba bai san murmushi na iya samunsa a wannan lokacin ba sai da ta yi furucin nan, yana murmushin a tsayen da yake yana kallon sabon haukar Hauwau ya ce " Kina manta ba ɗan da kika haifa bane ABDUL? A kiyaye harshe dai dan gaskiya bana tunanin zai tsinu fa"
Juyowa ta yi wajen Alkali , a hankali ta dawo gabansa ta sasauta muryarta da kukan ta ce" Alkali, dama kai ka hannashi zuwa dinern ka rufe shi da yarinyar nan?"
"Ashe ke shashasha ce? Ashe baki da hankali?" Baba ya fada muryarsa dage a kan tata sosai dan ta fara kular da shi
Itama da ihun kukan tace" Nice shashashar Alkali? Nice shashashar ? ABDUL ne a dakin nan? Me yake yi? Maganar me nake ji? Taimakon me zai mata? Me ABDUL yake yi a dakin nan da saka hannunka a cikin lamarin nan ko?"
A kausashe Baba ya kama hannunta ya mata wani jan da bata taba zaton da sauran karfi haka a tsintsiyoyin hannunsa ba ya nufi nata dakin ya bude ya turata ciki ya ja ya rufe yana kallonta ya ce" Abinda kike tunani, shi ya je yi, ko kinada matsala da haka ne?"
Ido ta kwalalo tana kallon Baba ta ce" Alkali, kana nufin ABDUL RA'UF ne ya tashi a yau ranar da nake shirin yi masa gata da yarinyar budurwar amaryarsa ya wulakanta wannan ranar ta hanyar zuwa ya samu matar da ta girme shi a duniya? ABDUL dina ne ya je ya samu wata mace cen marar daraja a cikin tsarin matan da suka isa ya duba har ya je mata a matsayin miji? ABDUL da aka daurawa aure da sabuwa dal din budurwa dake sonsa tamkar ranta wace zata tarairayeshi ta bashi soyayar da ta dace da shi ya zo ya tsinci me a wajen mai siyar da kosai?"
Ta karashe tana dafe zuciyarta tana wani irin haki tamkar zata sume , sai cire shigar jikinta take yi domin ji take yi sikewa zata yi
Alkali ya tabe baki ya gyada kansa ya ce" Ba mamaki ke kuwa abinda zai yi ajalinki kennan, watau yiwa lamarin ubangiji shishigi da saka damuwa a abinda bai dace ace ya dameka ba, sai dai ki sani idan kika mutu a haka sai ji je ki san abinda zaki fadawa ubangijinki Hauwau, dan bana tunanin in kinada abin fada gaskiya, kuma kin ga zan so Ki kiyayi furucinki, ki kiyayi harshenki, idan kina tunanin kin tara saloli kin tsaya a kan kafafuwanki a yanzu babu abinda zai daki rayuwarki ki sani da wanda ya juye duniyar kike son kawowa hali na marar godiya a gareshi" baba ya ajiye maganar a tausashe yana binta sa kallo har ta gama shan ruwan da ta kafa tana ta wani iri irin na mai jira a yi wace za'a yin nan
Zama ya yi shina yana fuskantarta ya ce" kina maganar daraja aka kai uwar gidansa daraja ne? Ki fada min akoy namijin da zai kara mace bayan wace ya sani ta sanshi a farkon haduwa suka kasance aminen junna suke rayuwa ta mutuntawa da kaunar junna har ya auro watanta ya bata darajar da ta wuce ta wace ta sakashi a duniyar manya?, Hauwau kin yi sake tunda farko da aurenta ya dauru, kika kuma yin sake ta zauna dar a cikin gidan nan, kika hada mata lefe da kanki, har kika barta da mijinta, ya je ya samu abinda ya dace ace ya samu daga gareta kafin koda wata zata samu ya zamto mai wajen ce ta fara samu, Hauwau ki gane Aminar nan dai talaka itace mai ABDUL, du wata wace zai kawo da sunnan siyaya ko macewa a soyaya sunnanta amarya, dama zulumina tsorona kar yaje gaban Allah a tuhumeshi da wulakantar da marainiya, a yau da ya aikata haka koda ba a son ransa bane Alhamdulilah, da ke din, da shi din, babu abinda kuka isa ku yi, ita amaryar da kuke takama kema da bakinki kin kireta amarya, idan yar mutunci ce ta shigo da mutunci ta mutunta yayarta wace ta bata hanya su zauna lafiya, idan ba yar mutunci bace ni Alkali Aliyu na sayi rigimarku daga ke har duk wani wanda yake gannin ya yi ruwa ya yi tsaki a lamarin!"
Baba ya sake tsayawa yana kallonta da fahimtar duka shirunta abinda yake nufi, watau jira take yi ya yi ya gama ta fita ko?
Murmushi ya yi ya ce" Ki sani idan kika fito daga dakin nan sai dai dan ki je ki taimakawa matar jikanki , idan dan ki wulakantata ne Hauwau rigima zata kulu da ni da ke koda ita zata yi sanadiyar da ba zaki yi min takaba ba idan na rigayeki zuwa gidan gaskiya!"
A zabure ta dago daga shashareshin da take tana jira ya gama yayaba mata maganar ta je ta nuna masa ta isa da jikanta ta zuba masa idannuwa da jin furucinsa na karshe wanda shi ya fi komai neman dakatar da bugawar zuciyarta
Ikon Allah, ashe zata wayi gari ta ga halaya irin ta da namiji?
Ashe zata bude ido ta ga wulakanci irin wanda karema ba zai ci ba daga mijinta abin kaunarta Alkalinta a kan wata cen? Ashe zata ga ranar nan ita Hauwau?
Daga haka BABA mai shanu ya sake mikewa ya juya ya fitowarsa ya kama hanyar dakinsa, domin ko menene ya san a yanzu kam zata samu sasaucin farmakin da ake kai mata, domin maganarsa ta nuna masa cewa ya daga mata kafa ne,
Murmushi ya yi yana ayanawa' rikicinma ya zi da sauki masha Allah, Allah kara tausasa halayar Hauwau'
Shigewa ya yi ya rufe abinsa ya sake daukan Alkur'aninsa ya ci gaba daga inda ya tsaya , dan ya zame masa sabo idan bai yi karatun Alkur'ani ba du dare baya iya rintsa idannuwansa da dadi
Jin shirun ya yi yawa ya sakashi cire kansa daga jikin kofar da ya kifa yana sauraron kalaman kakarsa
Abubuwa ne goma da gomiyatara suka taru suka yi masa yawa a cen kasan zuciyarsa
A hankali ya juyo da nufin sake kallon inda ya ajiyeta bayan ya talafeta ya sakata a ruwan zafin da ya farkar da ita daga yar kankannuwar summar da ta yi ta dora kukanta daga inda ta tsaya da tarin Allah ya isan da tana yi yaba nema mata yafiya a wajen Allah , tunda shi dai ya san ba abin a masa Allah ya isa ya yi ba, koda an yi masa ba kamashi zata yi ba tunda ai ba zuwa ya yi ya dage bujenta ya afka ba, sai da aka daura masa ita ai kau?
kukanta ya dauke tsit tunda ta ji muryar Hajia da tsoron kar hajiar ta shigo dakin ta sameta a irin wannan yannayi ta yi tsuru tsuru tana jira ta ga abinda zai sake samunta sanadiyar wannan bawan Allahn da ya shigo mata rayuwa da garaje yake son Kaita kabarinta da ranta ba tare da rai ya bar gangar jikinta ba
Walahi, wata mahaukaciyar faduwar gaba da