Showing 111001 words to 114000 words out of 145392 words
Chapter 38 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
cen ta kama ta yi ta nanaga??"
Abdul da hankalinshi ke kanta ne yace "Ban sani ba Hajia, sannu ko Amina? Taso ga ruwa" Ya sake fada ma Aminatu dake share fuskarta da gumin data fara hadawa, ta mike da kyar ta miko hannu ta amshi ruwan goran da ya dauko ya miko mata, hankalinsa gaba daya a tashe, sai ya nufota kamar zai rikota sai ya ga ta dan kauce dan idannuwan Hajia da kuma su Baba da suka karaso har suka zo summa suna tambayar lafiya?
Abdul ne ya fada mishi a taƙaice, hankalinsa a tashe, sannan yana ta auna abinda ke iya sakata a wannan halin, domin dukkan motsin Amina biye yake da shi sau da kafa
Ya fita sannin abinda ke tare da ita da dukkan hanyoyin da ya dace ace ya bi dan taimaka mata
A gidan Firdausi ta sani, Baba kauratu ta sani, su din da kansu sunne suke sake sakashi a hanyar da mai ciki keda bukata dan samun kwonciyar hankali irin su kwadayinta dai, da yan rigingimmun da na Amina ya zo mata da shi, domin bata laulayi sai na harshe da kuma ciye ciye
Da farko ita din da kanta ta fara damuwa da ciye ciyenta, sai kawai suka hada baki idan ta dan nuna yanzu batada aiki sai ci, sai a nuna mata ai hanjinta ne ya warware dole ta ringa ciye ciye, ai cenjin yannayin kennan
Sai kawai ta hau ta zauna, tunda ba taba yin cikin ta yi ba, bata sani ba ai
Ba zai manta lokacin da ta ce tana son cin abincij nan da ake kira da ABACHA na Yoruba, kafin a samo masa mai yinshi ta yi aman nan
A hankali ya kalli Hajia yace "Ina ga fa kamar dabinon da kika ci ne ya jawo hakan."
Da wani kallo ta bishi ta ce "Ban gane ba? Guba na ci ne? To me ya hada cina da amanta"
Girgiza kai yayi yace "A'a, nufina ko tana so ne, dan na ga tana ta kallo"
Kallon Amina tayi tana mata kallon sama da kasa, aman da ta yi ta kwaye hijabin da ya rufawa dima diman duwawunta asiri , yanzu da ta dan duka suka dan bayana kadan cikin tsalelen lesh din dake kasa wanda aka yiwa dinkin doguwar riga ya kamata sosai dan dinkin kamar cif da cif ne a jikinta tace "Sai ka ce wata dangin mayu? Dan kawai tana so sai ya kaita ga amai."
Murmushi Baba mai Shanu yayi Abdul kuma ya kyaɓe baki ransa na neman bacewa
Baba mai Shanu ya sake duban Amina da kyau, juyawar da Hajia tayi za ta shige cikin Baban bangarensu yasa Alhaji faɗin "Au! Ba za ki bata dabinon ba Hajajjuna?"
Juyowa tayi duk sun tsatsareta da idanu, sai kawai tayi kamar za ta fashe da kuka tace "Saboda Allah me ye haka? Kawai daga ganin abu sai a ce shi ya sakata amai, to idan na bata ta ci ta kara amai sai a ce ni ce kuma ko? Ga dukkan alamu itama yarinyar nan ba wani kaunata take yi ba ake min dole sai na sota"
Girgiza kai Mai Shanu yayi yace " Bafa haka ake nufi ba ke kuwa, Kin manta lokacin da kika taɓa ganin goriba a hannun almajiri daga mun tsaya a bakin danja?"
Ƙura masa idanu tayi irin tana son tunawa, sai kuma tace "E, lafiya?"
Saida ya saci kallon Abdul yace "Da na hana miki saboda a ganina a hannun almajiri yana cin abinsa yaushe zamu tsaya ya baki goriba tsakani da Allah, ba saida kika kwanta asibiti ba?"
Da yanayin rashin fahimta tace "E, sai me to ai a lokacin ni banida lafiya ne"
Shafa wuyanshi yayi da hannunshi mai carbi kamar mai rad'a yace "Sai ya zama dalilin da ya kwantar da ke ne ita ma ya sakata amai ai ur excellency ."
Zazzaro idanu tayi ta kalleshi da kyau, sai kuma ta maida dubanta kan Amina da ka rantse kuɗin aika ta ci tana tsatsare Alhajin da kuma Hajia da idanu, da muryar rawa rawa ta nuno Aminar da yatsa tace"... ke ciki ne da ke?"
A zabure Amina ta muke tsayinta gaba daya tana kwalalo idannuwanta, Risalama ta juyo a zabure gabanta ya yanke ya fadi kamar zai fito ta bakinta
ABDUL kuwa a nutse ya yi taku biyu ya tsaya jikin mota ya zubawa Amina ido zuciyarsa na begen abinda baya kwana da shi bale tashi da shi a zuci
Baba kuwa murmushi ya yi ya sake tsayawa kan kafafuwansa lokaci daya shi da Amina suka yi magana,
Amina ido a waje tana dafa kirjinta ta ce" Wa ni? Aa aa banida komai......m"
Baba kuwa ya ce" Kwarai kuwa shine dai "
A haukace Amina ta juya barin Baba ta ce"
Nzl 46
A rikice, tare da tarin tsoro, da mugun son kare kanta, da tsoron kakarsa da ya shigar nata zuciyarta tana kallon Baba ta ce" Baba, ni kuma? Baba banida komai, Baba walahi banida komai, Baba ni tsakanina da shi babu komai , gayanan a tambayeshi ni walahi baba bana shigama harkarsa, , Baba dan Allah ka rufa min asiri da maganar nan, idan kuwa inadama cikin Nan walahi sai a zubar shikenan ya bani takardata na tafi, dan Allah Baba kar ya zamto inada ciki"
"Ke!, Kinada hankali kuwa?, Kinada hankali?" Hajia ta fada da wata irin murya mai girma da bacin rai
Amina ta girgiza kanta tana neman tsugunnawa ta ce" Hajia, walahi walahi ba maganar soyaya bale a kai ta son ajiye iyali a tsakanina da shi, gayanan ku tambayeshi zai baku amsa, ABDUL, ABDUL, ABDUL dan Allah ka ce banida komai ka ji ABDUL?"
A irin wannan lokacin , ko baka san Amina ba sai ta baka tausayi, domin magana ne take yi dan ceton ranta, magana take yi dan a fahimceta, hankakinta a tashe burinta a fahimceta, a yi mata uzuri, sai dai ba kowa ne a wajen nan ya fahimci inda ta dosa, shin ina zata saka ranta ne?, Ina zata dosa ne? A gaban Hajia matar da ta tabata ba kaunarta take yi ba, ta tabata abinda zata guji ji a duniya kennan cewa ta dauki cikin jikanta daya kwal a duniya, ita din da kanta tashin hankalinta ne hakan
A rikice tana girgiza kai ta ce" Hajia, dan Allah, idanma haka din ne Hajia a zubar , a zubar Hajia"
"Dan tsananin kiyaya ne ba zaki haihu da Jikana ba?, Dan bakya sonsa?" Hajia ta sake fada a kausashe, Baba dake tsaye jikinsa ya dauki wani irin sanyi yana kallonsu shima, Gefe daya ABDUL na jingine da motar nan Amina kawai yake kallo, Uwa uba Risala da take ji duniyar tai mata zafi, take ji kamar zata mutu a tsayen da take itama tana kallon Hajiar da Aminar
Amina ta girgiza kanta ta ce" Hajia ba maganar Kiyaya bane, Hajia ba maganar kiyaya bane a lamarin, rashin cencentar ne Hajia"
Da haushi Hajia ta ce" Kin ga saurara, ki saurara min haka da magana kamar zaki summa, daj walahi kin ji na rantse maki idan wani abu ya samu cikin nan sai na yi shara'a da ke!, Ke har zaki yi maganar rashin cencenta? Kina nufin jikana bai isa ya zama uban danki ba ko me? Ki kalleshi da kyau, daga sama har kasa, ke kin san Allah ne ya wanke ya baki, kar ki saki ki yi gigin taba lamarin cikin nan , walahi walahi kin ji na rantse maki!"
Tana gama fadan ta juya ta cara hawa yar matakalar biyu, sai kuma ta juyo jin Risala ta fashe da kuka ta shiga fadin" Ciki? Ciki fa? Ciki gareki? Dan Allah ciki gareki? ......"
Sai kuma ta juya wajen ABDUL tana kallonsa ta ce" Ni me ka min na adalci kennan?, Kamar bambanci ke wakana karara tsakanina da kai ABDUL, haka ka mara gini a cikin gida nace zan koma aikina kace nima sai dai idan ginnin nake so, bayam ni ba zan iya sana'a a cikin gida ba, dama ba maganar aikina kace ba zan yi aiki ba, kuma yanzu ABDUL ciki ne da ita? Ni fa wani laifi na yi mai tsauri da ya zarce sonka da ni baka bani cikin ba?"
Hajia Kanta sai da ta zarro ido tana kallon Risala,
Baba kuwa kansa ya dauke , Abdul kuwa ya zuba mata ido itama yana kallonta
Hajia ta dawo ta ciro ledar dabinon har biyu ta kamo Hannun Amina for th first time a rayuwa ta damka mata dabinon tama fadin" Wuce ku tafi , Allah kiyaye"
Daga haka ta yi ciki, suka sake binta da kallo su duka, Harda Aminar, haka kuma lokaci daya yawunta ya sake tsinkewa da ta sake kallon Dabinon, ama sai ta dauke kanta ta ki ci
ABDUL ya bude motar ya shiga kansa na sarawa, Risala ta yi tsaye bata shiga ba hakama Amina
Baba ya dubi Amina ya ce" Uman biyu, jeki falo ganinan zuwa kin ji?"
Amina ta gyada kanta ta juya ta shige ciki
Baba ya dawo wajen Risala yana dubanta a tausashe ya ce" Risala, ki yi hakuri da jarabawar rayuwa kin ji?, Na san kina son mijinki, kuma shima yana sonki, wasu yan halaya ne da suka yi sabani da ra'ayin mijinki kike yarda sunna faruwa a tare da ku, da ace zaki duba ki gyara da kin ji dadin zama da mijinki fiye da tunanin ki, ki sani yata mijinki bai tsane ki ba, hasalima yana ra'ayinki, domin da akasin hakan ne na tabata da tuni ABDUL ya salameki, dan na san waye ABDUL, koda ya yi biyaya idan baya ra'ayin abu zai sabule masa ne bale babu wanda ya tsaya da bindiga a kansa dangane da ke, ki iya rike masa sirrinsa, ki masa biyaya da zuciya daya, na tabata zaki fi kowa jin dadin zama da shi kin ji?"
Risala dake hawaye bilhaki ta gyadawa Baba kai tana sake sada kanta hawayenta wani na korar wani
Baba ya sake fadin" Idan kin jw gida ki yi nazari a hankali ki ga idan har kin amince da maganar a yi maki ginnin a gidanku ki sanar min kin ji ko? Kar ki yi nauyin baki ko ki ce ai an baki kudin hakan, ki sanar min, kwonciyar hankalinku ake nema baki daya"
Risala ta sake amsa baba sannan ta je ta bude motar su Muhammat ta shiga, dan irin kallon da ABDUL ke mata ta tabata idan ta bishi a haka sai ta raina kanta , dan abinda ya fi damunta zai yi mata, watau ya yi watsi da ita baki daya
Baba ya je wajen motar ya bude gaba ya shiga ya zauna yana dafe habarsa hadi da zubawa madubi ido
Cen ya yi murmushi yana gannin har an rufewa Su Muhammat kofa sun tafi shi kuwa bashida niyar tada motar bale ya tafin, ya tabata kulafurcin abinda bai yarda bane ke damunsa
Dan murmushi ya yi ya ce" Karen uwan nana kaya, ka san na shirya tare Kakar gwamna kuwa? Na zata tana jin cewa Uman biyu nada junna biyu summa zata yi, ka ga sai ta yi wani abu mai kama da tana son cikin, ko dai bonono take son min ta lahanta yar mutane yar marainiyar Allah?"
ABDUL ya kalleshi da haushi haushi ya cire kai yana gyattu, shi fa gaba daya Baban yau ya kunnashi fiye da tunaninsa, wai ashema ya fada ne saboda matarsa ta ji, shi abin haushinma waye ya ce Masa Mom twins nada ciki? Ya wani zo ya bude haka kaai tsaye ?
Baba ya ce" Toh fa, yo ABDUL RA'UF ni menene laifina a ciki? Ai dai ba tsoron tace bata sonka ke damunka ba ko?"
ABDUL ya dube shi ya ce" Ka ga kawai ka yi shiru, aiki ne ka riga ka yi sai ka je ka sha juss ka huta, in bama abu ba ta yaya zaka kunnan mata biyu ka wani koma gefe kana kallonsu? "
"To nima tawa matar ba na bata mata ran ba?" Baba ya fada yana kallon Abdul
ABDUL ya ce" Wannan ku ta gano, yau kuke yaki ne? Haka kawai ina lalabawa ka zo ka bude a cikin jama'a, yanzu ka kyauta kennan?"
Baba ya karkato yana nuno shi da yar yatsa ya ce" ka ga Abdul RA'UFu ka ji tsoron Allah, yo ni meye laifina a nan kuma? Ni nace ta yi aman ne ko ni nace a tambayi me yake damunta ne? Daga fadin gaskiya sai ka rufeni da fada ni da ka raina ko? Ai su baka yi masu fadan ba , du abinda Uman biyu ta yi maka ai bakaa yi mata fadan ba dan kana jin tsoronta"
ABDUL ya sake kufula ya ce" Ninema nake jin tsoron matanaa ko? Na ga ai ni da na hannasu aiki sun yi? Ka ga kawai dai ji ka sakani a uku ka ji dadi!"
Haba Abdulahi, ni banma taba gannin jarumi tsaye gaban mata ya maze masu irinka ba, ka san ko yayane namiji a matansa akoy wace ke masa kwarjini, koma nace kawai take bashi tsoro....ama kai ana rikici ko a baka ce da ko daya ba, ai wannan sai mazaje"
Da mamakin Baban ya kame haba yana kallonsa
Daria Baba ya yi kadan sannan ya yi shiru yana dan girgiza kansa , bai taba tunanin zai ga reaction irin haka daga Hajia Hauwa ba, shi har ga Allah a ransa tsoro daya ya ji kar aje ta summa su nufi asibitin dole, duda magangannun da ta yayabawa Uman biyu ba dadin ji, ama abinda shi ya hanga a tatare da ita wanda shi kadai ke iya ganninsa, tarin ruwan da ya cika idannuwanta da son ta rukunkumi Uman biyu, ama ta gaza ko kunya ce ko menene oho, a bashi mamaki, to shi a tunaninsa ai du yadda take kaunar Allah ya nuna Mata ya'yan Abdul ya zata idan Amina ce dauke da cikin ba zata so abin cikin ba
"Shin, Shin , ba zata taba ajiye maganat girma a gefe ta fuskanceni ba? Ba zata taba yin hakan ba?......... ALKALI tauye yarinyar nan nake yi ne ko me?" ABDUL ya fada a hankali sosai, yana idasawa da dan jimke hannunsa kadan ya kai wajen hancinsa, sannan ya juyo yana kallon Baba da ya yi tsai yana kallonsa
"Kana son ta ne?" Baba ya fada a hankali yana kallonsa
ABDUL ya yi shiru, shiru na dan lokaci
A hankali ya sake duban hanyar falon, a sanyaye ya ce" Ban san me take tunani da shekara daya tak da ta bani ba......................, Ko kuma abinda ke riketa soyayar wanina ne?"
Baba ya sauke ajiyar zuciya, ABDUL dinsa abokin shawararsa ne, babar shawara ko karama, tun mahaifansa da rai , yakan yi masa hira mai girman gaske , a yanzu haka, duda harshensa yai masa nauyi a lamarin nan shi ya fahimci yana cikin zuciyarsa ya yi masa riko mai wuyar fasara
A sanyaye ya ce" Kar ka riketa da furucinta ABDUL, ka sani ta fadi haka ne dan tana cikin tsoro da firgicin abinda Hauwau zata yi mata a kan hakan"
"Koda da maganar tsoro, da maganar abinda yyake cikin zuciyarta, idan am tsorata ba karya ake nemowa ba, gaskiya ake fada Baba" ABDUL ya fada shima yana tare numfashin Baba
Baba ya sake fuskantarsa yana karantarsa
A nutse ya ce" Ko me ka fuskanta kar ka yanke hukunci cikin fushi ko rashin nazartar Abu ....... Ka yi mata Uzuri ka ji?"
Shiru ne ya dauki wajen, na lokaci mai dan tsayi domin Har baba ya fara kama abin motar zai fice dan ya kula sun juyo yan miskilancin ga kuma bacin ran da yake cinyewa baya so ya saki a fahimta
A hankali ya ce" Ko me zata yi, ta yi kokari kiyaye abinda yake cikinta.....Baba ina son abina ko menene, idan abin kunya zai zamto a gareta ta haifo min sai ta bar min, ko shege ne ba zan ji kunyar rikeshi ba bale dan halal"
Baba ya lumshe idannuwansa ya sake jadada masa kalmar hakurin dai sannan ya fice a motar yana tafe a hankali duba da yannayin girma da kuma yan ciwace ciwacen jiki, a dole kuzari zai rage sosai, danma ana cikin kula ne
Sai da Baba ya shige sannan ya ja motar ya wuce gidan gona direct, dan baya jin zai iya binsu gida a yanzu
Da salama Baba ya shigo falon yana fadin" Gafararku dai Uman biyu"
Nzl 47
Kafafuwan da Amina ta watsa tana hawaye ne ta tatare tana jan Hanci muryarta a shake hadi da fadin" Shigo Baba"
Murmushi ya yi ya shigo din yana fadin" Kai kai kai masha Allah, uman biyu wai kwonci tashi yau Rabi'u ya aurar da jikarsa mai sunnan Kulu, ni kam a da idan yar ta zo gaisheni sai ni kadai na ringa yunani, sai na samu kaina da tunanin oh sunna zannen mutun, to Uman biyu zanen mutun mana yarinyar nan baki ganta ba yar tsakure da ita yar kadan, ama akoy iya kwaliya da daukan wanka fa iya tafia , wani lokacin sai ka yi zatonma yar faransa ce"
Maman Biyu dake sauraronsa tana binsa da kallo har ya nemi waje ya zauna yana zuba sam bata gane ma maganar wa yake yi ba, ita abinda ke ranta yana ranta ne
Baba ya idasa zama yana fadin" Ya zuljalalu wal'ikram"
Dubansa ya maida wajen Amina ya ce" Uman biyu yau fa inada shekara Saba'in da kwanaki a sama, tsufa kam ya zo, Alhamdulilah, Allah dai ya sa mu yi tsufa mai alkhairi mai tatare da abin alkhairi sannan ya sa mu cika da kyau da imani"
Amina ta bude bakinta a hankali ta ce" Amen Baba"
Dabinon dake ajiye ya mika hannu ya dauko ya bude shi sosai yana kallonta ya ce" Maman biyu amshi ki ci dabinon mana"
Amina ta kalli dabinon, haushinsa da son cinsa na mata yawo a zuciyarta
A hankali ta girgiza kai tana son sadda kanta
Baba ya ce" Ba kyau ai mayar da hannun kyauta Baya, amshi yar albarka maza amshi, bara na dauki biyu nika na dandana, irin dabinon nan irin dadinsa, gashi bashida ila shi dabino ko kadan "
Tana kallonsa ya ciri biyun ya fara ci
Jiki a mace ta rarafa ta amsa ta koma ta zauna ta bude ta shiga ci
Ci take yi har tana lumshe idannuwanta, shi kuma Baba yana kallonta yana murmushi har ta