Showing 48001 words to 51000 words out of 145392 words

Chapter 17 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt

13 Dec 2024

8158

da waye waye? Me zai tsinta a ciki? Sai Mai Shanu yace da ita abinda kika tsinta da kika auri makiyayi, watau shi,
A yanzu kuwa har wani salo ake kiranta da shi, uwar mai sana'a goma bama kakarsa ba.....to ita kuwa wannan dadi har ina?


Sosai suke dan zantawa tana jefo nata maganar itama, duda bata san dalilin da ya sa za'a bar yaro zaune cikinsu yana cika yana batsewa yana sauraron sirinsu ta hirarsu tsakaninsu ba, ama irin yadda hirar ta dauko dadi ana ta maganar kudi ya sa ta lume take shawagi da sauraron manyan kudade na harkar neman jikanta, kai Allah jikan iyayen yaron nan, su suka faro suka bara masa gadon da ya sake rarabawa yau ya zama haka, lalle da kudi ake neman kudi, ba irin zazabin da bata yi ba da aka bashi gadonsa, ta ringa hauka da iface ifacen a kan me za'a danka masa kudi yana da danyen kai da kadarori yaje a yi masa wayo? Akace da ita harkar gado ba'a mata haka, idan har da rabon ya tara nasa zai tara, ama ba wai a kN gado ba, kar ta kankara hakori da rigimar gado,kayadadiya ce, iska ce mai saurin wucewa


Sai da ya gamsu da degrren saukowar kakan nasa sannan a nutse ya ce" Maganar wajen Risalah"


A zabure Hajia ta dago tana kallonsa da dan zarro ido, wallahi abin sai da ya daketa, bata taba kawowa kanta zai tunkaro kakan nasa kai tsaye da maganar a irin wannan lokacin ba, ta yaya ABDUL ya aikata wannan shirmamen aikin? ME yasa bai yi mata shawara ba kafin ya kawo zancen? Ta gama daidaita cewa zasu zo da baba Rabi'u a masa zancen sai gashi shi ya masa haka kawai?


Baba Mai SHANU ya dan yi jim, sai kuma ya ce" Uhum?"


ABDUL RA'UF ya ce " Ina so a turaa karshen watan nan a gama komai ne"


Baba Mai shanu ya gyada kansa yana fadin" Masha Allah, masha Allah, kace komai ya daidaita, nan da kwana goma sha shida kennan?, To yaya ina fata Uman biyun ta aminta da hakan?"


Tsatsare babban ya yi da ido yana son gane wai da gaske yake abinda yake fada kuwa? Ta aminta? A matsayinta na wa?


Shima yannayin sakewar tasa ya fara daukewa yana kallon Baban ya ce" Tana da hurumi a wajen da bata da zabi ne?"


"Kake tunanin bata da hurumi a wajen da yake malakinta kafin watanta? " Baba ya bashi amsa shima da tare numfashinsa


"Dama dunguru gum canki canka zai zamto malaki? Ko zabin rai kan malaki wani abin ne ba wannan ba, Baba dama akoy maganarta ne?" Ya fada shima yana sake kure kakan nasa da kallon da ya sa Hajia jin kamar ta zurma ihu ta dakatar da su, ama ba hali


Baba ya yi murmushi yana gyara zamansa ya yi sak irin zaman da ABDUL din ya yi shima ya hade hannayensa waje daya ya ce" Akoy gadama ne a wajen tafka kokowa? Ko so kake ka ce min ka tsinke zumuntar da na hada ba tare da shawarata ba?"


Abdul ya dantse lebensa na kasa da takaicin lamarin nan ya ce" Wai dama cencenta ka hango ? Ta wani fanni kennan?"


Baba ya gyada kansa ya ce" Ta fannin da ya fi komai karfi, ta koyi da wanda ya fi kowa daraja, sannan ta dacewar kamarin, ko kana so kace min baka son bak'ar fata yar talakawa?"


Hajia ta kalle shi a zabure, dan walahi sai ta ji kamar habaici ya yaba mata


ABDUL RA'UF ya sake tabe bakinsa ya koma ya jingina da kujerar yana girgiza kafarsa kadan yana sake tunanin amsar da zai ba baba a dunkule ba tare da danta dake wajen ya ji zafinsu ba, dan gaba dayansu sun yi magangannun nan ne a dunkule dan yaron dake zaune, ba zasu so hakan ya zama wani cin fuska ko bacin rai ga yaron ba,
ABDUL RA'UF ya yi murmushi yana kawar da kansa bayan ya gama ayana abubuwa masu zafin da suka fi kona masa rai, shi baba zai wulakanta? Ya dauko bazawara ya maka masa, ya kuma ce sai ya tambayi zabinta idan ta aminta a aura masa wace yake nema? Lalle


A hade ya ce" Ladabin ya fi dadi idan aka cikawa kowa burinsa, naka burin ka cika baka cika nawa ba, anya hakan bai zama wani bigiri na danne haki ba kuwa?"


Cicibawa baba ya yi daga zaunen da yake ya mike tsaye, wanda hakan ya kayar da gaban hajia ta yi tsuru tsuru da tsoron kar aje abinda ya yi zai sake maimaitawa, sai ta ga wannan karron ya kalli jikan nasa ido cikin ido ya ce" Baka fahimta ba kennan, du wani rikici da tashin hankali da kokowar a mace ko a yi rai na shirya mata tsaf a kan wannan lamari, ba gudu ba ja da baya ciki harda barazanar take hakin na dindindin, ni fa a gobe ina iya zuwa na sake daura maka aure da dayar idan mai wajen ta aminta da haka!, Ita din mataki ce ta tarda naka burin!, Idan kun shirya ta amince zan zartar, in kuwa kanada wani da ya fini yake iya wakiltata da raina da kafiyata kuwa fine, na ga sanarwar a TV ko a redio"


Daga nan ya juya ya shige uwar dakansa harda rufowa da ky


Sai da ta tabatar da ya gama rufewa sannan ta juyo hankali tashe kasa kasa tana fadin" Meyake damunka ne? Ka kuwa san irin girman abinda ke dawainiya da shi a kan yarinyar nan? Laifina ne da na yi sake take bashi Wainayana ci ba lokaci,zan iya rantsewa yarinyar nan ta asirce min mijina, yama yi kokari da ba kansa ya aurawa ita ba a yadda yake kaunarta!"


Da sauri ya kalli kakar tasa, da idannuwansa ya mata alamu da Hasan


Sai dai alamu sun nuna sam bata da niyar tausasawa, ita fa dama so take yarinyar ta ji, bata san a bayan kwarya take zuba ruwa ba, dama ace Husaini ne a wajen da ttsaf zai fadawa mamansa, ama hasan? Sai dai ya kulaceta , ba zai taba kaiwa mamansa maganar ba


A hankali ya ce" Boy, je kofar daki ka yi jirana ka ji?"


Hasan ya gyada kansa ya mike a hankali ya fice a dakin
Hajia ta juyo tana fadin" Waima meye hadinka da yaron nan ne? Meye hadinka da shi a ina ka ganshi ka dauko shi? Ka ga ABDUL ka kiyayi abinda ya shafi yarinyar nan, ba kai ba ita ba Ζ΄aΖ΄anta, ina dalili ka sungumi yaron nan har kirjinka ya amsa?, Naa hanna ka, na rabaka da ita ka ji abinda na fada maka!"


Bakinsa ya tabe yana girgiza kansa, to shi fisabililahi mema ya kawo maganar wani an hada shi da ita ko an raba shi da ita ne? Wannan duka ba matsalarsa bane, matsalarsa daya ne tak a kan wai shi ya je ya nemi izininta dan zai karra aure? Lalle kakansa ya dauko da zafi


A kausashe ya ce" Me yake nufi da ni ne?, Ni zan je na nemi izinin yarinyar cen a kan maganar aurena?, To a fasa auren mana!"


Hajia ta dafe haba tana kallonsa ta ce" Auren za'a fasa? Kennan ta ci galaba a kanmu baki daya, ina fada makaa yarinyar nan isashiya ce ta san abinda ta taka, tunda ta zo gidan nan bata taba takowa ta gaisheni ba dan ta san mai gidan na darajata fiye da ni!, Ka ga za'a yi magana da ita!"


Ido ya zarro yana kallon Hajia, cece kuce dinta shi du ba shine a gabansa ba, idan ya ji ana neman dangantashi da zuwa ya nemi shawarar mace kan auren da zai yi ke kular da shi


Hajia ta ce" ni zan ganta!, Zan bata abinda take kwadayi, wanda na tabata a kansa ta nace babar banza har ta auri kannin bayanta, zata amince ne da kanta, ka bari a yi auren ni na san yadda zan yi da ita!"


Dan karamin tsaki ya yi yana mikewa tsaye ya dauki takardun nan dake ajiye ya dubi kakarsa ya ce" Allah ya bamu alkhairi"


Hajia ta amsa shi tana sake jadada masa fita a harkar yarinyar da Ζ΄aΖ΄anta, sannan ta fada masa kar fa ya yiwa Alkali fushi, yana yin abubuwan nan ne ba a cikin hayacinsa ba, ita ta sani


Shi dai ficewa ya yi a dakin ya shiga saukowa kasa


A kusan hawa na karshe ya same shi a zaune ya jinginar da kansa a jikin karfe


Zama ya yi shiga a wajen bai ko duba suturar jikinsa ba ya yi shirun shima


Sun jima a haka, har sai da ya samu ya ji fushinsa ya ragu sosai sannan ya bude takardar dake ninke ya sake zuba idannuwansa yana nazarta


A bayane ya fahimci dalilin da ya sa mahaifiyar yaron ta dake shi
Shima abin ya dan bashi mamaki, dan haka ya dube shi wannan karron da yaren turanci ya shiga yi masa magana dan yana so ya fara nazartar yaron ya ce" Ama, kana kallon ina kai ka dauki wannan sakamakon, dan uwanka ya dauki na farko?"


Ga mamakinsa, da yaren da ya yi masa magana, da shi yaron ya bashi amsa tamkar yaren shine asalin yaren haihuwarsa
Hasan da ya yi kalar zai fashe da kuka ya watsa hannayensa ya ce" Nima ban sani ba, kulun haka nake kawowa, kuma tare ake koya mana komai, kuma ni da na zo zan yi sai bana gannin komai, kulun kulun haka ne"


"Kamar yaya baka gannin komai?, Wani irin komai? Rubutun ko harda mutanen? Ko kana nufin baka fahimtar komai?"
ABDUL ya sake tambayarsa yana sake kure shi da kallo duda ya fahimci barci ne ke cike da idannuwan yaron


Hasan ya ringa tare kwalar idannuwansa yana ta kokarin fahimtar da ABDUL, domin damuwarsa ce da ta fi komai damunsa, sanadiyar wannan mamansa ke yi masa fada, a kan wannan ta sha yin kuka, ta sha zuwa makarantarsu ta yi ta tambaya, bata da hutu kulun tana koya masa, a gabanta yakan shanye komai ya fahimci komai, ama a aji ba hus ba gaba ba baya, shi yasa ta kasa fahimtarsa, har kuka take yi idan zata dake ahin fa tana dukan nasa tana yin kuka ne hakama dan uwansa
Du irin kwatancen da yake yiwa ABDUL yana kallonsa ne har yaron ya kifa kansa a gefen kafar ABDUL din yana ta shasheka ya ce" nima ban sani ba, nine jakin ajinmu fa, kowa yanada ilimi banda ni? Kuma Mama sai ta yi fushi saboda wannan"


Shiru ne ya biyo baya yana dan shafa sumar kansa mai nuni da rarashinsa yake yi


A hankali ya ce" zaka je aski ne mu tafi ?"


Dagowa Hasan ya yi ya zuba masa ido, Aski? Wani daban zai kaishi aski ba mamansa ba? Kulun kulun mamansu ke kaisu wajen aski , sai su tarda maza cike a wajen kowa babansa ko yayansa ya rako shi, ama su mamansu ce ke raka su


Abinka da yaro, da kuma abinda ya bashi sha'awa sai murmushi ya nemi kubce masa, a hankali ya ce" Ama idan Mamana ta yarda, kuma da Hasan zamu je ko?"


Shima murmushin ya yi yana dan kama kuncinsa kubulbul ya gyada masa kai


Hasan ya ringa gyada kansa , a hankali sai gashi harda nuna irin askin da za'a yi masu yana murmushi da kada kai ya ce" Nima a makaranta sai na cewa Huzaifa Muma dai Elhajin gidan Papy ne ya kaimu aski ba mamanmu ba ko?"


ABDUL ya sake sakar masa murmushi yana sake nazartar yaron
A bayane yake yaron yanada ilimi, sai dai shima yana son sannin dalilin da ya sa yaron ke dauko irin sakamakon nan har uwar ke dukansa kamar jaki!


Mikewa ya yi yana fadin" Mu je ko?"


Hasan shima ya mike din ya sauko sai dai ya ja ya tsaya yana kallon kofar dakinsu ya kasa bin Abdul din


ABDUL ya juyo yana kallonsa ya ce" Mu tafi mana?"


Hasan ya takwakwabe fuska a hankali ya nuna masa dakin ya ce" mamana, da Husainin fa?"


Hannunsa ya kai wajen habarsa ya kama yana kallonsa


Dawowa ya yi ya dan rage tsayinsa ya ce" Baka tsoro ta sake dukanka ne zaka koma wajenta?"


Hasan ya sada kansa , a sanyaye ya ce" Bata dukanmu fa, kuma wannanma da ta yi sai ta rarasheni ba zata kara min ba fa"


Haka kawai ABDUL ya ringa kallonsa yana nazartarsa


Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Mu je na raka ka toh"


Kai Hasan ya gyada yana murmushi ya shige gaba ABDUL ya bi bayansa


Sake bude kofar ya yi a hankali Hasan din ya shige sannan shima ya bi bayansa


Gannin wayam basa dakin ya saka shi juyowa, sai ya gansu gefen kofar a zaune a kasa sun yi barci su dukansu,, Husaini a nanike da ita, ita kuma ta wani lankwashe har hijab din ya yaye gana barci da abin nan na fuskarta bata wanke ba


'ikon Allah ita kuma kawai kazama ce?' ya ayana a ransa


Wajen bed din ya nunawa Hasan , ya kuwa je ya kwonta yana hangensu


Dan gyarawa ya yi ya duka da nufin dauke husaini ya mayar da shi shima saman gadon idan ya so ita ta shekara a nan
Sai dai yana kama yaron da nufin dauke shi Husainin ya rukunkume Amina, wanda hakan ya farkar da ita a gigice kuma a tsorace ta saka ihun tsoro tana dadamke hannunsa hadi da cakumarsa lokaci daya tana fadin" Kwartttttttt












πŸ˜‚πŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™€οΈπŸ˜Œ kwar me? Mun shiga uku mu daiπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚






Salam alaikum😍😍😍😍😍








*NZL PAGE1️⃣9️⃣*










Furucin da ta yi na farko ya saka shi saka hannunsa ya janye nata daga jikin rigarsa sannan ya dauke yaron da ta rukunkuma da karfin da bata san daga ina ya janyo shi ba ya je saman bed din ya dora yaron sannan ya yi tsaye yana kallonsu, kamaninsu daya yaren, harta fatar jikinsu mai haske ce sosai, babu wani abu da suka yi na uwar, shi dai bai gani ba
Kallon da yake masu ya saka Hasan sakar masa murmushi yana lumshe idannuwansa barci na dauke shi


Murmushin ya yi shima ya juyo ya kama hanyar fita


A tsaye take sai zaro idannuwa take yi kamar zata fashe da kukan takaici har ya bar dakin sannan da gudu ta nufi yarenta tana duduba su da magangannu kasa kasa tana jan tsaki hadi da fadin" Shirmen banza yaro zaka daukar min d'a ka tafi da shi ba ko ra'ayina dan ba'a san soyayar da da uwa ba, ko kashe shi na yi akoy mai magana ne?" (😌 Aa hajia mai sannin zafin haihuwa🀣)


Yana fitowa suka yi ido hudu da Hajia, wace dama tunda ya zauna da Hasan take tsaye a sama tana hangensu


Fuska ya sake hadewa ya fice gaba daya a gidan ba tare da ya tsaya ya ji wani zancen bama


Da ido ta raka shi , sannan ta je ta saka hannunta for the first time ta bude kofar ta shiga tana karewa Amina kallo wace ta dago da sauri da tunanin ko shi din ne ta yanka masa kashedi a kan wannan abin da yake son bilowa da shi


Gabanta sai da ya fadi, ta ji kamar zata summe da ta ga Hajia, tunda ta zo gidan nan anya sun wani hadu kuwa?


Hajiar kuwa kallon sama da kasa ta yi mata ta kare nazartar ba wani abinda yaronta zai ci da yarinyar nan sannan ta tabe baki a dake ta ce" Gobe, karfe goma, ina son ganninki a bangarena"


Bata tsaya ta ji amsarta ba ta yi tafiyarta ta bar Amina cike da tunani da fargaba kai harma da tashin hankali kala daban daban
Sai dai abu daya ta fi barawa ranta shine zata amshi takardarta ne a hannun Hajia, domin ta fi kowa sannin Hajia itace babar makiyar hadin nan, bata san tana gaba tana biye da ita a baya bane, da ace idan ta je a goben nan takardarta zata bata da sai ta fi kowa yi mata adu'ar gamawa da duniya lafiya!
A kan kari take
A kan gaba take
Abin nan na girmamar tunaninta da kwonciyar hankalinta
Da kyar ta iya yin wankan da siracin lalle ya kamaa fatarta sosai sannan ta murje jikinta da dadadar humurar da Baba Lubabatu ta siyo, batama san a ina ta siyo humurar ba, ama tana tunanin Humurar daga garin maradi ta saka aka kawo mata ita, ta hadu iya haduwa, ta dai ji a laluwai tana maganar humurar Ramira harun, matar ta iya humura wai ba tsada ga dadi da kwontar da hankali (ku tuntubi Kwatena dan karin bayani a kan humura mai kkarko)


Yayanta ta rungume bayan ta yi masu addu'a sannan itama ta yi ta neman hanyar da barcin zai dauketa


Da kyar dai ta samu barci barawo ya yi awon gaba da ita tana ta jan numfashi da sauke ajiyar zuciya


Kamar yadda Baba Lauratu ta auri yin safiya tunda aka daura auren nan hakane yauma


Sai dai yau ta tarar da Aminar tuni ta kwaba Lalen hausan ta shafe jikinta da shi da hadin madarar tana zaune ga dukkan alamu har ruwan nata sun tafasa


Farin ciki ta ji a zuciyarta ta koma da kanta ta juyo ruwan sai turiri suke ta kawo mata ta ajiye mata sannan ta rufa mata bargon ta shiga yin siracin hayakin na ratsa mata kofofin fatar jikinta tana lumshe idannuwanta dan sosai hayakin ke tashi


Sai da ta gama siracin ta shige bayi ta yi wanka ruwan ya sauka da lallen ta dauko tawul biyu masu duhu da suka ware tunda suka fara gyaran jikin ta lulubo ta sake fitowa


Kwabin Nescafe da kwai da madara ta bita da shi, wannan karron ta yi ta murzawa a jikin nata sosai abin na kama mata fatarta sosai har sai da ta gamsu sannan ta sake shafa mata shi wannan karron ya yi lumbuk sannan ta shiga yi mata na gashin shima sala sala sunna bi har kwan ya bushe ta sake komawa bayi


Kafin ta fito Baba ta tatare komai ta karra kintsa dakin ta kawo turaran wuta na jiki da wani sabon zannin rufa ta zauna tana jiranta


Ta dauki lokaci a ciki domin karnin kwon ne bata so ko daya, sai da ta wanke tass ama ba soson wanka sannan ta fito ta je saman kujerar ta zauna baba ta zuba mata turaran wutar na jiki mai dadi sosai a hankali ya shiga bin jikinta, sannan babar ta shiga shafa mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login