Showing 57001 words to 60000 words out of 145392 words
Chapter 20 - NI ZAN LADABIH COMPLETE DOCUMENT By Sajida Nijar .txt
ci da sha da sutura ne a kan Aminar sai ta zauna gata ga shi, haka Allah ya rubuto tata salon kadarar, tana fata ba dare ba rana Allaj ya katse mata wahalar nan da take fama da ita
Dawowar Baba lauratu da leda ta ja gidan ta rufe da sakata ta ajiye ledar ta bude tana ciro dunkula dunkulan kaji gasasu da jus dan kwali da manyan ruwan faro ya saka Firsausin da Amina zarro idannuwa
Baba ta mikawa kowace nata itama ta ja daya ta ce" Yau ai juma'a ce, bismilarmu"
Amina bata san lokacin da ta fashe da dariya ba domin yadda Babar ta yago kazar nan kamar sunna gaba da junna ne
Itama Firdausin dariyar take yi, nan da nan yawunta ya tsinke tana kallon lazar da tsoron tabata
To sai ta ji tsoro mana, ita rabonta da ta gantama ba ta manta ba, sai irin wani lokacin idan tsuntsaye suka dan sauka dan kama wani abin su ci su yi tafiyarsu dan kuwa ko na anguwa masu kiwo basa samun shigowa dan gidan a rufe yake kulun
Ci suke sunna santi da dariya, Baba zuciyarta ta yi mata fesss tana kallon yan marayun da dariyar da suka samu
A ranta take adu'ar Allah ya datar da su da farin cikin nan, ta san dadi ko wuya ba masu tabata bane har karshen rayuwa, wata rana dole a ji dadin, wata ranar kuwa a sha wuya, sai dai tana dakin ranar da zata ga farin ciki mai sunna farin ciki a fuskokin marayun nan
Amina da ta koshi da wuri tana kora jus din nan mai shegen sanyi da dadi ta ce" Kai, anya akoy abinda ya kai kaza da yaji dadagage dadi kuwa?"
Fisdausi dake hannu baka hannu kwarya baiwar Allah kamar zata tsinke yan yatsunta ta girgiza kai tana fadin" A duniya? Aa babu gaskiya"
Baba ta yi dariya tana fadin" Akoy mana, miyar taushe ta sha dadawar batsi yara ta fi komai dadi"
Aminarma ta yi dariya ta ce" Haka fa babanmu ke fadi Allah ya masa rahama, yace babu abinda zai dauke masa hankali da irin girke girken mai sunnana, watau mamansa"
Firdausi ta kora ruwan ta yi shiru tana jin wata zufa mai sanyi n tsatsago mata sai gyatsa mai nutsuwa ta bi baya a hankali ta ce" Wayo Allahna, dadi zai kasheni, Allah ka sa mutu k raba auren Auntyna"
A dan zabure Ameena ta kalleta zata yi magana Baba lauratu ta amsa da ameen, sai kuma ta ce" Bama kya tambayar biyu?"
Firdausi ta yi murmushi tana fadin" ƴaƴan mamansu ni mamakin da na yi yau babu su a rakiyar kamar wutsiya du inda ta bi sunna lake da ita"
Baba ta wani karkace tana share zufa hadi da yin murmushi ta ce" Sun tafi masalaci da babansu ne ai"
Da mamaki Amina ta kalli Baba, waye baban nasu? Kai ita gaskiya ba'a kyauta mata a duniyar nan kwata kwata!
Baba ce ta hsde sauran ta mika ma Firdausi ta ce" Kauda a kasan gado inda bera ba zai ja ba ki boye idan ya fita salar asuba ki janyo ki kauda sauran ki zuba a masai "
Yadda ta yin ya karra basu dariya, irin karma ya ji koda kanshinta ne
Murmushi ta yi a ranta tana ayana' Kaya, ai na rabaki da talaka mai zuciyar fir'auna, shi bama zai saki ransa ya cin ba in dai daga hannun Amina ya fito, a fili zan ajiye dan na tabata masu fada masa ta zo zasu fada masa, ni kuwa yau cikina a cike ai ko wace wace kawai!'
Sake gididige watannin cikin suka yi, kafin su mike su yi mata salama
Ji ta yi kamar zata dane su su tafi da ita, tana jikin kofar tana saurare har motar ta tafi ta koma cike da farin ciki ta idasa tatararta ta sake zubawa dubu goman nan ido ta yi wani murmushin hadi da godewa Allah da ya bata Amina a rayuwa
Ta tabbata da kudin nan zata jima tana cin abinci, idan ya fita sai ta yi kiran yar gidan maman husnah ta bata ta amso mata abin tabawa su ci tare ta yi daidaya ta huta abinta.....................
Talaka bawan Allah, shi baban burinsa ya ci ya cika cikinsa koda babu dadi, sannan ya samu kwonciyar hankali komai kankantarsa.....Allah ka karra rufa mana asiri duniya da kuyama, sannan ka kara ba ba mai bamu😍😍😍😍😍😍🤣
*NZL PAGE2️⃣2️⃣*
Tun daga wannan rana Baba ya saka a yi masa bincike a kan lamarin yarinyar
A hankali aka ringa kwana ana tashi har ya rage kwana hudu da son turawar da ake so ya yi , ama bai ce komai ba
A kwanakin nan du wani kwontar da kai da biyaya yana samu daga Hajia, abin ba'a cewa komai domin harda Hajia a yan kicin dan yi masa yan girke girke
Idan ya sauko yakan zauna da uman biyu, da biyu, su dan zanta sai kuma ya fice rawatawarsa da datijan anguwa da abokanansa na arziki
Jikansa kan zo ziyarar kakannin nasa jifa jifa dan kuwa har tafiya ya yi ya yi kwana biyu ya dawo ita bata da labari, idan aka yi katari ya zo sun hadu ne a ajiye take sai sun taba yar tsamar da suka saba, yawanci kuma Aminar ce zata yi gaba rai bace tana gungunnin itafa bata son raini a kiyaye!, Shi kuma sai ya yi murmushi kawai ya cira kansa ya ci gaba da lamarin dake gabansa,
A haka lokaci ya sake zuwa, a daren da ya rage kwana biyu a tura mahaifin Risalah ya yi kiran Hajia ya fada mata cewa yau su Alkali sun same shi a gida shi da aminansa biyu, har sun tsayar da maganar auren komai da komai, Alkali ya nuna yana so matan su tare su biyu dukansu a gida guda? Shin Hajia dama bata ce masa auren na hadi ne Honorable din kansa baya so ba? Yarinyar dai gatacen sai murna take yi, aman mahaifiyarta ta rikice kan ba zasu zauna gida guda ba, wai ba za'a wulakanta mata y'a ba
Hajia tunda ta kashe wayar a zaunen nan da take ta kasa katabus
Hankalinta ya yi kololuwar tashi da irin hanyar kuma da mijinta ya billo mata
Shin yaya zata yi da Alkali ne?
Ita dake jiran ranar da za'a je tambayar nan ta yi gaya ta kasa da kasa manyan mutane su je tambayar nan shine kamar aurwn bazawara Alkali zai je ya yi tambayarsa a boye ya dawo? Shin me yasa Alkali yake son wulakantata a rayuwa ne a kan auren nan na Abdul? Du salon ta nuna wani abin ne ya hana auren? Ta tabata so yake ta yi wani abin kiris ya fake da shi ya ki maganar auren
Kasa fita ta yi, domin wata tsanar lamarin Aminar ya sake shiga zuciyarta, gani take yi ko menene akoy wani zagin kasa da yarinyar nan ke yi mata bata gane ba, ta yiwuma ita ta san da maganar nan bata fada mata ba!
A kasa kuwa Alkali ne da Rabi'u suke tataunawa
Da kula sosai Rabi'u ya ce" Aliyu, tunda muka je muka yi tambayar nan a haka kamar yadda ka bukata, in dai har mahaifiyar yarinyar bata watsa abin ba ka yi hakuri kawai a yi, kar ka manta jayayar kanta bata da wani anfani fa"
Baba mai Shanu ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Na sani Rabi'u na sani, abinda ke damuna bincike a kan yarinyar da ubanta da mahaifiyar tata kanta, lalle ba'a fada min wani tabo ko wani gigitacen al'amarin da ya gyasa yan matan zamani masu yayi selfi ba, ama magana a kan kudo da mulkin nan ya tsaye min a zuciyata, sai kuma natacen so da burin yarinyar a kan jikana na dawainiya da ni, shi yasa na yanke mu je din nan a haka dan na tabata ita da kanta ta cikin idan har ta ji to fa ko ana cen an fara raba hali ko ana jirana, ka san da har yanzu ABDUL bai nuna bukatar tarewar matarsa ba? Menene aibun uwar biyu ne ni?"
Baba Rabi'u ya yi dariya ya ce" Bata da wani aibu, kuma ai da kyauma da har yanzu take a matarsa, ita din uman biyun naka ba kai ke ce min ba uman biyu ba dai son girma ba? Aliyu mutanen nan biyu lokaci da garajensu zai shiryar da su ba tare da sun shiryawa hakan ba, ni bama na so ka saka damuwarsu a ranka, kamar yadda kace in dai sun baka amsar nan da kwana biyu sun shirya za'a daura auren nan da sati biyun to fa mu shirya mu kuma basu dama su yi bikinsu irin nasu na bajinta, kar ka hanna su yin komai , ka barsu su kashe koren arzikin su , su nuna murnarsu ka ji?"
Da wannan suka gama tataunawa suka yi salama
A daren bai leka dakin HAJIA Hauwau ba, sai da garin Allah ya waye ya shiga da sasafe
A zaune ya sameta a saman salaya ta kure waje daya da ido
Idannuwanta dake dauke da kunkumbali ya sheda masa bayan na shekarun da suka dan fara ja harda na rashin barci
A nutse ya zauna yana amsa gaisuwarta
Zai fara magana wayarsa ta shiga kuka dan haka ya janyo yana kankance ifannuwansa da dubawa
Sunnan da ya gani ne ya saka shi dagawa ya saka handsfree kamar yadda ya saba amsa kira
Gaisawa suka yi a mutunce, sannan mahaifin Risalah ke sheda masa ai har sun gama shawara sun yanke shawarar eh sun shirya
Jim ya yi da mamaki da wayar a hannunsa yana kallon Hajia da ta zuba masa ido
A nutse ya sake maimaita maganar da suka yi, Baban nata ya jadada masa kwarai kuwa hakan yake nufi
Murmushi ya yi hadi da yin adu'ar Allah ya sa alkhairi za'a hada ya basu zaman lafiya, zasu zo dan tabatar da saka rana da dukan sauran tadar malan bahaushe
Hajai kamar ta daka tsalen albarka ta saka ihun murna take ji , sai murza kafa take dan dadi tana kallon mijin nata
Murmushi ya yi ya ce" Kin ga, shigowa na yi dan na sanar maku jiya fa mun je gidan su sarakuwar taki, sai ga amsar uban yace sun shirya, " tiryan tiryan ya maimaita mata abinda ta sani tuni
Ai kam murna da farin cikinta ya kasa boyuwa har ya zuba mata ido yana murmushi yana kallonta
Hajia ta sake matsawa kusa da shi ta dauki kafafuwansa masu hasken gaske ta dora a saman cinyarta ta shiga dan mamatsawa ta ce" Alkali?"
Baba ya ce" Na'am Honorable?"
Murmushi ta yi tana sada kai ta ce" Dan Allah ka barmu mu yi bikin nan yadda ya dace mana ka ji?"
Murmushin ya yi shima ya ce" Ai ba zan hanna ba Hajia, damuwata daya ce zuwa biyu, ba za'a dauki sadaki dan duniya ta fada a maka ba, ba kuma za'a dauki kayan amaryar da ya wuce na uwar gidansa a maka mata ba, yadda aka yiwa Uman biyu za'a yiwa yarinyar itama, in sha Allah zan shiga dakin Uman biyun gobe da yama na ga kayan nata da kika ce an yi mata, idan ya so itama haka nake so a kawo mu zamu kai dan bana so mata su kai bi izinillah, albarkar abin nake nema da kuma kamanta adalci, domin bana so dan uman biyu ba zabinsa bace a nuna mata bambamci, koda ba zata yi magana ba ai mahalincinmu na gani, kuma har mu zia tsayar a kan wannan laifi, bayan haka na biyun shine ina so a ba Uman biyu dama itama ta yi gayarta ta yi bikinta ta yi wadakarta, ko ba komai ai ba Alkali bane zai karra aurw, mijinta ne zai karra ko?"
Hajia ta kume tans kallon Alkali
Gannin ya sake kafeta da ido yana tambayarta ta fahimta? Bayan wannan bashi da wata damuwa, gida kuwa zai sa a yiwa uman biyu jere a nata bangaren itama in sha Allah domin dama shi yake da alhakin yi mata kayan daki, ba yau ba ya daukarwa kansa wannan alkawarin
Hajia tana ji tana gani Alkali ya gama ya fice a gidan, watau suka nufi gidan gona da yaren
A haukace ta sauko ta fice a gidan tana waya da ABDUL
Ah toh ina ta ga ta zama wani aikin na shirin balo mata? Dama maza ne zasu kai lefen, abinda dai ta tsara abokinsa da abokansu zasu kai a yi jeren motoci da kayan setinnan akwatunna na gigita kwakwaluwar karamin mai kudi mai baban buri a kai gidan, dan so take tun daga kan kayan lefen nan ta fara nunawa uwar yar ita ba sa'arta bace, da mijinta zata ja , shima ba wai dan ya isa ba, aa dan dai mutun ne shi mai baki da kazagi a wajen manya, sai gashi Alkali na son kasheta da ranta
ABDUL dake cikin aiki gaba da baya , domin a lokacinma sunna cikin meeting ne ya yi excusing din kansa a sawake ya ce" Hajia, menene abin tayar da hankali a nan? Ki hada mata irin na wancen yarinyar mana menene a ciki?"
"Abdul? Kayan da banma san me da meye a ciki ba? Saitin akwati daya dal ne fa aka hada mata, shine za'a hadawa RISalAH? Ka san da ba zai taba yiwuwa ba ko?, Ka ga ka yiwa kakanka magana kana ji fa jerema shi zai saka a yiwa yarinyar nan, ni tsorona daya kar ya dauki bangaren da ya fi kyau din a jerawa yar kauyen nan da tarkacen ƴaƴanta!"
Abdul ya dafe kansa, tafia ce ke gabansa ta kusan sati guda cir kasar spain, harkar man fetur zata fitar da shi dan nan yake son fadawa kuma, ga kuma rigimar mutanen nan a gefe? Shi da ya gama magana da Risalah auren sai ya kusa zai sauka dan yanada abubuwan yi sosai, ama kakaninsa na son rikita masa lisafi?
A tausashe ya ce" Hajia kina ji? Ki kwontar da hankalinki Please, du ni ban ga menene na daga hankali a nan ba, maganar lefen ki zauna dukkan abinda kike da bukata in a nan kike so a hado maki a hado a kawo, idan kuwa kin fi son fita ki hado sai a duba passport dinki ki je inda kike so, plz bana sin fadan nan ke da Baba"
Hajia ta sake dafe kanta ta ce" Idan nace na fita zai ga kayan da na ba yarinyar nan, kawai gamunan zuwa NI da Uma kampani mu hada komai sai a loda a kai gidan, daga yanzu har gobe zan jure na yi zaben har mu gama"..
Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya kashe sannan ya koma suka gama meeting dinsu ya kuma fitowa ya nufi office din manager ya sheda masa a bude bangaren VIP na kayan lefe ga su Hajia nan zuwa, ko duka zasu kwashe a basu dama
Nan da nan aka bude bangaren VIP din, baban bangare ne da idan yayab manya zasu hada lefe suke zuwa, domin ko akwatunnan ba kowa ke iya siya ba ko a manyan bale mu (🚶🏻♀️🚶🏻♀️🚶🏻♀️)
Hajia da Hajia Uma sun rikice wajen daukan kayan amaren, sai dai a zaben nasu sun saka son zuciya a ciki, domin a duk wajen da ya dace su zuba abu iri daya wani abin sai su bambance su dauki wanda ya fi class su saka a kalar akwatunnan da suka daukarwa Risalah masu kyau da kalar yan gayu, sai su zuba sauran a sauran akwatunnan da suka daukarwa Amina color din zabin a cakule domin har kala biyar sula kwatsa mata
A bangaren shadoji dinkaku bugagu yan waje masu zubin manyan dinkunnama sai da suka yi san rai, dan harta yawan shadojin Risalah sun fi na Amina yawa
Haka a bangaren lafaya da abaya sun daukarwa risalah na lwaliyar amarya yar gata ne, su jefawa Amina na uwar gida sha gida zaunaniyar cikin gida
Takalma ne da jakunkunna na alfarma a nan kuwa babu na koma baya, kowane ka dauka na gani na fada ne
Atampopi da lesh , kananun kaya da kayan barci, sarka da yan kunnaye
Masu tsaron bangaren sai da zuciyoyinsu suka karye gannin yadda ake kwasar kayan ana jidawa , sai da magariba ta gansu a kampani sannan suka koma gida bayan an shiga sakawa kayan irin abin nan mai kyalkyali na amare ana yin yadda Hajiar ta fada, ga sunnayen da ta bada cewa a kowane a saka sunna, Amina da RISALAH
A daren hankali kwonce ta sha barcinta dan ta san an gama wannan rikicin kuma, yanzun ta shiga shirye shiryen biki ne na garari, duda haka tana cike da jin haushin wai Amina ce za'a ba wannan jerin kayan? Ta kaisu inama wai? Ta saka su ta yaya?
Washe gari ya rage kwana goma daurin auren da kusan karfe goma sha biyu a falon Baba mai SHANU Matarsa ce da Baba Lauratu, da shi Baban ana ta shigo da kayayakin da kallonsu kadai sun isa su haukata mutun a cikin akwatunnan bama a waje ba
Baba yana murmushi yana gyada kai har aka gama shigowa da komai ya dubi Baba lauratu ya ce" Allah mai iko, Laure wannan kaya ai sun isa a bude shago, Allah na tuba zamani mai tafe da rikici kin ga kayan yan mata biyu ne wannan, ai gwara da mun zo wannan zamani mun rufe daukowa bale mu gigice, kuma fa a haka sai ki ga ana saurin rabuwa da macen ta kwashe komai kana kallo kai ga shashasha ta tafi? Ai idan nine na zuba rabin wannan ba zan yi wasa ba gaskiya, kin san da lokacin Hauwa akwatin ta kwano ce mula kai kwaya biyar? Kar ki so ki ga yadda ake rububin kallo ana ka baki"
Hajia ta karra hade rai cike da takaicin yadda baba ya bararahe yake ba wannan mata labarin aurenta, hum, shi kam ya iya zubar da mutunci walahi da girma, ina shi ina wannan dadadaur matar da ko a yar aiki ita ba zata dauketa ba?
Baba ya sake yin murmushi ya ce" Masha Allah, to Hauwau kin ga wanda na zabarwa Uman biyu, ai uwar gida ce da daukan farko ko? Tunda na ga an raba abin biyu na tabata an gama gyara komai kai masha Allah "
Cikin Hajia sai da ya yamutse waje daya kafin ya bada wani kuka kuuuuuuuuu a lokacin da