Showing 24001 words to 27000 words out of 137802 words

Chapter 9 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

sosai, domin ya yi matuƙar wahala so yake ya huta.
"Dole na yi wa Hajiya biyayya, don na samu na gama lafiya, sannan duk wanda ke son zaman lafiya, dole ya yi mata biyayya."
"Ehe ga ya masa ni dakali ne dole a zauna da ni. Dukannnin ku albarkacina kuke ci, saboda ɗanane, ni na haife shi ba uban wani ba." Ta ƙarashe maganar cikin gadara da iko, har wani hura hanci take yi, sai kuma ta ɗora da cewa,
"Ai ni na san da arzikin shi na ke ci, da tuni ya sanya mini guba na mutu." Aby ya kalle sa da ya haɗe rai, burinsa kawai ya ji ya watsa ruwa a jikinsa.
"Don haka sai ka kiyaye, karka ƙara yunƙurin kashe mini uwa." Ya ce.
"Ka yi mana tsakani kawai." Ta ce tana kallo Ajmal da yake shirin miƙewa.
"Haba Hajiya ki bi abin sannu-sannu, kuma kin ga na yi masa faɗa, dukanninmu ikon ki ne."
"Humm." Ta ce tare da ƙara tsuke fuskarta sai ta ɗora da cewa,
"Da ma dai wasu 'ya'yan ba wannan ba, an riga an gama musu huɗubar tsiya, tare da dasa musu tsanata a zuciyarsu."
Karamin tsaki ya ja tare da fara tafiya." Shikenan, zan kiyaye ba ri na shiga ciki." Ya ƙarashe maganar yana ƙoƙarin buɗe ƙofa.


"Ka na gani ko, ka na ganin irin wulaƙancin da yake mini? Yanzu inda ace uwarsa ce zai rinƙa magana yana tafiya? Amma da ya ke ba ni da matsayi a gurinsa kalli dai ka gani da idanunka, ai gani, ya kori ji. Kai ni jikar mai gishiri na ga ta kaina, an na san za'a rina tun da ka haɗa jini da dangin jaraba!" Ta dasa aya cikin muryar kuka.
"Kai Ajmal ina za ka kan jin abin da take cewa?" Ya tsinci kansa da faɗin hakan, domin shi kansa ya gaji da rigimarta.
Tsananin takaici ya sa ya tsaya amma ba tare da ya juyo ba, sai da ya ɗan tsaya jim don ya saita fuskarsa, sannan ya koma ya zauna zuciyarsa kamar za ta fashe.
"Ma za duƙa ka ba ta haƙuri, kuma ya this should be last and end." Cikin zafin murya ya ƙarashe maganar.
"Ki yi haƙuri." Ya faɗa yana hararta da take masa murmushin tsokana.
"To in ban haƙura ba, duka zan rufe shi da shi? A dai guji gaba, mutum ya san kamar yadda ba shi da mutunci ni ma ba kanwar lasa ba ce ehe."
Har ya kai bakin kofa sai kuma ta juyo tana kallon Aby, bayan ta ƙwala masa kira.
"Wallahi daga gani, yaron nan ko ka mutu ba zai yi zumunci ba. Ƙiri-ƙiri 'yar'uwarsa ta zo, amma ba na jin ya ganta ballantana ya yi mata sannu da zuwa. Ana ci a ƙasar uwarta, ana taƙama da jin kai na banza."
Ba shi ba, hatta Aby sai da ya ji kamar zai saka kuka. Ya juyo ya kalle sa da idanunsa suka canza kala. Ajmal kuwa, sororo ya yi, yana kallon Aby da ya kasa cewa komai na ɗan wani lokaci.
"Kai anya, sun fa gaisa ko Ajmal? In kuma ba ku gaisa ba, ma za dawo ku gaisa."
Sai ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin,"Ma za shi tana ciki 'yar albarka, wacce ta yi gadon mahaifiyarta."
A wannan karon ma babu daɗi suka ji, duba ga yadda take tsine ma yaransa, tare da jawo masa jafa'i kala-kala.
"Haba Hajiya! Kamata ya yi ki kira ta su gaisa ba wai ya je ba, ko don gudun raini, kin ga yana gabanta ai."Ya ce da ita yana ƙoƙarin cire komai a ransa.
Ajmal ya kalle ta fuskarsa cike da mamaki. Wato sune jikokin da ta tsana kenan?" Tunaninsa ya yanke daidai lokacin da Hajiya ta ƙwalawa Jannah kira.
Jannah da ke zaune da wayarta akan gado tana hira da ƙawarta 'yar school ɗinsu, wanda kiran ya sanya ta kashe wayar tare fita.
"Aby ina wuni?"Ta ce tana ƙoƙarin zama a gefen Hajiya Baaba.
"Lafiya lau. Ga ɗan'uwanki ku gaisa, ganin ba ta da ninyar gaishe shi."
"Ina wuni?"Ta furta a gajarce.
Ko kallon inda take bai yi ya msa da."Lafiya." Ya fice da sauri daidai lokacin da ya ji tana ce mata.
"Ma za ki shiga kicin, ki zuba abinci kici, na lura sam ba kya son cin abinci. Shi ya sa gaki nan kamar a hure."
Jannah ta shige ciki ba tare da ta amsa ba, kuma ba wai don ba ta ji ta ba.
Suna fita ta miƙe cikin tsananin murna ganin yadda ta nuna masa iyakarsa, jin kiran sallah ya sa ta nufi bayi tana faɗin, Ma za ki fito kiyi sallah Jannatuu."
Ya jima a tsaye a ƙofar ɗakin yana mamakin halinta sannan ya wuce kai tsaye ɗakinsa, yana jin wani irin tsananin tsanarta na shiga cikin ransa, tare da zagaye duk ilahirin jikinsa.
Wayarsa ta yi ƙara ganin sunan Hajiya Baaba, sai ya kashe wayar gabakiɗaya ya kifa kansa yana mai da numfashi a hankali.
Miƙewa ya yi, ya zura doguwar riga jallabiya tare sa saka takalminsa zai fita, sai kuma ya fasa don ya gaji matuƙa, Nahlin ya kira tn ɗagawa ya ce,
"Ki kawo mini abincina, na gaji ba zan iya zuwa mu ci ba."
"To Yaya."Ta amsa ta bangarenta.
Ya kashe wayar tare da komawa ya zauna. Idanunsa ya lumshe yana jin yadda kansa ke sarawa.
"Adamuu, saboda iskanci ina kiran wayarka ka kashe ko? Ko da yake ba shi ya kawo ni ba, ina nonona?"
Zuru ya yi mata yana kallonta aransa kam yana jin Hajiya sai ta sanya masa hawan jini.
"Ban siyo ba, kuma mai nonon ba ta zo ba."
Tsaki ta saka jin abin da ya ce, "To dole sai ita? Ni wallahi ra'ayinka na riƙau na damuna."
Tsananin mamaki ya kama sa, domin ita ce ta hana shi siyen ko wane nono sai na ta.
"Haba Hajiya! Wallahi ki fita idanuna, kin san ni ma ba kanwar lasa ba ne..."
"Au fitsarar da ka saba za ka yi mini? To ina zuwa." Numbar Aby ta nema wanda ko bacci take yana tunanin za ta iya nuna ta, saboda a rana sai ta kira shi ta kai masa ƙara sau kusan nawa.
"Tsaya, ubanka zan kira sai ya siye mini." Bai ce mata koma ya tsaya kamar gunki.
"Ma za Muhammadu fito ka siyo mini nono, Adamuu bai siyo mini ba, saboda mugun abu."
Aby ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, sai ya rasa haushi wa zai ji tsakaninsu.
"Kai Ajmal ma za ka siyo mata hura, ai ka san dole sai ta sha take kwanciya." Ya ce tare da kashe wayarsa cikin ɓacin rai.
Juyawa ya yi cikin ɓacin rai ya ɗauki key ɗin motarsa zai fice, wanda ta yi kamar zai bangaje ta.
"Ni fa ban yi maka dole ba, ka bari ubanka ya siyo mini, ni kaina hankalina zai fi kwanciya, don kar ka sanya mini guba na mutu."
Nahlin dake riƙe da farantin abincinsa tana kallonsa sai tsananin tausayinsa ya kamata, ganin yadda yake layi idanunsa sun canza. Haushin Hajiya ya ƙara kamata, domin ji take wani lokacin kamar ta mutu su huta, gabakiɗaya ta takurawa rayuwansu da fita, don kawai ta haifi ubansu.
"Hararata kike don ubanki ko? Kin san halina tamkar zawayi na ke." Ta ce tare da kai mata bugu wanda ta kauce da sauri ta shige ɗakinsa tana harararta.
Bai dawo gidan ba sai da ya samo nonon. A lokacin d ya dawo, tana falo tana kallon dabbe a tashar tauraruwa. Kallon sa kawai ta yi, daidai lokacin da ya ije ledar ba tare da ya ce mata komai ba, ta ci gaba da kallonta.
Wani kallo ya watsa mata yana jin tamkar ya kai mata irin nushin da aka kai wa mutumin da suke dabbe.
Bai shiga sashin iyayensa ba, domin hatta Aby ya fara ba shi haushi, don shi yana ganin da ɗaurin gindinsa take gara rayuwarsu kamar ƙwallo. A hakan yadda take juya rayuwarsa, wai tana shakkarsa wani lokacin.
Bayan ya ci abinci sai ya samu ɗan sauki ya kwanta tare da ɗaukar wayarsa ya kira numbar sahibarsa Mushirat, da take ta kiransa tun da ya dawo, wanda tsabar takaicin da yake ciki ya hana shi ɗaukar kiran. Ringing ɗaya ta ɗauka cikin muryar shawaɓa. Sun daɗe suna waya daga bisani ya katse kiran ya shiga bayi tare da ɗauro alwala ya yi sallah sannan ya kwanta bacci




LONDON
Mom zaune akan kujera a cikin ofis ɗinta da mai tsananin kyau. Juyawa ta yi kan kujerar da take zaune, hannunta riƙe da waya tana magana cikin zafi. A jiyar zuciya ta saki tare da kashe wayar tana huci, sai kuma ta ƙara ɗaukar wayar, tare da kira ta ci gaba da cewa,
Look! Your attitude shows me that you are trustworthy, and I trust person once, when he disappointed me I can't go with him any more."
Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Daga can ɓangaren aka yi magana, sai ta yi shiru tana saurara, zuwa can kum ta ce,
Which evidence do you want me to show you? We cought you read-handed. So refund all the money and I cancelled the contract, in that case, I just give you the rest of today." Tsaki ta yi tare da ije wayar tana huci.
"Wayyo Allahna! Mai sa mutane suka zama haka ne? Ni kam na rasa mai na yi wa mutane suke ha'inta ta, a duk lokacin da na aminta da su. Honestly! I really don't know. Wataƙila kuma al'ummanne suka ko ɗauki son zuciya da hamdamar dukiyar mutane."
Sai ta miƙe daga inda take tare da fara safa da marwa a ofishin.
"Ya Allah ka ƙara ƙarfafa zuciyata akan kyakykyawar ninyata kar mutane su canza ta, don na fara tunanin na daina."
Ƙarashe maganar ta cikin ɓacin rai, sai kuma ta yi jida da glass ɗin dake ɗauke da kifaye a ciki suna ta wasannin su.
Ƙarar fashewar ya tsoratar da sakatariyarta ta yi ma za ta miƙe tana ƙoƙarin kauda gilashin da ya shafe.
"Take easy Ma'am."
"Please call James tell him that I want to see him urgently."
"Ok ma."Ta ce tare da barin abin da ta ke yi ta fice da sauri.
Zama ta yi tana jiran sa, sai kuma ta ji ba za ta iya zamar ba, miƙewa ta yi ta ɗauki jakarta ta fice dag ofishin.
A mota wayarta ta yi ƙara alamun shigowar tsako ta Whatsapp, wanda da sauri ta ɗauki wayar. Ganin Madam Ketric ce; shugabar marayu na Ƙasar Yukrain. Ya sa ta buɗe jikinta har kyarma yake. Idanunta suka kawo ruwa, sai take mamakin tsananin mugunta da son zuciya irin na Samuel da yake son ya yi handama da babakere akan kuɗin da zai kai musu.
Lokaci guda sai take jin memories da ya faru tsawon shekaru yana ƙoƙarin yin recalling a kwanyarta, wanda ita kanta ba ta son tuna lamarin, domin in ta tuna sai tafi wata ba ta dawo daidai ba.

Da sauri ta ije watar cikin tsananin tausayawa halin da suke ciki. Ije wayar ta yi, ba tare da ta tura mata da reply ba.
Maigadi na buɗe gidan idanunta suka hango mata dad da yake zaune a swimming fool, hannunsa riƙe da jarida yana karantawa, yayin da idanunsa yake sanye da farin tabarau.
Da sauri ta yi ƙoƙarin kauda abin da take ji game da shi, wanda ba ta gane tsana ce ko haushinsa take ji ba, don tana ganin shi ne silar duk abin d ya faru da rayuwarta.
Kafin direba ya gama perking ta buɗe murfin ƙofar ta fice cikim hanzari, ba tare da ta ɗauki komai ba, tana wani irin tafiya, wanda hakan ya yi matuƙar tayar da hankalinsa matuƙa, domin tun da ya ganta haka ya san babu lafiya. Tunanin hakan ya sanya ya yarda jaridar ya bi bayanta hankalinsa a tashe, ya yin da zuciyarsa ke fargabar isa gareta don ya san yau sai Allah a tsakaninsu.
"What's wrong Halima, are you alright?"Ya ƙarasa maganar yana kamata.
Watsa mishi idanunta da suka rine ta yi tana masa mugun kallo wanda ya sanya zuciyarsa ta buga da ƙarfi.
Dafe kansa ya yi da sauri ya zauna a kan kujera don ya san yau gidan akwai tremendous problem don ba ya tunanin za ta ba bar shi ya kurɓi ruwa lafiya, dama haka take yi in har ta shiga irin mood ɗin kasancewarta mace mai zafi.
"She is in trouble sir. Please try to pacify her."
Escort ɗinta ya furta tare da ije mata jakarta da takalmin sauran tarkacenta ya fice.
Ya bi ta da kallo daidai lokacin da ta ƙarasa cikin ɗaki tare da buga ƙofar da ƙarfi! Dabas ya zauna a kan two seater, ba tare da ya bi umurnin zuciyarsa da take mishi umurin ya bi ta ba amma tunawa da ya yi, she could hurt herself, sai ya zabura tamkar wanda aka yi wa allura ya bi ta, har yana tuntuɓe da center table, amma bai kula ba.
Ilai kuwa domin sanin hali yafi sanin kama. Ya same ta tana ta bubbuga kanta a jikin gado.
"Be patient Halee. "Ya furta cikin tautausar murya tare da haɗata da jikinsa.
"Haka zan cigaba da rayuwa ina mutane suna ha'inta na? Mai na yi nake fuskantar hakan? Mai ya sa mutane suke son ruguza kyakykyawar ninyar da na ɗaukarwa al'ummata. Ina tsananin tausayin talaka da halin da Ƙasarmu da wasu ƙasashen suke ciki, amma mutane sun son burina ya tashi a tutan ma'aho. Wurgi ta yi da laptop ɗinta.
Da sauri ya ƙara rungume ta ganin ɓarnan da take yi.
"Calm down. What go up, must come down..."
Wani irin kallon ta yi mishi da ya sa sauran maganar ta maƙale a bakinsa, sai ya ji duk kalaman da tattara su don ya rarrashe ta da su sun ɓace. To me yake son ya ce mata, kasancewar she was a victim because of his selfishness. Idanunsa suka canza kala, sai ya ji ya kasa cewa komai.
"Hence, I need to quit my good intentions." Ta ce tare da wurgi da ɗankwalinta ta fice daga ɗakin.
Tsananin ɓacin rai ya ƙara shigarsa, idanunsa suka kawo ruwa, amma sai ya yi namijin ƙoƙarin mai da su ta hanyar jan ajiyar zuciya mai ƙarfi, yana jin yadda zuciyarsa ke zillo tamkar za ta fito wajen.
Kusan minti goma ya na zaune a gurin ba tare da ya motsa ba, tunani barkatai suke damun zuciyarsa, wanda ya kasa samun mafita a cikin su. Kimanin 'yan daƙiƙa, ya yi nasarar miƙewa ya yaye labulen dake jikin windon yana kallon waje, ya yin da yake jin matuƙar haushin kansa akan yadda ya biye zuciyarsa ta yi galaba a kan farin cikin rayuwarsa.
Lokaci guda Jannah ta faɗo masa sai ya ji duniyar da abin da ke cikinta na son gimshe buƙatunsa.
Idanuwansa sauka hango masa ita da take tsaye a gefen filawowi, tana riƙe da wayarta, wanda ya tabbatar da hoton Jannah take kallo, domin y lura ko shi kansa bai yi kewarta kamar yadda ta yi ba, tana dai dojewa ne.
Hawayen da take ƙoƙarin mayarwa suka gangaro a saman kyakykyawar fuskar da yake tunanin ba ta cancanci zubar da hawaye ba. Sai ya ji tsanar kansa da damuwa sun ƙara ninka na da. Sakin labulen ya yi, yana mai jin yadda zuciyarsa ke ƙara zarginsa.
Mom ta ɗuke idanunta daga kallon hoton Jannah da take yi, wanda suka yi a lokacin da ta rakata Ƙasar India. Idanunta suka ƙara kawo ruwa, har tana jin yadda zafin su ke toya fuskarta.
"Ina matuƙar son Jannah. Why Jannah? Mai ya sa ki k zaɓi cutar da zuciyata ta hanyar nisanta kanki da ni?" Ta furta tana shafa hoton.
Sai ta rungume wayarta ta ci gaba da cewa,"Don Allah ki dago gare ni, kamar yadda ba zan iya komawa Nigeria ba, haka kuma ba zan iya rabuwa da ke ba. Allah shi ne shedata a kan irin ƙaunarki da na ke yi, amma sai kika sanya shamaki a tsakaninmu."
Tsakon da ta tabbatar ko ta tura ba za ta duba ba, kamar yadda take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login