Showing 87001 words to 90000 words out of 137802 words

Chapter 30 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

hon ɗin mota ta zura a guje dama tun da suka dawo ta kasa zaune sainsafa da marwa take tsakanin falo da harabar gida.




"Oyoyooo daddddd." Ta ce tare da faɗawa jikinshi ta saka kuka.


"A really missed you dad." Ta ce tana share hawaye ba tare da ta kula da mom da ta fito daga cikin motar da shiga ta alfarma ta tsaya tana kallonsu yayin da wani abu ya toƙare mata ƙirji.




Hajiya Baaba ta fito da sauri tana gudu ta faɗa jikinta.




"Allah na gode maka yu Halimatuu ta dawo Ƙasarta, Allah ya ci gaba da kare ki da idon maƙiya." Sai kuma ta saketa tana shafa jikinta da ta koma tamkar balarabiya.






"Oh kece kika koma haka? Ai zan tsaya tsayin daka na hana duk wanda zai ƙara sanya ki zubar hawaye har ki gudu ki barni sai inda ƙarfina ya ƙare."




Dad ya yi shiru sai ya ji babu daɗi domin ya san magana ta yaɓa masa, amma da yake tsuntsun da ya ja ruwa.. Sai bai nuna damuwarsa ba ya janye Jannah da ta maƙale a jikinsa tana kukan murna.




"Ki je ki yi hugging mom she missed you more than me." Ya ce a hankali yana tura ta gurinta ganin yadda gabaki ɗaya hankalinta na kanta sai kallon ta take yi.




Ɓata fuska ta yi sai kuma ta nufe ta kan dole ganin yadda ya haɗe rai.


"Evening mom, how was you trip?" Kowa a gurin bai ji daɗin yadda ta yi mata gaisuwar ba, domin murya ƙasa-ƙasa ta yi ba tare da walwala.




"Evening my daling baby, kin ga yadda kika ƙara girma kika yi kyau Jannah, me Hajiya Baaba take ba ki? Kin yi kyau." Ta faɗa tare da kamota ta rungume duk da ba ta so hakan ba, sai dai hakan kawai zai rage mata raɗaɗin ƙaunarta da ke addabarta a zuciya.




Da sauri ta janye jikinta ta koma gurin dad ta riƙe mishi hannu daidai lokacin da Ummu ta faɗa jikin mom tana ihun murna.




"Dad, duk da you suprised me, but I got you something."
"Ok." Ya ce yana shafa kanta.




Gabaki ɗaya suka tattara suka shiga falon Hajiya Baaba da ya sha turare sai ƙamshi yake yi.




Ammy ta ba da oder aka fara shigowa da abinci kala-kala da drinks.




Mom ba yi ta shiga ta yi wanka haka dad sannan suka fito falo bayan sun ci abinci aka fara hira.




"Yauwa, na ƙosa ku dawo ayi maganar auren Jannah tun da yanzu kun dawo sai a fara don wallahi na ƙosa na ga na haɗa wannan aure..."




"Haba Hajiya Baaba, kar ki manta yau suka dawo ya kamata su huta don Allah."




Hararar shi ta yi kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta fara da cewa," Ai da zafi-zafi akan bugi ƙarfe."




Jannah kuwa kallon banza ta yi mata a ranta tana faɗin," Ni ba ni da lokacinki, tun da Allah ya dawo mini da mahaifina na ga wanda za ki aura ma wannan tsohon."




A ranar wuni ta yi tana maƙale da dad har aka kira sallar magariba ya nufi masallaci. Ko da ya dawo daga sallar isha sai ta bishi sashin Ajmal da yake nan ya sauka.




Hannunta ya kama ya riƙe cikin so da ƙauna."Kinga yadda kika canza kika girma? Gaskiya Hajiya ta iya kula dake, gabakiɗaya kin juye kin koma sak mom ɗinki.




Ɓata fuska ta yi jin abin da ya ce," And I hated resambling with her da na yi, inda na gode ma Allah kalar fatarka na ɗauko, ba irin na ta jajakuwa ba."




Dariya ya yi sosai jin abin da ta ce ya kama kumatutunta ya ja yana faɗin, "Oh my little girl akwai rigima abin alfaharine kiyi kama da ita."




"Oh dad, let change the topic amma ni bana son haka. Ina matuƙar sonka na so ace komai na ka na ɗauko."




Dariya ya yi shafa kanta tare da miƙa mata tsarabar da ya siyo."Wow dad, thanks na ji daɗi sosai da ka siyo ma Ummu duk abin da ka siyo mini, cus she is alot to me."




Sai ya yi dariya tare da miƙewa ya kama hannunta.




"Dad, ka ga yanzu tun da ka zo sai ka tsawatarwa Hajiya Baaba maganar auren da take mini I'm sick of it kullum maganarta kenan."




Gabansa ya faɗi sosai har sai da fuskarsa ta bayyana. Gyara zama ya yi sannan ya ce,


"Ki kwantar da hankali kin san Hajiya Baaba, suruka take a gareni, so I must speek to her politely kuma duka when I have arrived? At least I have to rest to tomorrow."




Ɓata fuska ta yi don ita ba haka ta so ba, saboda ta so daga zuwa ya zare mata ido da nuna iko akan dole ba za a yi auren ba. Miƙewa ta yi.




"Ok dad, amma ka san dole sai ka zare mata ido ka nuna isa a kaina, don wallahi ba ta da hali ta cika shiga hanci da ƙudundune. Haka kawai ina zaman zamana ta jawo mini bala'i da musifa."



Shiru ya yi ba tare da ya ce mata komai ba duk da cewar kallonta yake yana sauraronta, amma ba shi da abin da zai ce mata domin shi kansa tsoro take ba shi, musamman wani mugun kallo da ya gani kamar tana masa.




"Dad, you remember that you promised to me you will stand by my side?"





Ta tambaye shi cikin sauri ganin yadda ya canza fuskar tsoro, domin gabakiɗaya tun da ya ga Hajiya Baaba ya firgice, gani yake kamar za ta iya nasarar ra ba shi da Halima a karo na biyu.



"How could I forget. I had been counting the days, to come back and be by your side my girl."




Murmushi ta yi jin abin da ya faɗa." Amma dole ka nuna ba ka tsoronta wani lokaci.








Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093




KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 24-25*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"How could I forget. I have been counting the days to come back and be by your side my girl."




Murmushi ta yi jin abin da ya faɗa." Amma dole ka nuna ba ka tsoronta wani lokacin she is so disgusting."


"Ok, I will Jannah, yanzu ya kamata ki je gurin mahaifiyarki ku yi hira domin ta yi kewarki sosai.




Miƙewa ta yi." I'm very exhausted I wanna rest, goodnight." Ta ce ba tare da ta ba shi amsar tambayar da ya yi ba.




Bin ta da kallo har sai da ta ɓace bayan ya ɗaga mata kansa yana murmushi. Mayar da kansa ya yi ya shiga duniyar tunani.






A falon Hajiya Baaba suna zaune suna hira bayan Aby ya yi musu sallama ya fice Hajiya Baaba ta kalli 'yarta cike da so da ƙauna.




"Ni kam Halimatu kin yi sakaci a rayuwarki, sam Jannah ba ta damu da ke ba. Tun da kuka zo take naniƙe da mahaifinta, amma kallon banza ba ki ishe ta ba."




Kanta ta shafa cikin tsananin baƙincikin hakan. Idanunta suka kawo ruwa sai ta yi maza ta goge da gefen hannunta.




"Na san cewa na yi kuskure a rayuwata na rashin kula da 'yar da na haifa, idan da ace ana maida hannun agogo baya ba zan barwa masu aiki alhakin kula da ita ba. Zan ware lokacina na kula da ita sai dai bakin alƙalami ya bushe, domin tamkar maƙiyarta haka ta ɗauke ni wanda hakan na mini ciwo kasancewa ita kaɗai na haifa."






"Daga baya kenan halimatu, wane irin jan kunne ne ban yi miki ba, amma ki ka ɗauki ɗabi'un yahudu kika ɗora wa kanki, ba ki da lokacin kanki ballantana na ta. Abin takaici kika gudu da ita duk akan banzan dalili na ƙi wanda kina da ikon kawo ƙarshen matsalar. Ai ni wallahi kin bani mamaki. Haihuwa sai dai kika ana yi ita ɗaya Allah ya ba ki, kuma kin ɓata rawarki da tsalle gurin tarbiyarta."




Hawaye ta share waɗanda suka zubo mata ba tare da ta sani ba."Na yi sakacin da babu gyara."




"Sakaci babba ma kuwa, domin Jannah ta buwayi kowa. Kin san yadda nake da iko a gidanan ba a isa na shata kara ba a tsallake, amma ina saka ɗauka take ta karya shi, ga shi nan yaran gidan gabaki ɗaya sun raina ni."




"Ki yi haƙuri hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yar."




"Haƙuri ya zam dole amma kin san ko ku da kuke 'ya'yana kuka yi mini saina ɗau hukunci a kanku. Wannan dalilin ya sa zan haɗa aurenta da Adamuu domin shine kawai maganinta, sannan na rama abin da kuka yi mini na auren waɗanda ba na ra'ayi sai kuji zafi da raɗaɗin da na ji."




"Haba Hajiya, sau nawa za mu baki haƙuri akan haka? Don Allah ki manta komai ya wuce. Ina lura da kallon da kika yi wa Injiniya, gabaki ɗaya raina ya ɓace shi ɗin fa mijin.."




"Rufe mini baki.. Har yanzu kina nan kina wahalar da kanki a kansa duk abin da ya yi miki? Ke kam soyayya ba ta amfanar dake komai ba. Kin dai rako mata duniya wallahi."




Shiru ta yi tana girgiza kanta sao kuma ta buɗe ba ki za ta fara magana ta katseta.




"Ke ni ba wannan ba, maganar auren Jannah shine a gabana, ba na son a ja da nisa kafin ki tafi Abuja a sanya rana kawai."




"Hajiya Baaba, don Allah karki shiga cikin rayuwar Ajmal da matarsa. Suna rayuwarsu cikin farinciki don Allah karki tarwatsa hakan. Kuma Jannah ba ta son shi, tsarin rayuwar..."




"Kin san Allah Halimatuu, in kika ga ba ayi auren ba mutuwa na yi babu fashi, in kuma ba kwa so sai na sha guba na mutu ku huta."



"Subuhallahi! Ba ta kai nan ba Allah ya ba ki haƙuri."




"Haƙuri kayana ai sai an cuce ka ake ba ka shi."




Shiru ta yi ba ta ce komai ba sai Hajiya Baaba ta kalleta ta ce,"A cikin gidansa nake son ta zauna don karya je ya ije mini ita a wani guri can, so nake ta zamo mowa a zuciyarsa.




Kallonta ta yi tana mamakin ƙarfi hali irin na ta."Ba komai duk yadda kika ce za a yi. Shi Ajmal ɗin ya nuna yana so.."




"Adamun banza shi a suwa da zai ce ba ya so. Na ga lokacin da kuka yi auren ku ina so ne?"




Girgiza kanta ta shiga yi ba tare da ta ce komai ba domin lamarinta ya fi ƙarfinta.




"To kamar haka yadda kuka yi mini ƙarfa-ƙarfa zan yi musu."




"Allah ya sanya alkhairi ya kuma ba su zaman lafiya." Ta ce sai kuma ta gyara zama tana kallonta da ta amsa da amin cikin sauri tana harare-harare.




"Zan yi magana kan kayan ɗakin da duk abin da ya shafi biki." Ta faɗa cikin rashin karsashi.




"Mom, is what I heard coming from you? The you mean you support her?"




Ta ce cikin ƙara domin tun da suke maganar ta ke jinsu sakamakon ɓoyewa a bakin ƙofa da ta yi.




"Calm down, you need to understand m.."


"Understand what mom? No it shouldn't be happened da bakinki kike maganar aurena as my age. To bari kiji na rantse miki babu wanda ya isa ya yi mini auren dole we have passed that era."




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login