Showing 99001 words to 102000 words out of 137802 words
Chapter 34 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
Murmushi ta yi suka ci gaba da waya, wanda sai da aka kira sallah sannan suka yi sallama, shi ma ba don sun so ba sai dai don su yi sallah.
A ranar mom ba ta samu damar ganawa da Mujee ba, domin tun da ta fita da safe ba ta dawoba sai cikin dare wanda tana dawowa ta shige ɗakinta, ta kulle ƙofa ta fara aiki a laptop ɗinta daga nan bacci ya kwasheta.
Da safe misalin goma da rabi Ummu ce da Jannah a dining suna karyawa, sai Hajiya Baaba da ke kallo Ammy da Nahlin suna ɗaki tana haɗa kayansu, domin gobe da safe za su tafi.
Mujee ta fito daga ɗakin da ya zama mallakinta, ta yi wanka cikin doguwar rigar da mom ta ba da umurnin aka siyo mata da hijabai har da gyaluluwa, domin kusan akwati guda aka yi mata.
Babu laifi ta yi kyau don har yanzu tabonnin fuskarta ba su gama washewa ba, amma ta ɗan ciko ba kamar lokacin da ta zo ba sai ƙamshi take bugawa.
Ture abincin da take ci ta yi tare da ɓata fuska.
"Kai wannan bagidajiyar mata ta sa na rasa appetite na, saboda am not more interesting. Bayan talauci ma har da mai da ta shafa suka ɓata mata fuska, ni wallahi in na ganta I fell like vomiting." Ta ce tana hararta.
"Please Jannah, stop is not good and is disrespectable. She is your mom's friend and old enough to be you mom."
"Tir! Never over my dead body, wannan kucakar ta zama mahaifiyata."
Mom da ta fito daga ɗakinta ta ji duk abin da take cewa, wanda tsabar baƙinciki ya sanya ta tsaya ta kasa magana domin ta rasa mai za ta ce mata, saboda lamarinta yana ba ta tsoro.
Ƙarasowa ta yi da nufin ta tsawatar ma ta daidai lokacin da Mujee, ta ƙarasa kan dining ɗin za ta zauna.
"Ke dalla can ki je ƙasa ki ci abinci, ko ba ki ga masu gidan suna karyawa ba ne." Ta daka mata tsawa tana faɗin haka wanda har sai da ta firgita Ummu ta miƙe a razane tana kallonta.
Da sauri Mujee ta matsa gefe hawaye na bin fuskarta ba tare da ta ce komai ba.
"Ke fa ba ki da kunya uban kowa sai kin tozarta har da ƙawar uwarki ba za ki raga mata ba." Cewar Hajiya Baaba.
Tsaki ta yi ta tura bakinta ta miƙe za ta bar gurin wanda daidai lokacin da mom ta ƙaraso gurin ba ta yi wata-wata ba ta ɗauke ta da mari.
Wani irin ihu ta sa har sai da gidan ya amsa ta yi watsi da lafiyayyen abincin da aka shirya akan dining ɗin.
"Wayyo Allah! Na shiga uku! Wataƙila sai kin kurmantar da ni da wannan ƙarar naki kamar gyare." Cewar Hajiya Baaba tare da toshe kunninta.
"Kika mare ni akan wannan matar?"Ta tambayeta tana kallonta ido cikin ido
"Na mare ki nan gaba duka zan yi miki matuƙar kika ƙara mata rashin kunya."
"Daadd! Ka ga mom ta buge ni akan wannnan matar da na tsane ta haka kawai nake jin kamar na kashe ta, kuma ba zan ɓoye ba dole sai ta bar gidan nan."
"Ki yi shiru Jannah, ki daina ɗaga murya ga mahaifiyarki, kin san ita ɗin wace ce."
"Ba na buƙatar sani burina ta bar gidan nan kawai, kai kake da iko da gidanka don Allah ka kore ta."
"Babu inda za ta je zama za ta yi gidan nan har sai ranar da ta yi ninyar barin gidan." Ta ba ta amsa tana zare mata ido.
Sai kuma ta kalli Mujee, da take tsananin mamakin kalaman Jannah gareta, domin ta gane sam ba ta da tarbiya idanu ta zaro daidai lokacin da ta nufi tibin bango za ta kai masa duka wanda fahimtar hakan Ummu ta riƙe ta.
"Wallahi sai ta bar gidan nan ko ba zan ƙara zuwa ba. Ki ɗauki duk lokacinki ki kula da rayuwar wasu, amma ba ki isa ki shigo da kowa a cikin rayuwarmu ba, wanda yin hakan zai kawo mummunar saɓawa a tskaninmu."
"Aiko ba ki isa ba matuƙar ni na haife ki ko kin ɗauka ba ta da galihu ce? Ita ɗin 'yar babban ɗan kasuwa ce, kuma mace mai aji da ilmi tare muka yi degree muka fara master wanda ta yi aure suka suka koma garin Abuja daga baya na neme ta na rasa har da shafinta na yanar gizo sai yanzu na ganta cikin mawuyacin halin da ke kanki ba ki wuce shiga cikinsa ba.
"Let her be whatever but, I don't care about her identity, cus I hate her ba za ta zauna a gidan nan ba." Ta ce tare da zare mata idanu.
Kuka mom ta fashe da shi tare da faɗawa jikin Mujee, daidai lokacin Jannah ta ruga da gudu ta shige cikin ɗakinta tana kuka.
"Kowa akwai kuskuren da yake yi a rayuwarsa amma na wa ya wuce mizanin hankali. Na raini 'yata cikin rashin tarbiya sam ba ta ganin darajata, tozarta ni take da gaya mini magana son ranta."Sosai take kuka har da sheshsheƙa.
"Kiyi haƙuri Halee, ba mu da ikon canza rayuwarmu kamar yadda bamu da ikon koma baya gareta, tabbas kin yi kuskure domin 'ya'yanmu sune sanyin idaniyarmu, da kalamansu da biyayyarsu yake sawa muji mu a duniya sarakai amma kuma kin tafka kuskuren saka mata tsoronki a ranta. Zan bar gidan nan na koma inda nake rayuwa cikin bola, saboda 'yarki ba ta sona sam ba na son na kawo muku rashin zaman lafiya."
"Sam hakan ba zai taɓa faruwa sai dai matuƙar ba na numfashi, ba ta da ikon da za ta ɓani zaɓi a rayuwata ni ce mahaifiyarta dole ta bi nawa zaɓin."
"Na cuci kaina na aminta da Kham ya cuci rayuwata ya bar mini tabo wanda ba zai taɓa goguwa a gare ni ba. Mai na yi masa ya zaɓi ya saka dafi wanda gubarsa ya fi na macici a gare ni? Na rantse da zan gan shi da hannuna zan kashe shi na miƙa kaina ga hukuma domin ni kaina ba zan yafe wa kaina na aminta da na yi da shi ba har na shigo da shi cikin rayuwata."Ta ƙarashe maganar tana kuka sosai.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 27-28*
*BOJUWA HERBAL'S*
*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅
*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*
*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"Ki yi haƙuri ki ba ni labarin abin da ya faru dake bayan rabuwarmu.
"Ba yan aurenmu da Kham, mun yi amarci cikin so da ƙauna, a lokacin da muka kammala masters muna zaune ni da shi babu aiki, ke kuma kun tafi waje za ki yi phd ya zo mini da murna ya samu aiki a Ilori kuma aiki mai girma.
Na yi murna sosai saboda kin san ko da muka yi aure mahaifina yake kula da mu.
Ba mu ƙara yin sati ba a Kano muka tattara muka tafi Ilori inda ya fara aiki cikin nasara.
Lokaci guda ya yi gida ya sai mota arziki ya yawaita sosai muna zaman mu cikin ƙoshin lafiya.
Babu yadda ban yi da shi ba akan ya barni na haifa ko yaro ɗaya ne, amma ya ƙin akan bai shirya haihuwa ba. Kin dai san yadda ya tsani haihuwa da irin yadda yake zagin matan ajinmu da ya gani da ciki?"
Ta ƙarashe maganar tana kallon mom wanda ta ɗaga mata kai cikin sanyi sai ta ɗora da ce wa,
"Ƙwasam ranar wata laraba ba ina zaune Kham ya shigo gida, cikin tashin hankali domin kuka yake yi, inda ya sanar da ni 'yan kidnappers sun kama iyayena.
Na shiga cikin tsananin tashin hankali wanda har sai da na yi kwana biyu ba tare da na san inda kai na yake ba.
Bayan na farfaɗo ake sanar dani sun kira har sun buƙaci kuɗin da suke son a ba su na ranson.
Na shiga tsananin ɗimuwa jin maƙudan da suka yi demanding duk da cewa mahaifina yana da kuɗi, amma kuɗin da suka buƙata ya wuce hakan.
Haka muka tattara komai muka siyar da komai aka kai musu kuɗin. A ranar da suka yi za a ɗauke su cikin tashin hankali, muka isa gurin da tsoron guda biyu, wanda sai gawan iyayena aka ɗauko mini har da ƙanwata sun kashe su."
Ka sa ci gaba ta yi da maganar tana kuka sosai, domin numfashinta har ɗaukewa ya ke ƙoƙarin yi, wanda sai da mom ta kamata cikin tsananin tausayawa.
"Ba za ki iya ƙarasawa ba ki yi shiru ki bar labarin zuwa wani lokaci." Ta ce mata cikin kuka.
Girgiza mata kai ta yi ta ci gaba da cewa,
"Na yi kuka na yi kuka har na ba uku lada. Na ji duniyar da nake ciki ba na muradinta. Rayuwa ta yi mini ƙunci babu iyaye kuma na rasa duka dukiyar da suka mallaka.
Na daɗe ban samu na dawo daidai ba don sai da Kham ya haɗa mini da rubutu na dangana na fara walwala.
A hankali kuma sai ya fara canza mini da na yi magana sai ihu da zagi. Idan na tambaye shi kuɗi sai ya taso mini tamkar zai cinye ni watarana har da mari. A wannan lokacin na yi tunanin ko zaman da nake yi bana neman na kaina ya sanyan hakan, wanda na kakkaɓe takadduna na fara neman aiki.
Cikin ikon Allah na samu aiki a wata ma'aikata kuma da kuɗi mai tsoka. Na dawo gida cikin murna na sanar masa a tunanina zai yi farincin, amma sai ya shafa ma idanunsa toka ya ƙi nuna farincikinsa ya ƙi amincewa, wanda ta kai mu muka yi faɗa sosai har sai da ya yi mini duka ya fasa mini jikina.
Na kafe akan bakana cewar dole sai na yi aiki amma sai ya ce mini dole na zaɓi ɗaya ko aure ko aiki, wanda take na zaɓi aikin domin a bana buƙatar sake zama da shi ganin yadda lokaci guda ya rikiɗe ya zama kura da fatar akuya.
Take ya rubuta mini saki babu ko tausaya, sannan ya sanar mini kan cewar shi ya tura aka yi garkuwa da iyayena, don ya kwashe dukiyar mahaifina. Na shiga cikin tsananin tashin hankalin da ban san lokacin da na yi kukan kura na fara kai masa duka, da duk abin da na gani ina zaginsa da ja masa bala'i da alkaba'i iri-iri.
Duka ya hau ni da shi har sai da ya fasa mini jikina, ya kuma kwashe komai nawa har da takaddun makaranta, bai barni na ɗauko komai nawa ba ya gudu ya canza gida, wanda na neme shi na rasa.
Abin duniya suka yi mini yawa ga shi ba ni da ko sisi ga yunwa ga ciwo. Da taimakon wata maƙociyata na kai ƙararsa ga hukuma, aka ba za nemansa amma ba bu shi, wanda kan dole na haƙura na dawo Kaduna ina zama a gidan Ƙanin mahaifina.
Sai zaman namu ya ƙi daɗi da duka mutanen gidan domin da kansa, kawuna yake ƙorafi a lokacin da mahaifina yake raye bai taimaka masa ba, don haka na nemi guri kar na ɗora masa wahala.
Ina zaune a gidan ba tare da na yi zuciya na bar gidan ba, domin ban san inda za ni ba, saboda mahaifiyata bafulana ne kuma an tashi garinsu, ba ta da wani na kusa da zan je garesa.
Wani irin manyan ƙuraje suka fara fito mini a ƙasana, suna ruwa su fashe su rinƙa fitar da wani irin ruwa mai ƙarni da wani ga azabar wari.
Ganin haka matar kawuna ta sa ya kore ni cewarta ba zan shafa musu lalura ba, tare da yi mini ƙazafin cewar a gurin biyan maza na ɗauko cutar, amma sai na ƙi tafiya domin babu inda za ni.
Tsana da ƙyara da tsangwama na fuskanta saboda ko kofin da na sha ruwa ba sa ƙara ɗauka.
A hankali ciwon yafi ƙarfina har ta kai ga na fara wari da mutane suna guduna.
Na ji na tsani kaina domin hatta iskan da nake shaƙa a duniyar ba na jin daɗinta. Sai kawai na yanke shawarar mutuwa kawai na sadu da iyayena, amma da mutum baya mutuwa sai lokacinta ya yi, kan dole na haƙura da jiran mutuwa na ci gaba da rayuwa ina bara ina cin abinci, don ba zan iya kashe kaina ba saboda na san hukuncin wanda ya kashe kansa.
Watarana ina cikin tafiya kawai na tsinci jaridar mai ɗauke da hotonki da sunan ƙungiyarki. Take na gane ki duk da cewar kin canza ba sosai amma ba zai hana na gane ki ba.
Na yi murna sosai domin ban ɗauka ƙungiyar ta ɗaukaka kuma tana aiki ba, wanda cikin farinciki na yi bara na haɗa kuɗina na taho Abuja, amma kwasam aka sanar mini da cewar ba kya Ƙasar wasu ne suke tafiyar da ƙungiyar.
Na yi baƙincikin ba zan iya ganinki ba. Duk irin yadda mahukutan ƙungiyar suka nuna mini za su iya taimaka mini ko da ba kya nan, sai na ƙi na gwammace na rayu a haka in har zan warke na yi rayuwa ni kaɗai babu wanda na sani.
Ganin halin da na shiga wani namiji ya sanar mini da akwai yiwuwar dawowarki Ƙasar saboda kin tsaya takarar Minister, wanda na yi matuƙar farincikin hakan na saka a raina zan jira dawowarki, ko har zan mutu ba ki dawo ba."Ta ƙarashe maganar cikin matsanancn kuka.
Gabakiɗaya ɗakin suke hawayen tausayinta ba kamar Hajiya Baaba kuka shaɓe-shaɓe har da su majina.
"Kin ga rayuwa Mujee, na tausaya rayuwarki haƙiƙa ya cutar dake. Allah sai ya saka miki Allah ya jiƙan iyayenki. Da ace na san kina cikin wannan halin da na dawo Nigeria ko da mutuwa zan yi a cikinsa, saboda ni ma ba daɗi ya sa na bar Ƙasata ba. Abubuwa da dama suka faru wanda ba na son na tuna domin komai ya wuce." Ta ƙarashe maganar tana kallon dad da ya sunkuyar da kansa jin abin da ta ce.
"Na yi miki alƙawarin nemo Kham, matuƙar ina raye sai na hukunta shi akan laifin da ya yi miki, sannnan ki zauna a gidana har ƙarshen rayuwarki, domin na san zalincin da ya yi miki abu mai wuya ne, ki ƙara aminta da wani ɗa namijin."
"Har abada ni da aure mun yi hannun riga, na gode ai kuwa in har kika kamo shi kika