Showing 75001 words to 78000 words out of 137802 words
Chapter 26 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
ƙofar aka yi aka shigo. Jannah ce sai Ammy da Ummu.
"Sannu Hajiya." Cewar Ammy
Wata uwar harara ta banka mata bata amsa ba sai girgiza kanta take kamar ƙadangaren kutu
Jannah kanta ta yi tana faɗin,"Na gaya miki ya tsane ni baya son ga shi yanzu har ke zai haɗa ya kashe, kuma Allah sai kotu ta ƙwato mana 'yancinmu." Ta ƙarasa maganar lokacin da ta isa gurinta.
"Matsa ki ban guri shashashar banza. Dama na gaya miki watarana bakinki sai ya yi ajalinki, saboda ba ki da kunya da ta ido. Jannatuu ban san inda kika gado halinki ba sai dai ƙila gurin ubanki don ni dai 'yata mai tarbiya ce. Shi yasa ake cewa in za a yi aure ki zaɓo abokan zama na kirki wanda kuka san asalinsu amma da yake 'yayana ba sa cin magana sukai kunnen uwar shegu da maganata. Ga shi yanzu har ni ya shafa dama iya kansu ya tsaya da sauki."
Turo baki ta yi tare da galla mata harara jin abin da ta ce har ta buɗe baki za ta yi magana sai kuma ta fasa don jikinta mugun ciwo yake mata.
"Ba dai ni kuka sa na yi kuka da girmana ba? Za ku sani, sai kun gane duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha. Yuawa kai Muhammadu, gara da ka shigo maza kira mini Halimatuu." Ta bashi umurni fuskarta babu wasa tare da miƙa masa hannu.
"Hajiya, na roƙe ki don Allah kar a kirata zan iya maganin matsalar duk ikona ne su."
"Za ka kirata ko ban isa ba na sa likita ya kira mini ita." Ta katse shi tana faɗin hakan wanda da sauri ya ciro wayarsa tare da miƙa mata yana faɗin,
"Allah ya sanyaya zuciyarki da dai anbi abin hankali."
"Ba amin ba in dai akan wannan ne ni ma sai na sanya sun ji azaban da na ji."
Bugu uku ta ɗauki wayar." Hello, Ya Muhammad sun amince za su saya a haka ne?" Ta ce bayan ta ɗauki wayar domin sun gama waya kenan babu daɗewa akan wani business.
"Ban sani ba. Na ce ban sani ba shashshar banza da wofi. Ke ba ki da aikin yi sai harkar kasuwanci da neɓan kuɗi da fakewa da kina taimako, amma 'yarki ɗaya kin kasa ba ta tarbiya kin kawota ta zame mini ƙadangaren bakin tulu."
Sai ta sauke ajiyar zuciya tana huci don ji take kamar ta jawota cikin wayar ta rufeta da duka.
"Na shiga uku! Waya taɓa mini ke, mai Jannah ta ƙara yi?" Ta tambayeta tana kallon dad da yake lissafi a laptop ɗinsa jina bin da take faɗi ya sa tsaya da aikin da yake yi.
"Ba ma wannan ba don ba shi ta sa na kira ki ba. Halimatu ni na haife ki ko da cikina kuma na yi ɗawainiya dake har kika girma ko?"
Tambayar ta yi mata banbarakwai wai namiji fa suna Hajara amma sai ta daure ta ce,
"Eh ke kika haife mini kuma ina alfahari da hakan. Lafiya Hajiya Baaba, mai ya faru, me ta aikata? Don Allah ki fahimtar da ni duk kin sanya ni cikin ruɗu kaina ya kulle sosai."
"Kuma na isa dake har da mijinki ko?" Sai ta ƙara ba ta mamaki ba ta amsa mata ba ta tsaya tana kallo dad da ya ji tambayar don ya ji mai zaice. Ganin ya ɗaga mata kansa ta bata amsa.
"Eh, yana jinki kuma ya tabbatar mini da hakan don Allah ki sanar mana da abin da ta aikata."
"Alhamdulillahi! Na gode. Dama auren jannah nake nema wa Ajmal, kune dole na nemi izininku amma Adamuu na isa da shi tun da na haifi ubansa."
"Gabakiɗaya ɗakin suka haɗa baki gurin faɗin, "Meee!" Da ƙarfin gaske.
Sai mom ta ci gaba da tambayarta tana cewa,
"Lafiya mai ya faru da za ki yamke hukuncin nan? Na ga ko shekara bai rufa da aure ba, matar tasa ko mutuwa ta yi? Mai ta aikata miki da za ki yanke wannan ɗanyar shawara na yi mata aure da ƙuriciya."
"Ai ina tunanin kunji tun da ku ɗin ba kurame bane, sai ku fara shiri za a yi tare da na Nahlin." Ta kashe wayar ta ije akan gadon ta bar mom cikin tsananin ruɗani.
Ganin yadda suka yi cirko-cirko kamar ruwa ya cinye su, doctor Irfan ya kwashi kayan aikinsa ya fice daga ɗakin yana mamakin rigimarta, domin a ganinsa an wuce wannnan zamanin.
Ajmal ya yi shiru tamkar ruwa ya cinye. Ba tunani yake yi ba domin ya rasa mai zai tunani don jin abin da ta furta yake kamar wasa.
"Aure kuma wai ni Jannah?" Kai in ba da ni take yi ba wataƙila ban ji abin da ta ce da kyau bane." Ya tambayi kansa cikin shakku tare da bawa kanshi amsa.
Idanunsa ya ɗaga yana kallonta da ta yi masa ƙuri sai harararsa take yi. Ya ƙara nazarin fuskarta don ya tambatarwa kansa wasa take, amma sai ya ga sam babu alamar wasa a fuskarta duba ga yadda ta ci magani sai huci take tamkar mesa.
Ƙafafuwarsa ya ji suna ƙoƙarin bijirewa ɗawainiyarsu. Idanunsa suka canza daga fari tas zuwa ja tamkar an zuba musu jar bula.
"Amma dai wasa kike ko Hajiya Baaba ko kunnuwana ba su ji mini abin da kika faɗa bane? Kai zai fi dai wasa kike domin ba ni da matsalar ji kuma daidai na ji."
"Wasa nake yi in dai ina wasa da ubanka, don na wuce na yi wasa da kai sai dai ubanka ga yi nan." Ta ce tare da tamke fuska tana harararshi.
"Ina Allah ya kyauta over my dead body. Ni na auri wan can abar? Ji beta ba bu tarbiya tana ji da siranta kamar taɓarya. In ma dai ba wasa dani kike ba to yau kin fara don babu yadda za a yi ni Sheshk na auri 'yar bariki kamar ta."
Taso wa ta yi cikin zafi tamkar za ta mare shi sai dai kuma rashin ƙarfin jikinta da ciwonta ya sa ta koma ta zauna tana dafe kai.
"Wash Allah! Wallahi Allah sai ya saka mini. Haka kawai ina zaman zamana ku fasa mini goshi, saboda mugunta ai za ku gani a ƙwaryarku."
Sai Kuma ta ƙara gallah masa harara tana faɗin,
"Idan mazan duniya take raba jikinta wallahi sai ka aureta, in dai ina raye."
"No impossible! Ke ma Hajiya kin san babu yadda za a yi ki haɗa auren Jannah da Ya Ajmal, they're not compatible at all, kuma yaushe ya yi aure.."
"A gaban iyayenki Hafsatuu, kike kallon tsabar idanuna kina gaya mini ban isa ba, ashe har wuyarki ya isa yanka haka? Ina miki kallon mutuniyar kirki, ashe kura ce da fatar akuya.." Sai ta fashe da kukan da babu hawaye har tana jan majina.
Ta juya ta kalli Ajmal tana zare idanu."Kai har kana da bakin cewa ba za ka aure ta ba, saboda ba ta da ƙiba? Ashe babu daɗi aka mannawa ɗana kullum yana wahala a kanta, amma babu amfani. Mene ne banbancin ta da uwarka da duk sati sai ana yanka rago amma kullum kamar ana ibanta ana miya? Kai har kana da bakin yi wa wani gori."
"Ka ga ni ko! Ga shi nan saboda baƙin zuciyarka sai da ka je ka rafke ta a ka gashi nan ka taɓa mata ƙwaƙwalwa ta taɓu. Ka ja mana bala'i da masifa, don tana da hankali ya muka ƙare ballantana ta taɓu. Bari na kira likita ga duba mana ƙwaƙwalwarta tun kafin ta fara duka." Ta faɗa tare da nufar ƙofar ita kuma har ga Allah da gaske take yi, saboda in ba hauka ta yi ba babu yadda za a yi ta furta haka.
"Ke mara kunya dawo. Ba haukacewa na yi ba sama nake cizo. Ko asibitin mahaukata ne ni. Kar ki kira likita mota za ki ɗauko ku kaini dawanau. Shashashar banza mara kunya. Ki bari nan da wata uku in kin tare a gidansa sai ki gane hauka tuburan nake yi."
Cak ta tsaya jim ba ta juyo ba sai kuma ta jiyo tana wani irin murmushi.
"To indai da hankalinki wasa kike yi don babu yadda za ayi kamata ni babbar yarinya 'yar uwa ba da mama na auri wannan bagidajen. To wai duka shekaruna nawa da za ki yi mini maganar aure, ki bari karki ɓata ni." Ta ce cikin ɓacin rai.
"Bariki zan kai ki mara kunya. Lokacin da kika kira saurayinki kina kashe murya da salo na jan hankalinsa kin san ni na koya miki. Duk kalle-kallen da kike yi na fitsara kin san ni nake turo miki. Ai ni nafi na yi wasa dake sai dai da mai dattin hula." Ta ja nu fashi tare da ɗora
TO MASU KARATU KUNA TUNANIN ANYA ABIN DA HAJIYA BAABA TA ƘUDIR DON ƊAUKAR FANSA ZAI YU? DUBA GA BAMBANCIN RA'AYI DA TSARIN RAYUWARSU. KU DAI CI GABA DA BIBIYAN LINTATTFIN "KURA DA FATAR AKUYA" KAR KU BARI A BAKU LABARI.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
KURA DA FATAR AKUYA
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)
*SADAUKARWA GA:-*
*BADAMASI (AUTA)*
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)
Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.
*PAGE 21-22*
*BOJUWA HERBAL'S*
*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅
*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*
*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
"To tsaya kiji da kunnin basira auren ku babu fashi sai dai ina mutu."
"Abu mai sauki saina saka miki gubar matuƙar kika ce za ki aura mini shi."
"Wayyo na shiga uku na mutu ba zan ƙara zama dake ba, kuma dole Halimatuu ta dawo cikin satinnan, ta ɗauke masifa da bala'in da ta kawo mini, don na tabbata za ki iya kashe ni saboda ba imani kike da shi, wanda baya sallah sai ya ga dama ina imani a ransa. Daga can a tattaraki akai ki gidansa kin ga sai ku kashe kanku in kun so." Bilhaƙƙi take kukan tana kallon mutanen ɗaki.
"Ai kuka yanzu kika fara matuƙar ba ki janye ƙudurinki ba, kuma ko baki faɗa ba dole na koma gurin iyayena."
"Ba ki da wannan hujjar na tursasa ni na aure ki don ba ki da iko da mu." Cewar Ajmal yana mata mugun kallo.
"Amma na isa da iyayenku, da suka haife ku ? Ni da ku mu zuba shege ka fasa."
Har ya buɗe baki zai yi magana Aby ya daka masa tsawa.
"Abin kunyar da za ku yi mana kenan? Kamar ƙananan yara haba Hajiya bai kamata ki biye musu ba saboda yara ne su."
"Allah Sarki! Da ma laifina za ka gani, tun da ni ba ni da iyayen da za su kare ni duk sun mutu." Sai kuma ta ƙara saka kuka." Allah ya jikan ku iyayena na san da kuna raye da kun kare ni. Allah ya jiƙan ku da rahma domin yau ga ranarku."
"Don Allah mu bar maganar nan mu tafi gida zai fi a sasanta kammu a can."
"Sasancin kenan ayi auren tun da na faɗa kai ma ka san babu uban da ya isa ya hana sai dai in Allah bai kaddara ba."
Lamarinta sai ya ƙara bawa kowa mammaki. Ammy ta ka sa cewa komai sai jinjina lamarin take yi domin ta san tun da ta furta sai wani ikon Allah, kuma in har ta sanya aka yi auren ba ta yi ma su duka ukun adalci ba. Da wani idon za ta kalli iyayen Mushiirat akan ɗan su zai yi wa 'yarsu kishiya auren da ko shekara ba a rufa ba. Sannan ita kanta Jannah ba da take karatu bai kamata ayi mata aure da wuri ba, uwa uba da ba ta da ra'ayin auren miji irin sa. Ga Amal da ya tsane ta da halayenta sannan ta ya ya zai fuskanci matarsa da maganar.
"Kai ina hakan ba zai taɓa yiwuwa ba!" Ta furta cikin tashin hankali tana girgiza kanta.
"To amma wa zai hana?" Ta tambayi kanta cikin tsananin ruɗani wanda in dai babu lallain akwai sauran rina a kaba.
Hajiya Baaba ta miƙe ta bangaje Ammy dake tsaye a gefenta wanda ya sa ta yi saurin matsawa domin ta yi hakanne don ta tofa albarkacin bakinta ta ƙara baƙin jini a gurin ta. A ranta ta yi alƙawarin ko tari ba za ta yi ba in suna maganar, ita dai na ta kallo da fatan alkhairi. Da sauri ta matsa gefen tana kallonta.
Tun da Abby ya tsawatar babu wanda ya ƙara ko tari har suka shiga mota, sai dai Hajiya Baaba da take dafe bandejin da aka lulluɓe mata ciwon da shi, tana musu Allah ya isa don rabonta da ta ji ciwo har ta manta.
Ko da suka isa gida Aby ya hana kowa tafiya aka zauna a falon Hajiya Baaba don yin taron gaggawa.