Showing 135001 words to 137802 words out of 137802 words
Chapter 46 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt
a ransa a fili kuwa ɗaukar wayarsa ya yi suka yi musabuha yana faɗin,
"Bari na wuce matar kirki yau za ta dawo."
"A masha Allah na ji ance ta samu ƙarin girma Allah ya sanya alhairi."
"Ai da yake kwanyarta na ja don ni kaina ban yi tunanin za ta ci jarabawar ba." Ya ce cikin farinciki da murmushi ɗauke a fuskarsa.
Haka suka fito suna tafe tana kuka wanda ko kallon inda take bai yi ba, wanda ya haɗa harda gudu ya shige motarsa ya tayar. Ganin haka taƙarasa da sauri ta shiga.
Suna tafe tana kuka da jan majina yayin da take jin inda aka yi mara allura yana tsikarinta, wanda in har ba ta sa ƙanƙara ba sam ba za ta ji sauƙi ba.
Da takaicin sawa da ya yi aka yi mata allura da zafin allurar suka ishe ta sai ta sanya ƙara ta ci gaba da kuka, wanda ya sanya cikin tsananin ɓacin rai ya gangara titi ya yi parking ɗin motar.
"Ke fito daga cikin motar nan domin ba za ki kashe ni da takaici ba " Ya furta cikin ɓacin rai yana watsa mata mugun kallo.
"Ba zan fito ba kuma na rantse ka yi ka maida ni gida in ba haka ba sai na ta kwarara maka ihu ince sato ni."
"Ok, haka kika ce? To Allah ya ba ki sa a ki fara tun kafin na fasa miki bakin ihun."
Ga mamakinsa sai ya ga ta sa fuskarta a saman kujerarsa tana goge ruwan hawayen da ya ƙi tsawa, sai kuma ta fyato majina ta goge, wanda ya sa ya ji tamkar zai yi amai yana kallonta cikin ƙyanƙyani.
"Ƙazamiyar banza fito mini daga mota na rantse sai dai ki nemi abin hawa." Ya ce tare da finciko ta ya direta a waje ya shige motarsa.
Kuka sosai ta ƙara saki har da su birgima a ƙasa wanda ya ji kamar ya shaƙeta ya mutu motarsa ya shiga ya tada tare da fara tafiya, sai kuna ya tsaya ya leƙo yna faɗin,
"Ba na gaya miki ki san yadda za ki yi ki kar ki aure ni ba, amma kin kasa haka to bari kiji na gaya miki, na rantse sai kin gwammace zaman gidan kurkuku fiye da zama a cikin gidana, domin ina zaman lafiya da matata ba ki isa ki rage mana jin daɗi ba." Ya ce yana watsa mata mugun kallo.
"Dube ki wata kucaka, ƙazamiya wawiya da ke. Gabakiɗaya ke ko ta ina naƙasa ce a jikinki. Mace babu addini babu tarbiya sannan jikinta kamar an ɗaura wa taɓarya zani gabakiɗaya babu shape kamar sanda haka kike. Tir mai zan yi dake bayan ga mace wacce ta masa sunanta mace take da komai na nake so."
Sai ya tofar da miyau yana faɗin,
"Ina miki albishirin aurena wanda za ki gwammace gara a kaiki ramin macizai ki rinƙa kwana da su, domin sai na mai da rayuwarki wulaƙantacciya. Dukan safe daban na yamma daban. Kuma sai na sanya rayuwarki ta gimshe ki. Domin zan zamo macijin da zan rinƙa sarar naman jikin ki a kullum, don haka ki aje rashin kunyarki da fitsararki ba yanzu za ki yi mini su ba, domin wataƙila su yi miki amfani a lokacin da babu mai ceton ki a gidana. Marin da kika sa aka yi mini kullum shine zai zama sallama da daddare a tsakaninmu." Ya ƙarashe maganar yana kallonta ganin yadda take mishi wulaƙantaccem kallo kamar ta ga kashi, kuma ko kaɗan kalamansa ba ta nuna sun firgita ta ko sun nuna ta ɗan tsorata ba.
"Wayyo Allahna! Ka ce zamu mai da gidanka gidan dabbe da tashin hankali da rikici. Sanin kanka ni ni ɗin ba kanwar lasa ba ce domin hatta wacce ta haɗa auren ba ta bani tsoro ballantana kai. Ka dai na tunanin wannan ɗinbegegen jikin na ka zai sanya na ji tsoronka. Ka ji na rantse a rayuwarka sai na zame muku ƙadangaren bakin tulu! Ruwa sai kun gagara kurɓa a gidan nan. A yadda kake kallona kamar wata fensir "KURA CE NI DA FATAR AKUYA." Domin ina cire fatar akuya rikiɗa harda na wacce ta haɗa auren. Yaga-yaga da namarku na cinye tas kuma na zauna lafiya. Matar da kake kira ta so ko? Watarana sai ta zame maka matar ƙi, domin sai na shafa mata baƙin tabon da kashin kajin da za ka ji ka tsaneta. Bayan na lalata rayuwar zaman auren ku sai na je na auri masoyina ɗan gata mai kyau a tashen kuruciya ba irin ka ba. Wannan abin da zan yi maka sakayya ce ma mayar da ni ƙaramar bazawara da ka yi."
"Ok haka kika ce mu zuba shege ka fasa." Ya ce yana mamakin tsaurin idanunta da fitsararta ko da yake bai kamata ya yi mamaki ba domin waɗanda suka kawo ta duniya ba ta shakkarsu. Don haka ya figi motarsa ya tafi ya barta a gurin.
Jannah kuwa ba ta matsa ba ta ci gaba da ihu tana kiran sunan dad, domin so take ta kashe shi da baƙinciki gane yadda ya ke ƙuluwa, in ta yi mishi abu kasancewarsa ba ya iya ɓoye baƙinciki.
A ranta ta ɗauki aniyar tun da yake kiranta da yarinya, wacce ba ta da abin da zai kalla ƙwaila ita kuma sai ta kashe shi da baƙincikin, abin yarintar da za ta rinƙa masa don sai ta mai da kanta tamkar 'yar wata bakwai.
Har ya yi nisa sai kuma ta ga ya fara dawowa da baya har ya ƙaraso gurin ta, sakamakon kirar Aby da ya yi masa kan ya yi sauri ya ga sun daɗe.
"Ki zo ki shiga motar nan tun kafin na fito na canza miki kamanni, kuma wallahi ba ki isa ki shi ga baya ba, domin na fi ƙarfin zama direbanki."
"Ba zan shiga ba kuma na rantse yau Allah kawai zai ce ce ka kan sharrin da zan yi maka mugu kawai." Ta ce tana ƙoƙarin tarar adaidaita ta hanyar tsayar da shi.
Da takaici ya kwashe shi ganin ta tsayar tana ƙoƙarin shiga cikwikwiyeta ya yi ya tura a gaban motar ya kulle tare da zagayawa ta gefen direba ya shiga, ba tare da ya damu da ihun da take yi ba tana neman taimako ɓarawo ne.
"Kai malam, lafiy kar.." Direban adaidaitar ya faɗi daidai lokacin da ya buga ƙofar da ƙarfi ya ja motar.
Wani irin burki ya ja wanda ya yi ƙara ƙiiiiiy.
"Ke na rantse ki kiyaye ni da wanan ihun don za ki iya sawa na zubar damu sam bana son iihu wawiya kawai."
"Ba zan dena ba har sai ka saukar da ni kuma in ka zubar damu sai me ai wallahi da aurenka gara na mutu na je lahira, kuma Allah sai ya saka mini na raba ni da masoyina da ka yi."
Ajmal da zuciya ta ciyo shi domin tun yana yaro ya tsani kuka da ihu yanzu zai rikice ya fita hankalinsa.
"Tun da haka kika ce kuma ƙin ƙi yin shiru bari na watsar damu kin ga duk mu mutu mu huta." Ya ce don ta yi shiru ya fara tagal-tagal da motar, amma sai ya ga ko gezau ta kalle shi ta yi dariyar takaici tace,
"Sai me don na mutu, wasiya kawai zan rubutawa masoyina na neman yafiya, amma bayan wannan ba ni buƙatar komai sai mutuwa."
"Au haka kika ce yau ni kuma zan nuna miki ƙaryar fitsara." Ya ce tare da sakin sitiyarin sai motar ta yi kamar za ta kife sai kuma ya riƙe.
"Na ka wasa ne bari na nuna maka na fi ka son mutuwa." Ta ce tare da saka hannunta iya ƙarfinta ta riƙe shi ta hana shi tuƙin wanda ya sanya iya ƙarfinsa ganin aika aikar da take yi, amma ina ta yi nisa ba ta jin kira don har sai da ya buga kanta da murfin ƙofar ta ƙi saki wanda kafin ya yi wani ƙoƙarin tsayawa ko wanin abun motar ta yi taga-taga da su ta kife, wanda Jannah da fari ko gezau kuka take tana tuna Huzaifah sai ta ke jin ta rasa komai na jin daɗin duniya domin shine ya yi alƙawarin kulawa da rayuwarta ya ba ta duk wani farincikin da iyayenta suka gaza zai zama tamkar mom ya kuma ninka soyayyar da dad yake mata. Amma sai dai kash! Wannan baƙin auren da Hajiya Baaba, ta maƙala mata ya zama cikas da zamowa shamaki a tsakaninsu. Yua ga Huzaifah yana can kwance mutu kwakwi rai kwakai, ba ta da abin da za ta yi ta ceci rayuwarsa, wanda ya sanya ta ƙudiri gara ta mutu da zama da baƙin kumurcin da ta tsana fiye da komai a rayuwarta, domin shine mutum da ya fara mata dukan da iyayenta ba su taɓa mata ba, ya takurawa rayuwarta tare da daƙile duk wani farinkici da na rayuwarta don haka ta gwammace gara mutuwarta.
Tunaninta ya katse daidai lokacin da ta ga mutuwa a zahiri raɗaɗin zabarta da tashin hankali da firgici har ma da alhinin da ke cikinta ya sanya ta tsananin razana wanda ya sa ta ƙwarma uban ihu numfashinta ɗauke.
Mom ta shiga cikin tsananin tashin hankali! Ji ta yi numfashi na neman gagararta. Ta rintse idanunta tana son gano wanda ya shirya mata wannan tungun, amma mizanin hankalinta ya gaza aiki. Sai ta fara wilƙita ido cikin rashin dubara tana ji tamkar ta yi hauka.
"Na shiga uku Allah ka kawo mini ɗauki ka fitar da ni daga cikin wannan sharrin da ake so a ƙulla mini." Ta furta tana share zufan jikinta daidai lokacin da wayarta ta ɗauki ruri, wanda ya ƙara dugunzuma sauran natsuwar da ke jikinta.
Ƙarar shigowar wayar ya sa ta yi ma ta maza ta ɗauka, yayin da zuciyarta ta buga da ƙarfi har sai da ta dafa motar, domin a tunaninta anonymous ne ya kira ta gabin sabuwar numba, wanda kamar ba za ta ɗauka ba saboda zuciyarta ya gaya mata ba alkhairi za ta ji ba, amma sai ta ga numbar Jannah, wanda ya sa kan dole ta ɗauka.
"Hello muna magana da makusantar me wannan wayar ne?"
"Eh ina daga cikin makusantarta domin ni ɗin mahaifiyarta c."
Kafin ta ƙarashe maganar ya ci gaba da cewa,"Ok, muna buƙatar kizo da gaggawa domin sun samu accident ita da wani namiji, a daidai 'yan goro yanzu haka an saka su a ambulance za a kai su asibitin koyarwa na shik..."
"Innalilahi wa inna ilaihir raju'un." Cewar mom tare da ɗora hannu a ka, wanda ya sanya Mujee, ƙarasowa gurin ta da sauri ta kamata tana faɗin,
"Lafiya Halee, mai ya faru."
"Jannah sun yi hatsari da Ajmal a hanyarsu ta dawowa daga asibiti suna asibitin shika." Sai ta rushe da kuka tare da durƙushewa a ƙasa ta ci gaba daɗin,
"Wane irin musiba yake shirin faruwa da ni? Ba zan iya rayuwa babu ke ba Jannah, domin saboda ke nake samun ƙarfin zama a cikin duniyar da sam bana jin daɗinta.
"Subuhanallahi! Yanzu ya za mu yi don dole mu kama hanyar Zariya, kuma waɗannan jarirai fa."
"Bari na kira 'yan sanda na yi musu reporting sai na barku a..." Sai ta kasa ƙarasa maganar tana kallon motar 'yan sandar da suka tinkarosu suna jiniya.
"Kamar 'yan sanda nake gani, wucewa za su yi ko gaya musu akai akwai jariran a cikin motarmu." Mujee ta furta cikin tsananin firgici tana ɓoye wa a bayan mom da ta sandare ta kasa magana saboda mamaki wanda take ta gana makirci aka haɗa mata.
Ba tare da ta ce komai ba ta zuba musu ido har suka ƙaraso suka fito daga cikin motar da bindigu.
"Kece Hajiya Halima ko? An sanar mana da kina fakewa da taimako kina sace 'ya'yan mutane don kiyi tsafi da su kici zaɓe."
Ido Mujee ta zaro jin abin da ya faɗi.
"No, ba halinta bane domin zuciyarta tsarkakarka ce, saboda Allah take yi ba don siyasa ba." Ta ce tana zare ido bayan ta rufe boot ɗin motar.
"Ok, tun da kin ce haka bari mu duba boot ɗin in bmu gani ba sai mu yarda."
Kare boot ɗin ta yi tana faɗin,"I said there is nothing in ku.."
"Matsa Mujee, let them see akwai, amma wallahi ba satarsu na yi ba, kuma ba ni da masaniyar yadda akai suka shiga ciki. Makirci ne kawai na maƙiya." Ta ce cikin muryar kuka tare da ƙarasawa gurin motar ta buɗe.
"Rufe mini baki! Dama irinku haka kuke 'yan siyasa ku rinƙa fakewa da taimakon al'umma bayan da jininsu kuke kuɗi." Ya ce tare da ciro ankwa.
"You are under arest!" Ya faɗa yana nuna mata ankwa wanda ya sa ta yi mutuwa tsaye, sai kuma ta saka kuka tana faɗin,
"Don Allah, ku sake ni 'yata ɗaya kwance na mallaka tana asibiti ta yi hatsari kar ta mutu ban gan ta ba. Akwai rashin fahimta a tsakaninmu in dai banje ba lamarin zai zafafa."
"Shout up kin san daɗin 'ya'ya amma kike yin kuɗi da 'ya'yan mutane don ki yi kuɗi da suna." Ya ce cikin zafi tare da fara tafiya za su sanya ta a mota.
"Wayyo Allah wai da gaske kamata za ku yi? Don Allah ku saketa wallahi bamu da masaniyar yadda aka yi suka shiga cikin motar. Ni sheda ce akan hakan, Halima mutuniyar kirki ce. Siyasarta tsarkakarka ce."
Mujee ta faɗi tana riƙe mom da wata mace ta sanya mata ankwa.
Har sun fara tafiya Mujee na kuka tana roƙonsu amma ba su kula ba.
"Na shiga uku! I dan Jannah na raye ta farka ba ta ganni ba za ta ƙara nisanta kanta da ni. Mujee, don Allah ki tafi Zariya ki je ki ganin mini ita, domin in har ta mutu ni ma mutuwa zan yi." Ta furta cikin matsanancin kuka a ranta tana tunanin wanda ya ƙulla mata wannan makircin yayin da zuciyarta take sanar mata da makusancinta ne wanda ya san duk motsinta yake tare da ita.
"Waye wannan kura da fatar akuyar?" Ta furta cikin tsananin tashin hankali, daidi lokacin da motar ta tashi tana kallon Mujee, da direba da suke kallonta suna kuka cikin tashin hankali.
"Oya maza kuma muje police station ɗin da ku a wancan motar don kuma sai mun bincike ku." Ɗada daga cikin Police ɗin ya furta tare da tasa ƙeyarsu.
Mom na ji na gani tamkar wacce ta yi kisa aka garƙame da ankwa. Wani irin tuƙuƙi ya turniƙeta. Kukan da take yi ta nemi hawayen ta rasa sai ta fara ajiyar zuciya mai ƙarfi wanda yake barazanar tafiya da numfashinta.
"Ni kuma shikenan, ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba?"Ta tambayi kanta cikin tsananin baƙinciki tana jin tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu, yayin da lokaci guda abubuwa da dama waɗanda suka faru suka fara dawo mata a ƙwanyarta tare da mayar mata da abubuwan tamkar lokacin ya faru wanda ya sa ta rinƙe idanunta ta fashe da kukan da ta yi nasarar yin shi tana jin rayuwarta ta zo ƙarshe.
Kash! Masu karatu anan na kawo ƙarshen book one na littafin "KURA DA FATAR AKUYA." Sai mun haɗu a kashi na biyu akan kuɗi naira 500 kacal in kuma aka gama 600 a account number nan 8144072423 Jamila Muhammed Lawal Opay. Masu tura katin waya sai ku turo ta nan:07072971093. Ƴan Nigar kuma za su tura ta nan:7 74007457 Isma'il Nita. Littafin ya fi na farkon haɗuwa domin yana ɗauke da tarin tambayoyin amsarku masu karatu kamar haka:
Shin wane ne wanda ya zamo "Kura da fatar akuya" Yake kai hari ga rayuwar taurarumarmu kuma uwa ba da mama?
Mai dad ya yi wa mom wanda ta kasa mantawa kuma ta gudu ta bar ƙasarta?
Shin Jannah ta yi nasarar kashe su domin hutawa da auren?
In har suna raye wane irin zama za a yi na aure da Jannah da ba ta gama fahimtar kanta ba ballaantana ta gane aure?
Shin Huzaifah zai hakura da soyayarta, ya ya halin da yake ciki?
Ya za ta yi ta samu soyayyar Ajmal da yake da matar da yake ji bayan ita duk sauran matan sun rako ta duniya ne, saboda hankali da biyayya da kissa da kisisina?
Wane hali Mushiirat take ciki na afakawa titi saboda jin aurensa?
Ina kham; mijin Mujee, wace duniyar ya shige ya yi ɓatan damo?
Shin Hajiya Baaba, ko za ta janye ƙudirinta na ɗaukar fansa kan iyayen da 'ya'yan ta haƙura da auren ganin in suna raye?
Duk tarin amsoshinku yana cikin littafin na biyu ku daure ku biya kar ku bari a baku labari. 'Yar'uwa in kika daure kika biya sai ki karanta hankalinki kwance babu damuwar kin karanta ba tare da kin biya ba.Sai mun haɗu a littafin na biyu. Taku Jamila Lawal Zango (Jamsy)
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093