Showing 108001 words to 111000 words out of 137802 words

Chapter 37 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

Cewa Hamisu mai-gadi yana tura shi.






Da sauri ya ƙaraso gurin har yana tuntuɓe wanda saura kaɗan ya faɗi ƙasa.






"Kai Hamisu ƙyale shi ya shigo ɗan'uwana ne." Ya furta daidai lokacin da ya ƙarasa gurin yana kallonsa wani iri.








"Innalillahi! Mudi, ashe da gaske ne kun dawo Nigeriya? Sannu da mantawa da mu."








"Shigo ciki Yaya Bala." Abin da ya ce kenan ya matsa ya basu hanya zuciyarsa cike da baƙincikin zuwarsu.








"Oh ni Jummai! Ka ga wallahi bai yi farincikin zuwanmu ba. Anya Mudi za ka wuce siraɗi kuwa."








"Haba Yaya! Na ce ku shigo kun tsaya kuna zuba kamar kaɗanya. In ke kike sa mutum ya wuce sai ki hana ni, ina zo wucewa." Ya ƙarashe maganar yana ba ta amsa.








"A mai da wuƙar ai ban isa ba, amma ka san duk wanda ba ya zumunci ba ya samun rahamar Ubangiji. Kawai saboda mace ka gudu ka barmu don ka ga babu idanun Inna da Baba."








"Ki ƙyale shi ai baƙin kwaɗayinsa sai ya ja masa wahala, domin na tabbata matar nan, yankan kan mutane take yi. Dubi daga zuwa Ƙasar waje, sun gina gida tamkar aljanna." Bala ya furta yana shafa get ɗin gidan.








"Za ku shigo ne ko na kulle ƙofar, ko sai kun gama tozarta ni kuna gaya mini asalina?" Ya furta cikin ɓacin ganin duk abin da suke faɗi maigadi na jinsu.








"Kai amma aradu wannan mata ta nemi duniya Allah ya ba ta, dubi irin wannan gida. Ni fa tun da uwata ta haife ni ban taɓa ganin bango da tayas ba." Jummai ta ce bayan ta tsaya cikin tsananin mamaki tana ƙarewa gidan kallo, sai kuma ta sa hannu tana shafawa tsantsin na mata daɗi, tana washe bakinta da ko wankin kirki baya samu.








"Ke dallah banza! Na taɓa gani a lokacin da naje neman kuɗi a birnin Legos. To ogana gidansa irin wannan ne haka na yi ta shafa tayas ɗin."








"Kai 'yan birni suna jin daɗinsu. Allah ya kai damo ga harawa, ko bai ci ya yi birgima."








"Yanzu don Allah abin da kuke mini ya dace, haka za mu shiga ku kunyata ni? Maganar gaskiya ku zo na sallame ku, ku koma gida."










"Wallahi ba ka isa ba Mudi! Ka gudu ka barmu ka bi mace tsawon shekaru, kuma yanzu Allah ya sa mun gano ka kace mu koma ƙauye. Ai nan zama nan kwana."










Tsananin baƙincikin abin da ya furta ya ishe ya buɗe baki zai yi magana sai Jummai ta maƙale jakar buhunta ta riga shi da cewa,








"To in ban da ya raina mana hankali, mu shigo irin wannan gidan ya ce mu koma ko shiga, ai ni ko kayana ba zan ɗauko ba, domin yadda maiƙo da zaƙi ya sa ya maƙale a jikin mace haka muma zamu zauna muci arziki."








"Ƙwarai kuwa Jummai, domin ƙauye zan koma na kaso matata da 'yayana."










Zare idanunsa ya yi yana faɗin,"Ku zauna a ina, wai ni wa ya gaya muku inda nake?"








Wani irin ranƙwashi ta kai ma kanta har sai da ya ce ƙas tana dariya ta maƙale a bango tare da ɗaga ƙafa.








"Wallahi abokinka Shafi'u, shi ya gaya mini za ka dawo birni, ni kuma da na ji haka na dame shi da ƙyar ya bani adireshin gidan, kuma ba shi na ciyo muka taho."










Ƙuta ya yi bai ce komai ba ya fara tafiya wanda suka bi bayan shi da gudu suna murna








"In isasshiyar matarka ba za ta yarda ba to ta ɗauke ni 'yar aikin zan yi, amma na rantse ba zan koma ƙauye ba."








"Ni kuma gadi amma babu maganar komawa, ai sai a yi mana dariya."










Be tanka musu ba ya ƙarasa shiga cikin falo cikin jin kunya, sosai domin bai san wani irin tarba za su samu da ga Hajiya Baaba da kuma Mom da Jannah.










"Kai dakata! Dakata!! Ku kuma daga ina? Idan bara kuke yi ai sai ku tsaya daga ƙofa ba, wai ka shigo mana da su ba Jabiruu." Hajiya Baaba ta ce tana kallonsu cikin ƙyanƙyani.








Shiru ya yi yana sosa kanshi sai kuma ya ce," 'Yan'uwana ne suka zo daga ƙauye."








"Gaya mata Mudi, mu ɗin ba mabarata bane muma 'yan gidane."Cewar Bala.








Da sauri Jannah da ta fito daga cikin ɗakinta jin muryar dad ta tsaya tana kallonsu.










Yadda take kallonsu zai bayyana maka mamakin da take yi.










"Dad, waɗannan ne 'yan'uwanka." Ta tamabaye sa cikin tsananin mamaki tana wani yatsina fuska tamkar ta ga kashi.










" 'Yan'uwansa na jini kuwa, domin Yaya Bala shi ne farko sai Ya Mudi ni ce 'yar auta Jummai." Ta faɗi tana washe baki tare da riƙe gefen rigar dad tana yamutsa gugar da tasha.










"Waye kuma Mudi?" Ta ce da sauri tana watsa mata kallon ƙyanƙyani.








"Jannah da gaske 'yan'uwana ne domin babu ƙaryar abin da ta faɗa."










"Laah! Wai kana nufin Murjanatu ne ta girma haka? Ikon Allah girma ba wuya. Ke Murjanatu ta ho 'yata." Ta ƙarashe maganar za ta rungumeta.












"Please don Allah dakata! Dad, na kasa yadda waɗananne 'yan'uwanka? Please do explain, saboda fitowar da na yi akan ka ɗauke ni ka kaini gurinsu." Ta faɗa cikin muryar kuka.










"Hehe, nananye, to ai ko yanzu ba ta ɓace ba, domin za ki iya bin su a koma ƙauye ayi daka da surfe. Kin dai gani ga dangin uban na ki nan da kike ta mana ɗagoshi da su." Cewar Hajiya Baaba tana dariya cikin tsokana.








"Don Allah ka fahimtar da ni domin na kasa yadda waɗannan kucakan sune 'yan'uwanki."






"Tabbas ba ni da waɗanda suka fisu, kamar yadda sune gatanki."






"No dad!" Sai ta sa kuka sosai tana faɗin,"Su ba 'yan'uwana bane I have nothing to do with them."








"To sai kije ki zaɓo waɗanda kike so su zama 'yan'uwanki, domin a lokacin da nake gaya miki uban na ki ba kown kowa bane kasa yadda kika yi, saboda yana cikin arzikin 'yata. Kin ga yanzu dole aure tun da ba ki da dangin zuwa, sai ki gane gata zan yi miki." Ta ƙarashe maganar tare da juyawa za ta bar falon






Mom da jin hayaniya ya sa ta farka daga baccin da take yi ta fito tana zuba hamma.






Turus ta yi ganin waɗanda suke falon tana kallonsu cikin tsananin mamakin yadda kai suka san ta dawo Nigeriya da inda take.










Tsuru-tsuru suka yi domin a tunaninsu za ta yi musu rashin mutunci ko ta kore su, amma sai suka ga akasin hakan duk da abin da suka yi mata ya dawo mata tamkar sabo.








"Barkanku da zuwa, baƙi muka yi?" Ta furta cikin sakin fuska tana ƙarasowa gurinsu.








"Sannu da zuwa Ya Bala, sannu da zuwa Anty Jummai." Ta furta a tare lokacin da ta ƙarasa gurinsu, wanda ganin sakin fuskar da ta yi musu yasa suka rage tsoro suna ƙaƙalo murmushi.






Tsananin mamaki ya kama Jannah matuƙa take ta gasganta maganarsa cewar 'yan'uwansa ne, sai ta rinƙa kallonsu cikin tana yamutsa fuska.








Da sauri ta juya ta shige cikin ɗakinta, daidai lokacin da Hajiya Baaba wanda fitowar mom, ya sa ta tsaya taga wani irin tarba za ta yi musu.










"Ba za ki kawo wa 'yan'uwanki ruwa ba." Ta ce tana dariyar mugunta.








Mom ta ba da umurnin a kawo musu abinci wanda suma ci har da dabbe. Bayan sun gama ta nuna musu ɗaki akan suje su yi wanka.






Falo suka dawo suka haye kujera suna ta kallo da ihu da shewa.






Jannah ta fito daga ɗakinta za ta shiga kicin domin matuƙar yunwa take ji, idanunta ya kumbura ya yi luhu-luhu saboda kukan da ta ji.








Wayarta a hannunta tana ta neman phone ɗin Huzaifah da iyayensa suka karɓe wayarsa.








Tsayawa ta yi cikin tsananin takaici da baƙinciki tana kallon su Bala da Jummai da suke zaune kan kujer suna ihu akan kallon da suke yi.








"Kai ka ga mini shegen mutum da mugunta ya kama mutum da duka ji yadda ya ji masa rauni." Jummai ta furta tare da miƙewa da sauri za ta je gaban tibin.








"Wallahi rama masa na kai, ni kam na tsani mugunta." Ta ƙarashe mganar cikin muryar kuka hawaye shaɓe-shaɓe daidai lokacin da mutum ya coka masa wuƙa a ciki, sai ta fashe da kuka da saka ƙara za ta nufi gaban tibin.








"Wallahi ya sokai, wannan sam ba shi da imani."






"Ke banza, shashasha fim ne fa, ke duk shiri ne bai mutu ba. Da yake ba ki shigowa birni ya sa ba ki sani ba, amma ni nasha kallon irin finafinan nan, duk da ni ma da fari na ɗauka mutuwa zai yi."






"Ai Bala, yanzu kana nufin tashi ya kai?" Ta tambayeshi cikin tsananin mamaki.






"Me zai hana ke jar bula suka shafa masa kamar jini."






"Yau ga lalalattun banza, wanga him ai ba abin kallo na bane, a kahe mana hi."






"A ke, barmu mu kalla ai shine birnancin kuma. Ke dai zauna muga abin mamaki." Suka zauna suka cigaba da kallo ba tare da sun damu da yadda 'yan falon suke kallon su ba.








Wani banzan kallo Hajiya Baaba ta yi mata tana mata dariyar ƙeta da ta ke tsaye tana kallonsu tamkar ta shaƙe su su mutu.








"Kin ga fa danginki na kallo da yake ke ba ɗiyar mutunci bane, kamata ya yi kizo ki taya su."






Wani banzan kallo ta yi mata domin ta san duk takalarta take wanda ta ci alwashin ba za ta ƙara mata magaba ba.








Wucewa kicin ta yi tana harararta da su Bala ba tare da ta ce mata komai ba, wanda Hajiya Baaba ta ci gaba da gyara hularta tana dariya ƙasa-ƙasa.








A ƙofar kicin ɗin suka ci karo da mujee, wanda da gangar ta sanya kafaɗa ta bangajeta har abincin da ta ibo a flate ɗin ya zube.








"Ka ga mini yarinya mara mutunci, wallahi Maijidda ki tsinka mata mari har sai hannunki ya kwanta tun ba ba ta da kunya."






"Ƙyale ta Hajiya Baaba, ƙuruciyace za ta bari." Ta ce tana ƙoƙarin tattara abincin da ta zubar.








"In ba da duke ni ba sai ki zo ki duke ni. Na gaya miki ki fita idanuna domin yanzu mun yi hannun riga dake."








"Au ni ma fitsarar za ki yi mini bari na taso ki gani don ba zan ɗauka ba." Ta ce tare da miƙewa cikin fushi.








Hannu ta ɗaga za ta wanka mata mari amma sai Mujee ta tare ta.








"Don Allah ki yi haƙuri karki biye mata."






"Ki barni da ita ta san halina sarai, domin wallahi sai na sanya kiyi amarci da kubburerren fuska mara mutunci kawai."








"Ki kashe ni shi zai fi mini domin auren nan da kike so ki ƙaƙaba mini is more than beaten Hajiya Baaba, you are killing me!"






"Kin ci albarkacin Maijidda da kin yaba wa aya zaƙinta mara kunya kawai." Ta koma ta zauna taci gaba da gyara hularta ba ta ƙara tanka mata ba.






"Haba Jannah, ki yi shiru mana muje na zuba miki abinci..."






"Dallah! Malama ƙyale ni!" Ta ce cikin tsawa tare da juya ta koma cikin ɗaki ta ci gaba da kuka, abincin da ba ta ci ba ke nan duk da yunwar da take ji.






Bayan dad ya dawo ya yi wanka ya ci abinci. Ɗakinta ya fara shiga amma sai ya ga tana kwance tana baccin da ga gani da tsiya aka yi shi, domin ko kwanciyar daɗi ba ta yi ba.






Gyara mata kanta ya yi yana kallonta cikin tsananin tausayi domin ya san Hajiya Baaba ta shiga rayuwarta na raba ta da masoyinta.








Wayarta da take waƙa ya ɗauka ya kashe tare da jona wayar a caji ganin ba bu caji da yawa. Ƙofar ya ja mata ya rufe sannan ya fita.








Ɗakin su Bala ya shiga suna zaune suna ta aika ma cikinsu abinci.








"Ya Mudi ka dawo?" Jummai ta ce masa tana yagar cinyar kaza.








"Eh, na dawo." Ya ba amsa a gajarce.








"Kai wallahi gidannan akwai daɗin zama ka na cin daɗin ka. Irin waɗannan girki shi ya sa ka yi kyau ka zama tamkar balarabe. Sam yanzu bana ganin laifin ka ba, domin ko ni da zan samu wata Hajiya ta yi wuf da ni, da gudu zan amince aradu."








"Ga gurin cin abinci mai ya sa za ku shigo ɗaki? Yanzu kalli yadda kika ɓata gurin da miya kamar me yoyon baki" Ya ce cikin ɓacin rai.








"Ba zamu iya cin abinci a gurin nan ba, saboda mutanen gidan kallon ƙasƙanci suke mana kuma harda yarka mara mutunci. Duk dai wulaƙancinta babu wanda take da shi da ya wuce mu."








Tsaki ya yi jin me suka ce. "Ita wannan tsohuwar sirikata ce, kuma ba za ta yarda ku zauna a gidanan ba. Jannah kuwa maganar aurenta ake yi."








"Yanzu Mudi, sai ka aurar da 'yarka ba tare da mun sani ba?" Jummai ta tambaye shi cikin mamaki ta riƙe da bakinta, sai kuma ta ɗora da cewa,






"Talauci bai yi ba domin na san saboda bamu da komai ne ya sa ka ɗauke mu wulaƙantantu."








"Na gaya muku tun da Inna da Baba suka mutu babu ruwana da ƙauyen nan, domin ba zan zo ku ƙara sani a keken ɓara ba, ku yi mini sakiyar da babu ruwa."








Tsuka suka yi jin abin da ya ce."Shikenan, tun da kai ba za ka zo ba, muna da ƙafa za mu zo ai. Ko ince mun zo sai dai mu kwaso 'ya'yanmu."










"Ku zauna a ina? Ku san Allah in kun daɗe ku yi sati biyu, amma ba za ku kashe mini aure ba."








"Ai dama mun san an wanke gaba an baka ta ina za ka yarda mu zauna." Cewar Bala cin ɓacin rai tare da ture abincin da yake ci.








"Ko ma me za ku ce sati ɗaya za kuyi zan haɗa muku abin arziki ku koma da jari."






Ɗan sakin ransu suka yi jin zai ba su kuɗi.






"Za a yi auren Lantana 'yata nan da wata uku..."








"Kar ki ji komai zan yi mata kayan ɗaki, amma dole ku bar gidan." Ya ɗan tsaya ya ji me za su ce, ganin sun yi shuru sai cika suke suna ɓatsewa ya sa ya fice tare da ja musu ƙofa, a zuciyarsa yana jin daɗin ganin ba su yi masa gardama sosai ba.










Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093


KURA DA FATAR AKUYA






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(JAMSY)


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation?)









Ban yadda a juya mini labarina ta ko wace siga ko karantashi ba tare da izinina ba. Aikata hakan zai sa mutum ya fuskanci doka.










*PAGE 30-31*






*BOJUWA HERBAL'S*


*KAYAN CHAD ƘARSHE NE WAJEN GYARA MACE DOMIN ASALIN SAIWOWI NE NA ASALI WANDA BABU ALGUS KUMA BABU ILLAH GA LAFIYA*
*KI ZO KI GYARA, KI MAGANCE SANYIN DA YA BUSAR DA KE, KO YAKE SA KI FITAR DA ISKA TA GABA, KO RASHIN SON YIN MU'AMALAR AURE*
*GYARA GASKIYA NE SISTERS*
*KO KUNSAN DUKKAN MAGANIN DA YAKE SAUKAR DA NIIMA YA HADE MACE YAFI TASIRI IDAN AKA DAFA SHI?*
*KI TABBATAR KINA CIN KAZA, TATTABARU, DA AKE DAFAWA DA SAIWOWIN CHAD NA MUSAMMAN*
*A KARAN KANKI ZAKI JI SAUYI BARE KUMA...*😅


*080327733332*
*KU TUNTUBI SURAYYA DEE A WANNAN LAMBAR*.
*DAN SON ANNABI SAI KINSAN KIN SHIRYA ZA KI YI GYARA*.
*NA GODE*






*Contact*
*Bojuwa HERBAL'S*
*For all your kayan mata and maganin sanyi original for women of class*.
*08032773332 Whatsapp only.*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Mom zaune a ɗakinta dad ya shigo ba ta ɗago kanta ba har sai da ya ƙaraso gefenta ta zauna.

"Injiniya, I was about to go to your room and inform you that wannan contracts ɗin sun yi approving so you will go to Paris within this week."


"Really! and when? Kin san Allah na ɗauka ba za su amince a haka ba, more especially da na ga how strict he is."

"Common, is like you don't know how bussiness is? Duk techniques na business ne."

Sai ya yi dariya yana duba takaddun dake gabanta."Haka ne fa, shi ya sa we have to be verry wise in all aspect."

Ɗaga masa kai ta yi tana murmushi tare da ci gaba da aikinta.

"Tafiyar it should be bayan su Ya Mudi sun wuce ko?"

"Eh, dole sai sun wuce. Ni ma ina son na yi magana da kai akan su, domin ya kamata a basu jari da tallafawa rayuwarsu."

Kallonta ya yi cikin mamakin kirkinta." Yanzu Halee, kin manta duk abin da suka yi miki za ki taimake su? I will not have the face to came, if ware them."

Dariya ta yi"Haba komai ya wuce. Na taimaka wa wasu ballantana dangin mijina, kuma tun da suka tako zuwa inda nake ai na san sun yi nadama."

"Haka ne, tun da kika manta da bin da ya faru kika karɓe ni a karo na biyu, tabbas za ki yi fiye da haka. You are so generous." Ya furta cikin muryar dake bayyana rauninsa.

Barin aikin da take yi ta yi tare da kama hannunsa ta riƙe tana kallon ƙwayar idanunsa.

"Ina sonka Injiniya, kai ma sheda ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login