Showing 3001 words to 6000 words out of 137802 words

Chapter 2 - KURA DA FATAR AKUYA Book Complete .txt

hakan cikin ranta dai-dai lokacin da suka karaso gurin ta tare da jefo mata tambayo yi marasa iyaka.
Ba tare da ta furta musu kalami ta ja hannunta suka shiga cikin mota, yayin da direbar ya ja motar da karfi, ya bar su jiki a sanyaye suna kallon hanyar da ta wuce. Jannah ta kwantar da kanta a kan saman kujerar ta ja karamin tsuka tare da faɗin, "Bloody cunts."
Misalin ƙarfe goma na dare suna zaune a falo yayin Jannah take kwance akan akan doguwar kujera, har zuwa lokacin a takure take duk da cewar sanyin ya ragu ba kamar ɗazu ba. Daddy ya rage ƙarar tibin da yake saureren labarai tare da gyaran murya ya ce,
"I was thinking the same as Doctor said Halee. You have to feel sorry for her and go back to Nigeria. It’s time for us to face reality and stop avoiding it. Abin da ya faru ai ya faru. "
Shiru ta yi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, duk cewar ta yi kewar ƙasarta, sai ai tana ganin ba wannan lokacin ya kamata ta koma gida Nigeriya ba, domin a wannan lokacin sam ba zata iya ɗaukar damuwa ba, musamman da take son saka hannun jarinta a kamfanin Badoon.
"I'm thinking she should go alone cus I don't have a plan for going back in ya so she can stay at Ya Muhammad’s house kafin na gama abin da zan yi na koma, ka san har yanzu James ya ƙi yarda na yi investing din share guda biyu a cikin kashi goma na hannun jarin."
Daddy ya ɗan musƙuta tare da ƙara rage sautin tibin. "Har yanzu kin ƙi fahimta ta Halimatu, a ko da yaushe burin ki ki rinƙa yin lamuranki da kanki, duk cewar kin san ni mijinki ne ya kamata ace ni na ɗauki ragamar komai, bawai ina ƙalubantar lamuranki ba ne, sai dai ni ya kamata na jagoranci duk kan lamuranki, domin ita ‘ya mace has limitation. "
Ya ɗan numfasa yana kallonta ganin yadda lokaci guda fuskarta ya canza ta haɗe rai tamkar wacce aka aiko wa da tsaƙon mutuwa. Ta ɗan ja fasali tare da kauda kanta barin kallonsa, bayan wasu ƴan daƙiƙa ta mai da ganinta garesa.
"Ina tunanin mun gama wannan maganar kuma mun yi alƙawarin mantawa da ita a tsakaninmu." Ta ce ba tare da ɗauke kanta daga garesa.
Ya ije remote ɗin hannunsa tare da takowa a hankali ya ƙaraso in da take zaune, daida lokacin da ta juya masa baya.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.






Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).


FOR WHATSAPP: 08144072423
CALL: 07072971093








*KURA DA FATAR AKUYA*






*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*


*SADAUKARWA GA:-*


*BADAMASI (AUTA)*




*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*


*Page 2-3*












BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


Hannunta ya riƙo da sauri. "Ki fahimce ni a ko da yaushe ba kya mini kyakykyawar Fahimta, ya kamata ace tsawon shakarun da muka ɗauka komai ya zama tarihi a tsakaninmu.”
Lokaci guda ta sa kuka. "So, are you saying I should be dummy? Me kake son ka ce injiniya? Mene ne ban fahimta? Ka sani tun kafin na gama sanin wace ce ni na fahimci komai dake tsakaninmu. Don Allah ina son ka manta da wannan maganar, ya wuce komai ya wuce kuma kai ma ka san hakan."
Ta karashe maganar cikin muryar kuka sosai, daidai lokacin Jannah ta miƙe a hankali ba tare da ta kalle su ba zata bar falon kamar yadda ta saba duk lokacin da suke queralling or dispute.
Mom kama hannun ta da sauri ganin za ta fadi, amma sai ta fisge. "Please, mom, I need a break." Ta furta bacin rai tare da barin wurin ba tare da ta ji mai za ta ce ma ta ba.
Tana shiga cikin ɗakinta garƙame ƙofar da makulli ta sharce hawayen da suke gangaro mata ba tare da ta ji saukarsu ba.
Faɗawa kan makeken gadonta da ya kusa cike ɗakin ta yi, ta cire ribon ɗin kanta ta watsa gashinta. Wani irin kuka ya goce mata ba tare da ta yi shiri ba, daidai lokacin da ta ji suna magana da ƙarfi.
"I used to believe that family is a source of happiness, but mine seems different. They’re always in conflict. Could it be personality differences affecting their marriage? Ta tambayi kanta cikin zubar hawaye.
Sai ta mirgina gefen gadon tana jin zuciyarta na mata suya, musamman da ta ji muryarta ya fi na shi. "She’s always like that, thinking she’s super-talented just because she is influential, but it’s not true—she’s only deceiving herself."
Idanunta ta suka kara kawo ruwa daidai lokacin da ta ji yana ba ta hakurin laifin da take ikirarin ya aikata all the time da ta kasa yafe masa. "Me yake tsakanin iyayena wanda suka kasa manta da shi, sannan suka ƙi sanar mini?" Ta tambayi kanta cikin rashin amsa.
Sosai take kuka har da buga kanta a kan gadon."Tabbas lamarin iyayena akwai ruɗu a ciki, na rasa yadda zan fahimci lamarin da ke faruwa. Wataƙila hankalina ba kai mizanin da zan fahimci haƙiƙanin abin da ke faruwa ba." Ajiyan zuciya ta saki mai ƙarfi lokaci guda kanta ya kulle.
"I’m feeling lonely. The loneliness is too much to explain, and no one seems to be there for me, even though dad tries his best." Ta karashe maganar tana cizon lebenta, sai kuma ta saki murmushi mai kama da kuka.
"I wanna go back to Nigeria." Direction na kwanciyarta ta canza tana kallon hoton 'yar tsohuwar dake manne a bangon daki da suka ɗauka ranar da tazo London lokacin da za'ayi mata aikin ido, wanda ta ci kwalliya ta kafe wai a dole sai ta kama kyanta. Dariya ta kwance mata babu shiri

Takowa ta yi a hankali ta ɗauke hoton tana kare masa kallo."Hajiya Baaba kenan! Yar tsohuwa mai ran ƙarfe. Ko yanzu ya kike? Na san wannan rigimar na nan."
Ta jima tana kallon hoton daga karshe ta mayar inda yake. A ranta tana jimamin halin mom, a kan na ci don har yanzu maganar take murya a ɗage. Sai ta kwana a kan sofa tare da ɗaukar wayarta, ta kunna waƙa ta saka earpiece tana sauraren waƙar har bacci ya kwashe ta.
Da daddare misalin sha ɗaya na dare, mom tana sanye da ash din duguwar rigar bacci. Zaune a gefen gado, da laptop dinta a saman cinyarta, ya yin da kuma wayarta ce saƙale a kunnenta tana amsa calls.
Dad da ke juye-juye a gado bacci, ya ƙi zuwa masa ya juya kwanciyarsa, tare da kallon ta da take waya tamkar babu abin da ya dameta. Kimanin mintina talatin ta kammala wayar, ta ije a kan stool ta ɗauki tea ɗin ta da ya fara sanyi tana kurɓa a hankali.
"See Halee, I’ve had enough of your negative attitude, especially the way you treat me like your son."
Ta kalle shi kamar ba za ta ba shi amsa ba sai kuma jikin ta ya yi sanyi, domin ita kanta ta san abin da take yi, was beyond limitation, amma kuma da ta tuna all the things that she went through, all the agony sai ta ga ai he deserved it, in fact, even more than that.
Ta bude Baki za ta yi magana sai ya riga ta ganin babu nadama ko kaɗan a fuskarta.
"Forget the fact that you’re more influential than I am—I can't tolerate this nonsense. You need to treat me the way a Hausa wife treats her husband, not like those fake people that surround you. Remember your culture."
"You’re a cheater, engineer! You know that, right? You make me look like a fool, acting all innocent and calm, but that ain’t you. You’re just like a chameleon!" Ta karashe maganar cikin zubar hawaye.
Ya yi shiru yana kallon ta aransa yana mamakin taurin kanta that she couldn't forgive. Sai ya mike zai fita komai ya tuna ya dawo tare da kamata yana ganin he deserved even more than that, tun da halinta ne, he has to take it.
"Fuck off, Engineer! You are a cheater, you cheated on me."
Ya hada ta da jikinsa. "It’s okay. Let’s focus on Jannah’s illness; she needs your help. We need to talk discuss her future." Ya karashe maganar cikin tsigar rarrashi.
"I’m sorry." Ya ji ta furta wanda ya sa ya kalle ta da sauri duk da cewar ba sabon wani abu bane, domin tana fada mishi fiye da hakan shi ne ya bata rawar shi da tsalle ya kuma yi nadama alokacin da ruwa ya karewa dankaɗa, don haka ya kyale ta akan maganar Jannah, considering that she didn't want to talk about it.
Washegari da misalin sha ɗaya saura kwata Jannah ta farka. Miƙa ta yi tare da salati ta ya ye bargon da take luluɓe shi ta zuro ƙafafun ta ƙasa.


Figigiyar rigar baccin dake jikin ta, ta cire sannan ta faɗa toilet ta ɓata lokaci tana wanka kafin ta fito ɗaure da sky blue tawu, kanta a jiƙe ya yin da ta ɗora ɗan ƙaramin towel tana tsane kanta.
Hand dryer ta ɗauka sannan ta kunna socket ta kunna tana busar da kanta, zuciyar ta ke ɗauke da tsananin damuwa wanda kana kallon face ɗin ta you can tell she’s moody.
Bayan ta kammala shiryawa cikin wata rigar pink mai kyau, ta ɗauki ribon tare da ɗaure kanta. Wayarta ta ɗauka tare da janyo ƙofar ta ta rufe.
A falo ta zauna kan doguwar kujera tare ta kunna kallo ta ɗauki remote ta koma ta zauna. Ganin labaren ake yi sai ba ta canza tasha ba ta ije remote ɗin a kan stool ta fara danna wayarta.
Mom ce ta fito sanye da wata fitinannniyar doguwar riga wace tasha ado sai. Siririn ɗankwalin rigar ta yi rolling ɗin sa a kanta, sannan ga jakarta da takalmin ta mai azababben kyau.
Jannah ta yi mata kallon uku tara duk da ta yi mata kyau sosa, domin ita kanta ta san she’s so beautiful and dashing. She looked elegant and so charming. Ga shi tana sa masifar tsafta sam ta tsani ƙazanta.
Mace ce da ba ta kula da shekarunta ko ta haifi Jannah in tana abu sai ta ba ka mamaki don jin ta take tamkar 'yar shekaru sha takwas. So, she could categorize herself as mace classical wanda a dalilin hakan ta ɗauka take gara mahaifinta kamar ƙwallo duk da cewar shi ma ba baya ba.
Ƙarasowa ta yi cikin tafiyar taƙama tana waya, ta zauna a gefenta tare da ci gaba da wayar, wanda hakan, ta yi matuƙar tsana domin sai ta ɗauki kusan awaya tana yi.
Hakan ta faru, don ta ɗauki tsawon lokaci har ta gaji ta ɗan saki siririn tsaki, tare da janye hannun ta da ta rike za ta bar gurin, ganin hakan ya sa ta sallami mutum ba don ta gama ba bayan ta riƙe hannunta, yarda ba zata iya fisgewa ba.
"Morning, sweetheart. You look pretty." Ta ce tare da ware hannunta da nufin ta rungume ta, amma sai ta matsa gefe ta ƙi amsa gaisuwar. "Jannah na gaya miki."
"Mom you constantly nagging, no matter what you do. Please bana so, you are provoking me."
Ta ɗan murmusa jin abin da ta ce sai ta ƙara rungume ta duk da ba ta dake zuɓɓurawa ta ja leɓenta tare da kama hancin. "Shiryaya kawai! kina ba ni mamaki, ban taɓa ganin 'yar da take against ɗin mahaifiyarta ba, but you do..."
"You caused it. Kece kika sa nake miki hakan, amma kin san babu wacce na ke ƙauna da so kamar ke, but I don't know why you do that to me and me father."
Ta katse ta tana fadin haka. "See, your dad deserves it, and I'm tired of this whimsical attitude of yours sai na dawo. Watch your mouth."
Sai ta fusata ganin ba ta da ninyar canzawa daga munanan ɗabi'un da take yi cikin muryar kuka ta furta bayan ta sha gabanta.
"I think you should go for a relationship therapy, you need that cos you have no idea ho…"
Wasu kyayawan mari ta sauke mata a fuskarta cikin ƙunar rai. "Ki san kalaman da za ki rinƙa gaya mini a matsayina ma mahaifiyarki, from now on I won't take your shit anymore."
Jannah ta fusata idanunta suka kawo ruwa sai ta sanya ƙara mai razanar ta tokare ƙofar da za ta wuce.
"Ba zan ƙara zama dake ba, ki mai da ni gurin Hajiya Baaba, na san za ta ba ni kulawa fiye dake. Mom, I can't stand your attitude much longer." Sai kuma ta yi shiru tare da jan majina tana ƙara sakin wan kukan ta ɗorawa da ce wa, "Idan kuma ki ka ƙi, kin ji na rantse miki, I will kill meself! I think suicide would be better for me than living in this hell you call a family."
Lamarin sai bata matuƙar mamaki, ta yi zuru tana kallon ta yadda take faɗin kalamai mara sa daɗin ji. Idanunta suka kawo ruwa, sai ta fara tunanin tarbiya ce ba ta iya ba, ko injiniya ya yi nasarar raba ta da 'yarta?
Ba tare da ta furta mata kalami ta ɗauki jakarta ta ture ta tare da fita daga falon idanunta na zubar hawaye daidai lokacin da take cewa, "I will get a visa, I have money on me."
Da sauri Rose da take kicin tana sauraron hayaniyar da suke yi ta fito tare da rungume ta "Please, Jannah, take easy; it’s okay." Sai ta kara sakin kuka tare da ƙara rungume ta.
"Ba ta sona! Mace ce mai son dukiya da duniya. Shi ya sa ba ta barina na huta kullum cikin karatu, saboda na yi ilmi na tara dukiya. Tir da dukiya irin na ta, wacce ta sa muka kasa samun kulawarta sai da ta ba wa duniya."
"Sorry." Ta kara ce mata duk da ba fahimci mai ta faɗi ba tare da kamata suka shiga ɗaki.
Da sauri Rose ta buɗe wardrobe nata ta ɗauko mata pills ta ɓalle tare da mika mata, amma sai ta karɓi na hannunta ta ƙara da guda uku ta watsa a bakinta.
Zare idanunta ta yi, sai juma ta kasa cewa komai, tana girgiza kanta kamar ƙadangaren kutu. Sosai take ganin sakarcin mom da ta kasa gane 'yarta tana shan maganin depression and anxiety. Koda yake she would not be surprised domin ba ta ba ta lokacinta ba balantana ta fahimci haka.
Ko da mom ta shiga mota kusan minti goma ta kifa kanta a sitiyarin motar hawaye ke zuba a fuskarta, bayan ta ba da umurnin kar a bar ta ta fita ko ƙofar gida.
"You are so insolent to me. Why?" Ta furta cikin tsananin ɓacin rai.
Da ta dawo aiki ko kofarta ba ta kalla ba, saboda haushin ta da take ji, amma tunaninta yana kanta, musamman da Rose ta gaya mata ta ƙi cin abinci.
Dad ne kawai zai iya shawo kanta, don haka ba ta damu kanta da ta je gurin ta ba ta yi kwanciyarta. Haka kuwa aka yi don sai da ya shafe kwana biyu yana rarrashi sannan ta haƙura ta saki kamar babu abin da ya faru, sai zaman na su ya dan yi daɗi babu laifi, duk da damar kowa harkar gaban shi ya ke yi.
Kasancewar Jannah suna lokacin hutu na first term inda za ta shiga e.s.s 3. Sai ya kasance gidan da ga ita sai Rose. Kullum tana cikin ɗaki, daga kallo sai bacci da chatting, sai in ta gaji ta fito falo ko ta je gurin Rose, don ko mom ta dawo ba ta kanta take bi ba, dad ne wani lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login